ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Rigar yasaka mata yana cewa”dont worry insha Allah keda ita ever and ever.” Maganarsa tamun dadi rirrigata yake yana kallon fuskarta yacigaba da cewa.
“Inama zaki ban ita idan anyi bikina ta zauna wajena,zulfa,a zata kula da ita fiyeda tunaninki because she love her so much,kamar yadda nakeson Airah itama tana sonta,pls inason Airah inaji kamar cikin jinina take,zaki ban ita oum Airah.?

Tunda yafara maganar naji zuciyata tana amsawa saboda dukan da take,kalamansa jinake kamar ni yake fad’a masu,saidai jin cewar inbashi ita zulfa,a zata kula da ita duk ya wargaza man mood dina……..bansani ba bansan yadda zan fasalta yadda nakejin kishin wannan matar ba,banson ko sunanta ana kira man.taya ma yake tunanin zan iya bashi y’ata ta zauna karkashin ikon wata,watarma wadda nakejinta tafita daban daga cikin mutanen da suke haska farincikina…….jinaima kwallah tacika idona,ban bari tafitoba tunda daman kaina k’asa yake……jinai ya sunbaci kuncinta yace”kinji inason Airah zakiban ita.”
Still kaina kasa nace cikin sanyin murya ina control din mood dina “kayi hkr bazan iya mallakawa kowa sweetie ba saboda nafi kowa bukatarta,kayi hkr sadda akai auren naku Allah zai baku taku kuma.”

Shiru yayi yana rik’e da ita har tayi bacci kafin ya mik’e ya isa ga gadonmu ya sakata cikin net dinta,bayan yasake sunbatar ta yace”sleep tight my angel.”
K’ofa ya nufa baice komi ba har ya b’ude kofar nace batare dana daagoba”tnx for helping me during labour.”
Idasa ficewa yayi bayan yagama jin abunda zance.

Kwata kwata ranar ban iya samun bacci mai dadiba,kawai ina imagining ne yadda yakeji lokacin dazanyi aure,daman haka yakeji haka kishin yake wannan zafin duk na kishinne,da ker da taimakon kaina nayi bacci.

Areef wannan daren yasha kuka,don duk sadda ya kusanci inda take kamar karamai wutar sonta ake,shiyazayyi da wannan auren bazai iya yin rayuwar aure mai dadi ba alhalin zuciyarsa daruhinsa gabaki daya suna gawata,bazai iyayimata adalciba zai tauyeta zai cutar da ita,taya zai ganar da ummi cewa bason zulfa,a khairat yakeso.
Taya zai fahimtar dasu cewar itace farincikinsa,itace burinsa tsawon shekara aru aru.ina zai saka ransa soyayyar da yake mata shikanshi tana bashi tsoro,Amman sanin halin ummi shike tada mashi hankali,don ko duniyar zata tsaya bayanshi akan bazai auren nan ba babu wanda ya isa ya canza mata ra,ayi saidai idan itace taga dama.
Jahid najinsa yana sabbatu yayi kamar baijiba,don yayi alkawarin bazai ce mashi uffan ba,ai kukama yanzu kafara Areef indai akan khairat ne badai ka wulakanta ta ba abaya tukunna ma dai.

        *********

Anyi sunan baby Airah taro yayi kyau,maijego da yarta sunsha kyaututtuka kamar hauka,don kudi masu sunan kudi khairat bazata iya lissafa yawansu ba,daga mai dubu biyar sai abunda yakai sama.
Sunsha kyau kamar kasace su karuga,masha Allah Airah tasha gayu kowa sai saka Albarka yake,gidan yacika sosai yan uwa nanesa dana kisa kowanyazo sai daidaiku da basu samu zuwa ba.
Haka dangin dr sun zo kuma sunyi bajinta sosai,ranar ma nasha kukan rashin dr don yadda yaci burin sunan lokacinan komi yace ai za,ai sunan da babu irinsa duk abuja.Ashe baida rabon gani Allah kakai rahma kabarinsa,itace adduata akodayaushe.

Taro ya watse saidai muce Allah ya raya maryam (Airah).

Bayan suna da sati biyu Areef ya shirya zai koma spain,saboda bai idasa aikin sa ba zaiyo wata guda,ga biki nata gaba towa baifi wata biyu ba,Abbu yaita fad’a cewar ba zaije ba ya tura yaronsa na office yatattaro mashi duk wasu ayyukan,amman taya zai tafi ga hidima anayi.

Haka dadynsa ma yace dadynsu yah meenah kurun yabashi goyon baya,yace ayi hkr yaje har yadawo abunda duk ya kamata ayi za,ai mashi sadda ya dawo saiyaji da sauran.
Kana dole suka hkr suka barshi ummi kiwa sai fada take,

“To wlh bazaka tai ba saika bada kudin da za,a idasa hada lefe,aibani zan maka lefenba.”

Muna falo take fadarhaka nidai ina gefe inashayar da Airah,maah tace”haba yaya,don Allah kibarshi haka mana tun safe kike mashi fad’a ko abincin kirki baici gidan nan ba,kin tasoshi gaba sai bambami kike,kwana nawane idan Allah yakaimu,indai donta lefe ki kwantar da hankalinki wlh ni nagama hada komi.”

Duk kallon mamaki sukwa maah,Annie xtace yaushe duk kikai bau sani ba,Amma gaskiya kin shaacemu.”
Dariya tayi tace”kallonku kurin nake nariga nagama da wannan babin wlh,nabar maku nasu mujahid da Shahid.”
Ummi tace”ai haka abun yake kinso danki ko zamugani dana shin danasu nawa zaifi kyau.”
Nan sukabhau hirar kayan,already ni nagansu nasan kuma daman nashine.

Kallona yayi nai saurin kauda kai,don tun wannan maganar bamu sake maganaba illa gaisuwa,
Miko hannu yayi yadauki baby Airah data gama shan nono,bance komi ba ya shige ciki da ita.
Nasan meyake nufi idan na matsu inbishi in ansota, ya samu damar yimun magana,buris nai dashi banma motsaba nake ma Su maa maganar makaranta tata,don su yah meena final exams suke yanzu.
Tace na bari Abbu ya dawo inmai magana tasan shima cewai zai inbari Airah tayi kwari.

Tashi nai nazuba abinci naci har karfe goma bai dawo da itaba,babu kuma wanda ya lura balle yace ina take.gajiya nai nanufi daki nayi shirin kwanciya wauata dake gefena naji tayi kara alamar tex massege,dubawa nai naga yace Come and take Angel tsaki naja najefawayar can gefe inacewa”wlh banzuwa inka gaji kakawota d’an rainin wayau,baka ga komi ba wlh saika gane baka da wayau.”

Mimi ta shigo ta zauna gefena tace”oum Airah shawara nazo muyi.”
Tashi nai ina kallonta nace”inajinki mekefaruwa.”

Murmushi tayi tace”babu batun b’oye b’oye,kinason yah hargobe,shima kuma bama sainace maki yana sonki ba,kinsani………enough mimi bansani ba,bansan komi yake ciki ba.”……..Aa oum Airah karkiyo saurin katseni,wlh duk wanda ke gidannan yasan halin dakuke ciki,kuma nayi imanin anyi shiru ne don aga iyakar gudun ruwanku,bawai ba asan halin da kuke cikiba.”
Cikin fushi nace”mimi pls kibari banson in nuna maki fushina shin waima meye naki ciki nacemaki ni zan sake aurene,nida aure saina gidan aljannah insha Allah.,and pls idan wannan maganar ta kawoki workout.”
Babu alamar fushi ko jin haushi kan fuskatar ta tace”shikenan,zaki gane menake nufi ni mai son farincikin kuce wlh i wish inganku kun mallaki juna……….oh may God,wai mimi nace maki knason mallakarsa ne……….kofar da aka bude yasa nai shiru,amman naso injuye haushina tsaye yake sab’e da Airah da alamar tayi bacci.
Mikewa tayi tace”saida safe”banza nai na kyaleta tazo zata wuce yawurga mata wani kallo,tab’e fuska tayi tace”wlh nifa banyi komiba……..common get out yaceda ita.”

Fita tayi sanna ya tura k’ofar da kafarsa,jallabiyace maroom da wani zanen kwalliya gaban ta,tayi masifar fiddo kyansa,haskensa ya sake bayhan cikin rigar,kauna kai nayi ina zaune fefn gadon ya k’araso yasaka Airah cikin net ya rufe sannan ya tsaya gabana idonsa akaina,aijinai kamar na kurma ihu azo afita dashi.
Tsaye yai rungume da hannunsa perfume dinsa sai bugarmun hanci yake,duk yayiman gigirin bisa kai.

“Nakiraki kin nunaman ban isa ba ko.”

Sai lokacin nad’ago kaina na kallai,saidai nai nadamar kallon don jinai zuciyata tana man wata irin rawa,sadda kai nayi nace.

“I’m sorry banji kiranba shiyasa.”
Stool yajawo ya zauna gabana sosai kamar zai shige cikina,yace”ban kirakiba text nai maki.”
Banyarda nasake kallon saba nace”Ayya ban ma san inda wayar take ba banganiba,sorry again.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button