ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Numfashi yafesar har kan fuskata runtse ido nai na wani lokaci na bude yace,
“What mimi said.”
Jinaigabana ya tsinke yafad’i,nashiga uku mezance mashi.

“She telling about me and u.”
Nabani karfa ace yaji.

“What she tell.”
“Nifa babu komi kawai tana maganar………karkiyi karya naji komi,don haka kikwantar da hankalinki indai nine kinsamu,inhar dai zaki iya zama da kishiya ba damuwa zan hada dake.”
Wani irin haushi da bakinciki suka cikaman zuciya cikin fushi da masifa nace,
“Ni bance komi akanka ba,hasalima ni babu wanda ke gabana inbanda Airah,bazan sake aure ba balle nayi ma mijina butulci,ni bazan iya mashi reable ba,don allah karka bata man mood dina nimezan dakai plstkatai dakinka kwanciya zan………….fizgo hannuna yayi idonsa cikin nau dasuka cika da kwallah yace,
“karya kike,u are lie kina sona kifito fili kifurta man tunkan lokaci yankure maki,karki damu zan soki ayadda kike i will manage u…………..wata irin fizga naima hannuna na kwce n tureshi daga gabana,hawaye tuni sun wanke fuskata cikin fushi da kuka nace.

“bansonka! I hate u too.”

“Ko maza sun kare bazan aure kaba,duk wanda yace maka ina sonka ya yaudareka,yes before bikina am sure Ilove u love u too,amman after and now Am sure 100% sure I HATE U I HATE U YAH AREEF,NA TSANEKA BANSONKA kadaina tunanin akwai tsarin sake yin aure cikin rayuwata,zaka yaudari makaryaciyar zucoyarka ne abanza don wlh bazan aurekaba ko duniya zata tashi ahalin yanzu …………….idonsa kamar anzuba garwashi fuskarsa tayi jajawur,ya fizgoni ya rike kafaduna yana girgizani,cikin daga murya yace,

“Karya kike khairat,u still love me ever and ever,kuma sai in aureni nine nan mijinki babu wani duk fadin duniyar nan saini………kofar dakin aka turo nafizge daga gareshi ina koma wa gefe ina cigaba da kukana.
Ummi ce da Annie sai su yah jahid da anty shida sai salma da yah meenah,shigowa sukai annie ketambayar lafiya.
Dagani harshi babu mai iya bada ansa,kukan danake yasa ummi ta sake tunzura ta daka mashi tsawa tace,
“Karkasake in sake tambayarka ,mekayiwa khairat kukan me take hayaniyar mekuke,dakai nake don ubanka………….mahana zaiyi ta daga hannu cicin karfinta ta kwasa mashi zazzafan mari……har cikin kokon raina naji marin,har saida na dago ina kallonta.
Kaina tayo tana masifa,
“daki ka dago rama mashi zakiyi don ubaki,nace rama mashi zakiyi ana tambayarku kin maida mu shashashu,………”
Kukana naciga dayi Annie tace”kiyi hkr inajin can tsakaninsu ne,ki kyalesu.”

Ummi tankamana harara sannan tafita kowa yafita,Annie ce kirin bata fitaba tura kofar tayi taiso inda nake tana bubbuga bayana.
Tsawkn lokaci tana lallashina har nayi shiru.

“Wannan kad’ai ya isa ya nuna mana cewar abunda muke tunani haka yake,kowanenku yana son d’an uwansa………saurin katseta nai nace”Aa Annie banson sa,ban kaunarsa pls kice yafita rayuwata,bazan iya wa dr kishiyaba……”shima cikin fushin yace”kinjiko Annie abunda take cewa,taya kunnena zai juri sauraren wadannan kalaman nata masu d’aci.”

Annie tace”ya isa haka ban son sakejin maganar kowa,yarage naku ku sasanta kanku,yarage naku karku sasanta kunaji kuna gani zaku sake rasa junama wannan karon,don haka bawanda zan hana duk abunda yaga dama,don haka shawara tarage gamai shiga rijiya,don ingaya maku iyayaenku maza babu wnda baisan wainar dakuke toyawa ba,hakan kuma bai hana aurenka kai Areef,don haka kunga tafiyata.”

Tafita tabarsu nan shima daga baya yajuya yafita cikin tsananin fushi………zan iya cewa wannan darw babu wanda ya rintsa cikinsu,gashi gobe zai wuce spain early morning.

Share it pls.

Mrs bb ce
Mom muhseen.
[7/6, 7:25 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

           47.

Washe gari tun asuba da mukai wanka nida Airah bamu tashiba sai eleven,sadda na fito ina sab’e da ita zanyi break naji gidan ya rage hayaniya.
Lami mai aiki na tambaya ina mutan gidan tace”maah dai tana ciki itada su shahida,salma da mimi sunje rakiyar Areef,………tundaga sannan naji jina gaba daya ya dauke bansan me take sake cewa ba.
Zamanai da Airah ga hannu kamar kwai ya fashe man ga ciki.

Kamar marar lafiya haka na koma,kukan airah ya dawo dani daga duniyar tunanina.har cikin raina banso tafiyar ba,duk da haushinsa dana kwana dashi,hakan bai hana ni jin kewarsa ba.
Dayanzu ya dauki baby bai maido man ita sai tafara kuka kokuma tayi bacci,hawaye naji sun cika idona nai saurin sharewa saboda mutsin danaji bayana.
Maah ce da anty shida suka shigo falo,ina kan dining nayi tagumi ga Airah sai kuka take bam jin kukan,saboda halin da zuciyata take ciki.

Jinai kurun Anty ta dauketa tana rirrigata,maah ta banka man harara.
“Wahalalla,kicigaba da yi kar Allah yasa kidaina,.”
Idona cike da kwallah nace”maah menayi menamaki kuma.”
Tsaki taja ba wuce warta ta cigaba da huddodinta,kuka na rushe dashi saboda banson abunda kuma nayi ba,meyasa maah keyin haka duk dan sabida ita nake treating yah Areef haka,Amma Ku ma still ban yi daidaiba…………Anty shida tace”ansheta kibata tasha sai kicigaba.”
Ansarta nai natashi na koma dakina abincin da banci ba kenan,yini nai daki duk mai son ganina can yake samuna.
Babu wanda yadamu da damuwata,abun ya hademan biyu koma ince uku.
Ga soyayyar wanda nasan har abadan bazan samesa ba,ga canjin hali daga maah sai hantara ta take,………ga kewa da tsananin begen Dr sai tunaninsa ya dawo man sabo.
Ganin abun ya isan naje na samu Abbu da safe kafin yafita.
Duk nayi zuru zuru cikin kwana biyu ita kanta airah,don Annie na shigowa tana ansarta da wuyar da xata sha tana da yawa,don ma tafara wayau yanxu.
Break yakeyi keyi na samu Maah tana saving dinsa,harara ta watsa man naji kwallah sun cika idona.
“Ta alkairin abbu iso mana.”
Shiga nai ina rakub’ewa jikin kunera nesa dashi,ina goge kwallata,
“Zomu Karya nasan baki kaiga yin nakiba,”
Girgiza kai nai cikin sanyin murya nace”Aa kaci naka Abbu idan nafita zanyi nawa,dama nazo ne kan batun makaranta anshiga sabon session.”

Kunun gyadarsa ya kurb’a ya saka tsokar nama baki sannan yace”nasan da haka,zan tura jahid sai yayi maki duk abunda yadace.,sai mekuma.”

Sadda kai nayi nace “bakomi”

Na zo tashi yace “zauna ban sallameki ba.”
Zama nai ina wasa da yatsuna……..duk gudan yafita kaina ummi kanta duk ta canza to wai menayi masu haka.

“Meke damunki kwana biyu,bakida walwala kina yini dki bki shiga cikin y’an uwanki………..meke damunta daya wuce wahala,yarinya tana son kunyatani tadauki son duniya ta dorawa mashi,kamar shikadaine autan maza……..”duk maah ke wannan maganar.

Tuni hawaye sun wanke fuskata shashshekar kuka nake kasa kasa,saboda jin abunda maah tace,ni yaushe nayi wani abu har da zai nuna masu cewar har yanzu inason sa,to banyi karya ba inasonsa har gobe amman me wlh yadda ta nuna bata sona dashi nima shiyasa nake mashi duk abunda nai,shine zata ce haka.

“Badake nake maganaba saudah karna sake jin bakinki.”
Ta banko man harara nasadda kai ina cigaba da kukana.
“Bakiban ansa ba ta Alkairi.”

Ina sharben majina nafara magana cikin rawar murya.
“Abbu maah ce……….sai kuka ya kubceman na tayin sa ina jan numfashi bai hananiba don daman kukan shine nakeyi nasamu sauki,
Saida nagaji nayi shiru nacigaba da cewa,
“Abbu bansan menayi mata ba,tun ranar da yah yatafi take daureman abu kadan taita hanta rata,kuma taki fitowa fili ta gaya man laifin danayi mata,inma don yah Areef ne wlh tallahi Abbu bana kulashi,ban shiga sabgarsa,shine yake damuna saboda ita ko maganar arziki bamuyi dashi.inbanda gaisuwa amman shine tace haka,wlh niban karya dokarkiba……..na karashe ina kukana.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button