ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Shiru falon yayi sai shashshekar kukana dake tashi cikin falon, duk na jike hijabita da majina da hawaye.

Cigaba yayi da cewa,

“Sanda kuka dawo nayi farinciki saboda ganin kamar abunda nake tunani zai tabbata,saidai kuma naga kamar ba haka ba, saboda kulawarka kaf akan salma kake yinta, sai kwatsa da kyara da kakewa khairat, har dalilin haka yaja zuciyarta hau hauwa, Wanda likita ya tabbatar mun da cewar wanan matakin shine na karshe data sake ta wuce shi babu makawa zata kamu da ciwon zuciya, shiyasa hankalina ya tashi na kasa natsuwa, gani nake duk sakacina ne, Amman sai naga wannan damar ce kawai zata warware komi.”

“Na samu saudah da maganar hadaku aure Amman Kalmar farko data furta mun itace cewa ta haramta maku juna kaida ita,saboda alkawarin da tayiwa ummin Dubai cewa cikin yaranta babu mai auren wani, ma,ana khairat ko shahida bazasu aureka ba, kai matsayin wansu kake uwa daya uba daya, alakar aure bazata tab’a shiga tsakanin kuba, don haka khairat saidai tayi hakuri Allah ya bata wani Amman ba kaiba.”

“Nikuma nace muddin ka amunce da tayin da nayi maka akan khairat, to kuwa wanan auren babu fashi saidai idan mahaifiyarka ta Dubai ce tace aa ko mahaifinka, kokuma kai da bakinka kace bazaka aureta bah.”

Shiru ya k’ara yawaita cikin falon zuwa yanzu kukana ya karu, don sonjin ansar da zai bayar, har ga Allah duk irin abunda yah Areef yake mun banji zan iya hakura dashi ba ina jinsa shine ABIN CIKIN RUHINA Amman ya na iya da hukuncin ubangiji, muddin yace zai auran, inkuma har naji sab’anin haka nayi alkawarin yafeshi har iyakar karshen rayuwata, haka zalika bazan sake tada hankalina akanshi ba zan d’auke shi matsayin yayana uwa d’aya uba d’aya.

Tsawon lokaci baice komi ba Wanda kowa sonjin ta bakinsa yake, har saida dady yace masa.
“Areef dakai ake kayi shiru.”

Ajiyar xuciya yayi yace,
“Abbu meye dalilin da yasa maah ta furta hakan.”

Baidamu da tambayar da yayi ba yashiga bashi ansa.

“Watau Areef bari nayi maku dalla dallah.”

Shekarun baya tun da mukai aure da sauda saida muka shekara goma ko b’ari bayi ba, nan yashiga sanar dasu halin da suka shiga, da irin takurawar da dangin Abbun suka mata, har sadda suka bar kasar……….

“Ranar da muka sauka kasar gidan ummin Dubai muka sauka, Wanda aranar aka haifeka Areef, tun da aka sallamoku asibiti nida saudah muka nuna sha,awar abamu kai, to sanin cewar suma kaikad’ai garesu yasa bamu rok’aba, to Ashe da saudah suka kebe da hafsat, ta sanar da ita halin da take ciki na rashin haihuwa, har gashi ance na k’ara aure saboda bata haihuwa.
Saboda son juna da tausayin halin da saudah keciki yasa umminku ta nemi iznin mahaifinka, akan zata barma saudah kai, koda yaji halin da muke ciki baiyyi jaa ba, yace har duniya tatashi Arref na mune halak makal, wannan yasa bamu dawo ba saida aka gama shayar dakai, ta dalilinka komi ya canza
Duk da saida kaddarar haihuwar salma tasa na sake wani auren, da marigayiya lantana uwa gareki salma, ranar da aka haifeki ranar mahaifiyarki ta koma ga Allah, saudah ta had’aki da khairat ta shayar daku batare da banbanci ba, kaji tushe mafari komi yanzu INA son ji daga gareka, shin zaka auri kanwar ka khairat kokuwa.”

Idona akansa hawaye kawai kefita, yayinda kirjina yake wata irin duka, gyara zamanshi yayi yace.

“Abbu kamar yadda maah tace nima ina ganin hakan din ne, kayi hakuri ni nadauki khairat kanwata ta jini ban tab’a jin sonta ba, koda na minty gudane idan nace zan amunce da auren zan iya kwararta, saboda bana son ta, gaskiyar magana ma SALMA NAKE SO BA KHAIRAT BA.”

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU, UN HAZBUNALLAHU WANI IMAL WAKIL………….kala man da nake ta nanata wa kenan cikin zuciya da kan bakina, duk iyayen AC din dake cikin d’akin sunkai shidda Amman zuface nakeyi ta fitar sharia, jikina har karkarwa yake gaba d’ayan falon yayi tsit bakajin motsin komi.

Abbu ne yayi karfin hali yace,
“Salma kina son yayanku.”

Kallonta nayi naga ta sadda kai tana wasa da yatsun hannunta, kafin Anni tace,
“Ansarta kenan Abbun khairat alamun ta amunce kenan.”

Jinjina kai yayi duk yana yinsa ya canza sosai, daka kalli fuskarshi zaka gane ranshi ab’ace yake.

“Kowa na iya tashi zan nemeku idan bukatar hakan tatashi.”

Daya bayan daya haka kowa kefita jiki babu kwari, maah duk jikinta yayi mugun sanyi, ta kasa yiwa Abbun magana.

Tashi nayi zan fita don har wata juwa ke kwasata, jinai Abbun yace,

“Yaki nan ta alkairi, kisameni da safe kafin nafita aiki, kinjiko.”

Ban iya bashi ansa ba kawai jinjina kai nayi nafita…………….

Mom muhsen ce
Mrs bb
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition isV to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

14&15

Basai na kwatan ta muku yadda daren ya kasancewa khairat ba,domin kuwa bacci duk yadda ya kware wajen sata to fah wannan ranar ya gagara satar khairat,yadda taga rana haka taga dare,don kasa kwana tayi dakin su itada salmar,kuka tun tanayi da hawaye har ya dawo idon ya bushe,wani irin zafi takejin kirjinta nayi kanta kamar zai rabe gida biyu,haka meenah tayi lallashin tagaji tayi bacci ta barta.

Duk wani tashin hankali da na kejin zuciyata aciki, nayi iyakar yina nayi control din kaina kafin gari ya waye,don nayi wa kaina rantsuwa da alkawarin idaniyata ta gama kukan SO kuma insha Allah zanba marad’a kunya.

Shirin bacci jahid keyi yana yi yana kallon Areef da ya kwanta kasa saman kafet din dake malale tsakiyar dakinsu,ko combus din dake kafarsa bai cireba balle ya samu damar fara canza kaya,girgiza kai kawai Jahid keyi don lamarin Areef abun yana kaishi Bango,tsaki yaja wanda Areef baisan ma yana yi bah……….

“Dallah malam tashi anan,kawani sheme kasa kamar Wanda aka aikowa sakon mutuwa.”

Kallon jahid din yayi yana sauke ajiyar zuciya,lumshe kyawawan idanunsa yayi yana sake yin filo da hannayenshi,baice ma jahid komi ba.

Haushi ne ya sake turnik’e jahid,don ganin yaki kulashi wani tsakin ya sake ja yana hayewa gadonsu wayarsa yafiddo yana danne danne……..tsayin mitina babu wanda ya sake kula kowa har jahid ya gama abunda yake yayi addua ya kwanta.
Sai lokacin yyi magana.

“Jahid baka ga kamar Abbu ransa ya baci sosai ba.”

Cikin kuluwa yajuyo yana cemashi,
“Au sai yanzu kagane haka ashe,ai babu anfanin hakan wallahi kabani mamaki Areef,yadda ka bashi kunya ka nuna cewar kana bayan maah,kasan me hakan kenufi kuwa.?to bari ni na gaya maka,kanuna cewar bai isa dakai ba,kuma shi ba matsayin mahaifi yake wajenka ba.”

Sai lokacin yayi saurin tashi zaune idonsa ya canza kala saboda damuwa yace,
“Karka fassarani haka jahid,taya zan dauki mutumen da ya haskaka rayuwata irin haka,kasan matsayin da naba Abbu ciki zuciyata kuwa.”

Wani tsakin yaja yace mashi,
“Duk irin matsayin da kabashi baida wani anfani,tunda har ka wulakanta bukatarshi gaban kowa,kadaina cewa yana da babban matsayi wurinka.”

Rutse idonsa yayi da karfi yana jin kamar ya kama jahid da mugun bugu,don jin irin kalaman da yake anbata mashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button