ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Cikin muryarsa data canza sauti saboda bacin rai yace,
“Karka sake anbata mani irin haka,na fadi iyakar gaskiyata ne saboda banson ya dauki amanar ta yabani inakasa rikewa,because i don’t love her salma nakeso itace wadda na zabarwa kaina matsayin abokiyar rayuwata,akanme zanyi karyar yin abunda nasan ba zan yiba,idan kadamu ne saboda nace bason pls and pls jahid marry her.”

Murmushin takaici yayi yana kallonsa kafin ya gyara jinginarsa jikin gadon yace,
“Areef kenan wallahi tallahi kaji rantsuwar dan musulmi ko,da ace babu wata acikin raina ban riga na furta inasonta ba,jiya dana baka mamaki gabankowa zan ce ni yabani aurenta,saboda khairat matan dake ma maza wuyar suce,kuma kaima nan gaba am sorry 2 say wallahi u will regretting.”

Wani wawan tsaki yaja ya mike yashige toilet yana cewa,
“U are not in ur sense wlh,nidin zanyi regretting akan wannan yarinyar marar hankali,mtsss amman babu wanda ya kasheni irinka Allah ya isana wallahi.”
…….yashige warshi.

Jinjina kai kawai jahid yayi yana hango yada lamarin zaikaya.

   *************

Tun da na tashi da asuba nayi sallah nake karatun qur,ani saboda in kara samun kwarin guiwa,saida naji zuciyata tayi sanyi sannan na tashi yah meenah har ta koma bacci,fita nayi don har lokacin banajin bacci sosai saidai kaina da yayi nauyi saboda rashin baccin,kitchen nasamu anni tana had’a break dinsu Dady don dashi suke tafiya,itada maah idan yau wanan yyi gobe wannan yyi,tsarinsu gwanin burgewa.

“Annie ina kwana,ai ina cewa sadaqallahul azim nayo nan,saboda k’amshin girkinki d a ya hana hancina sak’at.”

Murmushi a kan fuskarta tana motsa fruit salad da ta gama had’awa tace,
“Lafiya lau yar gidan Annie,Amman dai kinsan ko lashe bazan y’an maki ba ko.”

Ansa nayi ina zubawa cikin mazubin da take niyar zubawa nace,
“Ba komi k’amshin ma da naji is okay for me,zai cika mun cikina.”

Kallona tayi ina cigaba da idasa hada basket din break din nasu,cikin tausaya wa tace mun.
“Y’ar gidan Annie kallanni.”

Banyi musuba na d’ago ina kallonta.

Hannuna ta rik’o dana gama saka komi tace,
“Bakiyi bacci ba khairat,karkice mani abunda yafaru jiya shine ya hana idonki runtsawa,idan kuwa haka ne to banji dadi ba,khairat shin ko kin manta da cewar yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau imani ne,ladace mai tarin yawa karki soma yin halin irin na marasa ilimi,ke yarinyace mai ilimin addini dana zamani,zanso aduk sanda kika tsinci kanki acikin wannan halin kiyi anfani da iliminki,don haka kiyi mani alkawarin wannan shine karon farko kuma na karshe.”

Kaina yana k’asa nace,
“Annie nayi maki alkawarin haka insha Allah.”

“Yawwa diyar albarka naji dadin haka,nasan kuma tunda kikayi man alkawari bazaki karya ba,Allah yayi maki albarka ya kuma cigaba da karfafa maki akan komi,dauki break din kikai falon Abbunku shizai wuce dashi,dadynku sabko yayi don suna da bak’i.”

Dauka nayi na nufi cikin fat dinmu,
Kowa bacci yake don lokacin karfe bakwai da rabi,falon na sameshi yana karanta jarida,maah na zaune gefenshi, yana yin dana gansu ya nuna akwai damuwa.
Sallama nayi na ajiye ina gaida maah,ta ansa cikin kulawa shima na gaidashi.

Nai zaune ina jiran ya fadan abunda yasa yace in sameshi da safe,jinai yace mum.
“Ta alkairi kije zuwa dare mun hadu,amman ki tabbatar kiyi baci isashe don idonki ya nuna jiya bakiyi bacci ba.”

Ina wasa da hannuna nace,
“Insha Allah Abbu,saika dawo Allah ya kiyaye.”

Cikin kulawa yace,
“Amen Allah yayi maki albarka.”

Nace”ameen”na baro falon

Mom muhseen ce.
Mrs bb.
[5/27, 8:12 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

16.

Daki na koma nayi dakin yah meenah na sameta tashin ta kenan,tana mik’a da salati.
Murmushi nayi mata ina hayewa gadon nace,

“Morning my dear.”

Hararata tayi kafin ta sauka daga gadon tana cewa,

“Mai kukan banza kawai,wallahi saboda kuka wataran sai kin makance rab’o kawai.”

Dariya nayi don yadda ta dage sai hararata take tana fad’a,
“Kinyi dariya mana ni kinga shigata wanka,kinsandai yau muke fara attending lectures ko.”

Kwanciya nayi ina jan bargo tare da cewa,
“Wallahi yah meenah ko bature bazai nuna maki biting time ba,kiga fa kwata 2 eight muda keda lectures ten thirty.”

Ta na daga cikin barth room din tagama wankeshi tana hada ruwan wanka tace,
“Kanki akeji don wallahi bazan ringa let ba,dana gama inhar baki tashiba saidai kisaman can,don na lura nawarki is too much wlh.”

Dariya nayi nashige bargo don sanyi akeyi kwanan kamar kamarme.
Dandanan bacci yayi gaba dani don dama idon sai lumshewa yake saboda tsabar baccin dake cina.

       **********

Areef ne da jahid suna wajen exercise dinsu,don wajene keb’entacce wanda aka k’awatashi da abubuwan more rayuwa,babuce babu awajen Abbune yafito zaiwuce ya hangi k’ofar wajen abude,yafasa shiga ya cewa driver yasaka mashi jikarshi baya yana dawowa.

Shiga yayi ya samesu duk sunyi gumi,jahid na kan machine din gudu Areef na gefe yana kan na keke……hira suke jefi jefi saida yagama kallesu sannan yayi gyaran murya,duk juyowa sukai suka kallo wajen………..da sauri areef ya sauko daga inda yake ya iso inda Abbun yake,ya dan rugumeshi yana cewa.
“Good morning Abbu.”

D’agoshi yayi yace,
“Morning.”
Jahid ma yazo ya rungumeshi ya gaidashi,don wannan salon tun suna yara sukeyinshi kuma Abbun ne ya koyar dasu hakan,don yanajin dadin jin yaransa ga jiki,Allah kadai yasan irin son da yake masu.

Duk suna zaune kasa shi yana tsaye,
“Ya kamata dai kamar yanzu kunfara zuwa office,ai kun huta haka nan ko.”

Areef ya langab’ar dakai zaiyyi shagwabar da ya saba,Abbu yace.
“Karkace komi,sarkin son jiki kaikuwa wata macen ma tafika jarumta,don haka banason korafi idan na dawo am talking about that issue OK.”

Duk suka ce yes Abbu tare suka fito suka rakoshi har mota,Areef ya bude mashi baya yashiga sannan yarufe,daga mashi hannu sukai har yafita………..
Komawa sukai suka cigaba d aikinsu,Jahid yace.

“Don Allah bakaji kunya ba.”

Kallon haushi yayi mashi yace,
“Kunya! For what.”

Jinjina kai yayi yaci gaba da abunda yake,saida yadauki lokaci sannan yace,
“Ka wulakanta bukatarsa jiya sannan yanxu ko kunyar had’a ido dashi bakayi,meyasa akullum baka damuwa da damuwar wani sai taka,wallahi Areef ur Always selfishness gay ka gyara wannan ba rayuwa bane.”

Ran Areef yayi masifar b’aci ko kallon da yake ma jahid kad’ai zai tabbatar maka da hakan,cikin muryarsa data zama so deef yace,
“Duk Akan wannan yarinyar kake gaya mun magana yadda ranka yaso ko jahid,to bari kaji wani abu wallahi kalma guda da kake fadan marar dadi akan wannan vellege girl din karajin tsanarta nake cikin zuciyata,don haka ba zance ka daina ba plss continue.”

Shi ma cikin tsananin bacin ran yace,
“Uhmmmmm Areef kenan i know u hate her very much,kawai don baka da rabone Allah yajuyar da lamarin,domin kuwa khairat ta fi karfinka don class dinta bana irinku bane,Amma kasani wallahi ba ayin shishshigi cikin lamarin ubangiji,ni bansan gaibuba shiyasa bazan yanke maka hukunciba,Amman insha Allah very soon sai khairat tazamema dan hakin daka raina sai khairat ta saka idaniyarka kuka,sai khairat ta saka ka jinyar da tunda kazo duniya baka tab’a yin ir……… stop jahid……. stop stop Areff ya fada cikin tsananin tsawa da b’acin rai………takowa yyi har gabanshi ya daki kafad’arsa yace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button