ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Saida na gaido Annie sannan nafita cikin gida wajen maah,Falo na sameta itada mai aiki suna hira,na zauna ina gaidata.
“Ashe kin dawo,ya test d’in.”
Na yamutsa fuska”to da sauk’i dai kiyitayi man Addua kar nasamu fail,saboda wlh yau nayi ma lecturan laifi.”
Fada tayi man kamar zata dakeni,har nai nadamar sanar da ita.
Hakuri nabata take cewa idan nayi wasa wallahi karatun zan aje ayiman aure.
Wata irin zabura nayi ina kallonta,nace”maah aure fa kikace me yakawo wannan maganar.”
Sallamar mai aikin tayi tace idan zan kwanta in sameta d’akinta,nace to kurun tatashi tabar falon.

Abbu bainan shiyasa banma je inda yake ba,maganarta tayi man tsaye ga makoshi “Aure,ni za,awa auren,tabdijam.”
Tashi nayi nawuce d’akinmu salma bata nan nasan tanacan ta kasa ta tsare.
Tsaki naja nace”Allah yarabani da wanan wahalallar soyayyar.”
Kaya na fara had’awa cikin trolley,tun kan in tabbatar da anyarje man ko akasin haka harna hada kayana,inaba zuciyata tabbacin ai yama yarda yagama,saida na had’a akwati uku harda jakunkuna takalma dadai sauran abunda zan buk’ata.

Nafito na wuce wajen yah meenah nace tataso muje,tayi dani inzo muci abinci nace sai mundawo banda natsuwa harsai na samu abunda nakeso.
Fita mukai Annie nacewa Allah yabada sa,a muna dariya mukace ameen.
Tunda muka doshi b’angaren nasu zuciyata take bugawa kamar zata fito waje,na rik’e hannun yah meenah gagam har tana cewa”zaki karyani fah.”
Banmasan nayi ba bansan dalilin dayasa nake masifar tsoran saba,nidai banson had’uwa dashi harcikin zuciyata kuma haka yake,nidai yanzu ko kad’an banajin wani sonsa saboda yariga ya koya man tsoransa ya cireman duk wani feelings akanshi,amman ina mamakin abunda naji shekaranjiya……..wanda har yau inajin abun idan natuna da ranar……tura k’ofar falon yah meenah tayi nayi saurin b’oyewa natoge nakasa shiga,da alamun suduka suna nan,inajinma harda salma jinai yah jahid yace”waye nan.”
Yah meenah tace”yah mune.”
“To kushigo mana kuke lab’ewa.”
Jana take ina togewa don har jikina ya fara rawa,saboda tsananin tsoro……..dole tashige tabarni ina rawar sanyi.
“Ina kairat d’in.”
Cewar yah jahid
“Gata can bakin k’ofa ta k’i shigowa.”
Murmushi yayi ya kalli Areef dake kwance kan three seater yalumshe idonshi,ga salma zaune gabanshi da alama fad’a sukai.
Muryarsa yadaga yace”kishigo my dear bacci ma dodon naki yake.”
Aikuwa nai zuf nashiga na rakub’e bakin kujerar farko ta wajen k’ofa.
Duk nai tsuru tsuru me zasuyi ba dariya ba,har salma dariya take can kasa kasa…….hawaye suka silaloman natashi nayi hanyar fita naji muryarsa irin ta marasa lafiya yace”zo nan.”
Kasa fitar nayi najuyo ya kalli yah meenah yace”kubarnan.”
Kankace me taruga salma tatsaya nuk’u nuk’u yadallah mata harara sannan tatashi tafita,yah jahid yaketa jana nakasa biye mashi don jina nake kamar saman gajimare ina lilo.
Lumshe idonsa yayi bai sake kulani ba,saida naji zaman ya isheni nace”yah.”
Jahid murmushi kurun yake yanason wannan dramer tasu,
Jin yaki ansawa nasake cewa” YAH AREEEF
Tsintar kwayar idonsa nayi cikin tawa,sai bakina yayi nauyi na kasa cigaba da maganar………sadda kaina nayi ina sharar kwallah,nidai narasa gane kaina,dan danan idan ina gabanshi sai kuka……….”idan kuka zakiyi man get out.”
Jinai kukan ya kucceman nadunkule waje guda kaina cikin guyawuna,yi kawai nake ina sauke ajiyar zuciya.
Yah jahid da tasowa yayi zai lallasheta sai yayi wani tunani kurun sai yafita yabarsu.
Tashi yayi zaune yanajin kanshi yana tsananta ciwo,daker ya fizgo maganar yace”zonan.”
Kasa motsawa nayi jikina rawa kurun yake kamar anjonaman wuta……dafe kanshi yayi da duk hannunsa,cikin tsawar dabaisan ma zai iyayintaba tace”I said come here.”
Ina makerketa na isa wajenshi,rawa kurun jikina keyi hawaye kau kamar anbude famfo…….hannunsa yasa guda d’aya ya rikoni yana kallona da jajayen idonsa dasuka rine.
“Menene,mekike so.”
Muryata na rawa ina shashsheka nace”dama……..dam…..a..cewa za……nyi…….ka….barni na koma hostel.”
Tsaki yaja kafin ya saki hannuna yace”is that All”
D’aga kai kurun nayi yace”waye ya kawoki d’azun.”
Ai jinai fitsari zai kucceman girgiza kai nayi inaja baya…..fincikoni yayi ya zaunar yana kallona “I said waye yayi dropping naki d’azun.”
Fashewa zanyi da kuka ya tashi ya shiga d’aki belt ya d’auko yace”answer my question.”
Saboda tsananin firgitar danake ciki yasa bansan sadda idona yayi looooooo nazube k’asa bah………..

Mrs bb ce????????

Love u All my fans
[6/4, 9:18 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by (mrs bb)

Mom muhseen ce

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

          22.

Dafe kai yayi yana jin kan nashi yana sarawa,ruwa ya bud’e ya d’auko cikin frig mai sanyi yashiga shafa mata ga fuskarta,wata ajiyar zuciya na sauke mai nauyi…….lumshe ido yayi yana sauke tashi ajiyar zuciyar…..tashi nayi nafice ban sake mai magana ba,harna wuce bangaren maah nadawo don nasan munyi da ita zamuyi magana.

Ta na ta shirin kwanciya don Abbu sai yakwana biyu yaje wani taro libiya,idasa shiga nayi na zauna gefen gadon,idona rufe ajiyar zuciya kurun nake,ina mamakin yadda nakejin tsoronsa har cikin yan cikina,abun yana d’aure man kai…….”lafiyar kalau.”

Bud’e idona nayi nace”maah tsoron da nakewa yah Areef yana ban mamaki,inhar zan kusanci inda yake jinake kamar zan sik’e,maah bansan dalili ba tun ina ganin abun ba komi ba maah yanzu yana ban mamaki,yanzu fa zuwa nai kurun na tambayeshi idan yabarni nakoma hostel,amman karkiso kiga yadda jikina yake b’ari,karshe kan nafito har suma nai nadawo.”
Kallona take tana nazarina tsawon lokaci,kafin ta girgiza kai kurun tace”akwai wani abun,Aman kibar hakan cikin ranki zanyi wani abu akai,sannan kinyi sanyi da azkar dinki khairat,ki zama jaruma akoda yaushe karkibari wani yaga rauninki Addua takobin muminice kizage dayinta,sannan duk sanda zaki kusanci inda yake ya zamo kina karanta hazbunallahu wani imal wakil……kiyita nana tawa har kurabu understand.”
D’aga mata kai nayi ta cigaba da shirinta,nace”maah shikenan.”
Have”aa,saurin me kike.”
Shiru nai inajiranta don dajin maganar tana da matukar muhimanci.
Saida ta gama ta hau gadon sannan tace man,
“Salma taje ta samu Inna tagaya mata komi akan yayanku,harda soyayyarsu sannan ta k’ara dacewa ita bata son karatun aure takeson yanzu ayi mata.”
Kallon maah nake kamar itace innar ko salmar……gaba d’aya nayi huking,salmar da kanta tafadi wannan maganar,
“shin wai me salma keson zama shin meyashiga kanta,anya wannan tunaninta ne kuwa maah.”
Murmushi tayi tace”maganarki abun dubawa ce wannan ba tunaninta bane,karanta mata akai,ita kuma tahau ta zauna,salma data sha nonona zubarwa tayi,don banyi zaton hakanba Amman nasan mezanyi.”
“Maah karkice nafadi haka saboda kishi ko har yanzu inason yah,Anya salma ta dace da yah Areef,maah kar azo abubuwa su dagule.”
Gyara zamanta tayi takallan tace”kema ai Auren takeson aimaku kudukan ku harda shidah…….”
Zaro dara daran manyan ido na nai ina kallon maah,murmushi tayi tana kallona”maida idon karsu fad’o,wannan maganar bamai yuwu wa bace khairat kwantar da hankalinki,itadai dakeson auren za,ai mata amman ba d’anaba saidai tanemo wani,duk abunda yarinyarnan take ciki khairat wlh i know,I know everything about her.”
Jinjina kai nake kamar kadangaruwa,lallai mutun mugune duk da bansan me maah take nufiba,naji ajikina salma ba alkairi take shiryawa ba,cikin karyewar murya nace”maah me mukai mata,bamuyi mata komi ba,yadda kowa yake da yanci cikin gidannan haka takeda,akan me salma zatai haka.”
“Come down my angel,don’t mind her,everything will be Alright.”
Ganin dare yayi tace inzo yau tare zamu kwanta,dadi yakamani,yau zan kwana jikin maah d’ina after long time.
Naje na canzo kayana nazo na kwanta tayi mana Addua tashafemu mukai baccinmu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button