ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

????????????????????????????

Washe gari inada class 7:00 am. Tun wuri maah ta tasheni nashirya taje ta hadoman break dakanta,wani jidani take sosai nikuwa kamar na tashi sama don dadi,Annie tashigo ta ganmu tace”yau kuma shan nono ake,na b’oye ina dariya hira mukai tayi har nagama,yah meenah sai 4:00 pm takeda ita,don yanzu mawiyaci ne mufita tare,hka ma wajen dawowa…….yah jahid ne ya lek’o yace”ko my dear ta shirya zan sauketa makaranta.”
Nai saurin tashi nace” muje yah jahid.”
Muka fito ina yiwa yah meenah saita taho……muna dosar motar naji gabana ya fad’i rasss,jikina ya fara rawar da yasaba na kalli yah jahid ya girgiza man kai,adduar da maah tace nayi nacigaba da yi,harda karin wata yana zaune kujerar zaman banza,na shiga baya na zauna cikin kwarin guiwa yah jahid yatada mukatai.
Saida nayi jarumta sosai sannan nace”yah Aree ina kwana.”
Bai juyoba yace”lafiya lau.”
Har mukaje bai ce komiba kad’an kad’an yah jahid ya jani da hira har mukaje school d’in.
Fitowa nai inayi masu sai anjima harna juya naji yace”kayanki fah.”
Sororo nayi ina kallonsu murmushi yah jahid yayi yafito yana bude but,kayana nane kuwa wad’anda na had’a…..bansan sadda wani k’ayataccen murmushi nayi har dumful dina duka biyin suka bayyyana,kallona naga yanayi kamar ya samu tv,na sadda kai nace”thank u yah Areef.”
Wayata na fiddo cikin d’oki nakira husna tazo ta tayani d’aukar kayana.
Sunanan har ta iso muka kwashi kayan sai hostel,ranar inacikin farin ciki sosai,munfito break nakira maah na gaya mata, tace ai tasani kin gaya man tayi,nasiha sosai tayi mani maishiga jiki,sanan tace inri’e ibadata da azkar dina,idan na kwana biyu zata kawo man ziyara,aikuwa naita jin dadina.

(YANZU WASAN ZAI FARA,MASOYANA KUBIYONI DON JIN YADDA LAMARIN ZAI KASANCE.)

Zama na hostel tare da husna ba k’aramin dadi yake man ba,gashi karatunmu yana kara zurfi,komi yana kara gaba sai inyi wata banje gidaba wani zubin saidai Annie da maah su suzo su ganni,saboda munfara zama busy tsakanina da yah Areef kuwa zan iya cewa ni hakan ma yafiye man kwanciyar hankali,duk da yanzu alhamdulillah tsoron da nakeji nashi yayi mugun raguwa,duk da ba had’uwa mukeba amman sometimes yana kirana yaji ya karatun,ya kuma jaman kunne akan wasa da karatun,daga haka shikenan sai muyi sallama,rabona dashi tun randa suka kawoni,yah jahid ne duk weekend zaizo ya d’aukemu nida husna muje yawo,wani zubin kuma muyita fira har yamma sannan yatai.
Yah meenah ma takusan dawowa hostel din,sai dady ya dawo idan yabari zata zo d’akinmu muhadu mu uku.
Salma kuwa zuwa yanzu bansan wace take ciki ba,saboda koda wasa ban taba ganin ta kawo man ziyaraba,kuma konaje gidan bana ganinta……Anty shidah tadawo sunyi graduation,yah shahid ma yadawo,gidan yanzu gwanin sha,awa.
Husna duk ta rud’e da ganinshi yayinda shi baisan ta nayiba, zanso ace had’in yayuwu saidai yah shahid ba,amai cusu irin wannan bakke ince zan mashi maganarta,amman inanan ina tsara plan dina,don nasan yah zaiso ta kodan bata rasa komiba husnar.

Akwai wani abu guda dake faruwa dani,tsakanina da DR MK mutumin duk school d’inan yawancin yanmatan dake ciki bawacce bai burgeta,cikinsukuwa hardani eh sosai Dr yana burgeni ta b’agarori da daban daban,kamar natsuwarsa kamewarsa daga kula yanmata,rashin maganarsa,tsaftarshi gayunshi da kuma tsayuwa akan ra,ayunshi……..tun bayan da maah ta rabani da yaj Areef nayi jinyata na warke sainaji kamar anzareman sonshi dake cikin zuciyata,ko miskala zarratin banajinsa irin yadda nakejinsa dacan,inamashi kallon danakewa yah shahid…….Tun bayan dawowata hostel na kula da wani abu,DR mk lectura mune yana d’aukarmu course biyu,baya kula kowa amman ni sai yazamar mashi kamar jiki idan bai kulaniba,bakuma kulawa irin magana cikin mutane ba,koyace insamai office aa ba haka ba.
Idan yashigo class idonshi akan sit dina,idan yafara darasi bayafara tambayar kowa saini,dana san ansa da ban saniba, inharkuma banganeba bayagajiya zai tuso darasin tundaga farko harsai nace nagane,idan na makara zaita kallona harsai ni dakaina nafad’i dalilin makarar,inkuwa nasake nayi fashin zuwa class nabani duk da bazai mun maganaba amman fa ranar danazo bazai barmu mutashi ontime ba,duk abunda akai ban nan sai ya maimaitashi,bayajin komi.
Wannan abun dayake yasaka husna ankarewa kuma ta isheni da maganarsa,hakika nima nasan something behind,Amman kamar mekenan bansaniba nakanji babu dadi duk randa bamuda lecture dinsa,saboda gaskiyar magana Dr ya iya koyarda mutun yagane,kokai kwalwar kifine dakai dole zaka fahimci wani abu ko baka gane duka ba.
Yah Areef bai tab’a zuwa wajena ba kuma nima ban tab’a mashi complain din hakanba,kwana biyu banjin dadi kokadan masassara nake fama da ita saidai husna tayiman atendance,yau da yamma tadawo daga class bayan tayi man sannu tace”khairat kitashi fah yau wlh DR yayi magana akan rashin zuwanki,don bayan anfito yakirani yace ince maki kuhad’u sahad guiden 5:30. Anjima.”

Kallonta nake na kasa cewa komi,
Zama tai kusadani tace”khairat inhar maganar soyyyace yazo maki da ita pls,don’t reject,bance karkija ajinkiba amman karki nunamai wulakanci yacancanci asoshi baida wata mummunar halayya .”

Wayata tayi vibration ina dubawa sunan yah Areef ne text ne yayoman.
Budewa nai naga yasa.

meet me in sahad guiden 5:30pm

Kallon juna muke dandanan naji masassarar ta bar jikina,husna ta d’auki wayar tana duba sak’on.

Kallona tayi ganin na buga tagumi.
“Nikuwa khairat ban tab’a kokarin sanin wani abu dangane da yan gidankuba amman kiyi hkr yau inason sanin ya kuke da wannan yayan naki Areef.”

Maimakon na bata ansa sai kurun natashi nashige barth room.

Mrs bb ce????????[6/4, 7:16 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

WRITTEN BY (MRS BB)
MOM MUHSEEN.

(AGASKIYA MASOYANA BANDA KALAMAN DA ZAN GODE MAKU,ILLA IYAKA INCE ALLAH YABAR KAUNA DA ZUMUNCI,HAKIKA IN BABU KU BABU MU HAKA IN BABU MU BANU KU,KARKU KAMAN TA COMMENT D’INKU SHINE K’WARIN GUIWARMU,ALLAH YASHIGE MANA GABA YA BAMU RAI DA LAFIYA.)

???? KAINUWA WRITERS ASSO…….

              23.

Husna sororo tayi da wayar ga hannu tana bin hanyar ban d’akin da kallo,tabbas wannan abun ya sake tabbatar mata da cewar akwai wani abun,inbacin haka daga yin simple question sai ki canza,karshe kibarni nan zaune.

Tashi tayi ta d’ora sanwar indomi don tasan Khairat ba dora komiba,tunda nashiga barthroom din nai zaune kan abun bayaha,nadafe kaina dake mun masifar sarawa.
Nashiga ukuna ni khairat,idan yah yaganni da Dr mezan gaya mai shin zaima saurareni kuwa,mik’ewa nai cikin azama ina sabbatu”kai ina wallahi bazai saurareni ba,wannan b’akar zuciyar bazata barshi yaji komi daga gareniba,nabani yazanyi.”
Tunawa nai da Husna dana baro d’akin,idan ba itaba wazai bani shawarar yadda zanyi to kenan hakan nanufin saitasan komi kan family issue d’ina,wata zuciyar tace to menene Husna cefa tazama yar uwarta,kuma tana da tabbacin bazata bata shawarar banza ba kuma babu maijin sirrinta wajen wani.Dole na yanke shawarar sanar da ita komi akaina da gidanmu.
Wanka nai nafito ina kallonta tana cin abincin tana danna system,kamar komi bai faruba tace”kinga ma zaman kewayen kenan.”
Murmushi nai ina zaman kusada ita nace”bakiyi fushi bakenan.”
Tab’e baki tayi tace”kinsan dai ba halina bane ko,akanme zanyi fushi bayan nasan kina da dalilinki na kin gaya man a bunda ya shafeki,don kar husna soda uwar surutu ta zagaye school tana sanar da mutane.”
Dariya nayi nagane cewar abun yabata haushi nace,
“Karkice haka kema kinsan cewa ba haka bane,kiyi hkr insha Allah 2day am telling u everything about khairat,hakan yayi maki ko.”
Harara ta wurgoman bansaniba kusada ita na matsa”haba mrs shahid farouk ai bazakiyi fushi daniba nasani,yanzu kiban shawarar yadda zanyi inhad’u da kowanensu batare da guda ya ji haushina ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button