ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Ajiye plet d’in da kate cin indomin tayi tana kallona some seconds,sannan tace”ki kira yayan naki kice dashi baki fito lecture lokacinba,amman ya sameki school 7:00pm lokacin kinga kin dawo harma kin natsu.”
Rungumeta nayi inajin dadi,
“Thanks my d besty friend in d world.”
Murmushi kurun tayi mun tatashi tana had’a kwanonin wanke wanke.
Shiryawa nikuma nafara yi cikin natsuwa amman duk da haka ina kokonta yaya,nasan halinshi amman bari najarava wannan shawarar ta husna,ance da jarabawa jirgi ya tashi amman zuciyata sai bugawa take.
Nagama shafa mai najawo phone dina nashiga kiran sa,tunda na mallaki waya ban tab’a kiranshiba,ringinga take ba ai picking ba harna sare husna tayun zuru da ido, ganin duk nayi wata iri dani ajiye wayar nayi nace”kingani bai d’auka ba.”
“To kiyi mashi text mana”
Dafe kai nayi cikin rashin jin dadi na shiga typing text d’in kamar haka.
“yah ina class around 5:30,pls KO zaka zo school din 7:00 lokacin i’m free.”
Ajiyar zuciya nai ganin ya tafi,tashi nai naciba shiryawa.
Bawata kwalliya nayi ba don nibata damanba kyauna haka ya isan,asai na k’ara da waniba farar powder nasa itama don husna ta isan,sai kwalli turare nasa kad’an tunda nasan babu kyau tunda ga inda zanje.
Sai jana take wai nayi kwalliya don zanje tad’i da ai bayi nakeba ko hoda bana sawa idan zanje class,murmushi kurun nayi mata nace”babu rakiya kenan.”
“Wah! Kyaleni research ma zanyi wlh saikin dawo kiyoman tsaraba.”
Fita nai inajin kirjina yana duka.
Nai sa,ar samun taxi ta kawo wani student,natsayar da it nashiga na gaya mai inda zaikaini………..kallon wayar nake ba komi nake kalloba sai time,biyar da sha biyar jingina nai jikin kunerar har mukafice daga makarantar.
Minty talatin ya kaimu wajen,wurine na alfarma wanda sai wane da wane ke zuwa wajen,an k’awatashi da abubuwan sha,awa da more rayuwa,ni,ima ce wajen sosai iska mai dadi da fitulu burjik,idan dare yayi sai kace safiyace bazan kwantanta maki yadda tsarin wajen yakeba don yafi karfi alkalamina.
Tun daga bakin get d’in wajen nake baza idon ina zan ganshi,don baka shiga saida get fast,wanda duk zaishiga saiyabada kid’i sannan subashi get fast din,idan kuma kagama zaka barmasu abunsu nan.
Tsaye nayi ina kallon masu shige da fice,wani daga cikin masu kula da waje ne ya iso inda nake yace”madam bismillah,ga yallaban can yace ayi maki iso.”
Bin bayanshi nayi abayace jikina har k’asa saboda fakistan ne jikina riga da wando………..wajen babu yawaitar jama,a don inajin akwai ranakun da zakazo kasamu mutane fiye da haka.
Wani waje muka nufa naji zuciyata tana bugawa fast,runface maitsananin kyau wajen grass capet yakara fiddo kyan wajen,saidai zuwa yanzu bn ganin kyan wajen,saboda abun nani da firgtni,kocikin miliyoyi mutane naganshi dole shaida shi…..duk tuku guda danake jinake kirjina zaifad’o saboda tsabar fargaba da firgici……..bayashi kurun nagani Ammn zuciyata kakarwa take,meya kawosji wajen nan nashiga ukkua ni khairat.
Wlh ngaji pls sorry mu hadu gobe.
Mrs bb ce.????????
[6/5, 11:43 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA
WRITTEN BY (MRS BB)
MOM MUHSEEN.
GODIYA TA BATA DA IYA KA AKAN KU MASOYANA,HAKIKA KUNE JIGON LITTAFINAN,INA MATUKAR ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE,ALLAH KUMA YASAKA MAKU DA MAFIFICIN ALKAIRINSA,INASONKU KAMAR YADDA KUKE SONA.
JINA GAREKI UWARIDAN SARDAUNA FATIMA,MARUBUCIYAR SOORAJ ALLAH YABAR KUNA KEDA MAIGIDANKI????????
not editing
Idan kunga mistake kuyi hkr????????
24.
Wani irin tuntub’e ne nayi daya yi silar fad’uwar pos dina,dama d’an rakiyar tunda yashigo dani wajen yajuya tunda naga inda zanje,duk’awa nai na d’auka inajin d’an yatsana yana jinga babban,d’agowar da zanyi naga wayam inda yake zaune su biyun saura Dr amman shi banganshi ba,murje idona nayi sosai amman ban ganshiba ko iskar da ta d’eboshi ban ganiba,waige waige nake amman ko b’urbushinsa ban ganiba…….jikina yayi wani irin sanyi nabani uku wai k’alau nake kuwa kodai tsoron sa ne yasa naga kamar shine awajen da farko,k’arfafa zuciyata nayi na karasa wajen ina ajiyar zuciya k’asa k’asa.
Tun kafin na zauna yake kallona yana zaune kan kura ga table gabansa an k’awata shi da yan kayan ci kadan,yad’ora kafarsa kan d’aya yarik’e hab’arsa da hannunsa,fesincap ce kansa wadda ba sosai nake kallon cikin idonsa ba,tabbas Dr ya hadu hadedden guy ne,wanda ya iya daidaita wankanshi,jeans ne dark blue sai light blue d’in shirt tabi jikinshi ta kwanta,agogoce d’aure ga hannunsa na hagu sai daukar ido take,kamshi ketashi mai tsananin shiga rai da kwantar da hankali,har lokacin kallona yake nikuma ina tsaye,da hannunsa ya yi man nuni da na zauna,kujerar dake kallonsa jikina yayi wani lakwab haka na jaye hijab dina na zauna ina wasa da yatsuna,nakasa kallonshi,don bazan iya had’a ido dashi yana mun irin wannan kallonba.
Cap din naga ya ajiye gabanshi ya tashi zaune sabanin da dayake kwance cikin kujerar.
“Ina wuni.”
Wayyo kamar zan nitse haka nakeji,kunya ta kamani mema yasa tunda nazo ban gaidashi ba,kasa ansawa nayi inata matsar yatsuna kamar zan tsinkasu,kozafi banaji wanda da kalau nake bazan iya sarrafasu irin haka ba.
“Karkijima kanki ciwo,yana zuba lemo cikin cup fuskarshi da murmushi wanda kokad’an baya yinsa cikin class.
Mik’omun yayi “bismillah,ance in kayi bako first abunda zaka taryeshi dashi shine abunsha,kafin komi yabiyo baya.”
Duk na kasa sakewa gashi sai kallona yake ni kallonne bansaba dashiba,yana ban kunya kuma idaniyata bazata zureba.
Cikin low voice dina da bansan dalilin sanyinta ba nace”sorry sir good evening.”
Sautin murmushin sa naji yana rik’e da cup din ruwa saida ya kurba sannan yace”bazan ansa ba tunda nima baki ansa tauba.”
D’agowa nai nad’an kallai kafin nasadda kai nace”sorry sir bazan it ansa gaisuwarka ba,bacin ni yadace nafara gaidaka kuma banyiba,I’m sorry na shafa,a ne.”
Ajiye cup d’in yayi yana tattara duk hankalinsa kaina,
“Me ya shagaltar dake,nagadai ko kallona ma bakiyiba balle nasaran ko Muhammad kamees ne ya d’aukar maki hankali.”
Innalillahi wayyo Allahna wannan guy din ya iya bada kunya,jinai kamar inzura aguje.
(????????????basaban ba khairat)
Shiru nai inata murzar hannuna nakasa cewa komi,to mekuwa zance mai jinai yace”kinyi shiru,kisaki jikinki bafa sace ki zanba wallahi ban iya satar mutane.”
Dariya yaban bashiri murmushi ya kubcemun mai had’e da dariya,rufa bakina nayi nakara sadda kaina inayin abuna.
Inajinsa yana tayani amman nashi babu sauti sosai.
Saida nagaji nadaidaita kaina yace,
“Haka kika iya dariya,
Aikuwa zaki koya man nima naringa yiwa budurwata.”
Kallonsa nai bance komiba murmushi dai nake yi.
“Meya hanaki zuwa class 2days,anyi abubuwa dayawa bakyanan.”
Nad’an saki jikina nace masa
“Wallahi bana da lfy kwana biyu amman nasamu sauk’i,husna tana mun bayani idan ta dawo.”
“Kin tabbata tana yi maki,”
D’aga kai nayi murmushi yayi yace “to bari mugani idan bayanan sunzauna kanki.”
Tambayoyi yashiga yiman ina bashi ansa tare da bayani sosai.
Tab’i yashiga yimun yana cewa “good,very nice gaskiya husna ta cancanci kyauta kibata wannan inkin koma.”
Wata envelop ce ya mik’omun.
Kallosa nai nace”sir kabarshi ai basai kabata wani abuba.”
Gabana ya ajiye yana kallon cikin idona yace”don me basai anbata ba,bayan tayi abunda ya farata man,kefa ta yiwa taya bazanji dadiba.”
Sadda kaina nayi nama rasa mezance masa wlh
Dole na k’akaro smile nace”to tagode.”