ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Shiru muka sake yi na tsayin lokaci,kuma har yanzu idonsa akaina wlh jinake kmar in bace sabod wannan kallon nashi.
Ga magaruba tataho dandanan hankalina ya tashi,saboda ganin bakwai saura minty talatin.

“Da alamun dai kin k’osa kibar nan ko,ban tunanin wajen bazai burgekiba aida munje kalam guiden.”
Yak’e nayi nace”Aa wlh yayi kyau,sosai wajen akwai nishad’i.”
Mik’ewa yayi yana cewa”musanman idan akwai wanda ya sace mka zuciya awajen ba.”
Ban tashiba nabishi da kallo,shima ni yake kallo wanda bazan iya jure shiba,inda nake ya iso yad’an sunkuyo ta gefen fuskata kamar zai sunbaci kuncina,dandanan jikina ya kama kerma runtse idona nai injin kashin turarensa yana huda gashin jikina,i wonder nakejin something akanshi,mekenan nashiga ukkuna.
Cikin wata murya da tayi masifar tada tsikar jikina yace” ummulkhair,why kika mun irin wannan satar plsss ko kinsan kin kassarani akanta,na zama zero tundaga lokacin da kika yimun wannan satar,plsss ki maido man kayata in samu relief.

Tunda yafara magnar kirjina ke bugawa babu k’ak’k’autawa,na k’an kame jikina da nakejin kamar yana zarar raina kamar yana fiddamun duk wani kuzari dayayi saura cikin jikin. Wata ajiyar zuciya nasauke mai mugun sanyi jin yatashi daga inda yake,bud’e idona nai ina jin kamar na fasa ihu akan yanayin danaji.
Pos din ya d’aukarmu namik’e shikuma ya jaye kujerar nafito,tare muke tafiya zuwa inda yayi parking.
“Bakice komi ba.”
Fuskata kamar zanyi kuka na kallai nace’pls wlh bansan abunda na satar makaba kayi hkr.”
Dariya yashigayi yana shafa kanshi,hannunsa yana rik’e da cap dinsa,
“Gaskiya ba zanyi hkr ba sai kin biyani,idan kuma baki biyaniba zan rama idan na tashi ramawa naki sai yafi zafi,don ko har kuka saina saki.”

Shiru nai banda ansar bashi,a matsayina na yar jamia wacce ta waye tasan kuma me ake kira da so,to dole nasan me dr yake nufi da kalamansa akaina,nagane komi yke nufi dani nagane kenan yadda na sace mashi zuciya shima yna nufin zai sace tawa.
Hakika zan iyacewa zuciyata babu kowa aciki,empty set take amman kuma inajin can k’asan raina wani gurbi da wajen yake yawan bugawa,muddin naji wani feelings akan DR hakan meyake nufi,basan me hakan yake nufiba nabarwa Allahn daya halittamun wannan zuciyar.

Bud’emun gaba yayi nashiga yazagayo yashiga,fita mukai mukai mukanufi school,jana yake da fira anman nakasa sakin jikina nabiyeshi,saboda maganarmu dashi ta karshe itace kemun yawo akai,wani gefen zuciyata inajin tsoron Kamuwa da sonsa,wani shashen yana nuna man idan nakamu da son nashi menene,wanda kikemawar dai akwai babban ginshik’i tsakaninku,duk yadda kikakai ga son kasancewa dashi yariga ya zama haramiyarki.
Rutse idona nayi inajinsa yana ta gayaman wsu kalamai wanda babu tantama dr zai iya yin nasarar sacemun zuciya cikin d’an karamin lokaci,kamar yadda yafad’a man.
Bakin get d’in hostel ya saukeni saida nayi dagaske sannan yabarni nashige……….Allah Allah nake na isa d’aki,don inji shin an aiko nemana,inhar an aiko to tabbas yah yazo,inkuma bai aikoba hakan nanufin baizoba.
Don yanzu takwas harda minty ashirin.

Husna na tadda tana bud’e wata katuwar ledar shooping,kayane gasunan birjik kamar ba,asan zafin kudiba aka siyosu,tsayenai ina kallon kayan,nidai nasan Dr bai ban komiba ,haka bai aiko kowaba to waye zai kawo,kodai husna aka kawomawa.

Jinai tace”sai yanzu kenan,da alama Dr yasamu karb’uwa.”
Banbi takan kalaminta ba nace”bak’o kikai husna.”
Mik’ewa tayi tana jingina d bango tace”aa,ke aka kawowa yayanki ya zo bazan iya lissafa adadin mutanen daya turo nemankiba,inacewa baki fito lecture ba,karshe hardai nace bakidawo d’akiba.
Baiyi minty goma da tafiya ba ga kaya nan ya aiko dasu abaki,hada wasu cards idan kin duba duk zaki gani.”
Silalewa nayi k’asa wata zufa na karyomun zuciyata da sauri take bugawa…………

Mrs bb ce????????
Mom muhseen

09034722970.
[6/6, 12:48 PM] Mom Muhseen: ????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by (mrs bb)
Mom muhseen.

Dedicated by ZAUREN MRS BB ????????

watt pad
HUMAIRA 7531

GODIYA MARAR IDADI GAREKU MARANTA LITTAFINA,INA MAKU FATAN ALKAIRI.

     *not edited*

             25.

Duk nayi zufa hijab din tajik’e sharkaf,wallahi inajin tsoran yah inajin tsoron yasan wani abu tsakanina da dr,shin idan ya tambayan inda naje inazance mashi,bayan nidakaina nace ya saman school at 7:00 pm gashi kuma yazo ni bandawo ba,damuwata wannan karyar danayi cewar naje lecture bayan kuma tabbas yah ne nagani tareda dr wajen sahad guiden,nabani nalalace yazanyi.

Hus na ce tatako har gabana,ta durkusa tana cireman hijab dina da gyalen fakistam dina.
Cikin kulawa da nuna damuwa tace taso saga nan zauna nan,ta kamani muka zauna kan katifar mu.
“Meye faru,duk wannan tashin hankalin nameye,shin mala,ikane yayan naku da har kika tsorata dashi haka,haba khairat ki dawo natsuwarki mana,kefa yar jamia ce babbar budurwa mai daukar overaller na department dinmu,kyakkyawa maiji da wayewa da kudi da kokari,taya zaki ringa jin tsoron namiji irin haka duk da bansan dalilin tsoron nakiba amman yayi yawa,kozan iya sanin alakarku dashi.”

Jingina nayi jikin bangon dake bayana,ina dunkule kafafuna nasauke ajiyar zuciya maikarfi sannan na kalleta,
Cikin karyewar murya da low voice dina nace”husna,idan nace maki yah badan gidan mu bane hakan ba gaskiya bane,saidai zan iya cewa shid’in ba uwarmu daba haka ba ubanmu dayaba,shid’in dane ga yayar mahaifiyata maah.
Nabata labarin abunda nasani da wanda naji bakin su Abbu,da yadda nakamu da sonsa shekarun baya harda ciwon zuciyata,komi nasanar da husna har kan abunda kefaruwa yanzu da abunda salma keman.

Jinjina kai kurun take tana kallona,kafin ta nisa tace”tabd’ijam,yanzu ya kenan kina ganin cewa yanzu zai iya dawowa yanuna yana sonki,kokuma mekike tunanin ya kawoshi wajenki.
Ban bude komiba cikin ayancan akawai ina fiddo kayan ne,akwai cards ciki idan kika duba muna iya samun ansar abunda mukenema,kuma yanzu ke yakikeji cikin ranki akanshi.”
Zamewa nai na kwanfa ina kallon sama nace”banajin komi kanshi banajinsa irin yadda najisa shekarun baya,bana jin feelings akanshi irin shekarun dasuka wuce,husna saidai abu guda inajin tsananin tsoronsa wanda nikaina bansan daliliba,daidai da second idan muka keb’e ko nake kusada shi in takaice maki har suma ina iyayi.
Basan why ba inson daidaita alak’ata dashi kamar sauran yan uwana,amman nakasa wallahi bazan iya cemaki da reason guda dayaba dayasa nake mashi wannan tsoron,…………..

“Lallai na maganar maah,datace maki something behind,tunda ada kince ba haka kuke ba dole akwai dalili kece baki saniba,amman nasan maah tasani bazadai ta sanar dakeba.”
Kallon husna nayi nace”kin tabbatar da haka kuwa.”
Murmushi tayi mun”na tabbatar saboda tace maki tana ankare da duk abunda kowa keyi,kuma zata san abunyi.
Kishirya kije gida kuyi magana zaki tabbatar da maganata,ance zato zunubine koda ya kasance gaskiya,ina zargin yar uwarki da yin wani abu duba da yadda kika gayaman soyayyar da takewa yah Arref din.”

Tashi nai zaune ina kallonta kamar yau nafara ganinta,
“Husna mekike cewa,wace yar uwar tawa karkice salma salma duk son da takema yah bazata cutar daniba,tana sona bazata so abunda zai tab’aniba.”
Murmushin tayi mun”ada kenan khairat,kibude idonki kifahimci reality,ki auna abubuwa da yawa ada da kuma yanzu d’aya suke,son da kikace tana maki da yanzu tana makishi? Yaushe rabon da ta zauna kuyi hira,tunda kikazo school konace tunda kika dawo hostel ta tab’a kiranki awaya?ta zo inda kike common text wannan tayo maki?,ki bud’e kwalwarki dakyau kifuskanci gabanki makashinka na tare dakai salma bata sonki,zatayi komi don raba wannan kaunar.
Karkiyi mamakin idan nace maki yah Areef he love u he love everything for u,amman akwai abubuwa dasukai discouraging power nashi,kiyi mai uziri kisama ranki cewar yayanki bai tsanekiba,bai kikiba hasali kece wacce yabinne cikin zuciyarsa,bance kiyardaba amman wannan shine gaskiyar magana.
Wannan dalilin zaisaka salma taga tayi komi don ganin ta sameshi,don ba ita yakeso baba itace dreaming d’insaba thats why.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button