ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Halin da ake ciki kenan.
tunda yah yatafi baya waya dakowa sai maah da Abbu,kilan kuma sai yah jahid.
Sau daya naji sunyi waya har take gaya mashi nayi ciwo har nakwanta asibiti,sanda na same ta suna wayar zama nai kusa da ita nace taban mugaisa.
“Tace ga shima zata gaidaka.”
Sai cewa yai Kyaleta maah kidai ce inamata yajiki.
Wannan abun ya tsaya man garai ranar yini nai in kuka kamar bazan kai ba,sai daker na samu kaina.
Tunda na sanar da maah cewa dr zaizo taita shige da fice nidai iyakata shirya kaina idan yazo,babu laifi dr ya samu gurbi cikin zuciyata,saidai gaskiyar magana soyayyar da nakewa dr ko kwata kwatar wadda nakewa yah Areef bata kamoba,saidai inayin iyakar kokarina naga nanuna mai tawa soyayyar,kuma hakan yana matukar faranta mashi.
Zuwan husna uku gidanmu dubani,saida nayi yadda nai na had’ata da yah shahid har naroki ya maidata makaranta,to sonake na koma naji yadda suka kare don naga tunda ta gaida shi naga yaki tashi daga falon,yana satar kallonta nasan sai wani abu yabiyo baya.
Wanka nashiga ganin yamun text yana hanya,inaji maah tashigo tana fad’a “kullum sai kinga yakusan zuwa zaki tsiri wankan iskanci,kiyi ta shegiyar nawa kishanya bawan Allah yana jiranki,wallahi kishiga taitayinki kafin wata tayi maki kafa.”
Dariya ma tabani ina shigewa kurun bance mata komi ba,maah nason dr sosai,tana son aurena dashi.
Yah meenah tashigo kirana lokacin ma nake shafa mai,itama fadan tayi man wai ina gasa shi dayawa,don naga yana sona sosai.
Murmushi nayi mata kurun,don danayi magana zatace nacika gardama,ita tafiddo man kayan dazan saka,riga da siket sunyi mun kyau sosai,kasancewata mace mai dirarran jiki tako ina jikina adire yake,don namafi duk yan matan gidanmu kirji masha Allah,don cib da cib sukaiman,salma kuwa saita had’a da breziya mai soso.
Hips dina shima daidaidani baiyi yawa ba haka baiyi kadanba.
Itace tayi man d’aurin kallabi don yah meenah gwanace indai nan bangaren ne,gyale kalar kayana ta fiddo man sannan tafesheni da turare maishege kamshi,sanna taja ni muka fito falon bakin dake bangaren Annie,don acan ta saukeshi saida taga shigata takoma don kawo mashi abun tab’awa.
Tunda nai sallama ya mike yana wani irin killer smile,ya saka hannayenshi cikin aljihun wandon jeans dinsa,ya karkace kai kallona kurun yake babu kakkautawa.
“Wow wow my princess,irin wannan hadewa sai kija miyauna yayita zuba babu kakkautawa.”
Dariya nayi ina sadda kaina don dr badai sakin layiba,isowa yayi gabana yana bude duk hanayenshi,kallonsa nai ya daga a gira yace”yes come in”
Girgiza kaina nayi ina murmushi”Aa nagode da tayinka bismillah kazauna.”
B’ata fuska yayi yana zama saman hannun kujerar danake”bakison welcoming dina ko princess.”
“Aa ba haka bane kabari irin wannan welcoming din sai munje can sainayi maka amman pls not now.”
Gyara zaman shi yayi yana dubana cike da so,
“Dagaske.”
D’aga kai nai murmushin yasake yi yace”karkisa inje in samu Abbu ince pls Abbu amaido daurin auren nan gobe ta alkairinka tayi man alkawarin something sweet nikuma bazan iya jira har sai nan da 3week ba.”
Dariya yaban ganin yadda yake maganar cikin karya murya kamar mai shirin kuka.,
Dariyar yake taya ni yace”wallahi kin iya dariya rannan nace ki koya man kika kiya ko.”
Yah meenah ce tashigo hakan baisa ya tashi daga inda yake ba,saima murmushi yake yana yimata sannu.
Tana fara,a tace”yah muhd sannu da zuwa.”
Cikin sakin fuska yace”yawwa Anty Meemah sannunki da kokari,kina ji dani kullum bakya gajiya.”
“Wallahi babu komi ai kai nagida ne.”
Nan fa ya samu yar tayin surutu,don dr akwai zafin surutu saida tayi daker ya barta tatafi.
Jiyo wa yai kaina cikin salon kauna lemu ya zuba ga cup yanufo bakina,dole na bude na kurba har shatin jan bakina ya fito……..saida yalashe shi tas sannan ya aza bakinsa wajen dana sha,kunya ta rufeni duk da bayau yafara irin wannan abunba.
Nayi serving dinsa komi yadda yadace sannan nasauko kusa dashi k’asan don yace yafi jin dadin zaman kasan,yadanci yana jana dafira yaudai duk karatu yafi yawa.
Ya jima sosai don nan yayi sallar mangaruba,har suka gaisa da dady da Abbu.najashi cikin gida suka gaisa da maah,har ya ajiye mata rafar yan dubu guda gabanta.
Sanda na rakoshi salma tadawo daga rakiyar Ameer don yau yazo,ko kallon inda muke batai ba ni kunya ma naji don saida yace”kamar salma ko.”
Yake nayi nace “itace”
Bai sake cewa komiba
Har bakin mota na rakashi yabude baya ya miko man wata leda,
“Turarenki yana burgeni ummlkhair,kamshin sa yana sakani shauki matsananci,pls matso na sake jinsa.”
Matsoni yayi sosai har numfashin mu yana haduwa,dandanan naji tsikar jikina tatashi,sunkuyo da kanshi yayi gefen wuyana ya sauke numfashi mai zafi,saida na runtse ido, nai saurin ja baya.
Rungume hannuwa yayi yana kallona da idonsa daya canza yanayi,wani abu nakejin yana shigata bansan komeye ba,kauda idona nayi.
Yace”pls just a kiss.”
Ba arziki na Ruga nabarshi, don wallahi idan natsaya dr yau saiya tsotse man baki,har mamakin sa nake soyayyarsa dandanan take shigar mutun,ya iya tafiyar da ita yadda yadacesaidai idan kabiye zuciya taufa tuni zaku canza ma soyayya mazauni.
Mrs bb ce????????????????
[6/11, 12:28 PM] Mom Muhseen: ???????????????????????????????? ????
ABIN CIKIN RUHINA
Writing by mrs bb
Mom muhseen.
Wattpad name
Humaira7531.
DEDUCATED BY ZAUREN MRS BB
SABODA KAUNAR DA KUKE MAN YASA ZANYI UPDATE YAU,DON DA SAI GOBE INA ALFAHARI DA KAUNARKU DA ADDUOIN KU ALLAH YABAR KAUNA ????????????
Not edited.
29.
Washe gari mukai shirin koma wa school,nasa rigima dole yah shahid zai kaimu don inada wani plan……….saida yabiya damu mukai shopping sosai saboda semister mai tsawoce,duk da dai Auren yakusa inso samuna nane abarshi nagama aji ukuna,sai ayi lokacin mana cikin hutu,zan ma dr magana yayi wa su Abbu magana abarmu mukarasa wannan semister.
Hira muke tayi yana taya mu,ahaka har na sako batun husna inacewa.
“Wallahi yah meenah ban tab’ayi kawa irin Husna ba,tana da kirki ga kokari,kisan idan akai abu class tasan ban ganeba muna dawowa hostel mungama duk abunda zamuyi zata ce inxo muyi bita…..bata barina har saina gane,ina sonta sosai gashi akwai natsuwa.”
Ina maganar ina satar kallon fuskarshi murmushi yake amma baice komi ba,nace”yah kaima ai ka lura da haka ko rannan daka sameta gida.”
Shan mur yayi yace”don ubanki zama zanyi inta kallonta har naga wani abu tattare da ita.”
Shiru nai ina kunshe dariyata yah meenah na tayani,
Sai kuma yace”kawai dai tana da tarbiyya akwai girmama nagaba.”
Dadi naji ya kamani nace”sosai kuwa wallahi husna tayi,shiyasa cousin dinta dake sonta yake bala,in jida ita bayason kowa yana rab’arta kishinta yake sosai.”
Kallon fuskarsa nayi naga dandanan ta canza yah meenah banda dariya babu abunda take,ni kuwa na sha mur irin dagaske haka maganar take,bacin karya ce kurun na shatata don ingane yana ciki ko haukana nake.
Bai sake ce mana komi ba amman yanayin sa gaba daya ya canza,magana zan ciga gaba dayi ya dakan tsawa dole naja bakina naguntse,banji haushiba nasan kishine yake damunsa dadi yakamani na kaga mu isa in fesa mata albishi.
Har bakin get din hostel ya kaimu muka tsaya fiddo kaya,don suna da yawa saboda kayan yah meenah.
Kin tafiya yayi yana ta danna waya,zuwacan yace “kikirata ta taya ku daukar kayan mana.”
Wayyo dadi haka naji aikuwa nai maza na shiga contact dinta na danna mata kira.
“Besty nah gamu bakin get pls kizo ki taya mu kwasar kaya tare muke da yah meenah.”
“Besty ina hangenku ganin bayanku yanzu nadawo daga cefane bari in karaso.”
Dadi kamar yayi yaya dani don inson wannan kaunar ta jone,
Kamar wasa sai gata sai fara,a take tunma kafin ta san waye amotar,
“Yah meenah oyoyo,wallahi naji dadin zuwanku zaman nika dai ya isan,kewa tayi mun yawa.”
Rungume juna mukai ina mata oyoyo.
A kunne nayi mata rad’a nace”kalli gefenki pls.”
Juyawa tayi ta ganshi zaune cikin mota,kirjinta yabada rassss duk ta diririce daker tace tana yar fara,”yah shahid ur welcome.”
Dagowa yai ya kawata fuskarsa da murmushinsa mai kyau yace”Asma,u ykk ya makarantar.”
Tana wasa da hannunta tace”dasauki makaranta yah angode Allah.”
Jinjina kai yayi yace”Allah ya bada sa,a ga friend dinki nan na maido maki na fita ko.”
Dariya tayi kadan ta kalleni na kashe mata ido guda tace”ka kuwa kyauta wallahi thank you.”