ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Murmushin yayi mata yana tada motar,
“Ga wannan akara kudin siyen garin rogo.”
Dariya tayi ta ansa tana godiya tace”ai mu bama cin irin wadannan yah mu fa inkaga dish din damuke ci zakaso kazauna dakinmu.”
Yana dariya yace “ok zan gani wataran zan maku shigar bazata.”
Matsowa mukai muka mashi sallama yayi mana jan hankali kan karatu sannan yafita.

Ihun murna nake harda taka rawa,bada dariya babu abunda suke man har mukaje daki…………nan fa na sata gaba da tsokana badai tace komiba wai kunyar yah meenah take,
“Nace bur wallahi lallai kin ma daina wallahi,wai besty ya kuka kare rannan.”

Mikewa tayi zatabar dakin nai saurin rikota,
Yah meenah tana dariya tace”husna ya haka mun zama daya fa ki bar jin kunyata ni banajin taku,inkuwa haka ne daki zan canza.”
Dole ta dawo na matsa mata saita gaya man yadda sukai.
“Wallahi besty kinfi ciwon ciki katsawa,bafa wani abu ya faruba kawai ya na ta jana da firar school ne tare da cewa kardai na biye samarin makaranta su hanani karatu,shikenan fah.”
Murmushi nayi nace”soon zakiji ya kiraki yana cewa Asma,u in bakeba sai rijiya mai kwalabe.”

Gaba daya muka saka dariya,tun tana nokewa taki sakin jiki da yah meenah har ta sake,ranar munsha fira don babu mai lectures cikinmu sai tomorrow morning.

????????????????????????????????????????

A hankali rayuwar take gurgurawa har gashi fara shirin exams,saboda nayiwa dr magana yayiwa Abbu magana yabarni na gama aji uku na,ya kuma yi mashi yayarda ga shirye shiryen biki ga na exams,dole dr ya hakura da takura man kan kira da kuma zuwa,don ma ba sosai muke haduwa ba ko acikin schol din.
Saidai koran weekend yazo ya dauke mu muje yawo da shopping.

Duk abunda nakeyi ba wai na mance da ABIN CIKIN RUHINA ba ne Aa babu second ko awa da zuciyata bata bugawa dashi,daidai darana guda bai tab’a barin zuciyata da ruhina huta wa ba,banda wani abun tunawa dashi,illa kalaman sa na karshe nidashi airport.

ina maki fatan Alkairi matar muhammad kaseem,sai wata rana bazaki sake ganina ba,kiyi hkr dani mun haramta ga juna har abadan,domin bazan iya karya wa maah Alkawarin taba,zanje nayi jinyar zuciyata kikula da kanki And plsss forget About Areef farouk,good by ummulkhair.

Wadannan kalaman sun zamar mani kamar fatiha cikin sallar farillah,duk daren duniya sune suke amsa kuwwa cikin kunnena,juriyace da karfin hali kawai suke rike dani,don nayiwa Abbu Alkawarin hakuri da kaddarata,yace man na tai makeshi karya rasani,in nabiye shiga damuwa komi zai iya faruwa dani,don ciwon zuciyata zai iya tashi kuma likita ya sanar da su cewa inhar nasa ke irin wannan kwanciyar,komi zai iya faruwa dani don haka inyi hakuri kowa da kalar jarabawarsa ke kuma taki haka tazo,don haka ki yi wa Allah godiya tare da kokarin ganin kin cinye jarabawar.
Kalaman Abby kenan ranar dazan dawo makarnta,naji nasihar sa sosai don inason Abbu na ba zanso ya shiga wani hali ba saboda ni.

Zuciyata ta azalzaleni akansa har nakusan shiga wani yanayi,kalamnasa da ya gaya man ranar kafin mufita mota sune suke tunzura bacin raina,har ma inji to miye na kwallafa raina dashi tunda koda babu dr nasan yadda ya fadi kalaman hakan nanufin nai mashi kadan.

k’wailaye daku berori da bakusan kanku ba.

Wadannan kalaman sunfi komi kona man rai,har nakan kalli kirjina dake cike masha Allah,wanda nasan idan za,a tara mata goma cinkinsu da wuya asamu biyu masu irin breast dina,shine yake ceman k’waila,to nayarda dai salma k’walarce Amman ni wallahi ba ita bace.
Haka dai nake ta abuna abu wanda yasan halin nake ciki,illah yah meenah da besty husna.

Suma ba suda abun yi man face lallashi da ban baki,insuka na yini daki ko lecteres ban jeba nakicin abinci sosai sun san abunne ya tukoni,zasuyita lallashina suna gaya man kalamai masu kwatar da hankali,sai inji nasamu natsuwa.

Rannan dai nazauna nayi wa kaina karatun ta natsu,nace shifa wanda nake wannan haukan donshi yana can yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali,wata kila man ya shafe babina ya bude wani sabon shafin,kilama yayi budurwa ko ince yayi yanmata don nasa shi gwanin farin jinine akansu.
Tunda natuna haka nacire ma raina yah Areef,ganin gamai sona kamar yayi mani sujada saboda tsananin kaunar da yake mani,to akan me zan dorama kaina damuwar wanican da ko kirana mu gaisa baiyi,saidai najishi suna waya da yah meenah amman ko agaidani baicewa,to kan wane dalili wata jotter ta sabuwa da ban fara komi cikin taba nayi rubuta kamar haka.

NI UMMULKHAIR FAROUK,NAYI ALKAWARIN SHAFE BABIN SA CIKIN RAYUWATA,NAYI ALKAWARIN MAN TASHI CIKIN RAYUWATA,NAYI ALKAWARIN DAINA YIN CIWO SABODA SHI,BAZAN SAKE SAKA YAN UWANA DA IYAYENA CIKIN HALIN DAMUWA BA SABODA SHI,ZAN FARA SABUWAR RAYUWA DA MASOYINA KUMA MIJINA INSHA ALLAH.

na jefata cikin tarkacena ban sake bai takan taba,don promise ne bazan karya ba zanba marad kunya inaha Allah.
Cikin yardar Allah muka gama exams,kuma muduka muna fatan samun sakamako mai ktau,daga wannan hutunne zamutai pratical sai munyi six months sannan mudawo makaranta.
Shirye shiryen bikinmu ake babu kama hannun yaro,duk kullum husna nagidan mu sai dare yah shahid yamaida ta,kasancewar yanzu babu laifi sun saki jiki dajuna amman ban tunanin yafurat mata yana sonta,suduka dai idan kagan su tare kasan akwai soyayya mai karfi,amman kowa jinkai dajan class ya hanashi,amman inanan ina hada masu tarko sai yah shahid yafurta da tsiya ma bada arzikiba.

Mrs bb ce????????????
[6/12, 6:28 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira753.

DEDUCATED BY ZAUREN MRS BB.

NOT EDITED.

             30

Komi aka sama rana sai yazo,cikin ikon lillahi gashi dai bikinmu yarage saura kwana uku,yau mutanen dubai suka sauka,da iyalanta yah imaran da kanensa saifudden,sai yar auta mimi taci sunan mahaifiyarsu maah watau zahra,u shine ake kiranta da mimi.
Ummi kamar ta goyani don tsananin murnan ganina,nima haka nakeji don yinin ranar muna tare da ita,sai jana take wai ina surukinta yazo ya kawo gaisuwa.
Nace metake ci nabaka na zuba zaizo,har sata gaji dashi.

Wasu irin kayan kitcheen tazo man dasu new moden,kai daka gansu kasan an narkar da kudi waken,kuma abun jin dadin bani kadai ba harda sweetheart dina salma.
Naji dadin kayan sosai naita mata godiya, dun gureman kai tayi wai ai miye na godiya bacin hakkinta ne matsayinta na uwa,kuma haka batunta yake saboda ummi na sonmu tana kaunar maah batajin tsadar abu inhar mune zata yiwa alkairinsa.

Mimi tsararmuce amman mun dan girmeta da shekara guda,amman inka ganta zakace itace ta girmimu.
Don girman jikine da ita sosai,banyi mamakin rashin ganin ABIN CIKIN RUHINA ba don daman naji ajikina bazai halarci daurin aurena ba,ganin kamar zanji babu dadi yasa nai saurin kawar da tunanin hakan cikin raina,

Dadaddare Dr yazo gaida ummi sai nokewa yake tana masa dariy,don ummi babu ruwanta da jin kunya,maah cema kejin nauyinsa sosai Annie ma batajin kunyarsa sosai.

Gida ya dauki harami don yan gidansu Annie sunzo hada hajiyarsu,da kanwarta da yayarta sai hidima ke dasu,dangin maman salma kuwa basu zo nan gidaba sunacan wajen Inna,hakan yafi don sai anyi rigima yadda nasansu basuda hakuri kona kwabo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button