ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Gyaran jiki muke zuwa tunda yarage saura sati biyu,shiyasa gamunan ko ince ganinan nayi wata irin canzawa,don salma bansan wace take cikiba,taki shigowa cikinmu ko kadan,itada kawayenta su raihana kurun suke hidimarsu,har kararta nakai wajen Abbu yace in kyaleta tunda ta janye daga gareni nima injanye mata,idan nacigaba da cusa kaina wajenta zata yi kokarin ganin ranki ya baci,nikuma bazanso abunda zai taba rankiba har agama bikinku ta Alkairi.
Rungume Abbu nai ina fashewa da kuka,don tun yanzu nafara jin kewarsa inajin sa har cikin kokon raina,yadda yake tattalina yake gudun duk abunda zai shigar dani cikin damuwa,lallashina yake sosai daker nayi shiru.
Kallona yake yana murmushi yace”Kinyi kyau ta Alkairin Abbu,Allah ya kawo ranar da ta alkairina tazama babba zata tai gidan miji itama.”
Sadda kaina nayi inajin kunyarsa.
Dagoni yayi yana dariya yace”kiyi man alkawarin kulawa da mijinki da danginsa da yan uwansa abu mai muhimmanci ma ace mahaifansa,don hakan zai kara maki daraja da kima ga idon su da idon duniya,hakan yasaka mahaifiyarki kullum Allah yake daukaka darajarta akan sauran mutane,saboda tsaye take kan dangina da mahaifiyata,sujjada ce kurin bata yi masu,don haka kizama jaruma mai jajircewa acikin gidanta,hakuri shine babban jigo ga rayuwar Aure idan kika rikeshi kingama dacewa,sannan kizama mai rike sirrin gidanki,sirrin mijinki bakomi akeji da bakin matar gidaba,nasihata kenan wajenki ta Alkairi,ubangiji yasaka Albarka acikin rayuwar aurenku,Allah ya kareku daga sharin masu sheri,kiyi riko da Addininki kirike ibada,duk Abunda ya dameki ki gayawa Allah shi zai jibanci ramurranki.”
Kuka nake don hakika nasihar shi tashigeni,naji duk wata natsuwa tashigan,naji hankalina ya natsu da auren saboda kalaman abbu,yayi man addua ya sakaman Albarka wannan ma kadai ya isheni,don kowace amarya konace budurwa zataso ta rabu da yayenta lafiya yayinda zata gidan miji,su rabu suna samata Albarka.
Haka na fito ina share hawayena.
Yah imran tunda ya kyella ido yaga yah meenah shikenan ya zama kamar bindinta,saita boye idan zamu fita yo wani abun,don duk ya hanata samun sukuni,ga yah imran badai iya love ba duk yarudar man da yah meenata.
Yaune akagama man gyaran jiki,gobene daurin aure,don nidai nace banason kowane irin event,sai angama daura Aure sai ayi dinner gidan iyayen dr.
Mun shigo gidan kenan mukai karo da yah shahid,duk ya fita natsuwarsa murmushi nai don duk yau banbari sun hadu da mutuniyarba,kallonmu yai yasha mur.
“Ina Asma,u.”
Da yake sunsan kanun zancen sainai saurin cewa,
“Au nafa manta,yah shahid wannan wanda nace maka yana sonta din nan, yah kamal cousin dinta.
ya samemu wajen gyara,ana gama mata ya dauketa inajin sai anjima kadan zaka ga tashigo.”
Gani kawai nai yadafe kai cikin masifa yake ceman,
“Donme zaki bari wani yatai da ita wani waje,bayan kinsan amana mominsu tabaki,ehye maza kirata yanzun nan ta dawo.”
Mimi da yah meenah sabewa sukai suna dariya kasa kasa,don sun san idan ya kama su suna mashi dariya ran sune zai baci.
Sake shan mur nai nadanne dariyata nasake tun zurashi da cewa,
“Yah nace maka cousin dinsu ne,ansanshi gidansu,ko ita momin nasan bazatai fad’a ba don antsayar da ranar aurensu bayan sallah babba.”
Wayyo kuzo kuga tashin hankali karara kan fuskar yah shahid,
Cikin tsawa yace.
“Sa ranar banza da wofi, aure akai masu dazai bita wani waje ya dauke ta ehy,laifin kine da kikajata.
maza maza nace kikirata yanzun nan tabaro duk inda take ta dawo,inba haka ba daga ke har itan sai rayukanku sun b’aci.”
Ya bar wajen kamar zararre.
Saboda dariya har duke wa nake lallai yah ya kamu over,haka nakeso daman,dole ya sauke girman kanshi yafurta tunda shine namiji,wayata na fiddo ina cigaba da dariyata nakirata,
“Plan dinmu yayi Husna maza kishigo kafin yah shahid yasama gidan nan bom yatashi…..ina dariya.”
Itama dariyar takeyi tace,
“Ganinan tahowa ina cikin taxi,dama nasan za,ai haka saina iso kiban insha.”
Kashe wayar nai ina dariya sakon dr ya shigo man.
AMARYAR GOBE YAUDAI D’AYA ABARNI NAZO NAGA KWALLIYARNAN DA AKETAYI KUSAN WATA GUDA.
Murmushi nai inatura mashi sakonsa cewa saikazo.
Dakin yah meenah nanne madaddalarmu,can nanufa,.
Ina shiga kofar falon Annie naji munyi mugun karo da wani abu,har wayana tana faduwa…….duka wanai na daukota ina murza kaina,saidai sadda zan d’ago banga kowaba……..kirjina naji yace dammm saboda wani k’amshi da ko mutuwa nai nadawo bazan iya mance shiba,……….bin hanyar nayi da kallo jikina yana wata irin rawa………….
Taufah.????
Wani irin sanyi jikina yayi kamar ansakani cikin frig,ina waigen hanyar na karasa cikin daki,hayaniyar suce kurin ketashi,daki suna kyalkyala dariya suna maida yadda kai.
Kamar wadda akazarewa kuzari da lakkar jiki haka naji,ina sando na shiga dakin ina bin bango.
Silalewa nai kasa bakin kofar shiga bayi,wani irin kerma jikina yake………..wayata na ajiye kan madubi babu wanda ma ya lura dani saboda daroyarsu suke suna ta hirarsu.
Rungume kafafuna nayi ina dora kaina saman guiyawuna,ina sauraren bugun zuciyata.
Bazan iya cewa ga halin da zuciyata take cikiba,runtse idona nayi ina dauke numfashina na wucinngadi kozan daina jin wannan mayataccen kamshin,amman ina kamar ma hade yake da numfashina,duk sanda zan shakesa tare nake jinsu.
Husna ce tashigo tana sauke numfashi,duk suka juyo suna kallonta,mimi ce tai saurin jawota
“Ya kuka kare husna na matsu inji wannan dramer.”
Harararta tayi tana dariya yah meenah tace”Ai da kin jima baki dawo ba kilan yah shahid bulala zaisa ya zanemu tas har amaryar.”
Cu dariyar suke husna tace,
“Ina Amaryar take…….shiru tayi ganina zaune bakin toilet na kudundune kafafu,duk wajen suka kalla.
Husna ta ajiye jikarta ta iso wajena.
“Khairat,meye haka lafiya kike,yanzu fa muka rabu dake awaya lafiya lau,meya faru daga baya.”
Duk sun shiga damuwa kowa so yake yaji abunda ya saman,taya zan iya yi masu bayani mezance masu,karo nai da wani mai kama dashi,koko kamshin sa naji,wane daga ciki zan fada.
Nashiga ukuna miye haka zuciyata ya ina cikin farin ciki zaki yiman haka,gobene fa daurin aurena inkikamun haka kin zalinceni kin cutar dani da masoyana,plsss na rokeki kifitar mun da wannan masifar,bazan iya cigaba da jurewa ba,inason cigaba da ganin farinciki afusar iyayena…………ji sukai kurun na fashe da kuka maitsuma rai,suduka duk jikinsu duk yayi sanyi…….don dajin kukan kasan maiyinsa nacikin kunci da damuwa.
Mrs bb ce????????
Love u All ????????????
[6/13, 8:47 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA
Writing by mrs bb
Mom muhseen.
Wattpad name
Humaira7531.
DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.
Not edited
31&32
Saida nayi iyakar yina sannan nayi shiru,shigewa toilet nayi nashige cikin ruwan sanyi,ko sirkashi banba,shaya ce keta zuba bisa kaina nafi minty goma haka………injin karar wayana yah meenah na cewa,
“Wannan wankan ya isa haka ga dr nan nata kiranki yanzu haka zowa yayi.”
Wani kulutu ne ya tokare man ga makoshi,jinai banson ganinsa bana son jin sunansa……….zafin da zuciyata keman harga jikina don wata irin masassara nakejin tana saukoman.
Dole na jawo towel na daura nafito,kowace ta kama waya sai yitake……tsaki naja nafara shiryawa.
Doguwar rigace nariza nadan shafa lotion,da body spray na zuba abayata har kasa,don inason dogon hijab rayuwata,kocikin lefena da aka kawo akwatinsu daban wajen kala goma shabiyar…….wayar na dauka nafito compound din gidan,motarsa nacan gefe guda kasancewar filin wajen badai girma da fadi ba,mota goma saita shige har asamu sauran waje.