ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Fitilar ya kunna don nagane shine,tafiya nake kaina kasa inajin babu dadi,bazanso yaga damuwa tare da niba don ban san mezan ce mashi ba,dole na kakaro murmushi nasa ma fuskata……..
Budeman gidan gaba yayi yana murmushin sa mai kyau,yasha shadda gizner sai daukar ido take.
Shiga nai ina sallama.
“Wa alaiki salam,gimbiya Amarya da girman kujerarki,Amarya bakya laifi koda kin kashe dan masu gida.”
Bansan sadda dariya ta kucce man ba yana tayani,
Nace”irin wannan kirari haka,karkasa kaina ya fashe sir.”
B’ata fuska yayi kamar karamin yaro zai kuka,
“Ba nace banson wannan sir dinba,nace maki da munbar school to sir ta kare,saidai my only.”
Murmushi nai ina jin nauyin sunan sosai,shiru nai ina wasa da tsuna da suka gaji da kyau,don mai kunshi musanmman yayar Annie tazo mana da ita,ta zane mana kafafu da hannuwa,sai daukar ido suke.
Hannun ya kalla yace”bakiji wani miyau daya wuce man ba,inso samune wannan yan yatsun in tsotsesu.”
Bansan sadda nasa abayata na boye fuskata ba.
dariya yake sosai yana sake karkacewa yana kallona yace,
“Aini ban maga kwalliyarba my love,kidan cireman abayar ingani mana,wallahi tunda kikashigo kamshinki yaketa dukan hancina,ni ko wuyanki kibani in shinshina………”
Wayyo kunya kamar zan nitse don kunyar kalamansa,
Shagwabe fuskanai nace”pls si……..”
Wallahi dakin ida saina cinye wannan bakin tunda baijin magana.
Shiru nai inajin kunyar fadar sunan da ya keson in fada,jinai yace inajinki.
“Cewa nai pls kabari inkana irin wannan guduwa zanyi Allah ni kunya kake bani.”
Juyowa yai gaba daya gabana,ya riko duk hannayen nawa yace”sa idonki cikin nawa,yau kwana nawa rabon dana saki idona,kullum kina man wayau gyaran jiki kike,to tunda angama yau kibarni na mora ganina pls.”
Ya karashe maganar yana sunbatar hannayen,har wani lumshe ido yake.
Wani iri naji don dr akwai iya salon kauna.
Jaye hannun nayi inacewa”pls mekakewa sauri gobene fah.”
Murmushi yayi yace”shikenan,aidai daga gobe andaina man iyaka da halalina.”
Hira mukai tayi dashi duk wata damuwata dana taho da ita ya kawar mun ita,dr mutunne mai sanyin hali,hakurinsa mai girmane tsawon tarayyar mu ba taba ganin bacin rans ba,ko abu nai mashi na bacin rai bazai taba nunaman ba,zaidai ce kibaryin abu kaza babu kyau.
Any time ever moment fuskarsa dauke da murmushi,tabbas nasan na auri dr na gama damuwa,duk irin halin da nake ciki muddin mukai waya or muka hadu ban sanin inda damuwar take rugawa,tabbas maganar Abbu gaskiyace da yace dr shine ya dace dani,nima nayarda na amunce kuma ashirye nake nayi zaman aure dashi mai dadi,nayi damarar faranta mashi har iyakar karshen rayuwarmu.
Zamu yi rayuwa mai kyau da yardar Allah,hakika 100% na yarda dr ya zama mijina uban y’ay’ana.
????????????????????????????????
RANA BATA KARYA SAIDAI UWAR DIYA TAJI KUNYA
RANAR WANKA BA,A BOYON CIBI,ALKWARIN ALLAH YA TABBAT,UMMULKHAIR FAROUK TA ZAMA MATA GA DR. MUHAMMAD KASEEM,TAREDA MATA GA SHAZALLI YUSUFA DA AMARYARSA UMMUSALMA FAROUK.
dubunan mutane da bazan iya kwatan ta maku iyakar adadinsu ba suka shaida wannan Auren,Amare sunyi kyau har sungaji.
domin khairat musanman ummi tayo hayar maiyin kwalliya daga dubai,khairat tahadu iyaar haduwa,saidai muce Allah ya tabbatar da Alkairinsa……..tunda labarin daurin auren yazo ga kunnena nake kuka,badan komi ba sai don kawai cewar yanzu fa nazama matar Aure,wacce zata tashi daga gidansu zuwa wani gidan,zan fara sabuwar rayuwa da sabbin mutane,shin wace irin rayuwa zamuyi.
Shikenan babuni babu zama gidanmu kenan saidai nazo yawo,lallai Aure abune maigirman gaske,kaduba abunda zai raba uwa da yarta yaraba uba da yarsa,wane abune wanan inbada mutuwa da Aure.
Ina falon Abbu ankirani na gaisa da bakinsa,nasamu kyaututtuka har basan iyakaba,vanyi zaton friend dina zasuzo ba saigashi harda mazan department dinmu sunzo man daurin aure.
Durkushe nake nasha wani dankareren less,sky blue da pink color,nasha takalma na da jikkata duk farare sai mayafina babba da aka rufaman bisa kaina har fuskata…….majina kurun nake gogewa don kukan tunyaa zuwa da sauti har ya barfita da sautin,falon yarage mutane Abbune da daddy,sai maah Annie da ummi,sai yah jahid da yah shahid…………..wanine daga can bakin kofar shigowa,takalmansa sawu ciki kurin nake gani farare tasss,tabbas shine yanayin da zuciyatabtake bugawa ya tabbatar mun shine……hakanan banji dadin zuwansa ba hakika rashin zuwansa sai yafimun kwanciyar hankali,domin samun natsuwar zuciyata.
Alamu dai ya nuna fada za,aimun salma akejira tun dazun.
Abbune yake waya da driver da ya aika gidan inna dauko salam,
“Kashiga kace nina turo azo adaukota za,ai masu fada ita da khairat,……….muryar innar mukaji tafito sosai ciki wayar.
“Faruku kafita idona,dolene fad’a tace mun tsoron zuwa take kana iya dukanta,to nima na hana anan za,a dauketa akaota gidan mijinta,ruwanka ne kasamata albarka ruwankane ka tsine mata,inace saudah ce mai yinfadan itada yar uwarya,to itama ga nata dangin uwar nan suna mata,bazata zoba.”
Baice komiba ya sauke wayar,ummi ranta yabaci don daman ummi badai fada ba,inhar akatabota.
Yo ba,a tabota din bama wace allah ciki balle antabo……..cikin banbami tace,
“Wace irin yarinyace wannan kahaifa farouk,ace yau aurenki zakitai dakin miji bazakizo kiyi sallamar mutunci da iyayenkiba,idan ita wannan ta nuna maah,sannan tacigaba idan ita bata haifetaba kai aikaine ubanta,tazo kasamata albarka.
Kumaninda kara da mutunci saudah ba itace tashayar da itaba tsawon shekara biyu,tatarbiyantar da ita,amman dayake nonon datasha fitsarar dashi tayi ta nuna maku cewar itafa diyar lantana ce Allah yajikanta,ai saudah uawartace idan tasan kanta tasan mutunci,kuma inna saita biyeta inbacin kurun dama jiranmu take……”
Maah ce tai saurin katseta dacewar,
“Don Allah yaya kiyi shiru hakanan,kowa yaza ma nagari don kanshi,ni wallahi taje nayafe mata duk abinda tayi man,Allah yasa Albarka cikin auren.”
Magana zata sakeyi ummin dady yace”pls hafsat abar maganar kaima kuma kayi hkr duk yadda ranka yakai gabaci dole zakayi hakuri kabisu da Allah yabada zaman lafiya shi ake fata,shine kawai.”
Nanfa suka rufu kaina kowa da abunda yake fada,kukana kurun nake don jinake baza iya barin maah da abbuna ba.
Cikin yayyaena akace idan damai magana yayi mani ga mototci can zuna jiranmu.
Yah jahid yayi man nasiha sosai akan hakuri,yac”nasanki indai akan nan wajenne to kikara domin zamane baa yauba bana gibe ba,Allah yayiwa rayuwarku Albarka yakuma kareki daga makiya.”
Kowa yace ameen,yah shahid ma yayi man Anty shidah kiwa kwallah take tayi tama kasa cewa komi,duk ta kwakwumeni,itada yah meenah.
Har yanzu yananan inda naganshi,bai motsaba bai kuma tashiba kuma baice komiba,
Ummi ce tafita don wasu baki da sukazo mata biki,tare da maah suka fita tana cewa yah imran yaje yacewa masu daukar amaryar sukara hakuri gatanan za,afiddota.
Wannan kalamin yasake tunzura kukana har muryata bata fita,sumabyah meenah kukan suke,don Anty shidah yah jahid yajata sunfita.
Abbu da Dady daman suma bakin garesu dayawa zasu sallamesu,don yama tayi wajen biyar harda rabine.
Husna ce taje tasake tattaro man kayana danayi using dasu,babu kowa dakin dani sai yah meenah saishi dake can zaune har lokacin.