ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Isowa tayi wajenta ta na tadata zaune,
“wallahi sweetheart baki da lafiya, bafa tun yau kike wannan Abunba I think tun fad’an…………….
“bana son tada abunda ya wuce kinarni na huta pls sweetheart.”
“Shikenan kiyi hakuri, daman Abbu ne yake neman mu mu duka,ke kawai akejira.”
Runtse idonta tayi tanajin Wata matsananciyar fad’uwar gaba,tabbas maganar result d’inta za,ai kuma tasan Yah Aree ya binciko repiting d’in da akai mata………..yau ita tashiga uku idan ya kamata, babu abunda ya tsana sama da kafad’i exams,ko Su yah shahid idan yaga sun fad’i suna gane kurensu, zai kawar da komi ya baka punishment.
“sweetheart karfa yah Areef ya biyo mu,naga yau cike yake damu bama mu ba wallahi har su Anty ma haka.”
Tashi tayi tana jin wata masassara mai zafi na ratsa dukan jikinta,
Ko hijab d’in dake jikinta har k’asa bata cire bah tace,
“muje”
Haka suka jera suka tafi,yayinda Khairat duk taku d’aya gabanta yake tsananta fad’uwa, ji take kamar tayi fuffuke ta tashi ko kuma tayi Samara anemeta arasa.
Koda suka zo bakin k’ofar babban falon Abbu sai ta tokare ta k’ishiga, salma tayi tayi ta shigo ta k’iya dole ta kyaleta ita tashiga.
Zama tayi Maah tace,
“Ina Khairat d’in yo.”
Cikin karyewar murya tace,
“Maah don Allah Kice kar yah Aree karya doki sweetheart,wallahi kingan ta can ta kasa shigowa tsoro take ji.”
Dariya kawai Maah tayi don yau zata ga yadda za,a kaya Areef zai iya hukunta kannen nashi.
Abbu Ya kwala mata kira,
” ta Alkairi shigo kinjiko yayanki bazai maki komi bah.”
Dayake haka yake ce mata tun da aka haifeta.
kasa shigowa tayi ganin tak’i shigowa yasa ya bud’e deep voice d’insa yace mata.
“wallahi Idan na iso wajen nan jikinkine zaiyyi tsami,dani kike bayani yau Allah kuwa.”
shahid yace yana dariya,
“oga sweetheart ce fah.”
Harararsa yayi yace” to ina ruwanka y’an saka ido.”
Anty shahida da Yah meenah Su mujahid duk dariya suke mashi,
Kamar wadda k’wai ya fashe wa aciki haka ta fara bin bango kamar gizo gizo, sosai ta bashi tausayi, Amman baijin zai rangwanta akan wannan saken da tayi,tunda yasha fad’a masu cewar karsu had’a karatunsu da komi, karsu yarda damuwa ko wani Abu ya d’auke masu hankali akan karatunsu.
Kusada Anni ta zauna idonta ya cika tab da kwallah, k’iris take jira ta fashe kuka.
Abbu ne yace yah shahid ya bud’e taron da Addua
Yakaranto muka shafa.
Kasa Kallonsa tai don tasan had’a idonsu Wata masifar ce wajenta, Jitai Abbu yace.
“Kai shahid muga naka.”
Ba musu ya mik’ama Abbun yayi ba tare da wata damuwa ba, don yasan baida matsalar komi.
Yaba mashi yayi sosai tare da mashi kyauta ta musanman, key aka bashi na sabuwar mota y’ar yayi, nan Yashiga murna kowa yana taya shi,ita kuwa ta kasa cewa Uffan…….Anty shahida ma kusan duk iri d’aya ne sakamakon, don naga Itama anbata kyautar motar saidai yah Aree ya ansa ya ba Anni yace,
“gashinan Anni ki ajiye wajenki har sai ta natsu sannan ki bata, wallahi ko bayan bani nan naji labarin kin hau mota batare da izinina ba kingama hawan mota saidai Idan tukaki za,ai understand.”
Cikin rashin jin dad’i tace,
“yes.”
Iri d’aya ce ita da Yah shahid,yah meenah Abbu yace ta mik’o nata, hannunta yana rawa ta mik’ama shi, shirun da sukaji yayi yasa kowa ya tsareta da ido.
Abbu yace,
“meenah garin ya haka,kinsan wancan Karon ma saida mukai fad’a dake akan hakan ko, to donme zaki sake kawo mani irin sa,ok don wancan na hana Adokeki shiyasa yanzu ma kika sake ko.”
Hawaye keta zarya akan fuskarta, bakinta rawa yake tace,
“wallahi Abbu ba laifina bane wannan Karon, Yaron gidan Alhaji garba ne duk sanda nake rubuta exam d’ina sai yayita copying d’in nawa, nace masa yadaina yak’iya har yaja Anty cire mani rabin mark d’ina,kuma duk sanda na hana shi Idan akai break sai ya d’aukar school bag Ya sace mani books,ya yaga ko nakai shi k’ara ni ake duka……..ta fashe da kuka.”
Taba kowa tausayi wajen shiyasa Areef ya ki hukuntata ba, yace zaije yaga principal d’insu idan akai hutu.
“salamatuna ingani naki nasan bazan samu matsala dake ba.”
Jikinta duk yai la,asar saboda tana gudun atab’amata y’ar uwarta.
“Aaaaaa Lallai salamena irin wannan cinyewa haka, gaskiya kin cancanci rakiyar yayanku zuwa UK…….kagani Areef wallahi result din yayi kyau sosai, itace overalls d’insu duk term wallahi naji dadi.”
Ansa yayi yana k’ayataccen murmushi wanda daka gani Kasan yana cikin farinciki,jinjina kai yayi yace,
“please don Allah Mu bata clap.”
Aikuwa duk aka tab’a mata Amman banda ni saboda bana cikin ma hayyacina,saida naji yace man.
“ke ba zaki tab’a ba ko,oya clap for her.”
Jikina yana rawa na tab’a mata.
Abbu yace na bashi nau, Nayi fik’ik’i ina raba idon wanda har kwalla sun fara zaryar Su, Maah ce tace,
“wallahi Khairat ko kukan jini zakiyi sai kin fiddo result din nan idan ba haka ba, wallahi kashin tsiya yayanku zai baki.”
kuka na fashe da shi nace,
“Maah bafa abani bah formerster d’in mu ne yace Idan andawo hutu zai duba Mani nawa.”
Dariya duk suka saka mani banda shi da salma, Wanda ita jitake kamar ta tayani kukan, shikuwa bazan iya sanin meke zuciyarsa ba lokacin.
Abbu yace,
” ta Alkhairi,kinga dai nan babu abokin wasanki ko, to bani.”
Ya mik’amata hanunsa ta bashi Amman saboda taurin kai Irin nawa gashi fah ga hannuna cikin hijab, Amman na k’i fiddo wa…….sai sharab’en majina da hawaye nake ai kawai jinai an kasheni da wani zazzafan mari,cikin kakkausar muryarsa yace,
“bani”
hannuna alokacin wata irin karkarwa yake haka na fiddo shi cikin hijab d’ina na bashi, duk ya jik’e da zufah………fizga yayi ya mik’ama Abbu.
Salma kuka take tayani wanda ni jinai kamar andauke nawa,ashe kuka ma rahma ne don har kwallah din sun k’afe………sai zuciyata dake wani irin masifar zafi, ga masassarar ta sake rufeni dan danan idona ya fara dishi dishi,don banajin ma abunda Abbu yake fad’a sosai.
“kin bani kunya ta Alkhairi,ina yabonki sallah Amman kin kasa Alwallah ban sanki da haka ba, kina yo first position duk term d’in duniya, Amman wannan Karon kirasa ko na nawa zakiyi sai second to d last………banji dadi ba wallahi ko kad’an banji dad’in haka ba,shiyasa sukai maki repiting abun kunya tun kuna keji da yar uwarki kuke class mate d’in juna gashinan zatai gaba tabarki,anshi nan Areef duk hukuncin da ka ga yadace da ita kayi mata.”
Tashi yayi yabar shige bed room d’insa,
Maah ta rufa masa baya.
Anni tace,
“Areef karkai saurin yanke mata hukunci ka tambayeta damuwarta, wata kila akwai abunda ya faru,yaro mai hazak’a kullum don ya fad’i irin haka bincika ake bawai hukunci bah nidai shawarar da zan baka kenan.”
Mujahid yace,
“haka ne Anni tunda Kinga meenah ma tayi bayanin abunda yasa hakan ta kasance.”
salma ta rungumeni tana kuka sai lokacin nawa ya dawo, babu sauti saidai kwalla dake kwarara, da shashshekar kukan.
haka kowa ya kwatse yabarmu nan nidashi da salma, mik’ewa yayi yace musamai d’akinsa.
Haka muka rufa masa baya salma kamar itace tayi laifin.
Koda muka shiga yana kan one seater Ya mikar da kvafafunsa kan table, idonsa arufe, salma ce tace gamu yah.
bud’e idonsa yayi Sunyi fitinennen jaa ko na Miye oho.
Banzan iya kallon sa ba wanda nasan ni yake kallo, naki d’ago idona,ya maida Kallonsa ga salma yace Cikin muryarsa ta sauko ba kamar d’axun ba.