ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

“Shikenan kije kishirya lokaci na tafiya,kardai ki manta da zuwa wajen umminki.”
Dariya nai knacewa “insha Allah maah.”
Karfe takes da rabi dr yazo nan yayi break,yanata jan yah meenah wai ta kusan tsufa agida……..gardai ayi bikin itama tatare gidanta tana cinyewa su abbu abinci,dariya ta kamayi harda salmar aka rakamu airport duk sai naji kewarsu……rungume juna mukai muna share kwallah,aka kiramu muka shige.
Sai birnin london ta alkhairin Abbu.
mrs bb ce ????????????????????
????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA
Writing by mrs bb
Mom muhseen.
Wattpad name
Humaira7531.
DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.
ABOUL-NASSER (ALFAH) COMING SOON INSHA ALLAH.
FATAN ZAKU JIRAYE SA NAN BADA JIMA WABA INSHA ALLAH.????????????
GODIYATA BATA DA IYAKA GAREKU FANS BANSON HAKA KUKE SONABA,ALLAH YABAR MUNKU LOV U ALL.
????????????????????????????????
Not edited.
38&39.
Waje na samu na zauna inajin kafafuna baza su iya daukata no ba,banson had’uwarmu banso ko kadan,shiyasa tun farko naso bujirewa maah badan banson zuwa wajen ummin ba,saidon gudun irin hakan jikina rawa yake saboda wata irin yunwa da nakeji………youghout ko ice cream kurun nake son sha don sune kayan shana bana iya cin komi har gara cake amman ban dashi saifa kayan zak’i.
Wayata na sake dauka in kira ummin in roketa taturo man yah imran din………..saidai wata tsaleliyar mota data shigo ta shagaltar dani,farace k’al tayi masifar yin kyau dagani new modan ce.
Fasa kiran nai na zuba ma motar ido inson ganin waye ciki,zuwa wani lokaci na hango wani mutun yana nufo inda nake,hankalina yatashi ainun.
Tashi nai na fara neman guduwa don wallah mutumen ma ni tsoro yakeban,gashi dai gabjeje kuma baki kamar dai dan africa.
Ganin zan ruga mai yakara sauri nima na kara nawa saurin ina jin kamar zan saki fitsari,,,,,nayi wata irin zufa addua kurun nake ina rokon Allah ya tai makeni………jinai na karo da mutun dagowar da zan ashe mutumen nan ne wata kara na fasa na ina kwasa wa aguje……..ninai kurun anfizogoni anjefa cikin mota…….duk na gigice jikina tsuma kurun yake…….figar motar akai kamar zamu tashi sama muka bar fikin jirgin.
Saida mukai nisa sannan na dawo cikin hayya cina na tuna ban kwaso akutunana ba,cikin tashin hankalii nace.
“Driver wait na manto jakunkuna na filin jirgin don Allah kamai dani na dauko.”
Kamar daga sama naji muryannan da ko doguwar suma nai zan ganeta,saidai wannan ta shabanban da wadda na sani watannin baya,,,,wanan kamar an kara mata suger muryar jinake har sino take fitarwa don tsananin sanyi da zak’i.
“Uban waye drivernki.”
Shiru nai don tabbatar da shine naji zafi zagin,rabon da azagan harna manta dama shine keda sana,ar zagin to tunda yatai ban sakejin wandanyace don ubanki ko dan uwarkiba……….shiru nai na hkr nasan dai nayi asara don duk kayana dana siyo nawa dana tsarabar da zan koma dasu suna can cikin jakunkunan,…….har mukaje bakina bai sake maganaba illa skakar kamshin dake gauraye da motar danake inajin dadinsa,tunda nafara laulayi bayan kamshin turaten Dr babu wani turare da yadauki hankalina irin wannan danake shak’a, bazan iya tantance nashine ba ko na motar ba…….zanso insani………idona rufe yake banma kallonsa balle har nasaka ma raina wani abu tafiya ce maidan nisa mukai kafin muka isa,rabona da Dubai tun na gama primary nazo nai hutun wata biyu daganan sai fa yau,duk garin ya canza man ansake samun cigaba ta ko ina……..har naso inzama bakyauya duk da dai naje knda yafi nan din kyau datsari………
“Kina iya fitowa.”
Yafice yabarni tsaye bin bayansa nai da kallo mamaki ya cikani,kayana nagani zube ya fiddo daga but koyaushe aka saka su oho.
Ummi da Mimi da sadam suka iso suna man oyoyo sai na manta da bacin raina na rungume ummi ina murna nima,mimi da sadam suka kwaso mun kayana muka k’arasa ciki.
***********
Zuwaa dabai wani canjin yana yine gareni,tunda ummi tagane inda ciki ta shagwab’ani,sai abunda nace inso zanci,tunda Allah yasa yah Areef ya ajiyeni ranar dana zo ban sake ganin saba, sai bayan kwana biyu shima kuma a daining muka had’u na gaidashi ko kallona baiba bakke ya ansa,raina yayi babu dadi ai tunanina yanzu babu sauran takun sak’a,sai yasaki ranshi muyi zumunci,Amman duk wannan bobbotan ban san ko nameye bah……..har mimi tasan banji dadi ba ina daki mun gama waya da Dr yace daya gama abunda yake zai iso mukoma.
“Nazo ma dad I yya inba yar da hkr.”
Harara na banka mata na juya ina danna wayata waje ta samu tana cewa,
“Bari Kik dalilin jin haushinki da yake,duk baki son sani.”
Yinai kamar banson me take cewa ba amman kuma nan kunnena na saurarenta.
“Tunda yah yadawo daga bikinku kwance yake khairat,aikin da yazo yi saidai wani yake ashi shi,yafi wata asibiti anrasa gano kanshi…..yau sauki gobe ciwo,duk ya tashi hankulan mu Abbi kanshi kamar ya zauce akan ciwonsa,ummi kam wani sa in kuka take mashi akan ya tausaya masu yayi hkr da kaddara ita tasan duk dan bai sameki bane,to kanshi farau rashin masoyiya……wasu ma iyayensu suke rasawa duniya gaba daya sukuma hkr balleshi don kawai baisamu wacce yake so ba,to ita dayake tana jin maganar iyayanta kuma ta yarda da kaddara mai kyau da marar kyau ai gashi can tana zaune gidan mijinta lafiya lau bata dorama kanta wannan masifar ba,saikai kana namiji kakasa jurewa.
Banga anfanin kasancewarka namijiba Areef.
tunda har baka iya sadaukar da soyayyarka ga waninka,to ko kaki ko kaso khairat dai ta haramta gareka,kuma har abadan bazaka sameta ba,don ina mata fatan kasancewa da mijinta har karshen rayuwarta,don kuwa mijinta yafika sonta idan zaka tashi ka fuskanci gabanka to idan kuma nan zakai ta kwanciya bismillah ga wajenan iyaka abincine in daho inba kanwarka ta kawo maka, da kaci da karka ci uwarsu daya ubansu daya,wahalalle kawai.”
“Gaban yah jahid lokacin ya biyo shi shima zaiyyi wani aiki nan,ina gefe nima duk ummi take fadar wadannan maganganun,koda na kalli fuskar yah wallahi khairat kuka yake amman babu sati saidai hawaye dake zuba,fita nai inbasu waje don naga yah jahid yana son magana dashi………dama ummi tana gama fadan ta tafice rai b’ace.
Ina jikin k’ofar naji yah jahid yana lalashinsa,yana cewa,
“Areef ya kamata ka tashi hakanan,duk abunda ummi ta fad’a gaskiyane kaifa namijine kaine yadace ace kana yin juriyar da khairat keyi,barifa kaji itama fa badan tan soba,bata da yadda ta iya ne dasu Abbu……..”karya take jahid bata sona shi take so.ya katseshi da fadar haka.
Murmushi yayi yace”kishinka bazai barka kayarda da haka ba,amman kasani itama tana cikin irin wannan halin,tadai fika juriya ne.”
Wannan maganar ta sake har zuka yaya yace”shikenan aina an fad’a hakaan nai aka alkawarin baza sake kwaniya aka rashinta ba,ama abu guda da zakai mun shine kasanar dasu kar wanda ya sake anbata mun sunan ta gabana,,,,idan ba haka ba zasu neman su rasa,naji ma ni duk natsaneta wallahi banson maganinta yanzu,…..
Tun daga lokacin yah yadawo kamar bai taba ciwo ba arayuwa,saidai lokaci lokaci zaisha mgani saboda ciwon zuciyarsa…….ranar da kikazo dana sanar dashi ummi tace yaje yadauko ki kinga yadda ya har zuko man kamar zai makeni,aguje nabar wajen nai zaton bazai jeba sai muka ga yadawo tare dake…….tun daga ranar baya zama gia saidai gida uncle jabir (kanen su maah ne shine autansu shima baitab’a haihuwa ba)kinji haushinki da yakeji .”
Tsaki naja nace”ya dade baiji haushina ba angaya mashi ni tashi nake, ni ko tunashi banyi kimaji in gaya maki.”
Dariya tayi tana cewa”eh gaskiya ne naga alama. haba mata wazaki maida shashasha kawaidai kina waskewa ne saboda kina da aure nima kuma zanso kina yin hakan,yadda yake shareki baya ansa gaisuwarki kema kibar gaidashin,hakan zai bashi haushi,saboda ke duk yazama dan bala,i wlh.”
Dariya nai nace”dama shine wlh dama fitinannene ne,saidai kice karuwa yayi ninan nizan gaya maki masifarshi wlh.
Gyara kwanciya nai ina sake cewa”inyayi hkr na kusan tafiya don ma ummin tace saina k’ara sati wlh da da dr yazo zanbi mijina inkoma.”
“To masu miji muma dai ai mun kusan yin auren adaina mana gori harda goruba.”
Dariya nai mata mukahau wata hirar.