ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Yau mukai da Dr zaizo ya ganni jibi mu koma ban ma gaya mashi cewar ummi ta kara man kwanaki ba ,sai yazo inyi maganar gabanta don daker zai yarda amman idan tasa baki zai barni.
Don nima ba son zaman nake ba don duk nima naji yasire man kamar yadda yace ya tsaeni yanzu,harma ni zaice ya tsana lallai ma koda yake kodacan ai haka yake nuna wa,ni baitab’a nuna man alamar yana sona ba inba ranar da zai bar garin ba.
Ummi bata nan tun safe ta fita tace sai yamma zata dawo,bata son dr yazo bata nan kar ya daukeni yace zaigudu dani bamuyi bankwana ba daroya duk mukai nida mimi.
Yah imran ne yakaita
Nida mimi muka shiga kitchen muna hada ma Dr abunda zaici idan yazo,kasamcewar mimi badai iya girkiba don du itatyi wasu abubuwan,ina dai taya tane………juice kurun na had’a na kai frig din karamin falonsu.
Harda wani sweet cake tayi mashi,tace sairayinta Abukhalipa yana masifar sonsa wani irin cake ne yasha cream asamanshi,tace a frig take sashI sai yazo ma take fiddoshi don karyayi melting…..naji dadin sa sosai don saida naci miyauna kamar yayi tsartuwa.nasan kuma Dr zaiso shi duk na k’agu ya iso na yi kewarsa sosai.
Shima ga frig din na kaishi sanan nawuce nayi wanka,yanu banson yin kwalliya don ko kadan bansonta, saboda cikin anan doguwar rigace mai kama da jallabiya Dr ya zabo mansu da mukaje saudiyya red ce sai kwalliyar golding tun daga sama har k’asa,ta fitar da shaf dina ga dan cikina yafito d’an wata biyar,zari ido nai ganin yadda rigar tayi masifar daukata,ta fiddoni sosai,don yanzu nayi wani irin haske ga hutu ga ciki,har wani daukar ido nake,daman bana saka komi ga fuskar sai farar power da liptis saboda bushewar baki,amman duk dahak nai kyau sai murmushi nake,sanan Dr idan yaganni kilan gaban ummin zai daukeni ya rungume.,don shi kunya ba isar sa tayi ba bana saka turare tunda na samu cikin nan saidai yar sure danake goga ma anfit dina da matse matsina saboda smeling.
Fitowa nai da sauri don dauko wayata dake falo naji kamar sadam yana kwalan kira anan kirana,
Sauri sauri haka nakeyi inje ga wayar nason Dr ne yaketa kira kilan ya iso aje adauko shi,,,,,jinai kaina da kirjina sunbugi abuu bansan nace washhh Allah na tsaki naja nawuce do k’amshinsa kadai ya isa yaga yan waye yashigo.
Mikoman wayar yayi yana cewa “Number Dr ne sai kira ake.”
Ansa nai ina wucewa karamin falo don induba abunda nasaka ko yayi sanyi yadda nakeso,ina tafiya ina duba wayar kiransa nakeson inyi still yanzu ma karon mukai sosai,har wayar ta silale kasa ta fad’i………..wani kululu yazo ya tokare man wuya duk yadda na tsani kwayar idona ta kallai doke tasaka na zuba mai idanuna dasuka fito waje dukansu,,,,har wata ruwan kwallah naji suntaru acikin su bakina naji yana fada cikin jin haushi.
“Wai meye hakane ehy d’azu kabanke ni na kyale nai hkr yanzu ma kuma haka gashi kafasan waya mijina sai kirana yake yaz………..”shut up stupid girl”
Sake dalalo idona nai ina kallonsa tuni kwallah sun cika idon tab,nace”ni ……nice stupid…..ni…cikin tsawa yace “eh kedin! ba stupid din bace,kina tafiya kamar makauniya bakya kallon gabanki,,,comon ban waje nawuce nonsence…..”
WanI malolon kunci da bak’in ciki suka cika man zuciya…..kafin nayi magana ya janyeni gefe ya wurgar,bacin bango danai saurin dafewa da sai dai kan cikina zan fad’a………durkushewa nai ina kuka bak’in ciki rabona da kuka bazan iya tuna waba…..mimi ta karaso cikin sauri.
“Subhanallahi khairat lafiya,meyafaru mekikamai.”
“Mefa me zan mashi kawai zalincine da kuma daman jirana yake….banka ta fa yayi har saubiyu danme zanyi magana kina gani nan kadan ya hana bai turani k’asa ba da kan cikina zan fad’a……hakri taban taa tattara man wayata da ta tashi aiki,sim dina nacire na saka cikin wayar mimi nashiga kiran dr amman ban samu ba,kuka na kubce dashi yanzu haka akwai abunda zai ce man gashi nan yayi man sanadin rashin samunsa……..koda ummi ta dawo banji ko dar ba na gaya mata ai kuwa ta hau balbalin bala,i kamar zata ari baki…..sadda ya dawo daddare har lokacin wayar Dr bansamu ba,,,duk nashiga halin damuwa ko yana ina ya iso bai iso ba ina ya taya oho…..ina kwance kan cinyarta idona saboda kuka har yayi fushi….koda ya shigo shida imran suna hirar kwallon k’afa ummi tabishi da harara baisan ma tanayi ba,
Imran ya wuce dakinsu shikuma ya wuce karamin falo…..inanan kwance kamar ance dago ki kalli can dagowar dazanyi na hangoshi ya dauko wannan sweet cake d’in ya yanko kusan rabinshi kan plet,ga spoon dinsa yana yankowa yana saka wa baki…..kamar anzungura man Allura na tashi afirgice na nufi wajen da yake……
Tun kan na isa inda yake yasha mur kamar bai tab’a dariya ba,yace”ke….. kee…….karki sake ki iso maninan,wai bakida hankaline “ina zuwa na kab’ar da plet din ina hawaye nace”Wallahi da kacishi gara ya b’are ai bakai akaima wahalar ba,na rantse kuwa kozai tsutsa da hunhuna inhar wanda naimawa mijina baici ba kaima kuwa bazaka tab’acin sa ba…….”keee…………ni ….nikike gaya ma magana,don kinga ina ragar maki,zan daukeki da mari awajennan……..”ummi tace da kuwa baka kara marin wata mace ba aduniya Ashe baka da hankali Areef,yarinyar da ciki kakeson kassarawa,oh abunda kayi mata d’azun bai ishekaba yanzu ma gabana kake kirarin zaka kwad’amata mari,to kafara dani kafin ka yi mata nata.”
Juyawa yai yashege b’angarensu cike da b’acin rai……lallashina taitayi tana ban baki,har nahkr daker nasha maltina da cake din na wuce daki nai sallar mangaruba na kwanta,wayar nake kallo inajin kirjina yana dukan tara tara hankalina ya gaza kwanciya ……me yafaru da Dr na hawaye suka silalo man,,,jinai kawai zuciyata tana karkarwa dandanan jikina yafar daukar wani fitinannan zafi…..mimice tashigo “Khairat ga wayar kisake jaraba kiransa ko za,adace saurin tashi nai don inaji ajikina zan sameshi insha Allah…..hannuna har wata karkarwa yake ina danna kiran,jinginanai inajin yadda zuciyata take duka jinai kurun kiran yashiga………kafin bakina yaimagana naji wata murya bansanta ba tana cewa MAI WAYAR GASHINAN ASIBITI SUNYI HAD’ARI KUYI SAURI KUZO YANA GAF DA RASUWA.
wata k’ara na fasa wadda tasani rugawa ni ma don kunnena fashewa zaiyyi………
Mrs Bb Ce
Mom muhseen.
09034722970
[6/27, 9:41 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA
Writing by mrs bb
Mom muhseen.
Wattpad name
Humaira7531.
DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.
_ABDOUL-NASSER (ALFAH) COMING SOON INSHA ALLAH,NASAN ZAKU NISHAD’ANTU DASHI KUCIGABA DA TSUMAYINSA SOON INSHA ALLAH.
KUYI HKR KWANA BIYU KUNJINI SHIRU WLH JIKINE BANJIN DADINSA FATAN ZAKUYI MAN UZIRI,ALLAH YAYI MAKU ALBARKA YA KUMA BIYA MAKI BUKATUNKU NA ALKAIRI AMEEN INA SONKU IRIN BABU IYAKAR NAN.????????????????????????????????????????
Not edited
40.
Wannan karar dana fasa yasaka gaba d’ayan su kuka runtumo aguje gareni,shashsheka nake ina dafe da cikina da ya wani irin juyawa…………nishi kurun nake hawaye jage jage suna bin fuskata…….mimi ce a rikece ta d’agoni “kharat lfy maya faru ina Dr bai zo bane ina yasauka me yace maki.”
Cikin tashin hankali na dago nakaleta n kalli ummi nace”ummi……..numfashina yayi sama kamar zai dauke daker nace……”yana asibiti hatsari sukai sunce muje da sauri yana gaf da rasuw………….ban k’arasa maganar ba numfashina ya fizga suduka duk sun gigice afirgice imran yashigo yana tambayar lafiya,,,,,,,”imran maza maza fiddo mota Dr yayi hatsari wane asibiti yace ankaishi khairat ki natsu mimi dauko mata ruwa tasha.”