ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

baisake komawa ba wanka yayi yafice office don yana da aiki sosai,hankalinsa kwata kwata yana kan khairat,don ya tsorata sosai ganin halin da take ciki dazun.
Duk da irin yadda jikinsa ke tsananin ciwo kuwa,don yasha damk’a bakad’anba kafad’unsa kamar yaji targad’e da cinyoyinsa,daker ya iya tuka kanshi ga bacci cike da idonsa amman sanin ayyukan dole yayisu yau yasa ya hkr ya tafi.
*********
Kwanana biyu asibitin,sabida jinina daya hau don mutuwar jaririyar ta kasa barina,nasha kuka sosai saida naga b’acin ran Abbu sannan nayi shiru na hkr nabar kukan gaban mutane amman dana kadaice sainayi,saboda yadda naso ace naci kawa dr alkawarinsa na mallaka ma umminsa guda,yanzu ya zataji babu dai kokadan.
Nai mamakin rashin dawowar yah Areef,saibaza ido nake inga yazo har aka sallame mu baizoba,sanda mukazo gida angyara mana d’aki guda nida babyna,salma kamar ta had’iyae babyn,itadasu mimi sai nan nan suke da ita,yah meenah kuwa tani take sai sannu takeman.
Ranar umminsu tazo kasancewar batanan randa na haihu,rungumeta nai ina kuka nace”ummi kiyi hkr naso ace baby ta rayu nabaki ita,kiringa ganin jinin dr kina tunawa dashi,saidai kashh Bansan meyasa ubangiji ya ansheta ba ………kiyi hkr plssss.”
Lallashina take itama tana goge kwallah tace babu komi wannan ma Ta wadatar uabngiji yayi mata albarka,yakuma rayata yasaka tayo halin mahaifinta.
Ranar nayi kuka saboda tunawa da mijina nai mashi addua sosai tare da abunda nahaifa,wata irin kaunace nakemata nan take Abbu yayi mata huduba da sunan ummin dr watau maryam aikuwa ba karamin dadi tajiba don hada kwallarta taita sunbatar babyn tana hawaye,kafin tatai nace saita fadi nickname din daza ringa fadamata daker da sidin goshi nasata tafada tace akirata da Airah sunan yayi matukar dadi saidare tatafi.
Ina tunanin ganinsa da daddare amman har wayewar gari baizoba,annie keman wankan jego intayi mata shagwaba.
Airah kuwa ummi ke mata kusan kwana hudu kenan,duk wanda yakamata yasan anyi haihuwar angaya mashi,husna kullum tanan saidare yah shahid ya maidata.
Ina zaune falo inata kuka saboda ummi ta tsareni sananba Airah nono,nikuma zafin danakeji yasa nace nidai aa,shine ta ulaman bulala dole nabata ina hawaye itakuwa tsotsa kirun take kamar Allah ya aikota…….kamar ance na kalli kcofar shigowa naganshi yana murmushi,bayansa wata budurwace fara tas kamar zabaya,tasha gayu kamar zata zab’en sarauniyar kyau,babu karya akwai kyau jinai kirjina yabuga.
Pls share it.
Mrs bb ce
Mom muhseen.
Follow me on watt pad Humaira7531. And my what’s app no 09034722970
[7/5, 7:12 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA
Writing by mrs bb
Mom muhseen.
Wattpad name
Humaira7531.
DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.
46.
Wani kullutune ya tsaya man ga mak’oshi,daker nake had’iye miyau,banma lura ba ga hanci na keta gwagwad’a mata nono,saida ummi ta kaimin duka ga baya”don ubanki kasheta zakiyi ki kalli gabanki.”
Sai sannan naja numfashi sannan na maida hankalina kan Airah,amman badan ina cikin natsuwata ba. gaishe da mutanen wajen tayi,tana gaida su ummi cike da kunya.
Annie saijanta take wai amarya bata yawo,kartayi bak’i,basusan wadannan kalaman jinsu nake kamar wuta.mimi ce ta kawo mata lemu da snacks,suna ta janta da hira harda salma,kmar na kamasu da duka haka nakeji.
Kusadani yazo ya zauna yana danna waya,dama tuni su ummi sun koma ciki,Airah baci tayi ysa na maida nono na ina rik’e da ita ga hannun.
“Oum Airah ga zulfa,a tazo ganin baby baku gaisaba,saida nayi daker na fizgo murmushin da iyakarshi kan lab’b’ana,nace.
“Sannu da zuwa.”
Tana murmushi itama tace”barka khairat Allah ya raya Airah.”
Daker nake magana “ngd sosai ga tanan,na mik’ama shi ita yabata sai kokarin ganin yasaka idonsa anau yake nak’iya,.ansarta tayi tana yabawa da kyanta don Airah abun biyu ya hade mata,don dr kyakkyawane sosai haka nima badon yaban kaiba,nasan im beautiful more.
Hirar su suke kamar sun saba da ita,salma damar gwanar surutu.
Husna ta fito daga ciki tayo sallar laasar suka gaisa ta zauna gefena tana mun rad’a.
“Waccen ce kishiyar taki.”
Tureta nai ina banka mata harara nace”banson iskanci,karki sake mun haka don’t like.”
Dari ya tayi tana rufe baki duk yana kallonmu yace mata,
“Husna gulma ko,mekuke cewa.”
Sanin danai husna ba karamin aikinta bane ta fadi abunda tace yasa na tashi zanbar wajen,naji bakuwar nacewa”ansheta khairat wucewa ma zanyi wlh inason zuwa saloon,saimun dawo suna.”
Cikin rashin walwala nace”bawa mimi ta goyata zanje na kwanta inajin bacci,kigaida gida mungode.”
Nayi wucewa ta shiya tashi ya rakata tayiwa su ummi sallama,sannan suka fita ya maidata.
Gaba d’aya hankalinsa yana kanta sauri kawai yake ya dawo yaje gareta,duk da baisan me zaice mata ba,amman yanada bukatar magana da ita yayi tsananin missing ganinta kwana biyar,sadda yashigo get di n anata kiran sallar isha,i dole tafito yadauki buta wajen maigdi yayi Alwallah yashige masallaci.
Yau wankan magaruba mukai,don fitowa ta kenan ba adora ruwan da wuri bane shiyasa.
Ina daure da towel ina goge jikina da wani,ummi kuma nayiwa Airah wanka sai kuka take,ummi na mata tsiya wai raguwa…..dariya nake masu na zauna ina shafa mai harta gama mata sannan ta mik’omun ita.
“Anshinan kinji ko mijina nacan najirana kina iya shiryata.”
Shagwabe fuska nai nace”wayyo ummi wlh ni ban iyaba kar nakarya mata hannu,plss ki idasa ladarki shima dadyn ai bazai ce komi ba inkikace Amaryarsa kika yiwa shiri.”
Hararar wasa tayi man tace”zan makeki wlh nikadaice ga mijina har abadan,don haka inma baki iyaba ki koya,kinjama daga yau kece mai shiryata,nan gaba ma wankan ke zaki ringa mata.”ficewa tayi tabarmu murmushi nai ina daukota inajin wata irin kaunarta cikin raina,
“Kinji wai sweetie,ummi kishi take da ke karki anshe mata miji,kyaleta haushi takeji kinfita kyau.”
Na sunbaci goshinta ina dariya kamar almara itama tayi dariyar,nanfa naita dariya ina biye mata kamar zararrah.
Riga na dauko ta bacci na zira sannan na dawo ina shafa mata mai,kamar ina tsoranta haka nake shafa mata shi.
Bayan dawowar sa masallaci ya zube falo duk hira ake,ana kallo dan zauna wa yayi ya lumshe idonsa yana sauraren bugun xuciyarsa,yunwa yakeji amman son ganinsu itada baby ya danne yunwar………Annie tace “kana lafiya kuwa Areef.”
Idona ya danyi ja yace “ba komi kaina ke ciwo.”
“Ayya sannu kaci abinci kasha magani.”
Tashi yayi nufi cikin gidan karo sukai da salma tace”sorry yah ban ganiba,”
“Ba komi ina khairat.”
“Suna daki tana shirya baby Airah.”
Wucewa yai itama ta wuce sadda ya tsaya bakin kofar jiyai numfashinsa yana d’agawa,runtse ido yayi ya bude sannan ya shiga da sallama.
Tun d’azu nake son saka mata kayan na kasa,daker nasa mata pant.
Waigowa nai jin motsi wajen kofa………wani irin dokawa gabana yayi dandanan nad’an sha mur kadan,na ansa ciki ciki.
Isowa yayi ya tsaya bayana yana kallon mu sai jagwalgwala ta nake,me zatai ba kuka ba ni duk na rikice tunda yashigo,nama rasa me zanmata.
Jinai kurun ya sunkuyo ta bayana ya anshi rigar,sannan ya dawo gabanmu ya zauna daukarta yayi yana cewa”sorry my angel,ur mom she do not know yadda zata saka maki kaya gashinan duk ta karairaya maki hannuwa badole kiyi kuka ba.”
Kirjina ya bada rass jin yace na karyata,cikin rudewa nace”dagaske najimata ciwo,wlh ban saniba ummi ce tace dole saina saka mata,wlh kuma ban iyaba.”sai hawaye sharrrrr “donAllah mukaita asibiti,aduba karta mutu itama.”
Ina kukana ina kallon yadda take shashsheka.
Murmushi yayi yace”ruwa ruwa to wasa nake,saiki goge hawayen.”
Wata ajiyar xuciya nayi nace”ina sonta banson ta mutune kamar dayar.”