ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Ajiyar zuciya Abbu ya sauke yana kallonta cikin kallon tuhuma alamun ransa ya baci,
“Kin kyau ta saudah,yanzu da kanki zaki jefa wannan baiwar Allah kuka kijefata cikin kunci da damuwa,bacin wadda take ciki.shin kokin mance lalurarta ne saboda wani dalili can naki nabanza zaki ta kura ta,shin haramunne don ta so Areef,koko shi haramunne don y sota.kinsan dalilin ubangiji daya d’auke mijinta,kikasan hikimarsa nayi imanin saboda khairat rabon Areef ce shiyasa ya dauke mijinta,don shi yasameta.
Kifita sabgar Allah kifita lamarin ubangiji,kebaki isa kihana ba haka baki isa kisaba,don sai Allah yanuna maki ikonsa,babu ruwanki daga yau namaki hani da shiga tsakaninsu.”
Maah cikin b’acin rai tace”yallab’ai ni ban isa shiga tsakaninsu ba,akwai abunda ya tunzurani har nake mata haka don tasama ranta babu ita babushi”
Wani kallo yayi mata yace”mekike nufi inajinki.”
“Tun ranar dasukai hayaniya ita dashi Areef din,yaya ranta ya b’aci don tazo har d’aki ta sameni,cewa wai me khairat take nufi tana nufin har gobe tana kan bakata na son Areef,to ingar gad’eta don anriga angama komi kan batun auresa,kuma babu mai hana wannan auren na Areef,don tunda zulfa,a taga areef a UK take ma sonsa,kasancewar mahaifiyarta tasan ummin,sai tayi mta waya kancewar aikuwa yarta taga Areef ta haukace kanshi,babu wani jayayya tace insha Allah saiya aureta,mafarin taita taimakawa wajen ganin khairat bata auri Areef ba tun wancen karon.
Saboda taja mashi kunne kuma nima ta kalailameni da kalamanta har nayarda da ita.to shinefa ta sake jaddadaman cewar mai hana aurensa da zulfa,a sai Allah inmata magana ta rike jawarcinta………wannan abun shine yafi komi yiman ciwo yallabai,ashe har yaya hafsa zata ki jinina saboda wani abun duniya,ciki daya muka fito amman ta ki diyata da d’anta,taya kake ganin zanji dadi hawaye suka cika idonta tab……..sharewa tayi yayinda nima nawa kukan ya k’aru tace”wlh zanyi farincikin aurensu domin dukansu nice na renesu nasan halin kowa,amman taya kake tunanin zan yarda khairat ta cigaba da nacewa kan haka,dole tasa nayi mata haka badan komiba,kayi hkr banyi nufin b’ata ranka ba.”
Rarrafowa nai na rike kafafunta ina kuka sosai nace”maah kiyi hkr don Allah kiyi hkr wlh tallahi zan goyi bayanki,nima na janye daga kan maganarsa,dama kuma ba kulasa nakeba bazan taba aurensa ba,inacin mutuwa mai tonan asiri taya zan kasance haka,,,,,,nacigaba da kukana.
Shiru yayi yana auna maganganun da ta gaya mashi,tabbas baiga laifinta ba domin kuwa ba neman kai suke da khairat ba,abune na gida wnda idan akayi kowa ziyyi farinciki,amman tunda hakane abarshi ahakan……..
“Ta Alkairina,kinji duk bayanan mahaifiyarki,don haka banda abun cewa daya wuce kiyi hkr kibar komi hannun Allah,insha Allah zai kawo maki wani wnda zakiyi farinciki fiyeda tunaninki,fatana kiyi man Alkawarin kiyaue dokokin Allah,kifita sabgarsa tunda daman kince baki kulasa,to atai ahaka inso samuna ne kitai waje ki idasa karatunki.”
“Aa abbu zanso in zauna kusada ku,nai maka alkawarin kiyaye duk abunda kace.”
“Masha Allah haka akeso,Allah yayi maki Albarka.”
Nace”Ameen Abbu ngd,maah kiyi hkr kiyafe man don Allah banajin dadin yadda kike man kihi hkr pls.”
“Babu komi ya wuce kidai kiyaye,don zamu sab’a inhar nasake ganin wata hudda ta hadaki dashi,kina iya tafiya.”
Natashi na dawo cikin gida ina wondering halin ummi,lallai mutun ba abun yarda bane,taban mamaki banyi tunanin haka daga gareta ba.
*********
Shirye shiryen biki ake bakama hannun yaro,don ankai lefen yah shahid gidan su husna,ankuma anshi na yah meenah itada yah harun,dayake bayan da wowarmu daga dubai ya koma saboda aikinsa,amman tare zasu dawo da yah Areef.
Hidima ta nake kamar babu wani abu cikin raina,nan kuwa karkaso ka bincika karfin haline kurin da juriya.
Shima ankai nashi lefen amman saboda basusan darajar mutane ba suka wulakanta y’ankai lefen,har kuka maah tayi saboda yadda aka anshi kayan cikin renuwa da wulakanci,wai ai yarsu tafi karfin wannan yame yamen.
KO zinari babu balle gwal,saikace ba yar minister kudiba,,,,,,,bayan akwati goma sha biyu haka aka cika da kaya,wanda maah saida ta cika akwati bakwai biyar ne kurin ummi tayi mashi,ita kanta ummin ta tsargu sabida yadda taga maah tayi masifar canza mata,ba kamar da suka dawo daga kai lefen taje har falonsu ta sameta tace.
“Munkai lefe yaya hafsa,ankuma wulakanta mu kamar yadda kikazata an watsamana kudin tukuici a fuska,ance gashinan suba mata lauta bane da arzikinsu idan da munsan bamuda arxikin yi mata lefen,da munfad’a bazasuji komi ba don sun ranta mana,ummi ta kadu dajin irin abunda yafaru,tana kermar murya tace”wlh saudah bansan haka sukeba……….kinsani yah hafsa,wlh kinsani aibatun yau kike tare da hajiya safara,un ba,i think tun bakiyi aureba.shine kike son ansar yarsu matsayin surikarki gidan da ba,asan drajarmu ba ba,sa kimrmuba basusa mutunci da karamciba,no problem gashinan ayi mugani,amman kisani bazan sake shiga cikin wannan hidimarba wlh tallahi kau.”
Ta juya ta fito tabarota.
Jikin ummi yayi masifar sanyi sosai,don kuwa maah tayi buris da lamarinta,duk zafin ummi da fadanta ta koma kamar ruwa yacita,maah kuwa tayi fushi sosai abunka ga wanda bai saba irin wannan fushinba…….gidan duk yazama babu dadi wajen annie kurun nakejin dadi,duk da maah din ta sauko tabar fushin dani,amman kodayaushe bata da walwala don Abunda ummi yayi mata yayi bala,in daure mata kai.
Airah tayi wayau sosai don watanta uku yanzu,dariya kamar gonar auduga wadda kuwa halin mahaifinfa,tana girma kyanta yana karuwa.
Tuni muka gama wanka Annie ce kegyarani kamar wata amarya,har kunya nakeji tace aiba dole saika tashi aureba,dole kazama cikin kulawa don kowane lokaci mijin na iya zuwa.
Jinta kurin nake don ni bawani aure dazan sake,rainon diyata ya isan da karatuna,don tuni nakoma yanzu ma IT muke nan wani private ne,wani lokacin gida nake barin Airah,don bata barina aiki idan anyi sallar azahar indawo inbata nono tasha,naba yah meenah ita don sun kammala nasu tuni,don ma tanashan priso tayi wata irin kiba gwanin sha,awa kyanta sai sake bayyana yake kowa yaganta yayita santi,gata da shiga rai,kuma bata rigima sai idan yunwa takeji ko kuma bacci.
Tunda ya tafi na sauke layin sayasanni dashi,don ma karya kirani balle wani sakonsa na banza,bawai har cikin zuciyata inajin dadin abunda nake ba,banda wani solution daya wuce haka,babu anfanin inta saurarensa inasaka kaina cikin shaukinsa,soyayyarsa mai girmace cikin zuciyata inhar inajin muryarsa,bazan iya control din mind dinaba shiyasa mafi a,ala in nisanceshi.
Agajiye na dawo yau Airah naga nina taita mik’o hannnu,hararata nai ina cewa”acici ko hutawa baki barina inyi to kwalelenki yarinya,nai mata gwalo.”
Kamar tasan menake cewa ta fashe da kuka,dariya nai zanruga mimi ta rikeni,
Annie face”wlh bakishiga saikin bata,muguwa kibar yarinyar tun safe yau ko dawowar dakike bakiyi ba,shine kuma bazaki bata hakkinta bakini tsoran Allah.”
Dariya nai ina harararta itako sai miko hannu take,
Ansarta nai mimi nacewa”Allah zai saka maki babynah.”
Yinai kamar zan maketa taisaurin matsaw.
Saida nabata sannan na mikata ga mimin nashige ciki,don tafi yarda dasu itada yah meenah da Annie.ko salma bata son taje wajenta.