ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

“Aa ta Alkhairin Abbu meke baki tsoron.”

Sake share hawayena nayi Ina cewa,
“akwai ranar da sweetheart bata je makarantar islamiya ba, malamin mu ya gama mana darasin sa akan mutanen da ya halitta ka aura, da kuma wanda bai halatta ka aura bah, ban fahimce shi sosai bah Anni sai na bari da aka tashi naje har office d’in Su nasa meshi nayi masa tambaya,

“malam don Allah ko mutun zai iya Auren yayansa wanda suka fito ciki d’aya.”

Kallona yayi yace Meyasa nai masa wannan tambayar nace,
“wata ce tace na tambayar mata Kai.”

Jinjina Kai yayi yace mun,
“Aa Khairat haramun ne babu aure tsakanin su har abadan.”

Banjira sauran bayanin sa ba na tashi na taho,
Ko drivern mu banjira ba ranar nataho ina kuka, gida ban bari ko salma tasan me yafaru bah.”

“kinsan me yasani kukan Anni.”

Kallonta take tana jinjina kaifin tunani irin na Khairat,kafi tace”Sai kin fad’aman.”

Wani kukan ya kucce mani Nace,
“Anni ba komi ne ya sani kukan bah illah yadda nakejin yah Areef acikin raina, Anni ni Yarinyace nasan da hakan, Amman nima ina mamakin yadda akai har nasan so Anni bansan tsawon lokacin da na samu kaina tsundum cikin kaunar yah Areef ba, wallahi ban saniba kuka yaci k’arfina naci gaba da cewa, wannan abun da nakeji yasa nayi ma malam tambaya, sai kuma naji cewar babu aure tsakani da shi har abadan,kinji dalilin fad’uwata jarabawa na gaza sanar da kowa saboda dai wannan Abun kunya ne awajen kowa…………kuka yaci k’arfina Anni kiyiwa Allah da manzon sa karki gaya ma kowa, don nayarda dake ke bazaki dakeni ba shiyasa na sanar dake……….”

Tabbas wannan lamarin ya hargitsa kan Anni, duk ta diririce Lallai Allah mai hikima tunda har hakan tafaru akwai abunda da Allah ya b’oye,amma Duk da haka yarinyar na buk’atar lallashi da ban baki,zatayi wannan k’ok’arin Insha Allah.

lallashina take cikin kalamai masu kwantar da hankali,tare da cewa”ki fawwala ma Allah tunda shine ya sanya maki hakan, kiyawaita sallar dare nasan ki da wannan k’ok’arin,to kici gaba sannan kiyi yak’i da zuciyarki akan shi kiringa jarumtar danne komi kikeji Akansa, Allah zai yaye maki kinjiko y’ar gidan Anni,ki rage kuka ki rage taurin kai sannan yanzu so nake ki janye daga gareshi,ban kuma ce kidaina gaidashi ba Amman kijanye mashi idan bashine yakiraki ba karkije,hakan zai saukaka maki komi kinjiko y’ar gidan Anni.”

“to Anni nah Nagode zanyi Insha Allah daman ina tsoran gaya ma wani ya bigeni shiyasa nace bari ke in gaya maki, dama na yanke shawarar janye mashi.”

Haka taita lallashina har naji duk damuwata ta ragu sosai.

Bajima wa Anty shidah ta shigo da Kayan break tayi mamakin ganina cikin walwala, har ina yimata dariya ruwan zafin Anni ta had’a ta d’age mun rigata na yi kwanciyar rufda ciki take Gasa mun, tana cewa ai dole yamaki zafi duba kiga yadda ya fasaki…….tana Cikin gasawar Ya shigo……. Lumshe idona nayi inajin dadin gasawar.

Gabansa ya fad’i duk ni nayi mata wannan dukan, innalillahi dole kiyi fushi dani sweetheart,amman afili sai dai yace mun sannu kawai, tunda nace Yawwa ban sake ko kallon shiba komi Anni tayi mun, brush da wanka ta kuma bani abinci naci, Zuwa can saiga Maah da Dadyn meenah sai Abbu, sunjima kafin Su tafi sunata tsokana ta.

Har aka sallameni ba muyi wata magana da shiba, haka muka koma gida salma sai nan nan take Dani, idone nawa kawai………….

Na warke sumul Amman na shigo da Wata sabuwar d’abia ta rashin magana, bana shiga shirgin kowa haka duk maganar da zakai mun zan tarasu in baka one ansa.

Anni ce kurun nake hira da ita ko salmar na banzatar da ita,duk Inda hankalin Areef yake yakai k’ololuwar tashi saidai duk maitarka bazaka gane halin da yake ciki bah.

Kwamci tashi ba wuya wajen Allah har Gashi jibine tafiyarsu UK………….

mom muhsen ce
Mrs bb ????????
love u fan’s ????????❤????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

5.

Hana kowa shiga akai har sai na farka daga baccin dasu kai Mani Allurarsa.

Anni aka bari wajena da Anty shahida sauran yah mujahid yakoma dasu,salma hada kukan ta bazata tafi ba saida Yah Aree yayi mata jan ido sannan.
Shima d’in bai tafin ba zamanshi yayi duk yadda Anni ke fama dashi yak’iya,dole ta kyaleshi haka sukai ta zaman zuru har ten thirty,sannan nurse din ta lek’o tace shishiga na tashi,Amman wani Cikin su yaje doctor nason ganinsa.

Areef ya tafi Anni da Anty shahida suka shiga,

Gaisawa sukai da likitan sannan ya zauna,
Bayani yayi mashi akan abunda ke damunta.
“cewa damuwa ce ta sakar mata masassara sannan da alama ma andoketa ne hada wannan dalilin yasa fever d’in tayi zafi, sannan dole akula da cin abincinta don bata cin abinci sosai,idan ba haka ba ciwon ulcer zai iya kamata, ga magani kasiya can phamercy.”

Godiya yayi mashi sannan ya fito yaje yasiyo maganin ya jiyo zuwa d’akin da aka kwantar da ita,jiya ke kamar ya kama dukan kanshi haushin kansa yakeji sosai akan abunda yayi wa sweetheart d’insa, tsoro yake kar tayi dogon fushi da shi, don yasan halinta akan rik’o…….sallama yayi Yashiga Ya ajiye magungunan gefe ya kalli Anni,

“lafiya dai ko Anni.”

“da sauk’i dai tunda muka shigo ta k’iyiwa kowa magana, sai kuka da take duk lallashin munyi Amman taki yin shiru.”

Kallona yayi nayi saurin kawar da idona, Ina shashshekar kuka k’asa_k’asa yana son lallashin ta Amman Idan ya yiwa Khairat saku saku babu tantama raini zai shiga tsakanin su, so yake ya koya mata tsoransa wanda nan gaba baza ringa yi masa taurin kai bah,ya nason bata hakuri dukan jiya da yayi mata, Amman ya girmansa zai kasance a wajenta ba makawa raina shi zatai, Wanda shi bazai so haka ba zai nuna yama manta da abunda ya faru, Shan mur yayi wanda dole idan ta ganshi haka tashiga fargaba…… Cikin dakakkar murya yace,

“jiyo nan nace.”

Jiyowar tayi gabanta na fad’uwa yace,
“goge wannan kwallar banzai, me akai maki yanzu da zaki kama yiwa mutane kuka, kin ma gaidasu tukun koko islanci ya hanaki.”

Bani kad’ai ba su kansu sunsha mamakin Areef d’in,don basu tab’a ganin yayi mana irin wannan kakkausan lafazin, sab’anin y’an kwanakin baya ko fad’a zai mana cikin taushin murya da lallashi yake yi mana, baison ma wani yaji idan kuwa d’ayan mu tana kuka kamar ya taya ta saboda baya son kukanmu,amman yau shine ke d’aga mani murya yana kwatsata dole kowa yayi mamaki katseni yayi da cewa.

“maza ki goge wannan kwallar ki gaidasu Idan kuma na dawo baki saki jikinki kamar da ba nida ke ne.”

Ya maido dubansa ga Anni yace,
“Anni bari naje na kawo maku abun break, zo muje shidah.”
sunan da shikad’ai yake ce mata kenan.

Fita sukai suka barni da Anni, matsowa tayi jikin gadon da nake ta rik’o hannun da aka cire mani drip, tana kallona kallon da ban tab’a ganin Anni tayi Mani shiba jinai tace mun.

“y’ar gidan Anni yajikin naki.”

idona ya ciko da kwalla nace,
“Anni Ina kwana.”

Murmushi tayi tace,
“lafiya lau yajikin naki.”

“da sauk’i Anni saidai inda yah ya dokeni jiya Anni ciwo yake mun ko zaki gasa mun.”

tausayi ta bata Amman ta danne bata nuna hakan sosai bah tace,
“Ayya sannu kinji bari Antynku ta kawo ruwan zafi sai agasa maki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button