ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Mrs bb ce
Mom muhseen.????????[7/10, 3:04 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

          51.

Suna nan durk’ushe suna kukan likitan Areef ya iso wajen,saurin sakin juna sukai suka mik’e jahid ne ya taresa yana tambayar ko yafarka.
“Cikin ikon Allah mun samu mun daidaita matsalar,amman gaskiya kozai farka sai nan da gobe ko cikin dare,don muna son zuciyarsa ta huce daga zafin data d’auka,don waje guda yafara kunbura.”
Zaro ido duk sukai cikin kuka ummi tace”don Allah likita katai makemu ka ceto mana shi,karya mutu donAllah karka bari yamutu.”
Annie ce tarik’ota tana cewa”haba yaya,raida mutuwa suna hannun Allah shi zamu roka ya bashi lfy,kibar cewa haka.”
Jahid yace”yanzu zamu iya ganinsa don Allah kodan musamu natsuwar zuciya.”
Jinjina kai yayi yace b komi kushiga ku ganshi amma don Allah karkuyi Abunda zai tasheshi,idan kunsan kuka zakuyi plsss karkuje.”
Ummi tai saurin share hawayenta,tace”mun daina bazauyi ba insha Allah.”
Hanyar d’akin suka nufa kowa yana saurin shiga don ganinsa……..kwance yake kan gadon,cikin awannin da basukai biyar ba ya yi wata irin rama kamar wanda ya kwana goma yana gudawa.
Ganin ummi zata fashe da kuka yasa jahid fiddata……..suma bajima suka fito maah hankalinta duk yana kan khairat,zaman zuru suka cigaba dayi har zuwa sadda su dady suka dawo daga wajen d’aurin aure.
Masha Allah an daura aure saidai muce Allah yaba ma,auratan zaman lfy cewar Abbu dake sanar dasu maah.
Likitan khairat ne yafito yace insha Allah anjima kadan zata tashi,tashiga shock ne amman dasauki jikin.
Jin haka yasa Abbu yace duk su wuce gida,abar annie wajensu kawai itada salma..ke mimi kije ki kula da Airah tunda tafi sakewa dake……..badan sun so ba duk suka juya zuwa gidan,yadda nazaci bikin zai watse sai ba haka ba gidan acike suka samai da bak’i.
Dole maah da ummi suka saka fara,ar dole kan fuskokinsu aka shiga hidima ba kama hannun yaro.

Amman duk hankulansu suna tare da yaran nasu,bayan sallar la,asar aka kawo Husna wajen ummi aka sauketa,don daman duk gidaje guda zasu zauna.
Abbu ya fidda manya kudi masu kauri ya narka masu gini na gani nafad’a,Areef ya saka yazana masu gidan kasancewar yasan hardashi yasa yafidda k’yuya yazana tsantsarere,tunda akagama gidan Kowa yaje saiyayi masifar burgeshi,an narkar da kudi don ma Areef ya kama ma Abbun aka idasashi,50/50 sukai shima daker Abbun ya amunce.
Kowace amarya cikinsu anmata jere na gani na fad’a kowace set din gado da kujeru uku uku,komidai anyishi cikin wadata iyakar karfinsu sunyiwa yaransu hidima sosai.
Wajen karfe shida na yama nafarka daga dogo baccin dana tafi,dakin nake kallo cikin dimuwa don na mance mema ya kawoni nan…….runtse idona nai ina son tunowa………jinai kaina ya sara dandanan naji wasu kalamai suna amsa kuwaa cikin kunnena.

har k’asa yah Areef ya duka yana rokonta tabarshi ya aureki amman tasa kafa ta halbeshi,gashi can anfita dashi rai hannun Allah

Cikin tsananin kara na kwala kiran yah Areef,kuka nake ina fizge drip d’in da aka saman,dirowa nai daga kan gadon daidai fitowar salma daga kewaye………da sauri ta rikoni,tana cewa”khairat ina zaki bakida lfiya fa don allah kidawo jiba fa hannunki jini yake,kincire drip d’in,nashiga uku na don allah kidawo.”
Fizgewa nai ina kuka “kibarni ki kyaleni wajen yah zanje wajensa zani zoki rakani,wlh bazan dawo ba saikin kaini wajen yah karya mutu ban ganshiba haka ma dr ya mutu bamu wani gana ba kibarni nace kibarni.”
Ita kanta salmar kuka take ganin irin wannan kauna maizafi,akullum tana mai danasanin shiga tsakaninsu da yanzu sun mance da sunyi aure,tunda itace musabbabin duk wad’annan matsalolin.likiane yashigo jin ihu sa kururuwar marar lafiar…….salma tana sha re hawaye tace”Doctor yawa gata nan wai saitaje wajen yayanmu d’ayan marar lfiyar,gashi nan har tafizge drip din hannun yana ta jini.”
“Saketa.”
Saki na tayi na ruga zan fice yyi saurin tareni yace”kinsan inda yake ne zomuje in kaiki amman ki natsu inba haka ba bazan kaiki ba.”
Share hawayena nai ina sauke numfashi yajani har d’akin dake gaba danau……baka k’ofar nai har lokacin bai farkaba Annie ce ta gama sallar mangaruba ta ganni……….ban tsaya ko inaba sai bakin gadonsa kuka ya sake kubceman,ganin yadda duk yasake lalacewa na tuna hirar mu dashi jiya.

plss babyna karki bari arabamu,zanje in samu maah in bata hkr tabarmu da juna nasan Abbu bazai zama matsala ba kamar ita,na rokeki karki gujeni inada heart attack kuskure kadan zai iya jefa rayuwata cikin hadari,kece kadai zaki iya cetona plss babyna
Wani kuka na rushe dashi ina faduwa jikin annie,
“Annie kice yatashi wlh bazan iya rabuwa dashiba,kice mai yafarka nidashi mutu karaba wlh yah inasonka bazan bari arabamu ba kaine farincikina………..”banda lallashi babu abunda annie keyi…….tashinai daga jikinta na isa wajensa na rik’e hannunsa ina hawaye,duk jini ya wanke jikina wanda kefita daga hannuna.likitan yazo ya cire nashi wanda aka sama yah Areef din yamaida shi jikina……….yace”nan kikeso ko.”
Daga kai nai ina kuka yace”to sha zamanki gaki ga shi babu mai rabaku sai allah.”
Yacewa Annie akyaleni har sadda zai tashi hakan zai taimaka wajen samun saukar jinina,don yace jinina yahau gaskiya.
Jinginanai da bangon d’akin bacci yasace ni.
Ajiyar zuciya annie tayi itada salma,
Annie tace”wannan masifa Allah yaka wo mana karshenta,yara saikace kansu farau soyayya,kijifa yadda tabi ta haukace Allah naga Abunda ya isan,wlh gara azo ayi auren nan kowa yahuta haba wannan masifa dame tai kama.”
Salma ta share hawaye tace”wlh Annie tausayi suke ban,har gobe ban daina ganin laifina inajin zafin kaina sosai akan hakan,nayi nadamar duk abunda yafaru wlh,daba danni ba duk daba haka ba dayanzu anwuce wajen.”
Jawota tayi jikinta tana lallashi tace”koda badan keba salma dama haka kaddararsu take,dole sai rabon Airah ya shiga tsakaninta da Dr muhd,gashi ko shakara basuyi ba Allah ya anshe dr don hakan ne kurin zaisaka Areef yasameta.saboda rabonsa ce,shiyasa ba,ason kayi shishshigi cikin lamarin aure,don sai Allah ya kasheka kuma ayi abun,Alkah dai yasa abun yazo karshe don fitinar ta isa haka.”

Karfe goma daidai Areef ya bude idonsa,jin wani kusa dashi yasashi idasa bude idon,khairat ya gani tana ta bacci jingine da bango……..duk da rashin karfin jiki da yake ciki haka ya tashi zaune ita ya kwantar da ita……..kallon fuskarta kurun yake ko keftawa baiyi,yana runanin meya sameta ita kuma,don yini guda itama duk ta fita hayyacinta.
Jin motsin kofa baisa yadaina kallonta ba,Abbune da dadynshi Annie na biye dasu sai salma.
Ko kadan baiwaiga yaga ko waye ba,idonsa ker akanta jiyake kamar daya kauda ido zaiga gizo take mar ba ita bace……..saida yaji Abbu yace “Areef kafarka yajikin naka.”
Hannu ya d’aga mai yace”Abbu kayi shiru karta gudu,kallonta nake idan na kauda ido zanga ba ita bace.”
Kadan yahana basu kece da dariya ba.sai dai murmushi dasukai,yace”babu inda zata ka juyo ka hutar da kanka da waige.”
Juyowar yayi yana sauke ajiyar zuciya,kallonsu yayi yace”Abbu meya samu khairat kagani harda drip akasa mata.”
Dady yace”abunda kayi itama shine yasameta duk kunbi kun tada hankalin mutane don ubanku.”
Salma dariya take ita da Annie shima murmushi yayi yana kallon khairat d’in yace”Abbu a sallamemu haka mun warke.”
Wannan karon saida Abbu yayi dariya yace”inkai ka warke ita tawarke ne.”
Annie tace ga alama kagani Alhaji,tunda har tabaro dakinta kamar mahaukaciya tataho nan,bacinma dr ya kamota ai kila bakin titi zata yi.”
Duk dariyar suke sai lokacin Areef yaji duk kunyar duniya ta kamashi,sai soke kai yake k’asa.
Dady yace”ai anwuce wajen kuma.”
Bari akira dr ya baku sallama kun idasa warkewar can gida.
Idona nake budewa daker don hayaniyar ce tatasheni………….ganinsu nai tsaye cirko cirko sai raba ido nake,kallon inda nake nai na zaro ido nashiga uku badai nan suka tadda niba.
Ashe afili nai maganar ida naji salma tace ga zhiri ma kingani.ba arziki na diro ina boyewa bayan Annie duk suka saka man dariya,likitan yashigo ana hira dashi yace ai wadannan Kawai alhaji ku aura masu juna,inba haka ba wataran guduwa xasuyi suje suyi aure baku saniba,dariya aketayi nidai tuna na boye bayan Annie ban sak fitowaba…….ruguda mukai sai gida,salma sai tsokanata take ina hawaye,don wlh sai yanzu duk nakejin kunyar abunda nai,don bihakki banson nayi ba,nidai kawai zuciyata nagaya man ai yah ya mutu mafarin nai wannan rikicewar.
Saida salma ta kamani muka karasa cikin gidan don jikina babu karfi sosai.
Aigabaki dayansu suka rungumeni.abunda ma yafi ban mamaki harda ummi,don hawaye take sadda ta rungumeni……..ban fita wani na shiga wani mamakin naji tace “kiyafe man diyata kiyafeman,naso kaina najefa ku cikin halin k’ak’ani kaye……….rufe mata baki nai kawai na janye na isa ga mahaifiyata.
Kuka nasa mata inajin kaunar ta duk wanda yarasa uwa yayi kuka wlh,itama hawayen take ina share mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button