ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

“nagode Anni nah ke kad’ai ke sona ko.”

Murmushi tayi mata tace,
“Aa y’ar gidan Anni kowa yana sonki, meyasa kikace haka. “

“Anni yah Aree baya kaunata yafison salma akaina.”

Gabanta ya fad’i meke faruwa haka, Khairat yarinyar da bazata Gaza shekara 13 ba tasan kishi, danne fargabanta tayi tace,
“Haba y’ar gidan Anni Waye yace maki haka, aduk cikinmu in banda Abbu da Maah babu mai son farincikin ku sama da Areef.”

Hawaye suka zubo mani nace,
“no Anni wallahi yah baya sonah jiya naga haka yau ma naga haka, nidai daga yau babu ni babushi, Anni kinsan abunda yasa na fad’i jarabawa ta.”

Tana kuka take maganar hawaye share_share ga fuskarta,Anni gabanta banda duka babu abunda yake, sunan Allah kurun take anbata,don wannan lamarin na Khairat to saidai akira sunan Allah kurun.

sake danne yanayin da take ciki tayi tana yak’e tace,
“Ina jinki y’ar gidan Anni,meyasa kika fad’i exam dinki har kika bari aKai maki repiting.”

Wani kukan ta rushe dashi saida tayi iyakar Inda take so sannan tace,
“Anni don Allah karki gaya ma kowa kinjiko idan yah yasani sake dukana zaiyyi.”

Ai Anni jitake kamar ta zura Aguje,
(???????????????? yo baki bari Kiji komiye tun yanzu har kin shiga rud’u.)

“Namaki Alkawarin babu Wanda Zaiji wannan maganar sanar da ni kinjiko.”

share hawayena nayi nace,
“Anni tun daga ranar da Abbu yace su Yah zasu tai wata k’asa karatu nashiga cikin bak’in ciki, kullum saidai na b’oye toilet nayi ta kuka, ko idan naje makaranta inyi, har Cikin dare yi nake Anni saboda banson ya tafi, gashi maah tace idan suka tafi sai sunyo shekara shidda ko bakwai zasu dawo, Anni banson yah yayi mun nisa inaji kamar inbishi ko ince karya tafi, Anni kinsan abunda yake bani tsoro har yasa naki sanar da kowa.”

Anni tayi Wata irin zufah duk AC din dake sambad’owa ad’akin kuwa, daker ta had’iye wani kakkauran miyau amak’oshin ta tace,

“Aa ta Alkhairin Abbu meke baki tsoron.”

Sake share hawayena nayi Ina cewa,
“akwai ranar da sweetheart bata je makarantar islamiya ba, malamin mu ya gama mana darasin sa akan mutanen da ya halitta ka aura, da kuma wanda bai halatta ka aura bah, ban fahimce shi sosai bah Anni sai na bari da aka tashi naje har office d’in Su nasa meshi nayi masa tambaya,

“malam don Allah ko mutun zai iya Auren yayansa wanda suka fito ciki d’aya.”

Kallona yayi yace Meyasa nai masa wannan tambayar nace,
“wata ce tace na tambayar mata Kai.”

Jinjina Kai yayi yace mun,
“Aa Khairat haramun ne babu aure tsakanin su har abadan.”

Banjira sauran bayanin sa ba na tashi na taho,
Ko drivern mu banjira ba ranar nataho ina kuka, gida ban bari ko salma tasan me yafaru bah.”

“kinsan me yasani kukan Anni.”

Kallonta take tana jinjina kaifin tunani irin na Khairat,kafi tace”Sai kin fad’aman.”

Wani kukan ya kucce mani Nace,
“Anni ba komi ne ya sani kukan bah illah yadda nakejin yah Areef acikin raina, Anni ni Yarinyace nasan da hakan, Amman nima ina mamakin yadda akai har nasan so Anni bansan tsawon lokacin da na samu kaina tsundum cikin kaunar yah Areef ba, wallahi ban saniba kuka yaci k’arfina naci gaba da cewa, wannan abun da nakeji yasa nayi ma malam tambaya, sai kuma naji cewar babu aure tsakani da shi har abadan,kinji dalilin fad’uwata jarabawa na gaza sanar da kowa saboda dai wannan Abun kunya ne awajen kowa…………kuka yaci k’arfina Anni kiyiwa Allah da manzon sa karki gaya ma kowa, don nayarda dake ke bazaki dakeni ba shiyasa na sanar dake……….”

Tabbas wannan lamarin ya hargitsa kan Anni, duk ta diririce Lallai Allah mai hikima tunda har hakan tafaru akwai abunda da Allah ya b’oye,amma Duk da haka yarinyar na buk’atar lallashi da ban baki,zatayi wannan k’ok’arin Insha Allah.

lallashina take cikin kalamai masu kwantar da hankali,tare da cewa”ki fawwala ma Allah tunda shine ya sanya maki hakan, kiyawaita sallar dare nasan ki da wannan k’ok’arin,to kici gaba sannan kiyi yak’i da zuciyarki akan shi kiringa jarumtar danne komi kikeji Akansa, Allah zai yaye maki kinjiko y’ar gidan Anni,ki rage kuka ki rage taurin kai sannan yanzu so nake ki janye daga gareshi,ban kuma ce kidaina gaidashi ba Amman kijanye mashi idan bashine yakiraki ba karkije,hakan zai saukaka maki komi kinjiko y’ar gidan Anni.”

“to Anni nah Nagode zanyi Insha Allah daman ina tsoran gaya ma wani ya bigeni shiyasa nace bari ke in gaya maki, dama na yanke shawarar janye mashi.”

Haka taita lallashina har naji duk damuwata ta ragu sosai.

Bajima wa Anty shidah ta shigo da Kayan break tayi mamakin ganina cikin walwala, har ina yimata dariya ruwan zafin Anni ta had’a ta d’age mun rigata na yi kwanciyar rufda ciki take Gasa mun, tana cewa ai dole yamaki zafi duba kiga yadda ya fasaki…….tana Cikin gasawar Ya shigo……. Lumshe idona nayi inajin dadin gasawar.

Gabansa ya fad’i duk ni nayi mata wannan dukan, innalillahi dole kiyi fushi dani sweetheart,amman afili sai dai yace mun sannu kawai, tunda nace Yawwa ban sake ko kallon shiba komi Anni tayi mun, brush da wanka ta kuma bani abinci naci, Zuwa can saiga Maah da Dadyn meenah sai Abbu, sunjima kafin Su tafi sunata tsokana ta.

Har aka sallameni ba muyi wata magana da shiba, haka muka koma gida salma sai nan nan take Dani, idone nawa kawai………….

Na warke sumul Amman na shigo da Wata sabuwar d’abia ta rashin magana, bana shiga shirgin kowa haka duk maganar da zakai mun zan tarasu in baka one ansa.

Anni ce kurun nake hira da ita ko salmar na banzatar da ita,duk Inda hankalin Areef yake yakai k’ololuwar tashi saidai duk maitarka bazaka gane halin da yake ciki bah.

Kwamci tashi ba wuya wajen Allah har Gashi jibine tafiyarsu UK………….

mom muhsen ce
Mrs bb ????????
love u fan’s ????????❤
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

3.

Alhamdulillah gida ya tsaru iyakar tsaruwa,babban gidane mai fat Kala Kala wanda saboda girman Abota irin ta su Alhaji farouk yace da Amininsa jafar yazo su zauna tare,har kuka yayi saboda farin ciki haka suka dawo gidan rana guda, komi sabo aka loda masa yayinda tuni angyaare ma Inna wancan gidan ba zaka tab’a cewa shine bah.

Rayuwar ta cigaba da kasance masu Cikin jin dad’i da kwanciyar hankali,yayin da Wata irin shak’uwa mai K’arfin gaske ta shiga tsakanin AREEF da k’annensa khairat da salma idan Sun dawo makaranta shine wankansu ya shiryasu ya zubo abinci yaringa basu har sai sun koshi, sannan assessment d’insu zai zauna ya tusasu gaba yana guarding d’insu yaga Sunyi shi lafiya lau, Areef saboda k’annensa ko fita baya yayi, Duk nacin mujahid haka zai rabu dashi, haka shahid da shahida Duk yadda suka so Cikin weekend ya ringa binsu shopping sai yace bazai bisu bah, saboda suna cin zalin sweetheart dinshi,dole sukai hakuri saidai driver ya kaisu shikuma Ya ware rana ya kaisu da kanshi………wata guda kenan da kammala secondary d’insa,tunda twince suka girma Maah ta hana yaringa masu wanka da shiryawa,tunda yanzu ko wacece zata iya yiwa Kanta wanka da shiryawa, yanzu suna js one yayinda shahid da shahida Suke ss2, Muhajid tare sukai graduation da Areef, Neenah ce take js3.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button