ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Ganin duk yadda ta tada hankali tana fad’a yasa na bata hakuri ashe k’ara kular da ita nayi,moper ta d’auko zata maka mun na tashi na rugo ina dariya, ban tsaya ko Ina ba sai falon su Yah mujahid shida yah Areef.

Kuka na samu salma nayi tana gaya masu,abunda ya faru, sai naji tabani tausayi matuk’a jiki babu kwari na shiga can gefe na zauna na gaida yah mujahid sannan Shima Nace masa,

“yah ina wuni.”

Kallona yake bazan iya fassara shiba, kawai dai nasan kallon mai laifi yake mun kafin ya Kauda idonsa yace,

“haka zan tafi kuna fad’a da junan ku ko,na lura kin fara rainani Khairat sunan da ya anbata yasa babu shiri na kallesa, akai sa,a idonsa na kaina kallon Cikin ido mukai ma juna, sai naji ko kad’an banji dad’in sunan da yakira ni dashi bah, sadda kaina nayi naji kamar kwallah zata zubo mun,danne wa nayi daker ta tsaya.

Yace,
“kiba ta hakuri abunda kika mata, idan kuma kuka sake naji labarin kun sake b’atawa Allah takakkiya zan maku oya maza Kunshirya ina gani.”

“tabarshi kawai Yah bana so.”
Cewar salma.

B’ata fuska yayi.
yace,
“bana son taurin kai Kin sani salma ban sanki da haka ba, don haka karki fara kwai kwayon halayen da basuyi maki kyau kinji my Angel.”

Saida kirjina ya yi Wata irin bugawa na runtse idona kawai jinai ya dakan tsawa.

“zaki bata hakurin kokuwa sai na tattakaki awajen nan.”

Yah mujahid yace,
“haba Areef Meyasa Kwanan nan kakoyi yiwa yarinyar nan tsawa ne,ehyi ba halinka bane kadaina.”

Bai kula saba jikina yana rawa kaina na k’asa Ina zubar da kwallah ba tare da Sunyi shawara dani bah,bakina yana rawa Amman na kasa furta komi…….. Azafafe ya tashi ya d’auko dorinarsa jinai zau zau ga bayana……….k’ara na fasa inafashewa da kuka Yah mujahid ya anshe dorinar yana masa fad’a,kamar zai dakesa Shima Cikin zafin ran da bansan yana da shiba yace.

“wallahi muddin ba ta bata hakuri ba jikinta sai ya gaya mata, raini ya fara shigowa tsakani da ke ko, to mun k’ulla kenan nida ke daga yau wlh, zan saukar maki da wannan girman kan naki.”

jikina rawa yake kamar mazari, sosai na tsorata da dukan sa yanzu kam tsoran sa yafara shiga ta tabbas,don babu abunda yake firgita ni kamar duka, ganin zai fizge ya yo kaina yasa na sake rushewa da kuka ina mamuk’e kujera.

Saida Yah mujahid yace,
“oya Khairat ba y’ar uwarki hakuri kinjiko ai ba fad’uwa kikai bah.”

Bawai inajin k’yashin bada hakurin bane taurin kai ne irin nawa, Amman ganin zai sake dukana yasa nace ina kuka.

“kiyi hakuri bazan sake bah.”

Amman salma tai mun shiru jin haka yasa yace sai nayi ta bata har sai tayi magana.

saida na bata sau uku sannan tace tayi.
Zuwa lokacin fuskata tayi jajawur kamar tumatur, tashi nayi zan tafi ya fizgoni nayi wata irin fad’uwa saida yah mujahid ya tadani……..saboda haushin abunda yayi fita yayi yabar falon.

d’akin yayi shiru sai shashshekar kuka nakurum, da karar AC.

Ina jin sanda Ya ke Ajiyar zuciya kamar mai iska naji ya fara magana Cikin taushin murya,abun mamaki yabani yanzu fa yake kamar zai tashi sama saboda zuciya, Amman jibeshi kamar bashi bah.

“zan tafi na barku don haka kusan mekuke ciki, kar na sakejin wai kunyi fad’a,sanan maganar karatunku karkuga ban nan kuce zakuyi abunda kakeso, wallahi Ina biye da duk motsinku don haka amaida hankali a ajiye mun k’yak’k’yawan results,ke kuma da akama repiting sai ki maida hankali agaba kuna iya tafiya……..salma ta fara mik’ewa sannan ni bazan Iya kwatanta yadda zuciyata ta keba, nasan dai ina cikin kunan zuciya da wani irin yanayi marar misltuwa,daker nakai k’ofar har salma ta wuce jinai yace,

“zonan”

Tsaye nayi na kasa juyowa kuma na kasa tafiya,saida ya dakan tsawa sannan jiki na rawa na isa gabansa na sadda kaina……….shiru tsawon lokaci baice komi ba, nima ban motsa ba, na sadda kaina kurun kwalla na zuba suna d’iga ga hijabina.

Jinai dai kawai ya d’ago fuskata nayi hanzarin rufe idona yayin da wasu kwallan suke zuba, handcif ya saka mai fitinennen k’amshi ya na goge mun kwallar………….amman wasu na sake silalowa bai daina gogewar ba har saida suka k’afe, sannan ya saki fuskar.

Yace Cikin muryarsa da tayi matukar sanyi,
“idan kika sake kukan nan ko bayan kin tafi d’aki nida kene swe…..Khairat.”

Fita nayi inajin k’afafuna kamar ba zasu iya d’aukata ba,

wannan ranar yadda naga rana haka naga dare, tun asuba akafara shirin tafiyarsu, inajin sadda salma tatashi nayi kamar bansan me take bah…….sai tara na tashi nafito wanka kenan Ina tsane jikina naji muryarsa yana tambayar meenah Ina nake, tace ina d’aki………yana bud’e k’ofar ina shigewa toilet na da tse k’ofar……………….

Mom muhsen ce
Mrs bb ????????
love u wujiga wujiga fan’s d’ina ❤❤❤❤❤
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ???????????????????????????? ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

7.

Jingina nayi da k’ofar toilet d’in Ina sauke numfashi k’asa k’asa, jikin k’ofar yazo ya Jingina bayan sa Shima, murya can k’asa k’asa yake magana, tayi rauni sosai sai kayi tunanin kuka yake.

“zamu tafi sweetheart saidai abun haushin zamu rabu kina fushi da Ni,pls kiyi hakuri ki fito ko dukana kiyi Wanda zan ringa tunawa da shi.”

Kuka ya kucce mun mai tab’a zuciya,kamar numfashina zai fice runtse idonsa yayi yana jin babu dad’i, duk yadda yaso yasake ganinta k’iyawa nayi, haka yafita jiki babu kwari……..daman shikad’ai akejira gab’a d’aya gidan aka tafi masu rakiya banda Maah da Khairat.

Ina bayin nan har suka tai saida nasha kukana kamar ba gobe sannan nafito daga bayin,daidai shigowar Maah d’akin.

Zama tayi bakin gadon mu tana kallona bata dai ce komi ba har na gama shiryawa, nazo nayi walha da nake yi na gama sannan na kalleta nace.

“Maah ko wani abun zanyi naga tunda kika shigo baki ce komi ba.”

Wani kallon banza tayi mun kafin tace mun, in biyota d’akinta.

Jikina yayi sanyi Allah yasa ba laifi nayi mata ba, Ina tsoran fad’an ta Maah babu sauk’i indai wajen fada ne,duk na tsure tsoro nake kar ta dokeni gashi mai cetona bainan,don wata sa,in idan na mata taurin kai jibgata take kamar jaka, sai shine zai kwaceni.

Zama nayi k’asa wajen k’afafunta, na sadda kaina kamar munafuka.

Sunana ta kira.

UMMUL KHAIRI
D’agowa nai na kalleta nace,

“Na,am Maah.”

“Miye matsayina wajenki.”

“Maah ke mahaifiya tace.”

“idan ance mahaifi me ake nufi kenan.”

“ana nufin wanda ya yi silar kawoka duniya, kuma wanda nauyin kulawarka ci da sha da sutura suka rataya akansu, idan baka lafiya akaika Asibiti tarbiyyarka tana kansu.”

Wani dad’i ya kama maah lallai duk cikin yaranta babu kamar Khairat wajen komi, Amman sai ta sake Shan mur tace.

“sab’amasu yana nufin mekenan.”

“yana nufin ka sab’ama Allah [S W A] kuma duk mai ja dasu bazai tab’a ganin daidai bah.”

Jinjina Kai ta sake yi sannan tace.

“madallah da malamin islamiyyarku,tunda har duk kinsan wad’annan bazan sha wahalar yi maki bayani bah, kallani nan Khairat.”

Banyi musuba na d’ago Ina Kallonta ina ganin wasu maganganu masu tsananin nauyi cikin idonta, jinai taciga da cewa.

“matsayina na mahaifiyarki, na umurceki da cire duk wani Abu dake ranki akan yayanku AREEF,sannan na haramta Aure tsakaninki dashi har gaba da abadan, duk Yarinya ce ke nasan kinsan me ake nufi da haramci,to na haramta maku junan ku, kuma muddin kika take doka ta wallahi ummul khairi BAN YAFE MAKIBA.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button