ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Iya dauriya nayi bansan ni d’in jaruma ce ba sai yau, ilahirin jikina rawa yake amman nadanne na k’i bari Maah ta gane, idona k’em akanta nace.
“insha Allah nayi maki wannan alkawarin,saidai tambayar da nake da ita itace………..”
“Bana sonjin tambayar,duk motsinki na sani Khairat karkiga ina nuna halin ko in kula akan lamarin ku, wallahi kar nake kallonku, don haka idan na sakejin kun samu sab’ani da juna keda salma billahil azim zanar tsiya zan maku,kiyi k’ok’ari idan ta dawo ku sasanta kanku,sannan kan karatunki, wallahi Khairat idan kika sake barin damuwa tayi gala ba kanki nida kene.”
“don haka idan kunne yaji……….
Kaina k’asa Nace,
“jiki ya tsira.”
Tace,
“good girl,sannan kidawo da walwalarki, bana son wannan d’ari_d’arin da kike bance kuma kidaina yi masa magana ba,ko kuyi fira, Aa zakuyi duk wannan amman muddin kika sakejin wani yana yi kanshi………basai na ida ba kinsan sauran tashi Kibani waje.”
Jiri ke neman kada ni na dafa bango zan fita,sai kuma na juyo Nace,
“Maah.”
kallona tayi alamun tana jina.
Cikin karyewar murya kad’an ya hana kuka na bayyana nace,
“Maah, don Allah kiyi mun hakuri bazan iya cigaba da magana mai tsawo dashi ba,idan nayi hakan bazan iya hana zuciya ta jin wani abuba, kibarshi murinka gaisawar ya isa,sannan kiman afuwar yau bazan iya warware wa lokaci guda ba,amman namiki alkawarin bazan Kai lokacin da salma zata dawo ahaka bah…….plss Maah.”
Wani marayan Tausayin y’ar tata ya rufeta,jawoni tayi ta rungume,wanda ba zance ga tsawon lokacin da Maah ta d’auka rabon da ta rungumeni.
Cikin muryar lallashi tace,
“nayi maki wannan uzirin Khairat,badan na cuta maki nai hakan ba, gata ne nayi maki, ko ince nayi maku keda yayyenki, na kausasa kalamaina ne don na tsorata ki akan abunda kikeji kan AREEF,amman bazan iya hana Allah ikonsa akanku ba, kiyi k’ok’arin kiyayewa kinjiko ta alkhairin Abbunta.
Wannan kalamin yasa nasamu natsuwa, nasake mata alkawarin kiyayewa,k’arshe ajikinta nayi bacci, ta kwantar dani ta fita…………….
Mom muhsen ce
Mrs bb ????????
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA
Written by [Mrs bb]
Mom muhsen ce
________________________
????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________
9.
Shirye shiryen dawowar Su kawai ake babu ji babu gani,b’angarensu angyaare an cire komi ansa sabo, har kaya sawa saida Abbu Ya siya masu, Manya da k’anana.
Abun har mamaki yake bani, saikace shugaban k’asar mu ne zaizo,amman sai ban nuna ba nayi kamar ban san me Akeba,ban shiga mamaki ba saida naga ana sake fentin gidan, nace Eh gaskiya lamarin azimun ne.
Sweetheart kuwa duk tafi kowa zak’alk’alewa, banga wanda yayi mata magana ba,saidai suyi ta yi mata dariya.
Ranar da ta kama jirginsu zai sauka,washe garin muka tai registration,sweetheart cewa tayi zatayo daga baya, Amman bazata iya fita gida ba har sai sun iso.
Haka muka tai nida meenah wadda abun ya isheta har tace,
“rawan kan sweetheart d’inki tayi yawa Khairat,ba zaki ringa kwab’arta bah.”
Murmushi nayi Ina danna wayata, kasancewar itace ke driving d’inmu ni ina gefenta.
“Uhm yah meenah kenan, ni asuwa ince ma sweetheart ta rage rawar Kai, wai kokin San yadda take ji dashi kuwa!uhmmm muddin nayi mata Wata magana fad’a zamuyi, kibarta tayi tunda yanzu babu haramcin hakan,duk da har yanzu basan ainahin abunda ya faru ba.”
“Shikenan,Allah yasa mudace amman hakan babu kamun Kai gaskiya, koshi yana sonta yadda take masa zai ji tana sire mashi.”
“can su gane banda Wata matsala dasu, ni yanzu fata nake Mu gama registration d’in nan lafiya,so nake muje Dubai.”
“murmushi tayi mun tace, Kedai kawai Kice wajen heartbeat d’inki zaki.”
Dariyar da ban shirya mata ba nayi,
“kina da ban dariya,wai kin mance cause d’ina ne haba yah meenah wallahi ni ban shirya ma soyayya yanzu ba, saboda ita tana da zak’in da zata shagaltar dake daga komi ma,haka zalika tana da rad’ad’in da zata hana ki dukan wasu abubuwa masu muhimmanci,cikinsu kuwa harda karatunki, tsaf zata k’arar da farincikinki Arudun Allah.”
Dariya meenah taringa yi harda dukan Sikiyarin motar, haka suka cigaba da hirarsu har sukaje.
Kasancewar ranar farko ce shiyasa suka tadda wajen acike,kamar ana rabon kud’i shiyasa basu samu kansu ba sai anata salar magruba, wai ahakan ma basu gama ba sai sun sake dawowa gobe……..a matukar gajiye suka iso don yanzu Khairat kejansu,kamar tayi kuka don gajiya tana shigowa harabar gidan gabanta ya yanke ya fad’i……..ras ras kallon juna mukai nida yah meenah.
“yah meenah Bazan iya shiga gidan nan bah.”
Idona ya canza Kala kuka nake so nayi Amman Ina danne halin da nakejin zuciyata.
Dafa kafad’ata tayi cikin kwantar da hankali tace,
“come down Khairat,babu abunda zai faru, kiyi ta karanta duk adduar da tazo bakinki,Allah yana sane dake.”
Kwallah sun cika idona nace,
“yah meenah,inajin tsoran tashin wani miki acikin zuciyata,maah tace mun Idan nasake jin wani feelings Akansa bata yafe bah,yazanyi Idan zuciyata ta k’i saurarena hakan yana nufin na sab’a umurnin Maah, kuma Allah zai tsine mun.”
Na fad’a ina goge kwallah.
Ajiyar zuciya meenah tayi ta anshi key din ta kashe motar,sannan ta zagayo Inda nake na bud’emun,kallonta nayi ta jinjina mani Kai sannan nafito.
“Allah bazai kama ki da laifin da bakida tsumi ko dubara Akansa, shi ai yasan abunda yake zuka tanmu,bazai yanke mana hukuncin da yasan bamuda laifin saba, saboda bake kika sama kanki bah Khairat,don haka kiyi iyakar k’ok’arin ki kiyi wa Maah biyayya,sauran kuma kibarwa Allah,idan mun shiga ki saki ranki kamar babu wani Abu,kiyi mashi irin na y’an boko ke kanki zaki samu natsuwa,ok.”
Murmushi nayi inajin Wata natsuwa na Shigata,ina k’arajin Yah meenah cikin raina itace mai kwantar mun da hankali koda Yaushe sai fah Anni, don sweetheart bama ta natsuwa balle har tasan damuwata ta lallasheni.
Cikin kwarin guiwa muka nufi cikin gidan……….
[Wayyo tsoro nakeji???? anya kuwa Khairat,???? Amman duk da haka kin bani tausai????]
Tunda da kan Yah Areef d’in har kawo kan salma babu Wanda babu falon,kirjina kamar zai fito wajen daker nake yak’e, har muka k’arasa Cikin falon tsundum.
“Aaaaah kaga mutanen turai,iyyen bah wai kun ganku kuwah yah Areef,yah Muhajid kaine kuwa anya ba musanya mana ku akai ba.”
Duk ni nake fad’ar haka inajin dukan kirjina yana yawaita,amman duk da haka murmushi mai kyau akan fuskata.
Harara ya wurgomun cikin sigar wasa ya d’auke kai yana ma Yah meenah magana.
Murmushin na sake k’awata wa na isa ga Yah mujahid,zama nayi gefensa Ina lank’washe k’afafuna Nace ina rik’e ha6ata.
“wallahi yah mujahid idan a Wajene naganku zagaye ku zanyi in wuce saboda ko k’an wanda yasanku shekarun baya, yanzu bazai iya gane ku bah.”
Duk dariya aka saka mana,
Salma ce ta shigo d’auke da tiren dinner d’insu.
“sweetheart Kinga yah Aree, Kinga yadda ya koma wallahi nayi zaton irin turawan nan ne da ya shigo, ban zaci shine bah.”
nan ma dariyar ake na kalleshi Shima ni ya kallah, muna had’a ido ya sake harara ta,dariya nayi kafin na shagwa6e fuska na Kalli Anni nace,