GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Sagir yace’Mama nayi Tunanin a gyara Dakin nan sai ta zauna aciki.’ yafada yana nuna wani Dakin da ke kusa da dakim mama inda take saka Tarkacenta.
Mama tace”A”a duka duka nawa Inteesar take da zan raba wajen zama da ita..Tare zamu zauna da ita adakina ga gadona ta rika kwanciyarta ni kuma sai na kwanta a katifa ba Shikenan ba..”
Sagir ya Bude baki zai yi mgana kenan yaji Imran na Fadin”Mama sai an juma ni zan wuce..,!
Ashe Tun dazu yana Tsaye ba zai ce yana jinsu ba Sanin Halinsa ba komai yake bama muhimmanci ba abunda ma ya Shafesa bai cika Bashi Damuwa haka ba
Mama ta rakaahi da Saka albarka da Sakon gaisuwa wajen Abba Sagir ya saka Takalmi yabi bayansa yana Fadin”bari na rakasa Mama..!

Yana Fita yaga Imran har ya mika Hanya Dayake da kafarsa yau ya Fito bai Dauko mashin ba Da Gudu ya Cimmai yana Fadin”Kaifa baka da kirki..Sai ka Tafi ba Sallama..,!
Imran na takunsa na Sassarfa Duka Hannuwansa na Cikin Aljihu bai ce ma Sagir kala ba suna dai ta Tafiyansu Sagir ne yace”Yanzu da Daddare zamu je gidan Baba Manun kenan..?
Bai tankamai ba sai da suka iso Get din gidansu kana Imran yaja ya Tsaya yana Fadin”Karfe 8:00pm bayan an Fito Sallar Isha”i ka Fito kofar gida bana son ka batamin lokaci..!
Daga haka kawai ya Kwankwasa Get din gidan nasu Iro megadi Da Daman yasan ko waye yazo ya Budemai karamar Kofar ya Shige shi kuma ya leko yana gaida Sagir din Daya amsamai Lokaci Daya ya juya ya Fara Tafiya yana Fadi a Fili”Imran akwai iko..kamar jinin Sarauta wannan inda Dan wani Sarki ne da anga Iko..!
Bai koma gida ba Shima Shago ya Shiga yana Duba aikin Daya bar musu yau akwai masu karban Dinki da yawa da yayi ma alkawari,Ransa ya baci ganin basu ci karfin aikim ba Dayake Sagir ya sanu manya mata ke kawomai Dinki kuma akaci Sa”a ya iya Harda Dinkin Maza Shiyasa nan da nan Shagonsa ya Daukaka Har ya mallaki yaransa na kansa ganin haka yasa bai jira su ba Ballatana yaji Hakurin da suke bashi ya Haye keke ya Fara Rage wasu ayyukan Haka yake bai da Girman kai sam yana da Zuciya da Neman na kansa ko Domin Mahifiyarsa a koda yaushe yana so yayi ma Imran mgana kan yazo ya koyi Dinki zai Ragemai wani abun Tunda babu Abunda yake yi komai Yusuf ne ke Gudanar dashi.

Shakira…
3/22/22, 23:03 – Ummi Tandama😇: GIDANMU..!
(Our House)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)

          *🅿�5*

Da daddare

“Cikin Shirinsa na Fita ya Fito Daga Dakinsa Cikin Shigar riga da wando Black and white,na kamfanin Armani sai kafarsa sanye Cikin Bakin Rufaffen Takalmi na Fatar Damisa Sai hannunsa Dake daure da Bakin agogo na Fatar damisa mai kyau da yarari,Kwantacciyar suman kansa tasha gyara ta kwanta ta karama Fuskarsa kyau da Annuri Sai Bakinsa Wanda Bakin hayaki ya Fara mai dashi Duhu hakan sai ya karamai kyau da wani Haiba..
Fuskar nan nashi a Hade babu Fara”a ko kadan Key din Mashin Dinsa ne a Hannunsa yana Dakawa Sanda ya Fito Falon kamshin Turaransa na Man Daya saba amfani Dashi ya Fara ma Yusuf da Maimuna Sanar isowarsa Cikin Falon.
Ya yusuf na Zaune kan Daya Daga Cikin kujerun Falon Yana makale da waya a kunnensa yana mgana kasa kasa Cikin kwantar dakai Daga gani Da Safiya yake waya ko da wata Macen da Zuciyarsa ta gama yarda da ita.
Maimuna kuma Tana Wajen Dinning area Tana jera Warmers da Filets din Data kwaso Daga Kitchen
Tunda ya Fito ta Kuramai ido Ganinsa kamar kullum Ba Fara”a da Anuri yasa da Sauri Ta Daga murya Tana Fadin”Barka da Fitowa ya Imu..!
Bai amsa mata ba Sai ma wani kallo Daya Bita dashi kafin ya Dauke kansa Ya Juya ya nufi Dakin Abba Bata damu ba sanin Halinsa baki ta tabe kawai ta juya zuwa Kichen ta Dauko Ruwa da Kofuna,Yusuf kuma Dake waya bai katse ba ya bishi da kallo Har ya Bude Dakin Abba ya Shiga da yar Karamar sallamarsa Ciki ciki kamar wanda akace yayi ta Dole.
Har Gaban gadon da Abba ke kwance ya karisa cak ya Tsaya yana Kallon Abba Dake kwance Sambal akan gadon da ya zame masa Kamar wani Maginjini ko nace abun Dogaro ya kwana akai ya tashi akai ya kuma karishe wuninsa akai sanye yake da Farar Jallabiya a jikinsa Gashin Bakinsa da gemunsa ya cika alamun yana Bukatar a Rageshi Dogon Hancinsa ya kara Fitowa da Kyakyawan Fuskarsa ta Fulanin asali.
Kuramasa ido Imran yayi yana jin Taruwar wasu Hawaye a kwarmin Idanuwansa Durkusawa yayi agaban gadon yana kallon Idanuwan Abba suna Lumshe alamun ya samu natsuwa Cikin Barcinsa.
Hannunsa ya Riko Cikin Nashi yana Faman kokuwa da Numfashinsa Wasu al”amura da suka Shude suna kokarin Dawowamai Daki Daki yana Tuna Abba da Sadaukarwarn sa kan Iyalinsa da yan”uwansa ammh yau Dalilin Wata kaddara Kalli Halin Daya koma.
Rauninsa ne ya Fara Bayyana Kamar zai yi kuka ammh kuma bai yin ba yayi maza ya Matse Hawayensa suka koma Lokaci Daya ya Mike Bayan ya saki Hannun Abba Yana Fadin”Allah ya Baka Lafiya Abba..!
Daga Haka ya juya ya Fice Daga Dakin da Sauri Cikin Sassafarsa Daya saba akoda yaushe.
Wannan karon Munari bata Falon Sai Yusuf kadai Dake kan Dinning yana cin Abinci Fitowar Imran Da kokarin Fita Dayake yasa ya Daga murya ya kirasa
“Imu…!
Tsayawa yayi Lokaci Daya ya waigo yana kallonsa abincin gabansa ya Nuna mai da ido kafin yace”Ina zaka kuma ga abinci Munari ta gama..?
Yamutsa Fuska yayi kadan kafin yace”Am ok..!
Ya juya zai Sake yunkurin Fita yaji Yusuf din na Fadin”Wai ina Zakane da Daran nan kake ta wannan Uban Saurin..? Kodai kodai..?
Yafada Cikin Sigan Zolaya Jin haka yasa Imran ya juyo yana kara Hade Ransa yace”Kodai What..?
Yusuf na kai loman Shinkafa da Miyar da Munari tayi yake Fadin”Ko dai Zence zaka ne..?
Imran ya wani Kallesa Sheke sheke kafin yace”Menene kuma wani Zence..?
Yusuf yace”Nufina Tadi zaka je wajen Budurwan ka Dakayi..Domin wannan gayun ina hasashen nata ne..!
In ba domin ya yusuf bane Ashar yaso ya Dankara mai sai kuma ya Fasa ya karkace kai bayan ya Tusa Duka Hannuwansa Cikin Aljihun wandonsa yace”Abba nata barci ya ko tashi yayi Sallah..? Ya kauda Hiran Saboda bayaso Tayi tsawo Lokaci Daya kuma yana Fito da hannunsa agogon Dake Tsitsiyan Hannunsa yake Dubawa.
Yusuf ya kada kai kawai yace”bai yi ba..Kasan Dr.Ya sauyamai mgani wannan karon so akwai masu saka Barci sosai..Zuwa 9 insha Allahu zai Tashi da kansa.Ammh fa bazan fasa Fadin Zence zaka ba..!
Ya karishe Fada yana kunshe Dariyansa Lokaci Daya yana Tsiyaya Ruwa a glass Cup yasha ya koshi kana ya mike ya Zari Tissue yana goge bakinsa kafin ya Fara takowa Tsakiyar Falon.
Yana kallon Fuskar Imran din wanda yayi shuru kawai yana Kallon Yusuf din kamar ya Makeshi haka yaje ji..? Shi Imran ne zai je Tadi ko menene ma yace..? Allah ya Tsareshi..
Karamin Tsaki yaja kafin yace”Ni Imran ne zan je Zence kace ma kofar gidan wata yarinya..?Ni..Over my Death Body Wlh..!
Yafada yana wani mele baki Yusuf ya karosa gabansa Lokaci Daya yana Fadin”Common Kada ka Cika baki..Sai dai in bazakayi aure ba in ko Zakayi Dole sai ka Sauke wannan Ra”ayin naka kaji..!
Imran yace”Saboda me..? Nifa Shiyasa bana son Hada Shirgina da mata..Kasanni bana son Raini ko kadan su kuma da sunga kana Sakarmusu Fuska sai Raini ya Shigo Ciki..Ni aure bai Taba Zama Dole gareni ba sai don yana Sunnar ma”aiki in ma ya Zama Dolen zan yi auran sai na Ga wacce ita take sona zata iya Zama Dani tayi Hakuri dani kuma In har taji Tagani Shikenan Fine ammh ni kam bazan iya Lalacewa gaban Mace ina Rage Murya ba Allah ya tsari Imrana..!
Tunda ya Fara mgana Yusuf ke Dariya har yana zama kan kujera Ganin haka yasa Imran ya juya kawai ya Fara Tafiya batare Dayace wani abu ba
Gabda zai Fice Daga Falon Yusuf yace”Shikenan Imran Abubukar Malami We shall see..!
Cikin son Tabbatarwa ya juyo ya saki wani Mirmishi kafin yace”We shall see..!
Daga haka ya Fice Daga Falon yana sakin karamin Tsaki ganin Bata Lokacin Dayayi alhalin shi ba Mutum ne mai african Time ba.
Mashin dinsa yaHau ya kunnata Lokaci Daya yayi Hon Iro megadi Dake kan Bencinsa zaune yana Dafa Shayinsa ya Tashi da Gudu ya Bude get din Imran ya Fice da Gudu Baki Iro ya Rike kafin yace”Nidai Allah ya kawoni gadi Wani Gida..Gidan da ban taba ganin kamar sa ba.!
Yafada Lokaci Daya yana maida get din ya Rufe ya koma ya Cigaba da Fifita Rushin Dake Cikin karamin murhin gawayin Dake gabansa mai Dauke da Karamar Butar shayi yana Dafawa.
Yana isowa kofar gidansu Sagir din yaji wayarsa na kuka,Kafin ya Cirota Daga Aljihu Sagir ya Bayyana gabansa Cikin Harara yace”Karfe Takwas din kenan..? Kasani na Fito ina jiranka kamar wani yaron aiken ka..!
Karamin mirmishi Imran yayi yana Fadin”To da wanene..? Mallam Hau muje bana so mu yi Dare sosai..!
Sagir na Hawa mashin din Lokaci Daya yana Fadin”Dare na nawa kuma..Ai mun gama yinsa..!
Imran dai bai kara mgana ba suka Dauki Hanya Sagir ne ke ta maganarsa yana Fadama Imran din ya kira Baba Manun yace maizasu zo,Imran Yana Tuka mashin din yace”Waya aike ka..?.
Sagir yace”Bangane ba..? In mukaje bai dawo daga gareji bafa..!
Kai tsaye Imran yace”Mu bisa chan..!
Sagir yace”Mganar bata kamata ayita achan ba.Agidan dai ya Dace..!
Imran yace”Naji sarkin Tsari..Kamin shuru kasan na tsani ina Tafiya mutum na min Surutu a bayana..!
Sagir ya Gimtse bakinsa bai kara mgana sai da suka isa anguwan su Baba manu dake mandawari Road,Daman Imran yasan gidan Domin In Sagir zashi Wani Lokacin Tare suke zuwa da Imran din sai dai bai taba Shiga Gidan ba sai dai ya Tsaya Daga waje Sagir din ya Shiga ya Fito Shima Baba Manun ya san Imran din Abokin Sagir ne sau Daya suka Taba Haduwa Har ya gaishesa shima Sagir ne ya Dinga Taka kafar Imran din yana mai in kiya Daya gaida Baba Manun.
Akofar gidan suka Faka mashin din kafin Sagir ya kalli Imran Daya Coge gefen mashin dinsa yace”Shiga fa zamu yi..?
Imran yace”Saboda mene.? Ya fito waje mganar bamai tsayi bace!
Sagir yayi tsaki ya wuce yana Fadin”In kaga dama kazo mu shiga in kuma baka ga Dama ba ka koma!
Daga haka ya saka kanshi Gidan ya bar Imran din nan Tsaye yana kallonsa Kamar bazai Bishi ba kuma komai ya Tuna sai ya Daga kafa ya Rufama Sagir din Baya.
Da Siririyar Sallamarsa ya Shiga Sagir da Inna kaltume matar Baba Manu suka amsa,Wanda ke Zaune kan Tabarma kusa da Sagir din mgana yake a waya.
Kamar Imran ya juya sai kuma ya Tuna Abunda ya kawosa yasa yayi karfin gwiwan karisawa ganin yadda Daga Baba Manun har Inna Kaltumen suka Sakarmai ido suna kallonsa Dayake akwai Wutan Lantarki Haske ya gauraye Tsakar gidan.
Daga nesa ya Durkusa Kamar a Dofane yana Gaishesu sau Daya ina Wuni?
Inna kaltume ne ta amsa mai Cikin Fara”a Tana Tambayashi Mutanen gidan Dakyar yace Lafiya lau yana kauda kai itama ganin haka bata mtsa ma kanta ba Ta juya kan Sagir Tana Tambayansa Mama yace Tana gaishesa Daidai Lokacin da Baba Manu ya gama waya ita kuma Inna Kaltume ta mike tana cema Sagir azubo Tuwo yace a koshe yake ta kalli Imran wanda kansa ke kallon gefe yana jinsa kamar a Takure tace koshi bazai ci ba..?.Sagir ya kallesa kafin ya girgizamata kai yace mata Ta barshi kawai bata ja da Nisa ba ta Shige Daki ta basu waje suyi mgana.
Juyawa Sagir yayi yana gaida Baba Manu wanda da ga kanshi Zaka san sun Hada Jini da Sagir Saboda Zubinsu iri Dayane da kuma yanayin Dogon Fuskarsu
Amsa mai yayi Cikin Fuska Lokaci Daya yana Fadin”Ina Ita Aminan..? Ina fatan lafiya kalau take..?
Kan Sagir na kasa yace”Eh Baba Lafiyanta Kalau tace a gaisheka..?
Yana kallon Imran yana Nazarinsa acikinsa Ransa yace”Ina amsawa Daman gobe nake cewa zan leka mu gaisa kwana Biyu!
Sagir ya gyara zama yana Fadin”Baba ga abokin nawa danace maka zamu zo Tare..Imran yana so yayi mgana Dakai..!
Baba Manu ya maida Hankalinsa kan Sagir kafin ya kalli Imran yana Fadin”Topha dan Saurayi in ce dai ko lafiya..?ba wani abu Sangirun yayi maka ba..?
Imran da sai yanzu ya kallesa ya Girgiza kai yana Fadin”A’a ba mganar Sagir bane..!
Baba manu yace”To to..Ina jinka..!
Sagir ne ya kalli Imran din yana Fadin”Ka cire Takalminka ka Hawo kan Tabarman mana Imu..!
Bai kallesa ba ya gyra Tsugunnonsa yana Fadin”Nan ma is ok..!
Baba manu dai bai ce komai yana ta Tunanin wata mgana ce haka yaron da ba wani saninsa yayi ba yazo har gida saboda ita.
Bai gama mamaki ba Yaji Muryan Imran din Ciki Kaushi kai tsaye yana Fadin”Dama kan mganar Auran yayana ne…Gidan Dayake son yarinyar sun nemi Daya Turo mgabantansa Shine nazo na sameka ina so ka Shige masa gaba a Bangaran Neman auran..!
Ba wani Roko ko alfarma kai Tsaye ya Fadi mganarsa kuma bai Damu ba.
Baba manu mamaki ya kamashi ya kalli Sagir,wanda ya Sunkuyar da kansa domin bai ta cewa Sanin Halin wanda ya kawon.
Cikin mamaki yace”In shige masa gaba..? To ina iyayenku ko nace Waliyan ku..Ma”ana kanin Mahaifi ko Kanin Mahaifiya ko wani Daga Cikin Danginku..!
Imran kamar bazai ce komai ba sai Chan yace”Bamu dasu..Gidanmu mu kadai ne Dagani sai yaya na sai kanwata sai Abbanmu..Kuma shi din bai da Lafiya ne shiyasa nazo wajenka..!
Baba manu ya gyara Zama yana Fadin”To baku da yan”uwa ku din Daga sama kuka Fado..?
Sai alokacin Imran ya kara Dago kai yana kallon Baba Manu Cikin wani yanayi kafin yace kai Tsaye”Eh..!
Ba Baba Manu ba Harta Sagir sai da ya kalli Imran yana Auna masa Harara da ido Cikin Kufulwa da Rainin wayau Yaron Baba Manu yace”Kuma kace Min Eh..!
Imran yace”Eh..Ai kaima kasan ba wanda ya Taba Fadowa Daga sama..Ballatana ka Tambayeni ko mu Daga sama muka Fado..!
Hankalinsa kwance yayi mganar Zuwa Lokacin Ran Baba Manu ya Fara Baci Cikin Hargowa ya kalli Sagir yana Fadin”Au daman da saninka ka Kawomin wannan Tsagerin yaron har gidana zai Cimim Mutumci..?
Sagir ya kwaso Rantsuwa Baba Manu ya Dakatar dashi da Fadin”Maza tashi ka Tarkatashi ku barmin gida kafin na Saba maka..ko ce maka akayi ni Mutumin banza ne..!?
Sagir ya Sadda kai yana Fadin”Don Allah Baba kayi Hakuri..Ba Cin mutumci zai maka Shi haka yake don baka Sanshi bane..Imu ka bama Baba Hakuri don Allah..!
Ya karishe Fada yana kallon Imran Din da har ya Mike daga Tsugunnon Cikin mamaki yace”Saboda mene zan bashi Hakuri..? Nayi mai wani Laifi ne..? Mgana na kawo mai ni kuma ya Tambayeni na bashi amsa do i do Something wrong..? Bana bada Hakuri a inda ban aikata komai ba Mganar aure ai Mganar alherice balle yace Mganar Shanshanci na kawomai..!
Yafada Hankalinsa kwance yana Laluban Aljihunsa Cikin Takaicin ya manta bai Fito da Tabansa ba sai dai Lether din,Karamin Tsaki yaja ya juya zai Fice Daga gidan Baba Manu ya saka baki ya kira Sunansa Tsayawa yayi kafin ya juyo Da kai ya gyada mai kafin yace”Dawo ka zauna muyi mgana..Na Fahimceka!
Yafada da Dan Sakin Fuska Domin a kalaman yaron ya gama Fahimtar sa irin yaran ne kaifi Daya marasa Tsoro,Gaba gadi basu karya ba Munafunci.
Inda ya tashi ya koma ya Kara Durkusawa Cikin mamaki Sagir ke kallon Baba Manun sanin Halinsa na Fada ammh sai me sai yaji yace ma Imran din”Wani gida ne shi yayan naka yake neman auran..?
Ajiyar Zuciya ya sauke kafin yace”Gidan Alhaji Alhassan Buhari..!
Baba Manu yayi jim kafin yace”Kardai kace min gidan Alhassan malami a jami”ar Buk Dake Zaune a Zooroad..!
Da Dauri Sagir yace”Shi Baba!
Baba Manu yace”Ai ta kwana Gidan Sauki..Ai nasam sa makotan Marigayi yaya nane Mahaifin Sagir kafin Allah yamai Rasuwa a saida gidan suka Dawo nan gadan kaya da Zama..in hakane ba mtsala Zan nemi abokina Alh.sadi sai muje ayi mganar kada kadamu kaji..!
Imran yace”Shikenan kamar me dame ake Bukata..?
Baba Manu yace”To zuwan Farko dai Kudin gaisuwa ne za”a kai sai su Minti da goro ko Dabino da Tarbarmu ko Cafet na kayan na gani ina so..In kuma zamu kara komawa bayan mun yi mgana dasu Waliyan yarinyar sun yanke Sadaki sai muje dashi da kayan Saka Rana!
Imran yayi shuru kafin yace”in naso aje gabadaya Sau Daya fa…?
Baba Manu yace”Shi Alhaji Alhassan don ya Bukaci Haka..?.
Kai tsaye Imran yace”Ko bai bukata ba..Ni haka nake so ayi.Kuma hakan za”ayi yanzu Duka da komai da komai har Sdakin ita yarinyar nawa zasu isa..?
Abun sai ya bama Baba Manu Dariya Confident din yaron Cikin Dariyan yace”Ni kuwa ina zan san Sadakinta ni ba Ubanta ba..? Sai dai muje da kudin In sun yanke na Hannunmu sun kai mu basu in kuma da kari sai mu Dawo Mu kawo Daga baya..!
Imran ya Mike Lokaci Daya yana Fadin”Gobe in Allah ya kaimu zan kawo maka 200k..Zuwa Jibi nake so kuje gidan..!
Baba Manu yace”Wannan ba mtsala bace..Sai dai an sanar da megidan muna tafe jibin..?
Imran kai tsaye yace”Yarshi zata sanar dashi..Nagode..sai ka ganni.!
Daga haka ya juya Cikin Takunsa na Sarssarfa ya Fice Daga Gidan Baba Manu da Sagir suka Rakashi da Ido kafin Sagir shima ya mike yana Fadin”Baba sai da Safe..!
Baba manu ya Sauke ajiyar rai yana Fadin”ina ka sami wannan yaron..? Daga yanayinsa da mganarsa na gane akwai abunda yake Faruwa dashi koma ya Faru dashi Daya kara maidashi haka..?
Sagir yace”A anguwar mu suke Baba.Sune wadanda suka siya gidan Marigayi Habibu Daya rasu kwanaki fa!
Baba Manu yace”Au..Nan suke da Zama..!
Sagir yace”Eh Baba..Nima haka na gansa har muka fara abota basu da kowa anan garin koma suna dashi ban taba gani ba basu Hulda da kowa daga su sai su kawai sai ni kuma da Allah ne kadai yasan Daliln Abotanmu..!
Baba manu Dayaji Tsausayin su Imran ya kamashi yace”Allah Sarki Shi kuma Baban nasu Dayace bai da lafiya me ya same shi..? Kuma ina Mahaifiyarsu..?
Sagir yace”Wlh nima Bansani ba Baba..Abbansu dai kullum yana Daki yana kwance likita ke zuwa gida yana Dubashi kuma agidan banta ba ganin wata mace ba Daga Imran din sai yayansa Yusuf wanda shine komai nasu sai Karamar kanwarsu Maimuna..!
Baba manu na jinjina kai yace”Ikon Allah..!
Zai sake mgana suka jin Hon din Imran da karfi da Sauri Sagir ya Duka yana Saka Takalminsa Lokaci Daya yana Fadin”bari naje Baba kada ya tafi ya Barni.Labarin yana da Tsawo zan Sake dawowa sai mu Tattauna..!
Da toh kawai Baba Manu ya Bishi har ya Fice da gudu,Sai kuma ya Gyara zama yana Tunani da Nazarin Labarin da Sagir ya bashi game da Imran shidai yana ganin akwai wani abu mai Girma wanda yake cikin Zuciyar yaron kuma shike hanashi Sakin jiki Cikin mutane.
Koda Sagir ya Fita Ran Imran ya gama Baci yana Hawa Mashin din ya Fizgeta sauran kadan Sagir din ya Fadi sai da ya Rike karfen Mashin din kana ya iya Zama Dakyau Cikin Tashin hankali Sagir yace”Yanzu daman Saboda ka yi sanadiyar da zan mutu ko na jikkata ka je har gidanmu ka Daukoni..?
Imran ya saki Tsaki yana Fadin”Kamin shuru mallam..kafin na Sauya Shawara na Tsaya da Mashin din na Cikama baki da jini..!
Sagir na jin haka yayi Shuru da bakinsa Domin yafi kowa sanin Zuciya irinta Imran bamai kyau bace
Haka sukayi tafiyan ma wannan Karon Shiru har Imran din yakai Sagir din gida ko gama Sauka bai yi ba ya Figi mashin dinsa yayi Gaba Sagir ya Bisa da kallon kafin ya Girgiza kai kawai bai Shiga gida ba Shagonsa ya Shiga yana Duba agogon Hannunsa Tara ya wuce ya kamata su Rufe Shagon sai kuma gobe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button