GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai hakuri Team IMSAR❤️ kuyi Hakuri..ku kara Hakuri kila Burinku zai cika agaba ammh a wannan gabar Daada ke da Filin Dagar🏃🤣

Shakira
3/22/22, 23:14 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?6

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Mami Asma”u ta Rumgume Sajida ajikinta Tana Lallashinta ganin tana ta kuka,Dago kanta tayi tana Share mata Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin”Kalleni nan Sajida..In dai kin yarda ni Mahaifiyarki ce bazan taba bari a Rusa miki Rayuwa ta Hanyar aura Miki wannan Dan iskan ba..Ki daina kuka kinji ko My Sajida..!
Tafada Cikin son Tabbatar da mganarta ga yar Tata.
Khamis da Umaimai Dake zagaye da ita Tun bayan Ficewar kowa Daga Falon shine ya budi baki yana Fadin”Mami plz.Bana jin Dadin Abunda kike yi..Umarnin Daada ne kuma Kin Tabbata ko Dad bazai Tsallake mganarta ba ban ji dadin abun kikayi ba..Kamar yadda Dad zai bi Umarnin Daada kema Dolenki ne mganar wannan Yaron kuma am Begging u Mami ki daina Shiga Shirginsa zai iya miki komai domin baisan Darajanki ba..!
Yana mgana Mami Asma”u na Hararansa Sai da yakai Aya kana ta Saki Wani Dogon Tsaki kafin tace”Sai kawai nayi shuru a cutar dani da Rayuwar ya”ta to bazan yi Shurun ba..Mganar Dan iskan chan kuwa bazan fasa Fadin gaskiya ba duk abunda zai yi ya Dade bai yi Uban da ya fasa yaci Ubansa..!
Tafada cikin bacin rai jin haka yasa bai kara mgana ba ya Fice Daga Falon zuwa Dakunan da suke kwana Mami Asma”u ta Tada Sajida suka kamata Ita da Umaima zuwa Dakin da ta sauka ita da Umma,koda suka Shiga sun samu Umma na Sallar Shafa”i da Wuturi kan gadon dake Dakin ta Ssuke Sajida dake faman ajiyar rai Tana Lallashinta tare da mata alkawarin auran nan bazai Tabbata ba
Umaima na gefe batace komai ba ita karama ce ta Tabbata ta Fadi wani abu wanda ya saba Ra”ayin Mami Sai Ranta ya baci Sajida kuwa tana kwance lamo acikinta Ranta Tana Fatan Allah yasa a Daura auran nan Tunda take bata taba jin bugun zuciya kamar yadda take jin kan Imran ba Daman saboda shi ne yasa Har kawo Lokacin bata ga wanda yayi mata ba sai da ta gansa ta Tabbatar da yayi Daidai da Ra”ayinta Rashin Tsoronsa da Zuciyarsa ke kara Tsumata akansa Taji gabadaya ya gama Burgeta bata Damu da mganar Mami na Shaye Shayensa ba Ta tabbata in suka yi aureta Zata gyarasa ya Daina shan komai,Tasan in ta Bude baki tace wani abu Yau Mami Asma”u sai ta kwana tan Fada kamar ta ari baki Shiyasa tayi bakam kamar Itama tana cikin Damuwa da Umarnin Daadan ne nan kuwa bata sani ba Ranta Fes yake.
Umma na gefe Kanzil batace ba sanin itama Mamin ba Ragamata Zatayi ba Tunda Har Daddyn Intee Bata Ragamai ba Umaimai Dakin da su Munari suke ta koma Zata kwana Mami Asma”u na cikin Damuwa yasa bata ma bita kanta ba.
Bangaran Inteesar kuwa Kukanta gabadaya yaki Tsayawa tana kwance kan gado tana kuka,Munari da Hafsah na Zaune gefenta sun Saka Tagumi sunyi Tambayan Duniyan nan Taki ce musu komai.
Hafsah ce ta kalli Munari tana Fadin”Ko ciwon kan nata ne ya matsa mata..!?
Munari ta Sauke Taguminta tana Fadin”Ni bansani ta kuma ta ki tayi mgana..!
Tafada daidai Lokacin da Umaimah ta Shigo ganinsu haka yasa take Tambayansu ko lafiya Hafsah suka nunamata Inteesar dake kuka Har yanzu tana Dukunkune kanta Cikin Hijabinta tana Shesshekan kuka.
Umaima ta Zauna gefen gadon Tana Fadin”Ko mu kira Umma ne..?
Munari ta mike tana Fadin”Yauwa bari nayi mata mgana..!
Jin haka yasa Inteesar ta Dago kanta Cikin Shakewar Muryan data gaji da kuka Tace”Kada ki kirata Muna..!
Munari ta jiyo tana Fadin”Saboda Mene..? Kin ki gayamana meke Damunki ammh kin zauna kina ta kuka ba Dole Hankalin mu ya tashi ba..!
Inteesar ta Koma ta kwanta Tana Juya Idanuwanta da suka koma jawur saboda kuka wani suya take ji acikin Kirjunta da wani Nauyi,kamar an Dora mata wani Dutse mai girma,Cikin Dauriya tace”Ciwon kaina ne fa zai bari in na samu Barci kada ku damu dani ku kwanta abunku..!
Tafada tana kara Dunkule jikinta Waje Daya gabadaya kallonta sukayi Cikin wani yanayi batare da sun kara mgana ba suka koma suka Zauna Jugum jugum ganin haka ne yasa Inteesar din ta Mike ta Zare Hijabin jikinta Idanuwanta na Rufewa Ta Wuce cikin Sanyi sanyi ta Fada Tiolet Domin tayi wanka ko ta Daina jin Abunda take ji acikin Zuciyarta ita Damuwarta Daya Imran bata san Wani Hali yake ciki ba,Tasan Halinsa da bakar Zuciya yana Wajen nan bai dawwo cikin Gida ba,Gashi Har 11pm ta wuce Dare ya fara Nisa.
Ganin ta shiga Tiolet ne yasa sukayi Shirin kwanciya Hafsah ta Dauki Filo da blanket ta yada saman Cafet ta kwanta Munari ta saka kayan Barci ta kwanta saman gado ita da Umaima kowa na sake sake acikin Ransa.

Bangaran Imran kuwa bai san iya adadin Lokacin Daya dauka yana Busa Hayaki ba har sai da duka Sigarin ta kare gabadaya kana ya Hakura wani irin Turiri yake ji acikin Ransa sai yau ya kara jin Radadin Rashin Uwa ya tabbata da yau Anni na Raye da zama bango garesa ammh Saboda bai da Uwa yau ga abunda ya Faru dashi domin ya Daukesa ne a mtsayin Tozarci Abunda Mami Asma”u tayi mai Abba ba”a sakashi a Lissafi sanyinsa yayi yawa,agaban Daada da yan”uwansa Baya Daga Murya Tun farko saboda haka yasan bazai ce komai ba ammh shi Dole ne yayi mgana.
Kafafunsa ya Hade waje daya ya Saka kansa Tsakanin Cinyoyinsa ya Fashe da wani kukan Dayaji yana Tasomai Daga kasan Ransa,Rabonsa da kuka Tun Lokacin Rasuwar su Anni sai yau Zuciyarsa nada Taurin da kuka ba kasafai yake iya yinsa ba sai dai Zuciyata tayi ta kuna ammh yau yaji yana son yayi kuka kukan Rashin Mahaifiya agaresa,Kukan Rasa Anni yana Tuna Sanda Tana Raye mai kula dashi,Tana fadin Imran ka dinga shiga Mutane ka Rage wannan zuciyar taka Saboda Rayuwa in yau mune watarana bamu bane Imrana ina jiyemaka Ranar da zakayi kukan Rashina Rashin mai fadamaka gaskiya…
Haka yake jin Amon muryanta acikin kunnuwansa kamar alokacin take Fadamai sai ya kara Fashewa da kuka ammh Abun mamaki babu ko Digon Hawaye sai dai idanuwansa sun kala sun yi Jajir,Haraban gidan Tar yake da Hasken Wutar lantarki,Shiyasa Megadi dake zaune bakin get kan bencinsa yake Hangensa,Tun Lokacin Daya Fito ya gansa yana shan Tabarsa kada kai yayi kawai bai ce komai ba ya Cigaba da jin Radion sa.
Inteesar ta bata Lokaci kafin ta Fito Daga Tiolet din wanka Tayo ta Dauro alwala Domin taji barcin ya Fita Daga Idanuwanta kanta nata Sara mata ga Nauyin kirjin datake ji wanda ta rasa Dalili ta iske dukkansu sunyi barci.
Wata Rigar barcinta ta saka Riga da wando masu Taushi ta saka Hijabinta ta Daidaici gabas ta tada Salla Shafa”i da Wuturi tayi Kafin ta zauna nan inda Tayi sallar ta jingina da gado Ranta namata Daci ita ba wai wani abu ba Bata son Ya Imu ya auri wannan marar mutumcin bata Dace dashi ba sannan Cin Zarafin da Mami Asma”u tayimai yau ya bala”in sosa mata rai Bacin ran Imran bacin ranta ne in wani abu ya samesa sai taji duk ta Damu wayarta ta jawo Dake saman gado ta Duba Lokaci 12:12am na Dare jikinta yayi sanyi Tana Tunanin Ya Imran ya Dawo cikin gida ko yana Waje..!?
Wajen sako ta shiga ta Turamai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button