GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


Baffa Kabiru ya samu zuwa Anambara Har gidan Khamis inda yake Zaune gidansa Daya mallaka Halak malak,Halin da Baffa yaga Khamis sai ya Dawo Abuja yana kuka da Idanuwansa yana Durama Mami Asma”u Allah ya isa.
Yaje yaga Khamis ya Kazance ya koma Cikin Wata Rayuwa,Shaye shaye ga Shan Giya shi yaci Uban Taba,harda Wiwi yana sha,ga Harkan mata Koda Baffa Kabiru ya isa gidan cikin maye ya iskesa ya Tara Kasumaba Duk yayi kazanta Harda mace ya gani agidan,Baffa Kabiru kuka Shabe Shabe Bai iya kwana agarim ba,Har ya baro garin Khamis baya Cikin Hayyacinsa bai san ma yazo ba tun a Garin ya Daga Waya ya Kira Mami Lokacin Tana Hanya Zata Dawo makaranar su Sajida da aka Kirata Bata da Lafiya har an kwantar da ita a Clinic din makaranta Tayi kuka sosai Data ga Halin da Sajida Take Ciki sai dai Sajidan ta nuna ma Mamin Ulcer ce ke Damunta Saboda Tana Zama da yunwa ba komai ba ta Boyemata yadda Take Tarin jini wani Lokacin Achan makaranta ta wuni sai da Taga Sajida ta koma Hostel Tayi Tayi ta Bita Gida Taki ta Fake da Sun kusa Fara Jarabawa Bata so tayi Loosing abunda bata sani ba Mami Taje ta Duba result din Sajidam sai da taji Tsoro ta kuma Tabbatar ma kamta Sajidan Rabuwanta da Imran ya tabata Gabadaya Tayi kasa sosai G dinta Low,Kowa kuma yasan Sajida da Kokari ammh Yanzu Har an yi mata Warning din Kora Daga Deparmnt Mami Asma’u ta baro makaranta cikin wannan Damuwar Tana Tafe tana Driving Tana kuka Har ta kusa Bugama wani Mota ya leko yana ta Zagimta Dayasan Halin Datake ciki Da bai Tsayama bi ta kanta ba Da yayi mata Uzuri.
Bata kai ga isa gida ba Kiran Baffa Kabiru ya shigo wayarta karo na Farko Bayan Abunda ya Faru Wata Shida Cikin na bakwai.
Da farko ta Zata gizo idonta ke mata Har ta katse bata Dauka ba sai da ya kara Kira kana ta Zabura Tana Dauka Tana Sharan Hawaye sai Fuskarta ta Cika da Alhini da Kuka Data barke da shi bayan jin Abunda Baffa Kabiru yake Fadamata Cikin Kaushin Murya”Asma”u me zan ce miki..?in nace na barki da Allah Kamar nayi miki adalci Gwara na Miki Allah ya Isa Allah ya isa Asma”u ko naji Sanyi a Raina Kin Zama Silar Tsarwata Rayuwar ya”yana da bani da kowa sai su..kin ta aibanta Imran kina Kiransa Mai Shaye Shaye Dan iska To Shi Taba Kadai yake sha D’anki gashi chan yana Kora Giya da Wiwi yana Budema Mata Rayuwarss gabadaya kinga Illah aibata D’an wani da Mugun bakin ki ya kamaki me zaki ce..?Kin Ruguzama Sajida Duka Rayuwarta Kin saka Tayi Sallama da Farincikinta In ban yi miki Allah ya isa ba Me zan ce miki..?
Wlh bazan yafe miki ba Asma”u yadda Kika sani kuka Insha Allahu kema sai kinyi mafiyin nawa..!
Ko Cewarta bai jira ba ya Datse Kiransa yabar Mami da kuka Allah yasa Kafin ta amsa Wayar sai da Ta Faka Motar agefen Hanya da Allah kadai yasan Irin Hadarin da Xata Hada kanta ta Hade da Sitiyarin Motar Tana kuka kukan Wurjajan kamar Mahaukaciya afili Take Fadin”Ai nama Fara Kuka Kabiru..Na Dade ina kuka kai ne baka sani ba..Kaicona Ni Asma”u na Kashe Kaina da kaina na Illata Duka Rayuwar ya”yana ba Auran ba Farincikina ya”yana Innalillahi Wa”inna Ilaihirraju”un haka ta Ke Fada Tana Dafe kanta Datake jin yana Barazanar Fashewa Lokaci Daya Tana gunjin kuka.
Dakyar ta iya Rarrafawa Ta Tada Motar Zuwa gida aharaban gidan Da tasamu ta isa Dakyar bata iya Fitowa Da kanta acikin Mota ba sai dai Fito da ita akayi Jiri Take gani Hajiya Turai ta Firgita da ganin Mamin Aranar sai da Likitansu yazo ya Dubata ya Dauramata Drip tana kwance Tana Fadin”Kaico na..Kaico na ni Asma”u..Ya”yana mijina..!
Haka take ta Fada tana Kuka Hajiya Turai Jikinta ya gama yin Sanyin Ta Fita Taje wajen Justice tace ya Kira Kabiru ya Rokeshi yazo su Daidaita da Asma”u yace bazai Kirasa ya Tursasa ba Sanda yake bama Asma”u baki ai bata Jisa ba Shi ba Ruwansa abunda ta Zabama kanta kenan.

Shakira…
3/30/22, 20:57 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?30

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Asma”u ta rasa ta ina Zata farama Hajiyarsu bayanin abunda ya Faru Kunya take ji ita kanta in ta Tuna Kabiru yayi mata Allah ya isa ya Fada ya kara Fada Allah ya isa bai yafe mata ba Ta ina Zata Fara wazata Tunkara da zai saurareta Ballatana ya Fahimceta duk inda taje itace akasa Bata da gaskiya tabi son Ranta da son kanta Eh mana gaskiya ne Tana da son kamta mana in ba Domin haka ba da ta Duba Ya”yanta da Mijinta ta ijiye son Ranta da Tabi Ra”ayi da duka Muradan Mijinta da ya”yanta Kaiconta haka take ta Fada Tana kuka kamar Zatayi hauka.
Hajiya Turai ta Damu kwarai da gaske ganin haka yasa ta samu Mami Asma”u tana kwance bayan kwana Biyu Da kiran da Kabiru yayi mata Gabadaya ta Fige ta rame Ita kanta tasan bata da lafiya Jiri take gani in ta Mike duk da mgungunar Likita ammh Saboda bata cikin Kwamciyar Hankali ko sau Daya mganin bai mata amfani ba Batama sha sai Hajiya tazo ta mtsamata to gani take ko ta sha bai da amfanin Halin Datake ciki Mgani bazai Lafar da komai ba bazai Hana Wutar Nadama da kuskuran Data aikata ci acikin Zuciyarta ba.
Kwance ta sameta yaraf kamar ko yaushe kamar kayan wanki gabadaya Jikinta ya gama saki kamar mai Cutar Shanyewar barin jiki ba na barin Jiki bane na Mutuwar Zuciya ne
Kuka Take na Boye dana Sarari hawaye sun riga sun gama Samun Matsungguni akan Fuskarta Kukan Zucci kuwa Shi take kwana Tana wuni Tanayi,batare da tasan Hanyar da Zata Dakatar da hakan ba
Har Hajiya Turai ta shigo ta Zauna gefen gado kusa da Mami Asma”u bata sani ba ta Riga tayi Zurfi Cikin Tunanin Daya Zameta abun yi akoda yaushe Zafafan Hawaye suna Kwaranyomata.
Hajiya Turai Ta Kira sunanta Har yafi sau uku bata jita ba sai da ta Tabata kadan Tare da Girgizata Lokaci Daya Kafin tayi Firgigit ta dawo Cikin Hayyacinta daga Zurfaffan Tunanin Data Fada idonta ya sauka akan Hajiyarsu Saurin Share kwallah Tayi kafin ta yunkura ta mike Tana Fadin”Hajiyarmu yaushe kika shigo..?
Hajiya Turai tace”Ina Zaki san na Shigo kin Shiga Cikin Tunanin ki na Fama..?sau nawa zan Fada miki wannan Tunanin da kike yi da kukan nan bashi bane Mafita ba,Likita ya Fada miki ki Daina yawan Tunani da Damuwa saboda Jininki ya Hau sosai..!
Mami batace komai ba illah kanta Data sadda kasa Hawayenta na Diga har kan Cinyarta,Kafin tace”Ya zan yi Hajiya..?kukan shi kadai ne mafita na Na Rasa komai na Rasa aurena na Rasa Ya”yana da Duka Martabana Hajiya ya zan yi..! tafada tana Kara Sautin kukanta
Hajiya Turai kai Tsaye tace”Akwai mafita ki nemi Kabiru ki basa Hakuri ku Daidaita kanku..In ya”yanku suka ga haka suma Hankulansu zai kwanta..Nasan nima nayi kuskurre a Mtsayina ta uwa gareki ban Fadamiki Gaskiya ba sai na rika Zugaki Har Kika Tafkan wannan Kuskuran nima sai Daga baya na Fahimci Bamu kyauta ba Dagani har ke shiyasa nake so ki gyara Kuskuran ki ki same sa ki basa Hakuri ya maidake Dakin ki Daga baya sai komai ya Biyo baya..!
Mami Tasaki Mirmishin Dayafi kuka Ciwo kafin tace”Ai bazai Saurareni ba Hajiya..Gabadaya Tun bayan Faruwar lamarin Ya yanke duk wata Hanya da zai sa mu hadu..Bazai taba Saurarata ba Hajiya na Rantse..!
Hajiya Tayi shuru kafin tace”To ya za”ayi kenan..?
Gashi kuma Justice yace bazai Kira sa ba..!
Mami Asma”u batace komai ba ta koma Ta kwanta Tana jan majinan kuka,Hajiya Turai ta girgiza kai kafin Ta tashi ta Fice Cikin Nadaman Gudummuwar Data bata Wajen Kashe ma yarta aure da Lalata gabadaya Mafarkinta Tabbas itace sila in da a mtsayin ta na Uwa ga Asma”u ta bi Hanyar daya Dace da duk haka bai Faru ba Mami kuwa kuka kawai take Tana Tunanin mafita haka take Wuni ta Kwana cikin Daki bata Fita Tana Tunanin mafita da yadda Zata gyara Abunda ta bata….
Tayi ta Kiran Lambar khamis bata Samesa ba Ta Kira Wayar Sajida ta shiga ammh bata Dauka ba,sai Daga baya ta Kirata Daga yanayin Muryanta tasan bata da lafiya ammh sai tace mata taji Sauki Mami batabari Sajidan ta gane bata da Lafiya ba sai ta Boye mata adaran Jiya Ta samoma kanta mafita Batare da ta Yi shawara da kowa ba ita kadai ta Bata kuma ita kadai Zata gyara.
Bata cikin karfin jiki Jiri ma take gani Ta Riga Tama Direban da zai Tukata mgana Tun Safe ta Shirya ba wani Shiri Tayi ba Kamar ba Asma”u yar gayu ba Tuni Gilashin idonta ya kama gabansa ma bata san isalinsa ba Tana ta kanta ne Figai Figai da ita ta Fito Ta Samu Hajiya Turai ta Fadamata Zata je wani Waje sai yammah Zata dawo.
Hajiya Turai ta kalleta sai dai batayi mgana ba ta mata Fatan Dawowa Lafiya.
Daganan ta Fice Direba ya Tukata suna Fita tace mai Dukku Zataje ba Musu ya Take Mota suka Dau Hanya ta Riga ta gama Neman ma kanta Mafita Zuwa dukku shine Mafitanta zataje ta Duka har kasa Ta bama Daada Hakuri ba domin Kabiru ya maidata Dakinta ba ko Zata ga Haske a Rayuwarta Sajida tana Halin cutar da taki barin Ma a Dubata ballatana agane meke Damunta ga Khamis ya koma Wani iri,Irin yadda take aibata ya”yan wasu Kai innalillahi rayuwa ta Juya mata baya bazata iya ita Kadai ba Wlh bazata iya ba wannan Nauyin yayi mata yawa Tabbas bazata iya ba.
Har suka isa Dukku Mami Asma”u na kuka Hawayenta basu Tsaya ba lokacin da Baba Asabe ta shigo Dakin Daada Tana Fada mata zuwan Mami Asma”u din bata gama mamaki ba sai da Taga Mami Asma”u din Tsoron Allah ya kara kama Daada da Tsoron Duniya ganin yadda Mami ta koma Daada Sai Tayi kwallah Lokacin da Mami Asma”u ta Zube agabanta ta duka ta Dafa kafarta tana kuka Tana bata Hakuri Tana Fadamata irin Halin Datake ciki da Halin da Sajida ke Ciki da Halin da Baffa Kabiru yaje yaga Khamis aciki Mami Asma”u na Kuka hawayenta na Diga saman Kafafun Daada Dake Zaune take Fadin”Ki yafemin Daaada..Wlh nayi Nadama..Na Fahimci Abunda na aikatane duka suka Dawo kaina Daada Wlh bazan iya ba nayi Rauni nayi Laushin da bazan iya Daukan abubuwanan ba ni kadai Daada Kabiru ya Kirani yamin Allah yasa isa kan Ya”yansa Daada ina zan Saka kaina..?Wlh hakkin ku ne keda Imran da Malami da su Mustapaha da kukan da na Sakaki shine yake Bibiyata ban yi Tunanun kema kamar Uwa kike gareni ba ko Tsinemin kikayi sai na Bi Duniya..Don Allah da Zatin Allah Daada Kiyi Hakuri ki yafemin..!
Daada Kwallah sai da ta Cikamata ido Ta saka Hannu ta Dago Mami Asma”u Data Durkushe gabanta Tana kuka Hawaye Shabe shabe hannu Daada ta Saka Ta Share mata Hawaye Tana Fadin”Wlh ban ta ba Rike ki araina ba Asma”u na yafe miki..Kuma suma zasu yafe miki..Ai tunda kin gane Kuskuranki bawanda zai ki karban Tubanki..Kabiru bai Fadamin Halin Daya je ya Samu Khamis ba Bansani ba..Ammh Zan Kirasa baza”a Zura ido ba su hadu shi da yan”uwansa suje su Taho Dashi Damuwace tasa ya shiga Halin Daya shiga ammh da Izinin Lahi Komai zai koma Daidai ki Daina kuka bakomai Insha Allahu..!
Mami Asma”u na goge kwallarta Tana Fadin”Bayan Damuwa harda Silar Bakina Daada nayi ta aibata Imrana Ina Kiransa da sunayej banza..yau gashi Duka sun Tabbata kan Da”ana Daada Sakayyace Allah ne ya kamani Kaico na..!
Tafada Tana Kara Saka Kuka Daada na Lallashinta Cikin Zuciyarta Tana Tsausayin Kabiru Lokaci Daya Kaddara ta Fadamai Allah Sarki yana chan cikin wannan kunar ga Asma”u Yadda ta koma Ko da wannan ka kallah Zaka Gane Allah shine gagara Misali.
Bata yadda ta Fadama Mami Har Lokacin ita Matar Baffa bane sai dai ta Lallasheta ta kuma mata alkawarin Zatayi magana da Baffa Kabiru Sajida kuma zata dawo gida Domin asan meke Damunta Mami Asma”u bata jima sosai a Dukku ba Hankalinta ya kwanta jin Daada bata Riketa aranta ba Dakyar ta Tsaya taci abinci Sama Sama Tayi ma Daada sallama Direba ya Juya da ita,Daada ta bita da kallon Tsausayi.
Tana Tafiya ta saka Baba Asabe ta Kira mata Baffa Kabiru Dake chan yana Faman Kokuwa da Zuciyarsa shi kanshi Tun bayan Dawowarsa Anambara Da ganin Halin da Tilon Dansa ke ciki bai da Cikakken Lafiya yayi kuka har ya Gode Allah kwakwalwarsa Ta toshe yarasa Tunanin ma me zai yi..?ballatana ya Samu Mafita Lokacin Daada ke Fadamai zuwan Asma”u bai ji mamaki ba sai dai bai Zata Zata karaya haka Cikin Sauki ba ya Dauka Bata gama ganin komai ba yanzu ta Fara gani nuna ma Daada yayi karya Take duka kukan Munafunci ne Daga baya kenan bayan ta gama Lalata komai..?shi yanzu yadda zai Dawo da Rayuwar Khamis kamar baya yake Tunani Tunda Taje ta Fadama Daada komai,Daada tace maza ya Kira yan”uwansa aje a taho da Khamis Gida yafi a barsa chan inda bai da kowa abakin Daada yaji Labarin Rashin Lafiyar Sajida shi kanshi in da Zai kwanta adubasa Wlh Jininsa ya Hau har suka gama mgana Da Daada baya Cikin Hayyacinsa Hawaye da kuka sun Rufemai jinsa da ganinsa Allah yasa yana gida kwana Biyun bai je ko”ina ba.
Sai da ya Samu Natsuwa ya Kira Abba da Daddy ya gayamusu komai suma Hankalinsu ya tashi Daddy yace Da kansa zai hau jirgi zuwa Anambara Gobe zaiTaho da Khamis Basai Abba da Baffa Kabiru sun taho ba Yace Baffa Kabiru ya turamai Address din nan da nan kuwa ya Turamai sun Rabu kan Gobe zai tafi Sajida kuma Zai je Har makaranta ya Taho da ita Gida.
Ashe abunda basu sani ba Khamis bayan ya Dawo Daga Hayyacinsa budurwansa abokiyar Watsewarsa Tasa mai suna Suzana,Ta sanar dashi Zuwan Mahaifinsa da Halin Daya Tarar dashi,Batasan Baffa Kabiru ba ammh Kamarsu da Khamis da kuma cemata da yayi shi babansa ne aranar Dayazo bayan ta Budemai kofar Falon Gidan.
Gabadaya Jikin Khamis ya gama yin Sanyi Tsoron Allah ya kamashi da wani ido zai kalli Dad dinsa..?wata amsa zai bai bashi in ya Tambayesa meyasa ya koma haka..?yace Saboda Rasa Mace..?ya koma Sabama Allah..?wannan duka ba Hujja bane ya karya Zuciyar uban Daya Dora yakini akansa Tir da Rayuwar Daya Zabama kansa Tundaga Ranar ya Tattara komai ya Watsar Tare da alkawarin Har Abada bazai kara ko Busa Sigari ba ballatana Har ya Daga wata kwalba ya Rufe babin mata da komai na Harkan Shanshanci Har Abada ya Fara Shirin Tahowa gida Domin ya Nemi Gafaran Daad ya yafemai Laifin Daya aikata.
Aranar da Baffa Kabiru sukayi mgana da su Abba da asuba Khamis ya Sauka a Filin Jirgin Abuja Taxi ya samu zuwa Gida sai dai Baffa Kabiru da Umaima suka gansa Kwatsam Allah Sarki Rayuwa Khamis yayi kuka sosai Dayaga yadda ya tafi ya bar Baya da Kura Mami Ta Dade bata gida sun Rabu da Daad Sajida Tana makaranta Cikin Halin Ciwo shi kuma yana chan yana Shanshanci Kai consa,Abakin Umaima yake jin komai Domin Sanda ya iso Dad na cikin Dakinsa sai da ya Fito ya gansa..
Haka Khamis ya Duka ya Rike Kafafun Baffa Kabiru yana kuka yana Rokonsa Gafara Tare da alkawarin ya Daina Duka Abunda yake yi Har Abada bazai koma ga aikin Daya baro ba Me ya kamata Baffa Kabiru yayi banda ya Tallafi D”ansa da Allah ya Dubesa ya Karkatomai da Hankalinsa kan Hanya Madaidaiciya ya Rumgumesa yana Godiya ga Allah Hawaye na Ziraromai bai bari Khamis din ya gani ba yayi Saurin Dauke hawayen..
Nan da nan Baffa Kabiru ya Kira Daddy ya Fadamai ya Dakata da Tafiya Anambara ga Khamis ya Dawo gida da kansa jin haka yasa yayi Hamdala Daddy ya Kira Abba ya Fadamai Khamis ya Dawo gida Abba ma Nata Hamdala sun isa Barka.
Aranar ma Baffa Kabiru bai Fita ba yana Tare da ya”yansa Khamis da Umaima Domin ya Dauki Daraman Gyaran Duk inda ya Kuskure Domin Dawo da walwalan ya”yansa sun yanke Shawaran gobe da safe dashi da Khamis zasu je makarantan su Sajida su Taho da ita sai dai Misalin karfe Daya na Dare Sai ga wayar Mami Asma”u ta Kira Baffa Kabiru karo na Farko Bayan Lalacewar abubuwan Daya ga Kiran bai Dauka ba Tunda Idonsa Biyu Har Lokacin bai yi barci ba Mugun Haushinta yake ji Gani yake Munfuncine ba Tuban Allah da Annabi bane gani tayi ba Sarki sai Allah ta kuma Rasa komai Shiyasa ta Dawo Tana Rabe Rabe Macijiya.
Sai da yaga Kiran yaki ya kare kana ya Daga afusace ya auna mata ashariya ko Ta kyalesa sai da jinta Cikin kuka Tana Fadamai gasu a asibitin Specialist Hospital inda aka kawo Sajida bata da Lafiya Tana ta Tari da Jini Jin haka yasa Hankalin Baffa Kabiru ya kara tashi Cikin Tsananin Tashin Hankali ya Zura Jallabiya ya Fice Dakin Khamis ya shiga ya tasosa hankali Tashe yake Fadamai Halin da ake Ciki,Shima Hankalinsa ya Tashi Umaima ma Muryansu ya tasheta Daga Barcin Daya kwasheta itama jin Abunda ya Faru da yar”uwanta sai kuka Gabadayansu suka Dunguma suka Tafi.
Koda suka je sun Iske Mami Asma”u da Hajiya Turai da Justice Tafida yarkace yarkace sai kuka Take TanaTuma kamar Mahaukaciya Idanuwanta sun Kole saboda kuka Ita jenefer ta Kira saboda itace Lambar Karshe da Sajidan Tayi mgana da ita suna Kwance adaki Sanda Tarin ya Sarke Sajidan da Zafi Har ta Fita Daga Hankalinta Jenefer ita taje ta Fadama Maman Hostel dinsu ita kuma ta Sanar da kuma Hukumar makaranta aka Kwaso su zuwa asibiti bayan an Shiga Da Sajida Emergency ne Ta samu Wayar Sajidan ta Kira Mamin Ta Fadamata wanda Kurruwanta ya Fito da Justice da Hajiya Turai jin Abunda ke Faruwa yasa suka Rankayo Gabadayansu Cikin Tashin Hankali.
Ita uwa uwace ko ya ta Zama Haka Umaima da Khamis suka isa ga Mami Asma”u suka Dagota suka Rumgumeta suna Lallashinta Data kyalla ido Taga Khamis sai Rauninta ya bayyana ta Fada Jikinsa Tana Fadin”kaima ka Gujeni Khamis..Dad dinku ya sakeni Sajida Zata Mutu ta barmu Aman jini fa take..an shiga da ita Likotoci basu Fito ba Har yanzu na shiga ukuna na Lalace..!
Haka take fada Cikin kuka tana Rike Jikin Khamis da shima yake jin kamar ya Fashe da kuka Idanuwansa sun yi Jajir kukan Mami kuka ne da zai Kassara Duk zuciyar mai Sauraranta Ammh banda ta Baffa Kabiru bayan gaisawa da Justice Tafida da Hajiya Turai bai kara mgana ba sai gaisuwan abokiyar Karatun Sajida Jenefer Daya amsa ko Barayin Mamin bai kallah ba Ballatana ta saka Ran wani Rahma Daga bangaransa.
Gabadaya Hankula basa kwance Fin Mintina arba”in kafin Likitocin da suka Rufu kan Sajida su Fito basu tsaya amsa ma su Baffa Kabiru Tambayansu ba sukace jictice Tafida ya Biyosu Office shi da Baffa Kabiru Matan su Tsaya a waje.
Baffa Kabiru ya Razana Dayaji bayanin Likita kan Abunda ke Damun Sajida ta Hadu da Heart problem Ciwon Zuciya Wanda har ta Fara Tabuwa saboda matsanancin Halin Datake Ciki Ta fara ganin jini in tana Tari bata zo asibiti ba har abun yayi yawa,Ammh dai yanzu ta Fita Daga Cikin Hatsarin Datake ciki sai dai Duk Abunda akasan Tana son gani ko Tana so a kawo matashi gabanta da Zarar ta Farfado in ba Haka ba zata samu Heart Attack arasa ta gabadaya.
Baffa Kabiru Haka yake sharan kwallah Da Gaske Sajida take Tana son Imran Asma”u ta rabata dashi Gashi Soyayyarsa zai Zama ajalinta Shi kanshi Justice yaji Mganar sosai Jikinsa yayi sanyi shine ya iya Fita yayi ma su Khamis Bayanin da Likita yayi musu ai sai Wajen ya kara Rikicewa Mamin Har wani Suu Tayi Zata Fadi Hajiya Turai da Khamis suka Tarota kasa takai hannunta Saman kanta ta manta asibiti suke ta Kwarara Ihu Tana Fadin”Na shiga Uku..Na Shiga uku Ni Asma”u na lalace..!
Baffa Kabiru da Ransa ya baci Tana Neman Tara musu jama”a Allah yasa ma Dare da sanin su manyan Mutane ai da ba haka ba wata Gigitattaciyar kara ya Daka mata Cikin Kaushin Murya ya fara fadin”Dillah kima Mutane Shuru..Kukan Uban me kuma Zaki mana..?kukan karya da munafunci..?ko na nadaman Dole..?duk abunda ya Faru da Sajida kece Sila…ke kika Rabata da abunda take so kika yi Sanadiyar Shigarta wannan Halin sannan kizo ki Damemu da kukanki na Banza Baki bani kin Lalace ba Asma”u Sai Y’ata ta Rasa Ranta ta Dalilinki na Rantse da wanda Raina ke Hannunsa sai nayi Shari”a dake sai kin Biyani Diyar kashemin yata da kikay Muguwa kawai azzalumuma mai Zuciyar Zalunci wacce batasan komai ba sai kanta.!
Ya karishe Fada Cikin Sakarmata Jajayen Idanuwansa da suka Rine Saboda kuka
Ba wanda iya mgana sanin ai gaskiya ya Fada Mami Asma”u jikinta na rawa da bakinta ta kasa mgana Jikin Khamis ta koma ta Lafe Umaima ta Kwantomata Tana kuka ai ita kukan natama ya Tsaya ta shiga wani yanayin da bawa bai isa ya Fassara ba.
Hajiya Turai ne cikin Damuwa tace”Haba Kabiru don Allah ka Ragama yarinyar nan mana..Tafuskanci abubuwa da yawa ko baka Ragamata ba Saboda Zaman tare ba ai ka Ragamata saboda Daranjanmu iyayenta Dake Tsaye da su kansu Yayanku gasu nan da kuma Wacce ke kwance cikin nan Cikin Kokawaa da Numfashinta..!
Ai in ma ya Bude baki yace wani abu Allah Zagin Hajiya Turai zai yi shiyasa yayi Shuru ya Dauke kansa yana ajiyar Zuciya
Sai Wurin yayi Tsit sai Jan majinan Umaima ake ji Mamin kamar ai Wutarta ta Dauke justice kala bai ce Daman ba kuma zai ce ba Wanda bai ji bari ba bazai ji Hoho ba
Dukkansu Zaman jiran Farfadowam Sajida suke Gabadayansu suna asibitin aka Kira sallar asuba kana Mazan suka tafi masallaci cikin Asibitin Harda matan sukayi Sallah Kowa Zuciyarsa ba Natsuwa Jenefer sai alokacin Tayi musu sallama ta koma Cikin makaranta su kuma tunda suka Dawo Sallah ba wanda ya Mtsa suna Fatan Sajida ta Farfado Cikin Hankalinta.
Saboda Tashin Hankali yasa Baffa Kabiru ya mamta da Kiran kowa Sai da Sajida ta Farfado Daman Tana Emagency din har alokacin Likitoci sun Rufu kanta ammh ba sunan Datake Kira sai sunan Imran kuma Rashin Ganinsa Cikin Lokaci Mtsala ne haka Likita ke sanar dasu Baffa Kabiru Hankulansu ya kara tashi an basu Izimin Shiga su ganta Mami ce kan gaba Kamar Zata Kifa Tana Shiga Tafada jikin Sajida dake kwance Rai kwakwa Duk ta Rame tana mai Fashewa da kuka Tana Fadin”Ki yafemin Sajida..Dom Allah ki yafemin..!
Sajida Tana kuka Tana Rike Saitin Zuciyarta Tana Fadin”Mami Ku kiramin Imran in ban gansa ba Mutuwa Zan yi..!
Take Fada Tana kuka Gabadayansu Sun Zagayeta masu Saurin kuka irin su Hajiya Turai da Umaima suna ta Faman Sharbawa Justice Tafida ne ke Fadan Mami Ta Daga Sajida bata ga bata da Lafiya bane kuma ta Danneta Tana kuka Khamis kuwa Gefen Gadon ya Durkushe yana kokuwa da Numfashinsa.
Baffa Kabiru waje ya Fita yana Dauke kwallarsa bazai iya Juran ganin Sajida ahaka ba ba ita ya kamata ta Fuskanci wannan ba Asma”u ita ya kamata ta karbi wannan Hukunci.
Kai Tsaye Abba ya Kira da Daddy ya Sanar dasu abunda ke Faruwa Hankalinsu ya tashi Kwarai Tare da Tsausayin Dan”uwansu dukkansu sun Tabbatar mai gasunan zuwa yanzu zasu kamo Hanya.
Daga su sai Imran Baffa Kabiru ya Kirasa Lokacin ya bar Gida zuwa Wajen aiki ne Jiya gidan Abba suka kusa Raba Dare Khalil ne jiya ya zo Daga Lagos wajen Munari mgana har Taje kunnensu Abba Tunda Dr.Ali argungun ya Kira Abba sun yi mgana,Wajensa ya Tsaya suna Hira da kuma Rigiman Inteesar na da sai ya barta ta Kwanan anan ya Tubure mata ya dawo Mata a Imran dinsa da baya Daukan Raini ballatana Wargi Dole ta biyosa suka Dawo Ko yau da Safe ya Fita ya barta Tana ta Fushi ya Fita Batunta daya dawo ya Fara Lallashinsa Zata mamta komai ta bada kai Bori ya hau.
Lokacin da Baffa Kabiru ke Fadamai Halin da ake ciki jikinsa yayi Sanyi sai bai kara yin sanyi ba sai da yaji Baffa Kabiru na Rokonsa Allah da Annabi kan yazo yaga Sajida kafin ta bar Gidan Duniya yana mgana Daga jinsa kuka yakeyi Imran bai taba Jin Tsausayin Baffa Kabiru ba irin na Wannan Ranar ba har baisan Sanda ya Tabbatarmai da Insha Allahu yana Tafe yanzu da yardan Allah..
Jikinsa a sanyaye ya Tattara kayansa ya Biya Office din Manaja ya Fadamai Uxurin Rashin Lafiya ne yamai Izinin Tafiya ya Fito Daga Bankin kenan yaji Kiran Abba ya Dauka sukayi mgana Abba yana Fadamai Halin da ake Ciki yace Yanzu Baffa ya Kirashi shima Abujan zai tafi yanzu Abba yace yaje ya Dauko Inteesar gabadayansu Zasu Tafi da haka suka Rabu.
Gida ya koma Inteesar na Kwance da Matashin Cikinta yace ta tashi ta sa Hijabi su tafi shi ya Zata gidan Abba zata zauna kafin su dawo jin Tafiyace ta Mike da Murna ta saka Hijabi suka Tafi koda sukaje sun iske har Ya yusuf shima dashi Za”a tafin bai je aiki ba Khalil ma yace dashi Za”aje Kowa yace sai yaje harda Munari Anty Safiya ce kadai aka bari agida Tana jego Saboda Yadda Labarin ya same su sun matukar Tsausayamata da Halin Datake ciki,ganin haka yasa Itama Inteesar tace sai taje itama Imran bai da yadda zai yi ya Hanata zuwa ammh bai so bayaso gudan Jininsa ya Wahala sosai ammh baida yarda zai yi.
Ashe Labari Tuni ya Zaga Dangi suna Shirin Tafiya sai ga Wayar Sadam shima zai je basheer ya Kirasa ya Fadamasa yace ya Kira sa”id shima ya Tabbatarmai da yana Hanya Duk wanda yaji Halin da Sajida Take Ciki Sai ya Tsausayamata.
Sadam suka Tsaya jira ba Dadewa sai gashi Shi kadai ne Aneesa na Gida da Yara Imran ya Kira Sagir yace ya Shirya su tafi Daman jiya su ukun suna Tare sun Hade shi da Khalil suna ta Caccakasan yayi musu banza.
Imran a Motarsa ya Dauki Khalil da Sagir Ya Hada matan chan Motar Yusuf,Abba dagashi sai Direbansa hakama Ya Sadam suka Dauki Hanyar Abuja,suka bar Anty Safiya Dayake Tasleem na Tare da ita ga kuma Mama
Achan kaduna ma Daddy Da Umma sai Ya Basheer Dake Tukasu suma din duka Hankalinsu ya tashi goggo Bintali da goggo Maimunatu suma sun ji labari Daddy ya Kirasu ya Fadamusu,Daada ce kadai basu Fadamawa ba Gudun Tashin Hankalinta,Dukkansu sun kamo Hanya basu zauna ba Domin Haka suna da kara iin wani abu ya Faru da nasu kwansu da kwakwartansu.
Daddy su suka fara isa Abuja waya kadai yayi ma Baffa Kabiru ya basu kwatancen Inda suke,Daman yasan asibitin nan take sai gasu sun iso Lokacin an kai Sajida ma Daki na Musamman kebabbantacce.
Koda suka iso an mata Alluran barci Ta samu barci ganinta Tana ta kuka da Sambatun Kiran sunan Imran Umma ta kara jin jikinta yayi Sanyi ganin yadda Mami Asma”u ta koma Kunya Ya hanata ta iya Daga ido ta kalli kowa Kukan ma ya Daina zuwar mata sai ajiyar zuciya kawai ta Jeme kamar ba ita ba Shi kanshi Daddy sai da ya Jinjina.
Gudu sosai sukayi a Hanya kafin su iso,wajen azahar suma Direct asibitin suka iso,Mami Asma”u ta kasa Iya Hada ido da su Abba ballatana Imran Kusan Lokaci Daya suka iso da Inna Maimunatu da Mijinta ,Inna Bintalo ma ta iso
Daddy da Abba Dan”uwansu suka Rumgume cikin Damuwa da ganin yadda shima Duk ya Jeme Saboda Damuwa su Sadam suka isa ga Khamis shima abun Tsausayi Umaima ta Rumgume Munari Tana ta kuka,ba Dadewa sai ga Sa”id ya iso Shi da Fareesatu da Hafsah da yara Inteesar dai na makale da Umma itama Duk jikinta yayi Sanyi,Khamis kuwa Sau Daya ya kalli Inteesar bai kara ba haka itama Imran na Tare da abokansa Sagir da Khalil,Sai dai Kuma karo na Farko da yaji Taausayin Mami ya Darsun mai ganinta a rakube Duk ta Fige ta Rame kamar ba ita ba Rayuwa kenan Dayake Justice da Hajiya Turai sun Koma Gida Dazu bada Dadewa ba
Kamar Sajidan ta sani suna isowa ta Farka ta Fara Kiran sunan Imran,gabadayansu suka Nausa Cikin Dakin Baffa Kabiru ya bangaje Mami yana Hararanta wacce ta isa ga Sajidan Tana Riko hannunta Mami kanta na kasa ta kasa dagowa ma ta kalli kowa sai Hawaye dake bin Kumatunta Kowa adakin sai da ta bashi Tsausayi Umma ce ta Rikota zuwa gefenta ganin Tana neman Faduwa.
Baffa Kabiru ya isa ga Sajida ya Riko Hannunta yana Fadin”Sajida ga Imran nan yana jinki..Gashi nan kin gansa..?
Yafada yana Nuna mata Imran wanda Abba ya jawosa Gefen da Baffa Kabiru ke Zaune daga ido Tayi tana kallonsa Shima kallonta yake yi cikin Kallon Kuduran ubangiji ganin yadda Sajidan ta koma Lokaci Daya..
Idanuwanta na Zubar kwallah ta Kira Sunansa..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button