GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


Washegari ta kama Labara ne,basu da Lecture sai 10am na safe shiyasa ma basu Shirya ba,yau basu tashi da wuri ba,Anty Safiya tayi Breakfast Tunda dai basu tashi ba suna ta barci Inteesar 7:20am na safe ta Farka Daga kan Darduman Data idar da Sallar asuba Munari na saman gado tayi Daidai tana Sharan barci tana Fashin Sallah ita kadai tatashi da asuba Tama makara saboda bsu yi barci da wuri ba sun Tsaya yin Browsing din wani assigment da aka basu kuma yau din za”a karba

Agogon Wayarta ta Duba Taga Lokaci in taci sa”a Ya Imu bai ga Fita ba kenan,Yau za”ayi ta kare tagaji da wannan Fushin nasa In Horata yake son yi Wlh ta Horu har tayi Laushi,Da Dogon Hijabin Datayi Sallah ash mai Hannu ta Fito Daga Dakin,Ba kowa afalon sai karan Tafakeken Talabijin din Dayake tayi shi kadai Falon sai tashin Kamshin Girki yake da na Turaran Wuta aikin Anty Safiya ne ta gama Jera komai asaman Dining ta koma ta Taya Ya Yusuf shirya kafin su Fito tare domin yin Breakfast.
Bata Tsaya wani Tunani ba ta Fice Daga Falon zuwa Haraban gidan illah kuwa Ta hangosa Tsaye ya Bude bayan Motarsa ya saka Karamar bakar Jakar Briefcase dinsa kafin ya Rufe ya Zagaya ya shiga bangaran Direba sanye yake da American Suit masu Ruwan Toka na kamfanin Armani ya yi amfani da Tek tie ash ya Daure wuyansa dashi kafarsa sawu Ciki ne Bakake,na Fatar damisa sai agogon Hannunsa Shima mai kyau da yarari kirar golden kansa ya sha gyara yana Sheki ko kadan bai Rage Dadan Daya Tara a kansa ba sai hakan yayi mai kyau a kallon Farko in kayi mai sai yayi maka kama da jaruman Kasar Waje na Bolloywood.
Ganin ya shiga Motarsa ne yana Neman Tada ita ya Fice Daga Gidan yasa ta tattara Hijabinta ta Zura da gudu bai da Tsammani kawai yaji Mutum a kusa da Kujeran mai Zaman banza,Kukan ta kawai yaji da Shesshekanta ya Dago daga saka ma Motar key ya sakarmata Dara Daram Idanuwansa masu cike da Sheki yana kallonta itama shi take kallo Tana mtse ido tana jan Hanci alamun kuka Duk da ba hawaye adonta nata sai Tsabar Shagwaba.
Kallonta yake Cikin Salama da wani Sukuni Idanuwansa na bayyana yarda yayi kewarta sosai ammh Saboda kada ta Fahimci haka ya Hade rai yana Fadin”Ke miye haka..?
Baki ga zan tafi wajen aiki bane kika zo kika tasani kina min kananun kukan ki na Fama ko..?
Jin haka yasa ta kara Wage Murya ya saka kukamai kuka Harda Dora hannu a saman kanta Ido ya Waro yana kallonta Cikin mamakinta ganin fa sai kara Volume take yi yasa yace”Kin rainani ko..?Tukuna ma me akayi miki na kuka..?
Jin haka yasa ta Dago Tana kallonsa Tana Sharan idon da ba Hawaye tace Cikin Tura baki tace”Ba kai bane….!
Tafada Cikin Tabara da Sangarta Shagala da yayi da kallon Dan bakinta kafin ya kada kai yana Fadin”Uhm yarinyar nan kin cika Shagwaba Umma da Baffa Sun bataki..ni me ye namiki da zaki ce wani nine..?
Inteesar najan majina kamar gaske tace”To ba kai bane..Kana Ta Fushi dani nayi ta kiranka baka Dauka ba na Tura maka sako ba adadi kaki kulani kuma..kuma!
Tafada fada tana wani kara Goge Hanci kamar kuka Dariya ta kamasa ya kanne kafin yace”Ina jinki..kuma me..? Imran sarkin Laifi..?
Inteesar Da ta Fakaici idonta ta Debi Miyau ta goga i donta saboda yaga da gaske take tunda na gasken yaki zuwa batasan yana kallonta ba Dariya ta kusa Subucemai acikin Ransa yace”Yaro yaro ne..Yaro man kaza..!
Cikin Shagwabbiyar Muryanta tace”Kuma baka bari ina ganinka kafin na fito ka tafi aiki in kuma ka dawo da Daddare ne kana cikin Dakinka ni fa kuma na baka Hakuri kaki Hakura..?
Yana Mirmishin Saman baki yace”Au ai kin gama naki Fushin ne ni na Dauka ba shikenan ba..?
Fito da idonta yaga Hawayenta Tace”Ai nace kayi Hakuri fa..!
Tafada Tana kara Tura baki Yana Danne Dariyansa yace”Ok naji..Yanzu kin Hakuran ne na Rika zuwa Wajen Sajidan..?
Kallonsa Tayi kyam Ranta Tuni ya Baci Mood dinta ya Sauya kanta ta Kauda gefe ta Murgudamai baki ya ganta Sarai shiyasa ya Hade rai yana Fadin”In kika kara Juyamin baki sai na Bike Bakin yayi jini..? Am i ur Mate..? Saboda kinga ina Miki Dariya shiyasa Kika Rainani ko..?
Tana shirin mgana ya Dakatar da ita da cewa”bana son jin Wata mgana..Bana son Raini ni bana daga Ciki yayyinki wadanda kike rainawa kina ma Sangarta yadda kikaga Dama Ina nan a Imran din da kika sani Wlh ban Sauya ba u better Behave ur Self kuma ma naje wajen Sajidan ke kin isa ki Hanani ne..!ke ce zaki bani Umarni ko ni ne zan baki..?
Baibata Zarafin mgana ba ya cigaba da Fadin”Ni namiji ne Mijin Mace Hudu..Zan iya auran mata uku nan gaba Bayan Sajida kuma infact ma ke Matatace da zaki hanani zuwa wajen wata..?
Yafada yana kallonta Saurin Sadda kanta tayi kafin Cikin cikin Sanyinta Idanuwwnta sun ciko da Hawayen gaskiya”Kayi hakuri bazan kara ba..!
Sai ta bashi Tsausayi wani abu na yawo acikin Ransa kai ya kauda yana Fadin”Is ok..Tunda kin bani Hakuri nima na Janye Fushin..!
Kallonsa ta dago tanayi ido Cikin ido Hawayen kishin Sajida suka Zubo mata Karamar Dariya yana Duba agogon Dake Daure a tsitsiyan Hannunsa yace'”Sai yanzu kukan gasken yazo..?bakya Bukatar saka Miyau bakin kii ko..?
Kunya ta kamata ta Rufe Baki Tana yar Dariya Cikin shagwaba tace”Duk ba kai bane..!
Nishadinsa ya kasa Boyuwa yace”Ni kuma..?laifi na baya karewa..Kedai Kazama ce kawai..!
Yafada yana yar Dariya ganin Zata faramai shagwabanta ne ya nuna mata agogon Hannunsa yana Fadin”8am na kusa..Kada ki sakani na Fara abunda ban saba ba plz ki goge wannan Hawayen naki ki koma gida Zamu hadu in na Dawo wajen aiki..!
Kallonsa Tayi kafin tace”alkawari..!
Tare da Mikamai karamin yatsaanta bai Rike ba yadai murmusa yace”Cikawa..!
Sai Lokacin Hankalinta ya kwanta ta Share Hawayenta ta Bude Motar ta Fito Lokaci Daya tana Rufomai Murfin Motar,Tana Tsaye a wajen Tana Dagamai Hannu har yayi Hon iro megadi ya Budemai get ya Sulala Waje,sannan ta koma Cikin Gida Cike da Wani Farinciki Tana shiga Falon Taga Ya yusuf da Anty Safiya suna karyawa Gaishesu tayi kafin ta shige ciki Anty Safiya na mata mganar Karyawa tace sai tayi wanka Lokacin Munari ta Farka Daga Barci in bata Farka ba ita zata tasheta.


Shikenan Fada tsakanin Inteesar da Imu ya kare suka koma kamar baya Yawancin sunfi mgana ta Test Messages,Tunda bai da wani ishashen Lokaci,waya sai Lokaci bayan Lokaci in Bukatar hakan ta taso.
Suna Haduwa yawanci a Haraban gidan ko kuma aa kitchen in yaje Daukan Ruwa ko Zai Hada Tea ko Zai Dibi abinci Wani Lokacin kuma yanzu in yana Daki yana Bukatar wani Abu ita yake kira takaimai.
Koda basu yi wata mgana ba They are ok Tunda suna ganin juna Koda yaushe sun dai yima Mama yaji sai dai suje da wuni badai da kwana ba Tuni Inteesar ta kusa kwshe kayanta Duka Zuwa Gidan Abba Mama bata isa ta Raba Kaunar Munari da Inteesar ba,Shiyasa bata Damu ba Tunda suna kusa kuma nan din ma Gida ne ba wanda ya kawo wani abu sai Munari Domin ita tasan komai Abba bai Fara zuwa Offife ba sai Farkon Wata Lokacin komai ya Daidata Harta Motar da sukayi Shawara da Imu zasu siya ma Abba da Sauran kudinsa da na Marigayi Nura zasu siyama Abba Mota mai rai da lafiya da Direban da zai Rika jansa batare da sun Fadamai ba sun fi so yaga komai kwatsam
Karshen Wata nayi Daada ta Kira Duka ya”yanta ta Fada musu tana son ganinsu bazata mtsa sai da ya”yansu ba ammh wanda ke da Hali yazo,ta kuma ce Mami Tazo da Sajida Khamis yazo,Imran Daman suna Waya daya Kirata ta gayamai daman Wannan Lokacin yake jira ya shirya ma Hakan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button