GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


After 2 Month

Bayan Wata Biyu da Daidatawar abubuwa Tsakanin Inteesar da Munari Daada ta Zame a bandaki Tayi Gocewar Kashi da sai da aka Dangantata da asibiti,Hankalin iyalanta ya tashi sosai da duka Jikokinta,gabadaya kowa da kowa sai fa sa yaje saboda jin Halin da Daada ke Ciki,ga Jikin Tsufa ga Kashi ya Tabu Baffa Kabiru da Abba da Daddy tun da abun ya Faru suka bar komai nasu suka Tafi Chan An gyara Kafar Kwananta Hudu aka Sallamota su Goggo Maimunatu ne tare da ita,Jikokinta duk sun zo su Sadam da su Sa”id ya su ya Basheer Ya Yusuf ma yaje Imran dai sai Weekend suka Tafi da Inteeear lokacin Harta su Abba sun koma Goggo Bintalo ne ke Zaune da ita Har Lokacin.
Daada kamar bakinta zai yge Saboda Murnan ganin Inteesar da Imran Cikin Farimciki da annushuwa Daman abunda take Fata kenan tayima Allah godiya ta kuma kara Godemai da ya Hada kan Iyalanta Waje Daya Kwana Daya sukayi suka Juya Inna Bintalo kam ga Gulma abakinta ba wajen Fada Tunda Mami Asma”u da Rayuwa ta gama ma kullin Goro ta Daina Daukan Wayanta Tun bayan Bikin Imran da Inteesar Data Kirata Tayi mata Tas tace kada ta kara Nemanta indai ba Alheri Zata Fadamata ba in kuma ba Daidaita abubuwa Zatayi ba ta barta da Halin Datake Ciki Tundaga Lokacin bata kara Sauraran Inna Bintalo ba.
Mami Asma”u ta gama ganin Rayuwa ta kuma Sarewa da al”amarin ta Tabbatar ma kanta ta riga ta rasa komai,ita ba Miji ba ya”ya ba Khamis ma bata samunsa kwata kwata awaya Sajida kuma ta Zama sauran Cutar Namiji Baffa Kabiru ya gama Toshe duk Wata Hanyar da zasu hadu ballatana ta saka ran in suka Hadu yaga Yadda ta koma zai Tsausayamata ta Rame ta Fige kamar ba Mami Asma”u in lissafinta yayi Daidai Tama Fita Iddanta Kenan Aure ya Haramta Tsakaninta da Kabiru sai in har ya Sake yarda an Daura musu aure gashi Tun tana Boye abun har ya bayyana yan”uwanta sun gane Sakinta Mijinta yayi mgana har wajen abokan aikinta ana ganinta ana Gulmaanta a kawayenta ma duka sun samu Labari Harda wadanda suka Tareta suka mata mgana Mami Asma”u Wlh ta yarda Duka Kuskuranta ne ammh bata san ya Zata gyara abunda ta Riga Ta gama batawa ba.
Bata da wata Hanya Hatta Hajiya Turai ta Sare tace Mami ta Kira Baffa Kabiru ta basa Hakuri Mami kunya ya Sata kasa Kiransa sai dai ta bama Umaima Sako ita kuma Data Fadamai bai ce komai ba Saboda ai bata gama Nadama ba In ta yi Nadaman da gaske Tasan yadda Zata gyara komai,Shi kanshi baya Cikin Natsuwarsa kan Rashin Sanin Halin da Khamis yake ciki,Yaso yaje tun sanda sukayi mgana da Imran sai dai wani Case ne ya Rikesa yasa ya kasa Tafiya yana so sai sun yi Covering din komai Tukunnah ya Shirya yaje Har Chan Anambara ya gani ko Lafiya..?shiyasa ya Share Mamin Asma”u yasani akwai Watarana da Zata gane Duka abubuawn Data aikata kanta suka Dawo,Shiyasa ya Kyaleta sai Ta Fahimci Kuskuranta da kanta.

Su Inteesar na Tsaka da Karatu Anty Hauwan Ya Basheer ya Ta Haihu Ya mace Murna wajen Inteesar ba”a gama sai dai Murnanta ta koma Ciki Tunda sai ana gobe suna Imran ya bari suka tafi Tare da Anty Safiya da itama Cikinta Haihuwa ko yau ko gobe da Munari da Anty Aneesa da Fareesatu da Hafsa,suka Tafi Kaduna suna shima din Inteesar sai da Abba ya Saka baki ya barta tayi kwana Biyu,Yarinya Takwaran Inteesar ne Domin taci sunan Maryama ne kuma Itama Inteesar za”a rika Kiranta ai ko Auta Tayi bajinta ita Goganta Imran sun Siyama Mejego da Baby kaya na alfarma,Domin duk wacce taci sunan Inteesar abar karramawarsa ce a zuwan su suna ne kowa yake jin Labarin Soyayyar Hafsah da Sagir da na Munari da Khalil kuma kowa yayi Na”am Tunda Sagir yaje Dutse sau Biyu,kuma ya Sa”id yayi Na”am Dashi Shi Sagir din bai gayama Imran ba Shi Sa”id din shi ya Kira Imran din sukayi mgana Anan ne yaji Sagir din yaje har Dutse Imran aransa yace Uhm da gaske Yaron nan yake Shiyasa yadda bai Gayamai yaje ba Shima bai Numamai ba Kowa yaji Abun sai yace Hadin ya kayatar Ita ma Munari Khalil din yana nan tafe Kafin Iyayensa su suzo shima ya gabatar da mganar awajensu Dr.Isa Ali Argungu
A kuma Lokacin ne aka kara Tattauna Lamarin Mami Asma”u da Baffa Kabiru,Tunda Labari ya bayyana acikin Dangi Auransu ya Mutu kowa sai Fadi yake ai mganinta keman Taga Karshenta goggo maimunatu bata zo ba ammh ya”yanta su Zainab da Karima sun je Daga Kwana Biyu sai ga yan suna da kwana Hudu Imran ransa ya Baci Inteesar sai ta Saki jiki ta Rama mai Kwanakin da bata nan ya Kwashi Dadinsa Shine yasa ya Dan Hakura Kadan Daga baya kuma sai da yayi mata Fadan nan nasa ta gama Tura Bakinta ta Hakura tunda itace bata da gaskiya.
Tsakanin Haihuwan Anty Hauwa da Anty Safiya Kwana Hamsin ne Itama Allah ya Sauketa Lafiya a asibitim Murtala,Danta Namiji kyakyawa mai kama da Imran kamar shine Ubansa yana Kama na Jini da Mahaifinsa da Mahaifiyarsa.
Haihuwan nan Kamar wani karin Haske ne a wannan Gidan Tun a asibiti Yusuf yayi mai Huduba da Imran,Masha Allah Imran baki yaki Rufuwa Ya Yusuf yamai Takwara Yaji Dadin har yakasa Boye Murnansa Inteesar sai rawan kafa Take Takwaran Gwarzonta Anty Saratu ke Tare da Anty Safiyan har suka Dawo Gida Mama Ya yusuf ya kira Tazo sukaje asibiti tare,Suna Dawowa Gida ta Saka Ruwan Zafi tayima Maijego wanka Ta kuma Gyara mai sunan Imran,nan da man gida ya Cika da Dangin Anty Safiya Abba kuma baki yaki Rufuwa Anyi jika Daddy da Baffa Kabiru sun kira sun yi barka da Fatan Alheri.
Tunda akayi Haihuwan Inteesar chan take wuni Sai Dare Imran ke Daukanta su koma Gida,da sun Dawo Makaranta nan suke yada Zango,Alhaji Alhassan da kansa yazo Har gida yayi barka ya bama mejego 50k Amtsayinsa na Uba bayan kuma akwatin Kayan Daya shako Cike da kayan Bby da Na uwar,Alhaji Alhassan ya Riga ya gama yin Nadama ya Zama Mutumin kwarai yana so ya gyara Halinsa ya Roki Hajiya Mero Gafara ita da Danginta da nashi Dangin.
Inteesar Taci Darajan mai sunan Imran da kuma Darajan Ya Yusuf yasa Imran ya Sakarmata kafa sosai tana Wuninta agidan,Shima amtsayinsa na Wanda Jariri yaci sunansa yayi rawan gani Shima akwati guda yayi na kayan yaro Inteesar kuma ta siya mai Jego atamfofi.
Anyi suna Taro sosai an tashi Lafiya Mama ita ke zuwa Tana ma Safiya wanka da Imran junior safe da yammah Mommy Taji Dadin haka Daman ta Fara Tunanin wacce zata Zauna da Safiyan sai ga Mama Abba ma Kyautar Dubu 100ya yi ma Jikansa na Farko Duniya kuma mai sunan Dansa Gabadaya Ahalin Daada sun Hadu Hatta da inna maimunatu sunzo sunan da su Inna Bintalo,kuma sai da sukayi kwana Biyu kana suka koma,Raguna uku Yusuf ya yanka ma takwaran Imran an sha Shagali sosai kam sai Fatan Allah ya Raya Imran karami.
Bayan suna kuwa Inteesar ta Gayama Aya Zakinta Domin Imran sai da ya Famshe kwanakinsa Inteeear ta Jigata sosai a Hannunsa Sai ta Fara Hadamai da kuka da magiya yake kyaleta Tunda yanzu ta Fara Zama Raguwa Tun Sunan Anty Hauwa bata jinta Daidaita Tunda suka Tare bata Taba Jini agidan ba sai dai Kafin Tarewar ne tayi period,Bata Dauka komai ba Saboda yana mata haka Shiyasa bata Damu ba,sai bayan sunan ne na Anty Safiya ta Fara Zazzabi da Amai Ta Rame duk ta Tsurr har da kwanciya asibiti lokacin da aka Tabbatar da Inteesar nada Cikin Wattani biyu da wani abu Murna wajen Imran kamar Zai Shide bai Taba Zaton Watarana zai Zama Baba ba sai gashi da kanshi ya Kira Sagir da Khalil ya Fada musu ya Kusa Zama Baba suna nan a yara Su kuma sukacemai Suna kan Hanya da yardan Allah
Samuwar Cikin Inteesar ya Zaga Dangi Har kunnen Daada,Sai Jin Dadi Take Tana saka albarka,Inteesar kuma Cikimta mai Laulayi ne ga makaranta Dole Munari ta koma Gidan Tana Taimakamata Tana ganin Abu Su Ya Imu asan ya”ya Wato na wasu ne bai Damu dasu ba ya Damu da nashi Tana kallon Rayuwa yadda Inteesar ke Zuba Shagwabanta Dama gata mai Raki Baban Urborn kuma na Tarairayanta,kuma bai jin kunyar Munari Ko ajikinsa ammh da sun Hadu ya Hade rai yana Hura Hanci Munari tace aranta Daman ai nasan Watarana Mace Zata sauya ya Imu ko bai gama Dawowa Daidai ba Watarana in ya zama uba zai dawo Daidai yanzu ma Shan Taba ya Ragesa Saboda Intee abun ya Zame mai jiki ne yasa yake sha asati sau Daya wani Lokacin balle yanzu Data samu wannan Cikin Inteesar ta kara Lalacewa Tsurfa kala kala batacin komai Daga Goriba sai tuwo sai su Fante da sauransu Imran shine da baisan Hanyar kasuwa ba ya sani yanzu Tunda zai zama Baba Munari kuma ke ta Wahala da tsurfan Inteesar Umma Daman dataji Labari tace Imran ya shiga Uku Daddy na Dariya yace ai Daman sun Hadu da sun Dace ne Dagashi har Inteesar din.
Allah ya Taimaki Inteesar basu Fara Test da wuri ba sai da tadan samu kanta Kana Munari ta koma Gida Bayan sun gama Test suka fara Jarabwwa Lokacin Laulayin yayi Sauki aman ya Tsaya suka samu hutu na Sati uku Imran yaji Dadin haka ta koma Gida tana Hutawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button