GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Shakira…
3/24/22, 23:22 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?18

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Washegari da safe Tun karfe 7:30am na Safe Inteesar ta gama shirinta saboda suna da Test karfe 8am daidai na Safe ne ta Kira Munari tace mata ta jirata kofar gidan Mama gatanan Fitowa.
Ta fito tana Tsaye sanye da shigar riga da wando,wandon plazo ne red sai Rigar top ce mai Dogon Hannu,baka ta sanya bakar abaya tayi Rolling da bakin Vail kafarta sanye cikin Takalmi mai tsini baki mai igiya Ta sanya karamin Farin glass ta zagaye idonta dashi,Karamar jakace a Hannunta da wayarta Lokaci bayan Lokoci Tana Duba Agogon Gucci Dake Daure a Tsitsiyan Hannunta bata so su makara Dr Mahadi bai da Mutumci ko Minti Daya ka kara bazaka shiga Test dinsa ba.
Rumgume Wayarta tayi Saman Kirjinta Tana kallon Hanya ba Kowa sai Wucewar Daidaikun Mutane Tunaninsa take yi mamaki take yanzu wai suna Mtsayin mata da miji..?har yanzu bata Daina mamakin haka ba komai ya Faru Cikin Lokaci,Lokacin da basu yi Zato ba.
Tundaga Nesa ya hangota Tana Tsaye ita kadai Fitowarsa daga gida kenan Zai tafi wajen aiki Sanye yake cikin American Suit na kamfanin Armani,mai Ruwan kasa ya Matse Wuyansa da Tie,Mamakinta ganinta tsaye ya fara Daga farko har yana Duba Agogon Fatan Dake hannunsa sai kuma ya Tuna makaranta Zasu Tafi.
Dan Tsagaida Gudun Motar yayi Daga nesa yana kare mata kallo Daga Sama Har kasa Wando..?Haka kurum Dresing din bai kwantamai ba Duk da ta saka Bakar abaya Daga Sama yarinyar nan bata da Hankali ne..?batasan ita matarsa bace da Zatayi wannan Bazan Shigar tatafi Cikin Dubban maza?Wato ta Rainasa ma kenan..?daman jiya ta gudu bata ma Tsaya ta gaisheshi ba Hakan ya sosamai rai kwarai da bacin Ranta ya kwanta kara gudun Motar yayi bata ankara ba Kawai taji Tsayuwar Mota a gabanta Dago Dara daran Idanuwanta Tayi ta Sauke akansa Daidai Lokacin Daya Sauke Glass din Barayinsa
Suka Hada ido hudu Lokaci Daya kuma atare gabansu ya amsa Ras!
Yadda yazo da Masifarsa kallonta kawai Da yayi sai yaji komai yana Sauka ita kuma karon Farko dataji wani irin yam acikin Jikinta da suka Hada ido Lamgwabe kai Tayi idanuwanta ya ciko da kwallah Ware ido yayi akanta ya kasa ma ce mata Komai jira yake yaga Zata gaishesa ballatana ta amsa Laifinta..?
Ita kuma Jikinta ne ya fara rawa bata Shirya Fuskartan Ya Imu a Mtsayin Mijinta ba yanzu kwata kwata ta Rasa Ina Zata tsoma kanta wani irin Feeling neyake Fito mata Daga karkashin Zuciyarta wanda yasa Hawayen idnta suka zubo Saman Fuskarta
Dakuna Fuska yayi yana kallonta Kuka..? Ni take ma kuka ko auran da aka Daura mana?
Ya kasa gano ma Dalilinta ya Bude baki yayi mata mgana yaga ta Juya da Sauri Gudu gudu Ta shige Zauren Gidansu Sagir Baki da Hanci ya Saki kawai yana kallonta Tuni yaji Bacin Ransa ya kara Ninkuwa.
Wata zuciyar tace mai Imran kagani ko..?Duk abunda ka Hada da mace sai kaga ba Daidai ba,Macen ma karamar yarinya Raini sai abunda kagani
Shi yarinyar nan zata Sakama kuka ko mgana fa bai mata ba,
Afili ya Furta”Shagwabbiya ce..Mtsawww..!
Tsaki yaja kafim ya Tada Motarsa ya Wuce da Gudu a Fili yake Fadim”Imran be a Man..Kada ka bari Yarinta yarinyar nan ya bata maka rai juz ka kyaleta zata gane bata da wayau ne inaga ta manta Wanene Imran ne ban Sauya ba ina nan a yadda nake Mace bata isa ta zauna ina Lallashinta ba banda wannan Lokacin.!
Haka yake ta Fada yana so ya Kure baacin Ran abunda acikin Ransa Ahaka ya isa Titi ya Dau Babbar Titin da zai Sadashi da Brach din Bankin Dayake aiki yana kokarin manta komai da Lamarin Inteesar sai ta nemesa da kanta Zata gane bata da wayau.
Sanda ya isa Ma”aikata sun Fara zuwa ya Fito Daga Motarsa Cikin Takunsa na Sassarfa da Zati,Rike da Karamar Briefcase dinsa,Suna ta gaisheshi hannu kadai yake Daga musu har ya karisa Office dinsa Dayake Tsaf kamar bai Taba Datti ba ya zauna yana kokarin yakice Inteesar acikin Ransa ya Fara aikinsa gadan gadan sai dai duk Motsinsa Inteesar Tana makale acikin Ransa Ta Riga ta samu matsungunnin da bazata iya Fita Cikin Sauri haka ba.
Inteesar kuwa a zauren Mama ta Labe Tana lekensa Sai da Taga ya wuce kana ta Sauke ajiyar zuciya Tana maida Numfashi kanta ta Dafe Lokaci Daya Tana fadin”Kash..Meke Damuna ne Inteesar..?Me na aikata ne..?
Tafada tana Dangwalo Hawayenta Tana kallo Dariya Tayi afili ta Furta”Wawiya Inteesar..!
Sai kuma tace”Ai ya Imu ne yana da Kwarjini gabadaya kallonsa Daburta Mutum yake yi..!
Kiran Wayar Munari ne ya Katseta Fuskarta ta goge da Sauri taci karo da Munari tana kokrin shiga gidan,ganinta yasa ta Dakata Tana kallonta Cikin Nazarinta Ganin haka yasa Inteesar tayi gaba Tana Fadin”Allah ya taimakeki ki Tsaya kallona har ya hanamu shiga..!
Munari agogon Fatan Dake Tsitsiyan Hannunta takai Duba kafin tabi bayan Inteesar din Tana Fadin”Ina ganin Amarya ce..Amarya tasha Kamshi..!
Mirmishi kawai Inteesar Tayi batayi mgana ba sun Fara Tafiya zuwa Titi Munari ta Kalleta Tana Fadin”Kinsan Cewa fa yanzu kin tashi Daga yan mata kin koma matar aure..Taku Daya in kika yi batare da Izinin mijinki ba Kina Cikin Tsinuwan Mala”iku..Ina Fatan kin Tambayi Mijinki kafin ki Fito..?
Munari ta Karishe Fada Tana yar Dariya Inteesar ta juyo ta Harareta Tana Fadin”Ban Tambaya ba..Kuma bazan Tambaya din ba..!
Munari ta Zakuda kafadarta Tana Fadin”Daga mgana.?gaskiya fa na Fadamiki..? Ke kika sani koda yake ai Jiki Magayi matar Ya imu..!
Tafada Tana Dariya Inteesar na jinta tasha kunu Tayi mata banza ammh jikinta yayi sanyi sosai yanzu ita din Komai Zatayi sai da iznin miji..!? Harda ma makarantar..? Tura baki tayi acikin Ranta tana Fadin ai ba sai na Tambaya yasan ina zuwa makaranta!
Munari na kallonta Tana Danne Dariyarta Har suka kai Titi suka Samu adaidaita suka Hau zuwa New site.


Abuja..
7:40am

Cikin shirin Tafiyarsa ya Fito Daga Dakinsa jikinsa sanye da kayansu na Sojijin Sama Ruwa Navy,Bayansa goye da wata Jaka irinta Sojojin,Kafarsa ma Cikin Wani katon Booth din Takalmi,Yan aiki ne kadai ke ta Kara kaina Atsakar Falon suna ganinsa suka Fara gaisheshi hannu kawai ya Daga musu yana Kokarin Haurawa Sama Inda jerin Dakunan Dad yake Hade da na Mami.
Suka ci karo da Umaima ta FitoCikin Shirin Tafiya makaranta Sanye Cikin Uniforman dinta,Jiya Hadda ta tafi Tun safe Sai s yammah ta dawo yau kuma makarantar boko Zata tafi
Rumgumesa Tayi tana gaishesa ya amsa mata cikin dan yake da Rinanun Idanuwansa da suka Rine Saboda Damuwa.
Cikin Mararaice Murya tace”Ya Khamis Me ya Faru a Dukku ne..?Tunda kuka dawo na kasa gane kan Dad da Mami,Kuma ina Anty Sajida..? Ban ganta ba nazata ta wuce makaranta ne inta kiranta bata Dauki Wayata ba..!
Kallonta yake yi kur yana wani Tunani Umai tayi kankantar Sanin Wani abu Shiyasa yadan yi mata yake yana Fadin”Don”t worry kin ji ko Umai..Bafa komai kinsan Halin Mami da Rigima Dad kuma da kyaluwa ko..? Zasu Daidaita kansu Sajida kuma Tana makaranta she is ok..Kila karatu ne yayi mata zafi yasa baki jita ba!
Yafada yana Shafa Kumatunta kallonsa kawai tayi tafa gani a group na Daurin auran Imran da Inteesar jiya da Daddare ma ta Kira Hafsah ta kara Tabbatar mata Tana da Tabbacin komai ya Faru to yana da nasaba da hakan.
Bataso ta kara cewa wani abu,Shiyasa Tayi mai mirmishi Tana Fadin”Nasan Tafiya Zakayi..So safe landed bro..!
Kai ya gyada mata yana Fadin”Tanque Lil sisy..!
Daga haka ta wuce saman Dining ta Nufa Domin tayi Breakfast shi kuma ya Cigaba da Haura Stairs din Dakin Baffa Kabiru ne afarko yasa nan ya Fara Shiga yana Shiga ya iskesa cikin Shirin Fita shima Sanye cikin Suit ya Matse ga Rigarsu da Hulansu ta Lauyoyinan saman gado shi kuma yana daga Tsaye yana Duba wasu Takardu Khamis yayi knooking Lokaci Daya yana Turo kofa ya shigo.
Baffa Kabiru ya dago kansa Daga Duba Takardun Dayake yi yana kallon Dan nashi Cikin Dan bayyana Damuwa kadan asamar Fuskarsa.
Khamis ne yadan Ramkwafa yana Fadin”Gud mrning Dad..!
Ya ijiye Takardun hannunsa yana Fadin”Mrning Son How was ur Night..!?
Khamis a saman lebensa yace Fine ba Domin haka din bane Kallon Tsab yayi mai Kafin yace”Na ganka da Jaka are u going..?
Khamis na Duba agogon Farin Azurfan Dake hannunsa Lokaci Daya Yana fadin”Eh Dad..jirgin 8:30pm zan bi Zuwa Anambra Insha Allahu..!
Kai ya gyada yana Fadin”Allah ya Kiyaye..Allah ya bada Sa”a..Be a Man kaji.!
Yafada Lokaci daya yana Dafa Kafadarsa Cikin Alamun Lallashi Domin ya karanci Tarin Damuwa da Rashin wani abu Acikin kwayan Idonsa Mirmishi kawai Khamis yayi kafin yace”bakomai Dad..Kai ne ma Zan bama Hakuri akan Abubuwan da suka Faru plz ka yafema Mami ku Daidata kanku Dad..!
Kallonsa yake yi ko Kiftawa bayayi wani abu nayi mai ciwo acikin Ransa Dan Mirmishi saman lebe yayi kafin yace”Ai bani nayi mata Laifi ba ita tayimin..Kuma kana dai ganin abubuwan da suka Faru son..Ya Dace na kyale Asma”u taci Zarafin Daada a banza kuma na koma ina bata Hakuri..?in nayi haka kai kanka bazakayi Tunanin wani irin Uba ne ni ba..? Ko kuma wani irin D’a ne ni..?
Khamis ya Girgiza kai yana Fadin”A”a dad ba haka nake nufi ba..Ina Nufin ka Nuna mata kuskuranta abunda tayi gaskiya bata kyauta ba ka nuna mata Bata yi Daidai ba ku Daidaita kanku Taje ta bama Daada Hakuri is better in mu ya’yanku indai kuka Shiryan kanku..!
Kai ya kada mai kafin yace”Shikenan..!
Khamis ya Rusuna yana Fadin”Zan ga Mami kafin na wuce Dad..!
Yana Daukan Takardunsa yake Fadin”In bazaka Dade ba sai mu ijiyeka Airport kafin na wuce Office..!
Khamis ya juya yana Fadin”Yanzu zan Fito Dad..!
Yafice Uban ya Bisa da kallon Tsausayi ya Tabbata karfin Hali kawai yake yi ammh abun ya tabasa Asma”u batasan ta Ruguje Farincikin ya”yanta alokaci Daya bane,Sakarya kawai.
Takardun Hannunsa ya ke sakawa cikin Karamin Briefcase dinsa.
Knooking ya farayi yaji Shuru jin Kofar tana Bude yasa ya Tura ya shiga Lokaci Daya da Sallama.
Tana zaune kan kujeran Dreesing Mirror Tana waya shiyasa bata ma ji knooking din ba.
“Ka shirya komai..Yau nake so na shigar da Complain din Brr.Zailani..!
Iya abunda yaji kenan ya Kira Sunanta da dan karfi.
“Mami..!
Da sauri ta waigo cikin dan Tsoro jin kira Daga sama ganin shine yasa ta Sauke ajiyar Zuciya ta Mike Lokaci Daya Tana Fadin”Zan Sake kiran ka Brr.Zailani..!
Daga haka ta Datse kiran Tana kallonsa lokaci Daya Tana Fadin”Son badai har zaka wuce ba..?
Tafada tana kokarin Zama gefen gadonta.
Kallonta yake yi cikin Tsaisayinta ganin yadda tayi wani Figai Figai Cikin kwana Biyu ba gayun nan sam kamar wacce ta tashi Daga Cuta Idanuwanta duk sun kode saboda kuka da Damuwa.
Ajiyar zuciya ya Sauke kafin yace”Why Mami..? Meyasa bazaki bar mganar nan ba..? Daad zaki kai kara ko Daada ko su Baffa..?
Karamin Tsaki taja Kafin tace”Yancina Zan kwata son..Rayuwar yata suka Lalace Wlh bazan bar wannnan abu ya Tafi a banza ba ka duba ka gani Sajida Tana gayamin mgana ni Mahaifiyarta gaban kowa da kowa..? Wlh Bazan Lamunci su Rabani da y’ata ba Dukkansu zan maka su a Kotu Dad dinka naga alamun yana so ya manta da ku ya”yansa ne zai Biyema yan”uwansa to bai isa ba ko ya amince ko bai amince ba sai na shigar da Complain..!
Tafada cikin son Tabbatar da mganarta.
Khamis ya Dafe kansa yana Fadin”Mami why nace.? Inace ke kikace baki son Auran Sajida da Imran kuma yanzu komai ya kare Why kike hakane.?
Inace abunda kike so aka yi miki..?me yayi Saura..! Don Allah ki bar mganar nan ki Je ki samu Dad kuyi mgana ki basa Hakuri sannan kije har Dukku ki bama Daada Hakuri Saboda mganar Gaskiya baki kyauta ba Uwa uwace kuma ana Sauya mata ammh Mami Ki Sani ba”a Sauya uwa kamar yadda Muma kome kika mana kome kika Zama kina nan a Mtsayin Mahaifiyarmu bamu isa mu sauya ma Tuwo suna ba kuma sai in da karfin mu ya kare in muka ga wani zai Tozartaki..!
Mami Asma”u baki ta saki da Hanci Tana kallonsa kafin ta Mike Tsaye da Sauri Tana Fadin”Au Shi Kabirun ne ya aiko ka ka gayamin haka..?
Yana kokarin mgana ta Dakatar dashi da Hannu Tana Fadin”Ya isa..Basai ka kara cemin wani abu ba..Bana Bukatar jin komai Daga gareka ai ka Riga ka Fadi sakon ka Shikenan sai ka bari nima nayi mgana.!
Shuru kawai yayi yana mamakin Taurin kanta Cikin bacin rai ta Cigaba da Fadin”To in aiko ka yayi kaje ka Fadamai bazan je na bama kowa Hakuri ba Domin ban Batama kowa ba Ni ya kamata ba abama Hakuri ni da aka Lalatama Yata Future dinta Bazawara zan kirata ko Sakin Wawa..?wannan ai Cutar ma tana da yawa in shi yayi shuru ni sai nayi Shuru..? Wlh basa kaunarsa sunan yana Dan”uwansu ne da basu yi mai haka ba In shi bazai iya cewa komai ba Ni zan iya kan wannan mganar sai inda Karfina ya kare..Ni ina da kudi kuma na gaji kudi da asali Zan iya shari”a Dasu har Mahadi ya bayyana Shege ka Fasa..!
Kai ya gyada kawai kafin ya Juya yana Fadin”Mami kiyi Tunani..Ki kara Tunani abunda kika aikata bai Dace ba..kuma wanda ma zaki aikata bai Dace ba..Ina Tsoron abubuwa suxo su Lalace..!
Tsaki taja Tana Fadin”Komai ya Dade bai Lalace ba..Bazan ja da baya kan mganata ba..!
Ficewa kawai yayi ransa na kara Kunci In Mami ta aikata abunda tayi Niyya komai fa Zai Lalace wazai Dakatar da ita..?
Dad bafa bazai iya Dakatar da ita ba,Ta gama Rainasa sai dai in Justice Tafida zai kira ya Fadamawa Mahaifinta Kila in ya mata mgana Taji Hajiyarsu kuwa bama zai kirata ba Domin kamar gadon Hallayanta ne Mamin ta Dauki bama zata Dakatar da ita ba sai ma kara mata Karfin gwiwan da zatayi.
Koda ya Fito Dad na Jiransa ya shiga Mota suka Fice Umai ta Dade da wucewa makaranta a Airport suka ijiyesa kafin Baffa Kabiru ya wuce Wajen aiki Kafin Jirgin su ya tashi Khamis ya Kira Kakansa Tsohon Alkalin Alkalai na kasa Gabadaya Justice Tafida bayan sun gaisa ya Kwashe komai in Brief ya Fadamai sannan ya karishe da rikonsa kan ya Dakatar da Mami kan shigar da wannan Complain din..!
Justice Tafida ya Fahimci jikan nashi kuma yayi mai alkawarin Zai kira Mami Tazo gida ta samesa zai mata mgana Daga haka suka Rabu Lokacin ma Jirgin su ya kusa tashi sai kiran suna akeyi kashe Wayarsa yayi ya Hau kan Layi yana Tunanin in ya tafi zai Dade bai Waiwayi gida ba sai ya manta da Bacin Ransa ba zai kara Dawowa kuma wani Bacin ran ya kara adding kan nashi ba.
Koda karfe 9am na Safe yayi jirgin su ya Lula Sararin Samaniya yana Fatan Allah yasa Kakan nasa yayi wani abu In kuma bai yi ba to abubuwa fa zasu Kwabe ne,Domin yadda yaga Dad ya Shirya aikata komai kamar yadda Mami Tace baja da baya.
Ashe duk wayar nan da Justice Tafida yayi Hajiya Turai Mahaifiyar Asma”u Tana Zaune ta gama jin komai suna gama mgana ta fara Bala”i tana Fada Tana Fadin”Wlh kada kace Zaka Hanata Kwatan yancinta..Wannan ai Ya saba Sharia..auran kaskasci sukayi mata da Farko ni nan na Taushi Asma”u ta yi Hakuri da mganar kuma Shikenan yanzu sai a sakar mata yar da ko Gidan auran ma bataje ba?
Ai ko Kabiru bai Taki gaskiya ba Shi din banza waye shi?Takala dan talaka Asma”u ai ba Kalar sa bace Soyayya ce kawai da Allah ya Dora mata ammh ai Wlh ko Daya Kalan Zaren ai ba Kalan yadin bane in shi yana Tsoron yan”uwansa bazai iya mgana ba a kyalemin ya’ta ta kwaci Hakkinta amfanin Ilimin kenan!
Justice Tafida ya Murmusa kafin yace”Hajiya Turai kubi komai a Sannu..Kada kimanta Kabiru ke auranta..Sannan wannam mganace ta Danginsa fa da Mahaifiyarsa..Anya Asma”u ta taki gaskiya?Daman ai tace bata son Auran yar taata da shi yaron Dan uwwn mijin nata ba ya Saketa ba ba shikenan an muku abunda kuke so ba kuma mganar shigar da kara For What Turai..?Wlh ki shiga Hankalinki kema ki Fadama yarki Kada ta Sake ta shigar da wata kara in kuma taki ji bataki gani ba..!
Daga haka ya Dauki Farin Glass dinsa ya sanya ya Cigaba da karatun Jaridarsa yana jinta Tana ta Masifa Tana Zagin Kabiru wai dan Talaka bai da komai Mirmishin gefen baki yayi aransa yace”A”a fa Kabiru fa ba Talaka bane…Shi wani ne Mahaifinsa Har ya bar Gidan Duniya Alkali alkalai ne na Kotun musulunci kuma Talaka bai Taka wannan Mtsayin..!
Hajiya Turai Daki ta koma ta Kira Yarta Tana Fada Tana Fadin ita ta bata goyon baya Shari”a zuwa Kotun koli su bazasu ji tsoronta ba Mami Asma”u ta Fashe da kuka tana ta Fadamata irin yadda yan”uwan Baffa Kabiru suka Tozarta tare da Mahaifiyarsu Ta kare da Fadin”Hajiya Sun Rabani Da Sajida..Wlh neman zagina take saboda wannan Tsinannen yaron..!
Hajiya Turai tace”Rabu dasu duk zasu gane basu da wayau..Saki ne dai Matakin da Kabiru zai dauka na karshe ko..? To in ya fasa ya sake kin yagani in baki samu wani Babban goron Daya Takasa ba..!
Dayake Idanuwanta ya Rufe bata Fahimci Zata Tafka kuskure ba Mami Asma”u na Fadin”Wlh Hajiya..Ai daman ance Babban goro sai magogim karfe..!
Sun dade suna mgana Hajiya Turai bata Taushi Yarta ba ko Daya sai ma kara zugata Da tayi shi ya kara mata Kwarin gwiwa suna gama waya tayi wanka ta Fice a gurguje ko Karyawa batayi ba Ta fita taje Office suka Hadu da Brr. Zailani kan Tana so Ashigar da karar kai Tsaye ne Daga Kotu ta Cike Complain Form kuma ta na karan Daada ne da ya”yanta Guda Biyu Mustapha Hamisu Dukku da Abubakar Hamisu dukku..!
Abunda bata sani ba suna gama mgana da Brr.Zailani ya zagaya ya Kira Baffa Kabiru ya sanar dashi komai,Daman tun sanda Mamin Ta Kirashi kan Complain din yaji mamakin wai zata shigar da kara kan Mahaifiyar Brr. kabiru da Yan”uwansa Shiyasa ya Kirasa ya Fadamai shi kuma yace da Zarar ta Cike Complain Form ya fadamai Lokacin ne zai yi mganin Asma”u Zata ga True Colour dinsa da bata taba gani ba sai ya Koyamata Hankali Zai nuna mata ana Sauya mata ammh ba”a Sauya Uwa da yan”uwa.
Gabadaya Ransa ya gama baci yau Za”ayi ta kare Baya so ya yanke Hukunci cikin Fushi shiyasa bai Dawo Gidan ba yana son ya yanke komai a Saukake.
Yana Office Sajida ta Kirasa Tana Fadamai ta Dawo makaranta yau daga Dukku yana ta mamaki Tsausayinta ya kamashi Data gayamai a Motar Haya ta dawo ya sani itama ta Guji Gidan ne saboda Mahaifiyarsu ta gama Illata Zuciyarsu,Yaji kamar yayi mata Kwallah Fatan alheri yayi mata da kuma Nasihan ta Cire Damuwa tayi Facing din karatunta ta amsa mai da Insha Allahu.
Dukkansu sun kashe Wayar kowa Zuciyarsa ba Dadi,Baffa Kabiru kamar yayi kwallah,Kudi ya Tura mata 30k yace ta siya abunda bata dsshi
Lokacin Dataga Sakon nasa Tana libary ne tazo Karatu ba Domin Tana Fahimta ba sai domin shine Mafitanta.
Yau da Safe goggo Maimunatu ta koma Bauchi Mijinta yazo duba Daada Daganan ya wuce da ita Daman itace ke Kula da ita goggo Bintalo ba Ruwanta Ballatana Daada da Fushin Mami da Dad ya shafeta
Ta riga tasan tayi rashin Rashim Masoyin da bazata taba maida kafarsa ba,Mami Ta riga ta gama Lalatamata Farincikinta gani tayi Zaman bai da wani amfani yasa ta fara shirin Tafiya Duk bata wani jin Dadi ga Sakewar jikiga na zuciya.
Sai da tagama Shiryawa kana taje Dakin Daada Tayi mata sallama Daada Tsausayin Sajida ya kamata ta Rumgumeta tana Lallashinta da ban baki Sajida na kuka tana Rokon Daada ta yafema Dad dinta Daada tace bata Rikesa ba in ya gano kuskuransa ita Tafi kowa Murna da haka.
Ita ta bama Sajida 5k duk da tace tana da kudi tace ta kara Tunda makaranta Zata koma
Bayan Tafiyar Sajida Daada tayi kuka,Yarinyar abar Tsausayi ce Dama Dama haka bai Faru ba data Hakura da Cin Mutumcin Asma”u sai dai ai ba ita auran ke hannunta ba Wanda Auran ke hannunsa ya warware kuma bazata Tursasamai kan sai ya maida Sajidan ba, tayi alkawarin ta bar kara Tursasa kowa koda ya”yanta na Cikinta ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button