GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr.Is Ali Argungun Koda yaushe zai shiga gida ko zai Fita sai ya kalli get din gidan nan ko zai ga an Budesa Shekaru uku da wani abu bai Taba ganinsa a Bude ba sai yau daya Dawo Daga Wajen aiki yaga Gida a Bude mamaki ya kamasa haka ya Shiga Cikin Gida yana Fadama Hajiya Barira Ita ma tayi mamaki suna cikin mganar ne sai ga Khalil ya shigo shima Dai zencen yake musu shine Dai Hajiya Barira tace su leka su gani ko yan”uwanshi Daga Dukku ne kila zasu samu wani labarin suna zuwa kuma sai suga Abba sai Sabon Labari ya tashi anan Falon gidan Dr.Isa Ali Argungun Abba nata bashi Labaran bayan Rabuwa shima yana gayamai Faculty dinsu tayi rashinsa Wlh kuma yana mai Tabbatarmai ko yau ya koma Zai koma da aiki Jami”ar Lagos bazata yi sakacin rasa Zakwakurin Malami kamarsa ba,Nan sukayi Lunch Cikin Farincikin kara Saduwa da juna Hajiya Barira ta Fito suka gaisa Jin cewa su Abba kano suka koma da Zama yasa Dr.Isa Ali argungun yace ma Abba ai kano gida ce Hajiya Barira yar Fagge ce dake kano ne suna zuwa kano Sosai Rashin Sani sun gaisa ta karamai gaisuwan su Anni ya Amsamata Cikin Jin Dadin karamincinsu yana ta godiya.
Hajiya barira bata da wani D”a gabanta sai Khalil shi kadai ne bai yi auree ba kuma shi kadai ne Namiji Sauran duk matane suna gidajen Auransu,Shiyasa Gidan Daga ita sai yan aikinta da Mijinta da Danta Khalil.
Sai da suka yi Sallar Azahar anan cikin Gidan Yusuf yayi musu Limanci,bayan sun idar ne kuma suka kara Tsinkewa da Hira Khalil ma da Imran Cikin Ikon Allah suna ta mgana kan abunda yashafi aikinsu Yusuf da Basheer suna ta mamaki duk da Daga Khalil din Har yusuf din Daya ne bama su son Hayaniya bane da yawan mgana ba.
Daddy shi yayi ma Dr.Isa Ali Argungu mgana kan wanda za”a Samu ya rika gadin gidan Abba,Dr.Isa Ali argungu yace Faduwa tazo Daidai da Zama Megadinsa Buba Dan BAuchi ne Bahaushe ne nan suke Xaune dashi Shi da iyalansa suna BQauters,Daman kaninsa yazo kwanakin nan Wajensa yake yana ta neman Aikin gadi bai samu ba in hakane sai ya koma Gida ya Dauko iyalansa su zauna a BQuatre suna Kula da gidan Allah barshi Duk wata sai arika Biyansa Abunda ya Sauwaka Duk da yaso Abba ya baro Kano ya Dawo Lagos kamar baya su Cigaba da aiki Tare Abba ya nuna a”a Shi Zaman Lagos ta Fitarmai arai kwata kwata bai mtsamai ba Tunda Daddy yace A Buk kano zasu neman ma Abba aikin su gani ko Za”a Dace Tunda Lokacin aikinsa bai Wuce ba..
Ba bata Lokaci akayi ma Buba Megadi mgana Shida kaninsa Lurwanu sun ji Dadi Matuka Abba yace yaje ya Dauko iyalansa su zauna agidan su Rike Amana su kula da gidan sannan Yusuf ya Dau alkawarin Biyansa Kudi mai Tsoka Duk wata wannan abun yayi Musu Dadi suna ta Godiya.
Aranar basai da aka kwana ba aka Fitar da komai na Gidan Daya Lalace aka Zubar Motocin kuma aka Saida su aka Karbi kudadensu kalilan ba masu yawa ba Aranar basu koma Hotel ba agidan Dr.Isa Argungu suka kwana Washegari da Safe Lurwanu ya dau Hanyar gida zai je ya Dauko Iyalansa Kudin Motan da komai Dr.Isa Argungun ya basa,Yana Tafiya shida Abba da Daddy da Ya Yusuf da Basherr suka tafi Jami”ar Lagos inda Abba yayi aiki Shekaru ashirin abaya Abba yaga Tarin Sauye sauye yaga wadansu wanda sukayi aiki Tare Lokacin wasu kuma sun bar Wajen wasu kuma sun Rasu,Shugaban Jami”ar da kansa ya Nemi Abba ya dawo ya Cigaba da aiki da inda ya Kwarewa Ammh ya nuna ya Gode bai kara Sha”awar Zama a Lagos,Basu damu ba sun mai Fatan Alheri sanin duk inda yaje Takardunsa da kwarewarsa sun isa yasa a kowata jami”a ta Daukesa ma Bama Buk ba.
Koda suka Dawo gida Imran da Khalil basa Gida kuma basu gayama kowa Zasu Fita ba,ba wanda ya Damu Sanin kila sun Fita Zaga gari ne.
Ashe abun ba haka bane Bankin da Imran yayi aiki Khalil ya Daukesa yakaisa Kafin ma Imran ya yarda Zai shiga sai da aka kai Ruwa Rana da Lallashi da ban baki Khalil ya nuna mai Hakan nada Muhimmanci sosai.
Tare suka shiga Har Ciki shima din yaga Tarin Sauye Sauye a wajen yaga wadanda sukayi aiki tare wasu kuma da yawa an sauya su wasu kuma Rai yayi Halinsa,wadanda suka sansa sai Turruwa suke wajen gaisawa dashi To alokacin Waye baisan Imran Abubakar malami ba kan kwarewa a aikinsa da Miskilancinsa iya Daukan wanka bama aiki Muhimmaci gabadaya Dokokin bankin shi nashi Dokar ma ya Take nasu shiyasa ba Ma”ikacin da Manaja ke ji dashi Alokacin Irinsa Saboda yadda ya maida kansa kamar wani bawa gwannati na amfana da Tarin baiwarsa da lafiyarsa.
Manajan Wajen ba”a Sauyashi ba wani Bayarbe ne Mr Tunde Abdulwasi yana ganin Imran sai da yayi wani ihu ya Rumgumesa Tsakani ga Allah sun yi Rashin Zakaran ma”aikaci kamar sa haka yake ta Fadama Imran da Khalil sun nemesa har sun gaji sun Nemi Wayarsa shuru sun ta Turamai Sako ta Email dinsa ma Shuru shi ko Imran yama manta yana da wani Email Tin bayan Faruwar abunda ya Faru ya Daina Mu”amala da Duk Abunda ya Shafi Socoal media ya koma Rayuwarsa yadda yake yanzu sai dai ammh yana ji ajikinsa kila Lokacin da Wannan Imran din zai sauya ne zai Dawo ainihin Imran Abubakar Malami A Banker,Manaja yamai Tayin Dawowa aiki kan Mstaayin da yafi na Baya Imran ya nuna mai A”a Baya Bukata Duk mganar da suke yi Cikin Rantsantsan Turacin kasar Amurka ne in kaga bakin Imran yadda yake Tsara mgana Cikin Harshen Turanci sai mamaki ya kusa sumar dakai ka Fara Tunanin Anya wannan Imran din ne mai Shan Taba..?
Khalil ne yayi ma Manaja Tunde Abdulwasi bayanin a takaice na Komawarsu Imran kano da Rasuwar Mahaifiyarsu da yan”uwansu bai ji Dadi ba ya Tsausaya musu,Ya kuma Dage Imran sai fa ya Dawo aiki ko ba anan Lagos ba zai yi waya da Manajansu na Gtbank din su Dake Reshen kano,zai Turamai Duka Bayanan Imran da Takardunsa ta Email Zasu kirashi da Zarar ya koma Zai Cigaba da aiki kamar baya bazai Taba barin wanda aikinsa ke da Mutumci Fiye da komai a idonsa ya Zauna haka ba ballatana tun abaya suna da kyakyawan alaqa da Imran din Hallayarsa na Burgesa rashin Shiga Mutane,baya da shiShishig baya Shiga Harkan kowa baya Hulda da mata sai yazo aiki ya Wuni har yammah ya tafi bai tanka ma kowa ba sai ya Zama Dole aiki ya Hadaku Mutane da yawa acikin bankin suna jin Haushinsa sai dai basu da yarda zasu yi dashi,Ko ya sani bai Damu ba Tunda bai isa yaasa su so ra”ayinsa ba Shidin Kaifi Daya ne.
Bashi da yarda zai yi ya karbi mganar sukayi Sharing din Lambar juna shida Manaja Tunde Abdulwasi,kuma bazai iya Turo Alfarma Khalil ba yana nuna Kulawa akansa.Daganan bakin Ruwa suka je suka dan Huta duk da ba wata Hira suke ba ammh yanayin yayi ma Imran Dadi yana gefe yana kallon Khalil Dake waya yana wani Narke Murya Kila da Budurwansa yake mgana Tsakani ga Allah Tsausayi ya bashi Namiji har Namiji ya Zauna Mace na Juyashi har yana neman mata kuka Duk da abaya yasan Khalil din kamar shine yana da Miskilanci Ammh jisa ya zauna yana wani marairacewa kamar zai yi kuka karamin Tsaki yaja yana kallon Daidaikun Mutanen Dake wucewa Idanuwansa yakai inda yaga wasu Beatifull Couple Duk da bai sani ba Zuciyarsa ta basa Ma”aurata ne,suna Rike da hannun juna suna Tafe Cikin Soyayya da kauna yana kallonsu yana jin wani yanayi kansu kawai yake Hangowa shi da Inteesar Tuna ta yayi sai da yaji wani Sanyi a fili ya Furta”Shababbiyar yarinya..Na kawota nan ai shagwabarta zata yi tamin..!
Yafada yana jin wani Annuri na Shigarsa Wayarsa ya Dauko ya Tura mata sakon

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button