GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Ajiyar zuciya Sagir ya Sauke,Yana kokarin Daga kiran ta yanke sai yabi bayan kiran Shima Gabda zata Katse Imran din ya Daga kiran yana Fadin”Kai dai banza ne Wlh..Kana ina ina ta kiranka baka Dauka ba.?
Yafada cikin Kaushin muryansa Wacce bata da Laushi Sagir yace”Dilla ina makaranta fa!
Imran yace”Ok..Gani kofar Shagon ka..yanzu zaka dawo ne ko na Shigo School din na Same ka..?
Da sauri Sagir yace”A”a gani nan Dawowa daman Lacture din Safe ce kadai garemu..Ka shiga ka gaida Mama kafim na Shigo..!
Shuru Imran yayi bai yi mgana ba Jin haka yasa Sagir yace”Dom Allah ka shiga ku gaisa..Mama nata Tambayanka kwana Biyu bata ganka ba..!
Imran yayi karamin Tsaki yana Fadin”Ba wani bata ganni ba kai ka mata wani Munafuncinka..!
Sagir na Dariya yace”Ka tsargu ne..? Tsaki Yaja kafin ya yanke kiran Yana Fadin”Ina jiranka kawai mallam..!
Imran bai yi Niyar shiga Gidansu Sagir ba sai dai bazai iya Juya alfarma da Kimar Mama ba Macece mai kirki da Dattako Yana Bala”in ganin kimarta Duk kuwa da irin yanayinsa.
Cikin Takunsa na Sassarfa da Kazarkazar dinsa ya Nufi Gidansu Sagir din yaran Sagir Dake Shagon suna Nuna sa da baki,suna mamakin yadda Oga sagir ya iya abota dashi Tunda suke dashi bai taba Musu mgana ba kogaishesu sukayi baya amsawa sai dai ya kalli Mutum ya kauda kansa Ko da zai zoSagir baya nan bazai Tanka kowa ba Ko Sallama acikinsa yake,Suna ganin Miskilan maza ammh wannan nashi Miskilancin sun Dangantashi Harda Wulakanci

Ya Dade tsaye a zauren gidansu Sagir din ya kasa Shiga yana Tunanin ya Shiga ne koya koma..? Sai dai yana Shirin juyawa ya koma yaji Muryan Maman Tana Fadin”A”a wanake gani kamar Imranu..?
Tafada Daidai Lokacin Data karisowa Cikin Zaure Shara tazo Zubarwa Tunda Abun sharan nasu na Zaure ne in ya cika ne almajira ke zuwa ya Zubar ta Biyashi
Fara ce sosai ba Yar gajeruwa bata da Tswo mai Fara”a Da Faramfaram da Mutane ba wata Babbace bace a shekaru iyakarta 45,,don ma Wahala da Rayuwa ce data samu jin Dadi datafi haka Yarinta Daga ganta kaga Sagir Saboda Fuskartane ya Debo Musamman ma karan Hancinta Sai dai Tsawon kila Dangin Mahaifinsa ya gado.
Cak ya tsaya Tunda ta Riga tagansa juyowa yayi yana Sosa keya Dan ramkwafa Yayi yana gaisheta Mama ta amsa Cikin Sakin Fuska tana Fadin”Ikon Allah kake tsaye kuma a zaure Imrana kamar bako..? Meyasa baka Shigo ba Sagir din ya Fita makaranta Tun safe..!
Kansa na kasa yace”Eh munyi mgana dashi..!
Mama tace”Shine ka tsaya Daganan Imrana..?sai ya kasa mgana Kansa dai na kasa Mirmishi TayiHaka Allah ya Doramata kaunar yaron ba Domin abotar Dake tsskaninsu da Sagir ba Imran yana da Shiga rai Duk da Muradaddun Hallayarsa
Juyawa Tayi tana Fadin”To shigo Daga Ciki ka jirashi ya Dawo..!
Bai da yardazai yi Dole ya Cira kafa yabi bayansa Daki ta Shiga ta Daukomai Tabarma ta Shinfidamai a Karamin Tsakar gidan nasu da Maman tagama Shareshi yayi kal kal Dashi Zama yayi kansa na kasa yana jin kansa a Takure haka yake baya iya Sakin Jiki matukar ba a Gidansu ba.
Mama ta kawomai Ruwan Purewater Tana Fadin”Ga Ruwa Imrana kasha..! Bai isa yace mata bazai sha ba Bai isa ya kauce ma Kararramawar ta ba,haka ya amsa ya Fasa ya sha kadan ya Rike Sauran A hannunshi yana Tunanin Sagir ya batamai Lokaci.
Ganin yadda yayi Shuru ne yasa Maman tace”ya wajen Baban naku Kuma..? Ya su Yusuf da Maimuna kwana Biyu ban shiga na Duba baban naku ba..?
Imran ya Saissauta Muryansa yace”Suna lafiya..!
Daga haka bai kara mgana ba ya kauda kansa yana kallon wani barayin Mirmishi Mama tayi kafin tace”masha Allah..Allah ya kara lafiya Acigaba da kula kaji Imrana..Rayuwar nan duka sai Hakuri watarana sai Labari..!
Kullum yazo sai tayimai wannan Nasihan Dakyar ya iya Bude baki yace”Insha Allahu Mama..”
Taji Dadin haka tace”Allah yayi muku albarka..”Aciki ya amsa da Ameen Daidai Lokacin Data mike Daga Kan kujeran Tsugunon Data kai nan kofar dakinta Sai ga Sallaman Sagir ya Shigo Gidan Mama ce kadai ta Daga kai ta amsa banda Imran da kansa ke kasa bai Dago ba saboda ya Shaida Muryan Sagir din.
Takalminsa ya Cire ya zauna kusa da Imran din yana gaida Mama ta amsa tana Fadin”Ga Imrana nan tun dazu yana ta jiranka..!
Sagir na kallon Imran ganin yadda ya wani Hade rai yasa ya juya ya kalli Mama yana Fadin”Ai mama ni na Turo miki shi nace ya Shigo kina nemansa..!
Mama tace”ai ka kyauta Sagir gashi yazomun gaisa..!
Sagir na Dariya kasa kasa ganin wani uwar Harara da Imran yake Sakarmai kafin ya Mike yana kokarin saka Budadden Takalminsa na Fatar Damisa yana Fadin”Amobe in kagama munafuncin naka Muje waje ina son mgana Dakai..!
Sagir ya mike kenan Mama Data shiga Karamin kitchen din da akayi shi da ginin Bulo an buga kwano ta sama harda kofar Katako Tana fadin”‘A”a ina zaku kuma Ga Abinci na sauke Mutumin Imrana nayi Danwake..!
Tafada da Fara”arta Sagir ne yayi Saurin cewa”Mama ba Nisa zamu yi ba..yanzu zamu dawo..!
Kada kai Tayi tana Fadin”To shikenan ammh ku dawo da wuri kada ya huce kusan baya Dadi kaji Imrana..!
Dole ya Bude baki yace’To mama..!
Lokaci daya suna Ficewa Daga Gidan Imran na gaba Sagir na Binsa a Baya.
Kai tsaye kofar shagon Sagir Imran yaje ya zauna Shima sai Sagir yazauna gefensa yana Fadin”wai menene kake nema na ne..?kayi kayi mganarka yunwa nake ji yau tun safe ko Ruwa bai Shiga Cikina ba mallam..!
Kamar ba da Mutum yake mgana ba Shi Imran din ma Hankalinsa na kan Sandar dake hannunsa yana Ta Tada kasan Dake gabansa Sagir ya Kufula yace”kafa Shanyani ina da abunyi mallam..!.
Kai tsaye Imran yace”Ni kuma gani wanda bai da nayi ko..?
Yafada hankalinsa kwance batare dama ya kalleshi ba
Sai kuma sagir din yaji Kamar bai kyauta ba kada kai yayi yana Fadin”Ni ba haka nake nufi b..!
Bai gama Rufe baki ba Imran yace”What ever kai ya shafa..Zuwa nayi na gayamaka anjuma zaka rakani gidan Babanka Manu..!
Sagir ya kalleshi Cikin mamaki yana Fadin”Wai Baba manu kake nufi..?
Imran yace”Kana da wani Baban Bayan shi ne daka ke Tambayata..?
Sagir yace”Bansani ba..Kai ne in zakayi ma mutane mgana Gatse gatse..!
Mirmishi Imran ya saki kafin ya Gintse Fuskarsa yana Fadin”mutane sun fi gane irin haka ne shiyasa kake ganin ina amfani da hakan..!
Sagir yace”Bama wannan ba Me zakaje yi gidan Baba Manu..?
Har Sagir ya Cire rai da zai ce wani abu,sai kuma ya Mike Tsaye yana Tusa Dukka hannuwansa Cikin Aljihun bakin wandon Dake Jikinsa,Dayan hannu ya Zaro mai Dauke da kwalin aspen Taba sai kuma ya Zaro Lether bayan ya Zari Daya ya saka abaki ya Kyasta Lether din ya kunnata yayi mata kyakyawan zuka yana wani Lumshe ido Lokaci Daya yana Fesar da Hayakinta zuwa ga Fuskar Sagir wanda yayi Saurin Tashi yaja da Baya yana Fadin”Kaga wulakancin ka ko Imu..? Kafa san bana son warin Taba!
Imran ya kallesa da Lumsassun idanuwansa kafin yace”Kuma gashi kana abota damai shanta sai yaya kenan..?
Hararansa Sagir yayi yana Fadin”Mallam ka Fadamim me zakaje yi gidan Baba Manu..?Nidai nasan bama Haduwa kuke yi ba in yazo ballatana nace wani abu ya shiga Tsakaninku..!
Imran yayi karamin Tsaki Lokaci Daya yana Zukar Tabarsa sai da ya Zuketa son ransa kana yasaketa a kasa ya saka kafa ya Taketa ya Murjeta yana Fadin”Kai banza…Zuwa zan yi nace ya shigema Ya yusuf gaba kan mganar auransa..!
Sagir ya saki Hanci da baki kafin yace”Aure kuma? Zai yi aure ne..?
Tafiya Imran ya farayi yana Fadin”Eh..Safiya wacce mukaje gidansu jiya ita zai aura Tsohonta yace ya Turo mgabantansa to Abba ne kuma kasan dai Halin Dayake ciki,shine na yanke Shawaran neman Baba manu sai ya Nemi ko abokansa ne suje ayi mganar auran..!
Ya fada daidai Lokacin Dayake Tsayawa kofar Gidansu Sagir din Domin Tunda Mama tace Danwake take yi yaji bazai iya Tafiya ba sai yaci Duk Duniya bai ga Wanda yakai Mama iya Danwake ba ko Munari yasa tayi mai in tayi Bai iya ci sai yaji bai ka na Mama Dadi ba.
Sagir ya tako ya Biyosa yana Fadin”Anya Baba manu zai yarda kuwa Imu..?
Imran bai kallesa ba yace”Saboda mene bazai yarda ba..Aure fa akace ba wani Shashanci ba..!
Sagir yace”Ba wannan ba Kasan dai ba mganar aure ba abun wasa bane..Ya kamata ace wannan karon kun Shigo da Danginku cikin mganar Imran..!
Yafada yana Fatan Imran dinyace wani abu yau ko zai samu wata makama kan Abunda ya Shafi Imran din da bai sani ba har yau.
Ammh sai me Ko kara mgana Imran bai yi mai ya Nufi Cikin Gidansu Sagir din yana Fadin”Mallam ni ban ce kamin Tsarinka ba..in baxaka Rakani ba nasan gidan..!
Daga haka ya shige ya barsa Sagir ya Dade yana auna wasu abubuwa,Tunda yake da Imran bayan Abba da Maimuna da Ya yusuf bai taba ganin wani nasu ba ko wasu sun zo gidansu ba su kadai suke Rayuwarsu kuma Dukkansu basu yarda suyi mganar Wani nasu da kowa koshi Duk yadda yake ga Tambayan Imran bai Taba gayamai komai ba sai dai ya Taba Cemai Abba Bafullatanin Gombe ne, wanda Daman ba wanda zai kalle su yasan cewa su din ba masu Hali bane,Tabbas basu yi kama da wadanda Halin Rayuwa ta gasa ba kodaga Gidan da suka Siya suke Ciki Dankakeren gida ne,ammh bai karaya ba zaicigaba da Bin sa har ya gano Abunda yake son ganowa.
Shima jikinsa a sanyaye yabi bayansa koda ya shiga ya iske Imran zaune kan Tabarmulan da suka tashi Dazu,yana cin Danwaken da Mama ta Zubamai itama Tana gefe kan kujeran Tsugguno
Karisawa yayi shima ya Cire Takalminsa ya zauna kan Tabarman kusa da Imran ya saka Hannunsa cikin Filet din Dake gaban Imran din ya Dauki Cokali ya Debo Danwaken ya kai Bakinsa sai da ya Tauna ya Hadiye kana yace”Wato shine kazo kana ci ko ka jirani ko..?
Ko kallonsa Imran bai yi ba yana Cin Danwakensa Mama ce tace”Inafa zaijiraka Tunda kai ka Shiga wata Sabgan.!
Bakin Sagir cike da Danwake Yace”Wlh mama muna fa Tare ne muna mgana ya taho kawai ya barni..!
Mama tace”Ai kunfi kusa ba Ruwana da shiga tsakaninku Sagir..!
Tafada Tana Dariya Shidai Imran bai ce komai ba sai daya koshi ya sha Ruwa bayan ya Tashi yaje bakin makurara ya wanke bakinsa Daidai Lokacin da Sagir ke cewa”Mama Inna Salaha ta kiraki yau..?
Mama tace”Eh munyi mgana da ita Dazu take gayamin gobe in Allah ya Kaimu Megidan nata zai kawo Inteesar din da kanta har nan gidan..!
Sagir yace”nima Bashir ya kirani Dazu ina makaranta..Shi yake gayamin Baban nasu da kansa zai raka Inteesar cikin makaranta tayi Registration da wasu abubuwan domin akwai Abokansa sosai Laccharori abunda bata karisa ba yana Rokona dom Allah na Taimaka mata ta karisa..!
Mama tace”Eh nima bayanin data min kenan ina Ruwan Inteesar..”
Sagir yace”Mama gaskiya Suna ji da yarinyar nan kalli fa bama Bashir din ba Baban nasu xai bar komai nashi ya kawota..!
Mama tace”Yar gatace sosai..Ita ce fa Autan Salaha har ta Fidda rai da samun Ciki ta samu Cikin Inteesar Tana ganin gata Mussmman wajen Uban..”
Sagir na shan Ruwa baysn ya gama yace'”Ni kuwa ban santa ba..!
Mama tace”Eh bazaka santa ba Kamar sau Daya Salaha ta taba zuwa Da ita tun tana karama Tun mahaifinka ma nada rai..Duk Zuwan Datakeyi Ita kadai take zuwa gaskiya kai kuma baka  Zuwa gidan Salaha in kaje  kaduna gaida su Inno  Balle kasanta kafi sanin Bashir dim Tunda shi yafi kawota in zata zo..!
Sagir ya Jinjina kai yana Mikewa Lokaci Daya yace”ina zuwa Mama in naje nida Muda ammh fa da Dadewa..!
Mama tace”Ai abunda nake nuna maka kenan yaran zamanin nan bakwa son zumunci Shi kanshi Mudan yaushe Rabonsa da nam..Ammh nayi mai uzuri yana Taimaka ma Mallam Babba a kasuwa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button