GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Daada na chan na Nazarinta ita kadai Imran ma nayin nasa shi fa a Tunaninsa zai yi Taimako ne Tunda Inteesar bata son khamis bazai bari a aura mata shi ba,Kuma bazai yarda Daada ta kawo wani ba Shiyasa yace Zai aureta ba domin ya yarda da mganarsu na cewa ko yana sonta bane baiyi Beleving kan wannan abun ba.
Daada ta Sauke Numfashi Tana Fadin”Zan yi mgana kan auranka da Inteesar kuma bamai Tada mgana ta..Sai dai kaima ina so kamin wani abu Guda Daya..!
Kallonta yake yi bai yi mgana ba Daada ta gyara ZAma Tana Fadin”Da Farko Dole zaka Dawo Imran din ka Dana sani..Ka daina shan Taba ka koma aiki ka zama Mutum wanda zai iya Rike mace saboda Nauyi ne zai Hau kanka Ina so don Allah ka Dawo Rayuwarka ta baya komai yayi Tsanani Saukin sa na wajen Allah indai zakamin wannan alfarman nayi maka alkawarin Karshen Wata Zan kira kowa da kowa kuma baza”a Watse ba sai da auranka da Inteesar da yardan Allah..!
Kamar Daada tayimai gafara haka yaji Cikin Farimcikinsa Daya kasa Boyuwa yace”Insha Allahu Daada..!
Daada taji Dadi sosai ta Rika sakamai albarka Kiran La”asar ya tadasu ya tafi yayi sallah Daya dawo ya shiga ya kwanta yana Barcin gajiya bai tashi ba sai gabda mangariba Ya tashi yaje yayi salla ya Dawo barcin yammah Cikin kunci ya tashi ga kuma Fushin Inteesar bata Kirasa ba sai shima ya Shareta.
Da Daddare sun sha Hira Daada Shi kanshi yana ta mamakin kansa ko Saboda Rabi Hirar Daada ke yinsa kuma Duka Labarkn Anni ce shiyasa yake jin Dadin Hirar kuma bama Haka ba Zuwansa Dukku yazomai da Sauyi sosai yaji Dadin zuwansa Wajen Kakarsa sai alokacin yake jin Dadin da Sauran mutane ke ji in suka zo wajen kakkaninsu bai taba Samun kusanci da Daada ba sai wannan karon.
Washegari daya tashi da Safe yaga Kiran waya da bakuwar lamba ba adadi,ga Sako yayi mamakin wanda ya Kirasa,sai dai sakon Daya gani ya bashi amsa Sajida ce.
Tsaki yaja yayi Bloking dinta ya Share Sakon nata Domin baya Bukatar Wata mu’amala da ita bashi da akala da ita
Ita kuma Daman Umaima ta saka Ta Tambayan mata Munari ita kuma ta Turo ma Umaiman ta Tura mata,Shine ta Dinga Kiransa bai Dauka ba ta Turamai sako Daga baya ta Dinga Kira bai shiga ba ta Fahimci ya Kulleta ne Tayi kuka sosai kamar Ranta Zai Fita kuma ta Dora Bleeminng din komai kam Mami Tama ganin koma menene ya Faru itace Sila,Shiyasa bayan sun gama Test tayi zamanta a Hostel bata Dawo gida ba saboda Haushin Mami Asma”u take ji.

Sai ga Imran dayaje Dukku da Niyyar kwana Daya ya shantake har kwana Biyu sai dai Ranar Lahadi da Safe Bankin GTB, Reshen Jahar kano suka Turomai sakon suna son ganinsa Karfe 8:00am na safe tayimai a Office din Manaja Ranar Monday abaya bai Damu ba da aikin ba,ammh yanzu ya Damu ko Saboda mganar Daada,Khalil ya kira ya gayamai sun Dade suna mgana yana bashi Shawarwari da Kwarin gwiwa kafin suyi sallama alokacin yayi shirin Tafiya Kano da shirnsa ma ya shiga Dakin Daada yayi mata sallama Tana ta mamakin Tafiya ba Shiri yace mata wani abu ne ya taso.
Kamar kar yatafi haka Daada taji shima haka sai dai ba yarda zatayi haka sukayi sallama karfe 12, yana gombe,Daganan ya Hau Motar kano sun samu Goslow a hanya da kuma Wahalan Mai yasa basu shigo da Wuri ba sai bayan mangariba suka Shigo kano.sai dai su Abba suka gansa kamar Daga sama.

Naji Sauki Sosai…Nagode da addu”o’inku..Allah ya bar Zumunci Ameen..

Shakira
3/22/22, 23:15 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?13

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Ganinsa Kamar daga sama bai sa wani ya Tambayesa Dalilinsa ba,Sanin halinsa shiyasa ba wanda ya Damu daya cemai wani abu ko Abba ya saka ma Ransa ya gaji da zaman Dukkun ne Shiyasa Lokaci Daya yaji dawowa gida,ba wanda ya kawo Tunanin wani abu,Shima baice ma kowa komai ba so yake sai komai ya tabbata ya bama Abba da Yaya Yusuf a big Suprise.
Inteesar da Munari suna gidan Tunda Mama bata dawo ba,Bai bi ma ta kanta ba saboda Ransa ya baci da abunda tayimai Yayi Doguwar Tafiya ko ta Kirashi Taji lafiya ya sauka Shiyasa yayi shigewarsa Daki bayan ya barsu afalo tare da su Abba Ko kallonta ma bai yarda yayi ba ita kuwa Tana kallonsa Cikin wani Shaukin Dake Fitowa daga kasan Ranta.
Wanka yayi ya sauya kaya yayi Sallar mangariba,sannan ya fita yaje Kitchen ya Hada Tea ya Fito Dauke da Mug din kan Dinning ya zauna yasha Abunsa Inteesar da duke zaune afalon Tana ta satar kallonsa sai kuma Taga ko kallonta ma bai yi ba yana shan Tea dinsa yana Nazarin abubuwan da zai Faru gobe shiyasa yana gamawa ya mike ya Fice Daga Falon Inteesar ta Bisa da kallon kauna.
Masallaci ya nufa,Saboda yaji kamar an Tada sallah Su Abba ma sun tafi tun Dazu,koda yaje Raka”a Biyu ya samu Sauran sai da ya Rama yana cikin Masallacin Abba da Ya yusuf suka Fice Sai Sagir ne ya Jirasa ya idar suka Fito tare.
Akofar gidan su Sagir din suka Tsaya Sagir na Tambayansa ya sukayi da Daada bai gayamai ba yadai cemai komai lafiyalau Key din mashinsa ya amsa,yace ma Sagir gobe da Safe akwai inda Zashi ganin Imran din bai gayamai inda zashi ba yasa Shima bai Tambaya ba,Ba Dadewa sukayi Sallama Sagir ya Fada shagonsa Shima Imran din ya wuce gida.
Da wuri ya kwanta Saboda akwai Gajiya ajikinsa Har ya kwanta ya Tuna da Inteesar karamin Tsaki yaja kawai Mikewa zaune yayi ya Dauko Wayarsa ya Kirata alokacin bai da Riga Dagashi sai Boxer Imran ko ana Sanyi baya shiri da Zafi kwatakwata
Wayar ta shiga sai dai bata Dade Tana Ringing ba yaji ta danna mai Nomba busy,ido ya waro yana bin wayar da kallo Zuciyarsa na Zafi kamar Shine Inteesar Zata kashe ma Waya..?Shi Imran..?ko abaya ba wacce ta isa ballatana ma yanzu Dayake jin kansa Daidai da kugun kowani Dan iska Shiyasa Tun Farko baya harkan mata Saboda Raini,Inteesar ta gama Rainasa Wato saboda taga yana mata Dariya Shine Zata Kashemai waya ga Dan iska ta samu ko..? Ko ma ace yaje Wajen Sajidan ne da gaske ta isa ta Hanashi zuwa ne?Shifa Namiji ne kuma yaya yake gareta ya bata Shekaru ba iyaka in Haihuwar kaji ne zai iya Haifarta Wlh shi Namiji ne Mijin Mace Hudu wata mace bata isa ta Zauna tana Raina mai wayau ba Ko Wacece ita kuwa,Ahaka ne Sagir ke cewa yana sonta..?aikin banza in taji ma wannan mganar sai Rainin nata ma yayi yawa shifa ba macen da Zata Zauna yana bata Hakuri yana Lallashinta yana da abubuwan yi masu Tarin muhimmanci da suka fi bata Lokacinsa kan Shirme Duk yadda Ransa ke Tafasa haka ya kanne ya Cije yayi ma kansa alkawarin Fita Sabgarta Domin Tsira da Mutuncinsa sai dai yadda yake ji game da ita ya Kasheshi daya zauna yana Fuskarta Raini da wannan Wulakanci a wajen yarinyar da bata wuce yar Cikinsa ba badai shi tama haka ba ko..? uhm Fushi Ta Cigaba da yi daga yau har Mahadi ya bayyana yafita Taurin kai da Zuciya.
Duk yadda yaso barci ya Kwasheshi a wannan Daran ya kasa,sai da ya tashi Sauran Sigarinsa Daya siya a Dukku,Tun Da yaje bai wuce sau biyu yasha Sigari ba yana da Sauranta ita ya Dauko ya Dinga ban kama Cikinsa Har sai da yaji Zuciyarsa ta Cunkushe Kirjinsa da Kansa sun yi masa Nauyi kana ya Hakura ya koma ya kwanta yana Sauke Numfashi Daya bayan Daya.
Ya Dade bai yi barci ba sai chan Dayayi Ruf da ciki duk da ba kyau ammh bai da Zabi,yayi Filo da Hannayensa saman Fuska sai Lokacin ya samu barci yaso ma ya makara ba Domin Abba ya Bugamai Kofa ba sanda Zasu masallaci shi da Yusuf Dakyar ya iya tashi da jan kafa ya shiga Tiolet,in ya Tsaya yin wanka zai Rasa Salla Shiyasa ya dauro alwala yabi bayan su Abba zuwa masallaci Allah ya Taimakesa an Tada Sallar ammh ba”a kai ga Ruku”u ba,Bayan an Idar da Sallar ya Dade yana addu”an Nasara a Rayuwarsa yana addu”an Samun wannan aikin Duk da Manaja Tunde ya bashi Tabbacin ammh bazai kwanta da hakan ba ayanzu yana Bukatar aikin Ko domin cikama Daada alkawarinta,Uwa uba kuma Lokaci Yayi da komai zai Sauya ko domin ya maida ma wasu martani irin su Mami Asma”u.
Sai Bakwai Saura ya baro Masallacin zuwa Gida yana zuwa wanka yayi a gurguje baya so yayi african Time Daman chan ba Tsarinsa bane bayan ya Fito ya shafa lotion dinsa ya Taje Sumar kansa bayan ya shafamata Mai gyaran gashi,Wardrope dinsa ya Bude yana Duba Jerin suit dinsa Dayake dasu wanda ya Taho dasu Daga Lagos bai Taba sakasu anan garin ba barshi da Saka Saukakun kaya.
Suit din na kamfanin DKNY ne sai na kamfanin Armani suna da kyau da Quality shiyasa Har Lokacin basu yi komai ba suna Sagale cikin Hanger wasu ma Sabbi ne suna da Leda ajikinsu bai Taba sakawa ba.
Daya Daga Ciki ya ciro na kamfanin Armani Kalan Black and White ya Dauko Daya Daga Tektie dinsa Baki,Lokacin yana Lagos gabadaya kayansa Suit ne saboda yanayin aikinsa Wlh bamai nuna mai iya saka kaya a Tsuke wannan yana ma Daga Cikin Tsarin aikinsu
Cikin Lokaci yayi shirinsa Woww..Nace Lokacin da ya Tsaya gaban Madubi yana Daura Tek tie dinsa,ya Hade har ya gaji da Haduwa Cikar Zatinsa ya kara bayyana kamar wani babban Mutum,baza kayi mai kallo Daya kace Imran ne mai Busa Hayaki ba sai ka karemai kallo kafin ka iya Tantace shine ko ba shi bane.?
Agogon Azurfa ya sanya atsitsiyan Hannunsa na Hagu,silba ne yana Kyalli,Yana da irin su Dadama sai dai baya amfani dasu,bai cika damuwa da sai Rayuwarsa ta dawo kamar baya ba ammh a yau kam gabar ta bayyana Dolene ya Dawo Imran dinsa in yana son Cimma Burinsa.
Takalminsa Rufaffa ne na Fatar Daminsa baki shima suit din baka ce haka ma wandon baki ne sai Rigar Ciki ne Fara,Imran mai kyau ne kuma shidin Dan baiwa ne Tuni ya Fito a ma”aikacin bankinsa da ba wanda ya isa ya Kallesa da kallon Raini Karamar Wayarsa ya Dauka ya Saka Cikin Aljihu yanzu bashi da komai sai dai in yaje komai ya kamkama akwai Bukatar ya mallaki wasu abubuwa kamar su Laptop,da waya saboda aikinsu baya Tafiya sai da haka Lokacin Laptop dinsa ma bazai iya Tuna ina isalinta ba,ana ta Rai wake ta abun Duniya alokacin.
Key din Mashin dinsa ya Dauka saboda shi yake dashi alokacin ya Fito bayan ya Fesa Saukkan Turaransa mai Dadin kamshi na azzaro Visit.
Dukkansu suna kan Dinning suna Breakfast,ya Fito Cikin Shirinsa Gabadayansu baki suka saki da Hanci suna kallonsa.
Inteesar kuwa kamar Idanuwanta Zasu Fado Tunani take yi anya wannan Imran ne ko mai kama dashi..?gabadaya zuciyarta wani Tsalle take yi waje Daya dashi ta kwana acikin Ranta Kiran da yayi mata Jiya tazo Dauka sai bata sani ba ta kashe Kiran batayi Tunanin bazai kara Kira ba Domin har Ga Allah ta Saki Fushin taga alamar ita ce Zata sha Wahala daga baya daga ga Shuru bai Kara Kira ba sai ta Kirashi Sharrin Network yasa bata Sameshi ba.
Yadda ta kafeshi da ido sai da gabansa ya Fadi ammh ya Kauda kai bai yarda ma ya kara kallonta,Daga tsayen bai karisa ba ya kalli Abba Dake kallonsa Cikin Mirmishi da Alfahari yace”Gud mrning Abba..Zan je wani waje bazan Dade ba zan dawo..!
Abba kai kawai ya gyada Farinciki yasa ya kasa mgana ganin Imran cikin wannan Shigar ya Tunamai da abubuwa da dama ashekarun baya Lokacin yana ainihin Imran dinsa mai ci da guminsa,Yana Fatan wannan Fitar ta saka na alheri ne yasa Addu’arsa ne Allah ya amsa Imran zai sauya zai dawo Imran din Dayake so kuma yake Fata.
Ya Yusuf ne ya ijiye mug din Tea din Dake Hannunaa yana Fadin”Woww..Long Time Imran Abubakar Malami..!
Yafada yana bayyana Mirmishinsa da kuma bayyana irin kyan Zatin da kanin nasa yayi yau daya Dade bai yi wannan Shigar ba.
Safiya da Munari suma ayyanawa kawai suke acikin ransu ko cikin Dubbam Maza Imran na Musamman ne banda Inteesar data riga ta zama gatanan ne azaune saboda wani Rauni Dataji ya kamata ganin yadda Imran din ya nuna bama ya son ganinta din

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button