GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


Washegari ma haka gidan ya tashi acike da yan”uwan Munari Farincikinta yaki Boyewa tana cikin Danginta ta kwana cikinsu ana Hira Imran dai Daki daya suka kwana Da Sagir,Wanda Imran kasan Cafet ya kwana ya barma Sagir gadon domin bazai iya barci da wani akan gado ba.
Basheeer kuma dasu Sadam dukkansu Daki daya sukayi kwanciyarsu ko ajikinsu suka kusa Raba Dare suna Hira.
Su Abba ma Daki daya suka kwana Abunsu hakama su Inteesar da Hafsah da Munari su Aneesa ne da Safiya da Fareesatu da su Zainab daki Daya Mami Asma”u dai ita da Umma suka Kwana Daki Daya Inna Maimunatu Dakin Daada tayi kwanciyarta.
Kamar koyaushe ma yau din Baba Asabe sukace ta Huta su sukayi Breakafast kowa ya Fito banda Imran Daada tace ahada kayan karyawansa akai mai Daki Munari ta Zare Jikinta Inteesar da Hafsah suka Dauka sai gashi sun dawo dashi sunyi ta Knooking bai bude ba Hankalin Daada ya tashi ta fara Tunanin ko wani abu ne ya sameshi Abba yace mata kada ta damu lafiyansa Kalau kana ta koma ta Zauna ammh duk ta Shiga Damuwa Bata kai Inteesar shiga Damuwa ba.
Daki ta koma ta Dauki wayarta ta Kirasa bai Dauka ba Har sau uku,sai na Hudu ya danna mata Busy sai ga Sakonsa.

“Kada ki dameni da Rigimarki da safan nan..Am not in d Mood..Barci nake yi..Kuma an sure kece kika zo kina min knooking ko..? Don’t let me Catch u bazaki ji da dadi ba..!

Data ga sakon sai da ta tintsire da Dariya kafin ta maida amsa.

“Daada zaka kama ko..? Domim ita ta aikoni na kawo maka Breakfast dinka..”

Amsa ya bata da cewa”Nidai ke nace ba Daada ba..!
Dariya tayi sosai tana Jin Dadin tsokanansa Kyaleshi tayi jin yace baya cikin Mood din.
Falo ta dawo domin bata gama shan Tea dinta ba ta zauna kenan taji Daada na Fadin”Kabiru ya mganar zuwan su Hamisu ne..? Binta kefa kin kirasu Hamidan..?
Baffa Kabiru ne yafa fadin”Eh Daada na Kirasa ban samesa ba sai dai na Turamai sako nasan yan gani zai Dauki Excuse wajen aiki ya taho..Su Sajida kuma Asma”u nace tayi mgama Dasu..! Kai Daada ta jinjina batace komai ba.
Inna Bintalo tace”Su Hamida suna Hanya na Kirasu..!
Daada tace”Yayi kyau..Asma”u Su Sajidan kinyi mgana dasu..!
Cikin Mganarta Tace”Eh Daada. Nayi mgana da Sajida duk da sun kusa Fara Text nace Direbansu ya kawo su yau ita da Umaima..!
Tafada cikin jin Haushi Tsakani ga Allah an takurama ya”yanta.
Daada tace”Ai ba Dadewa bane abun Asm’u zuwa gobe ko jibi in mun gama Abunda ya taramu kowa zai koma bakin aikinsa Tunda ai kowa ma yana da ayyukan ya Saukesu ya Taho..!
Cikin hikima Daada ta maida mata mganarta Inteesar kuwa Farincikinta Duk ya tsaya Lokacin dataji ance Khamis zai zo acikin Ranta Tana ta addu”an kada Allah yasa yaga ma Sakon na Baffa Kabiru ballatana ya Taho.
Bayan sun gama Karyawan su Inteesar suka Tattara komai zuwa Kitchen ita da Munari suka Fara wankewa Hafsah taje yima yaran su Anty Aneesa wanka su Waleeda.
Su Abba kuma suna nan afalon Tare da Daada Mami Asma”u daki ta koma ta Kira Sajida tana Dagawa tace”Mami ko mu yi zaman mu ne..?.
Mami Asma”u tace”A”a ku taho kawai yanzu Sajida..Daada ta matsa sai kun zo..!
Sajida ta bata rai Tana Fadin”Mami to me zamu zo muyi..? Nifa i hv alot to do Mami kinsani Test zamu fara Next Upper week..Ina son kadaici na samu nayi karatu..!
Mami Asma”u tace”Nasani buh ai zuwa Gobe ne zamu dawo kada ki Damu bzai shafi karatunki ba ni kaina ban so ba To kinsan Daada rigimarta Tayi yawa kuma Dad din ku bazai ce komai ba ammh banga Abunda zata ce sai yara sun bar karatunsu sun taho ba..!
Sajida ta Tabe baki kafin tace”Wai to ba Baffan ya dawo ba? Ta gansa Inace ba Shikenan ba..?
Mami Asma”u tace”Uhm kya fada kema..Ina Umai..!
Sajida ta juya tana kallon Umaima Data Fito wanka tana shafa Lotion sai Murna take tace”Gatan nan tayi wanka..Sai murna take Mami kinsanta..!
Mami Asma”u tace”Bata da.wayau ne bata san ciwon kanta ba..Ku taso yanzu kada kuyi dare..Make sure kun dauko duk abunda zaku nema kuma kizo da komai na Karatunki harda Laptop dinki kinji..!
Sajida tace”Ok Mami see you..!
Daga haka suka yanke kiran Umma na gefe ta kishingida Tana jinta batace mata komai ba itama bata mata mgana ba Sanin Halinta yasa Umma ke cin mganin zaama da ita.
Imran bai fito ba sai azahar da zashi Msallaci Sagir ko ta kansa bai bi yana cikin su Basheer abunsa,bayan ya Dawo a masallaci Aharaban gidan ya Tsaya ya sha Sigarinsa Baffa Kabiru ma ya Fito ya gansa yayi kamar bai gansa Baffa Kabiru kuma bai nuna ma ya gansa saboda yadda Imran yake Tabbas zai iya zaginsa in ya cika Shigema yaron.
Bayan ya gama shan kayansa ne ya Shigo Cikin gidan ba kuma wai domin yana jin Tsoron Shanta acikin Gidan ne,A”a saboda Abba ne shi kadai ne yake Gudun bacin ransa sai Daada Dake yake ganin Girman Tsohuwan da kuma Kaunarta Dayake yi ko domin kaunarta ga Abba da Anni dasu Gabadaya.
Yana Shigowa Falon su ka kusa cin karo da Inteesar da Suke wasan banzan Ita da Munari da Hafsah Daga gyaran Falo suka Fara Wurgama Juna Cussion din kujerun falon.
Batama san ya kawo ba ta taho bata ganin gabanta,Kawai ta Fadamai da yayi baya sai tatafi luu zata Fadi ya saka Hannunsa ya Tallafota ta Fada kan Kirjinsa male male ta Rikesa gam tana Sauke Numfashi.
Munari da Hafsah suka Tsure kowacce ta Tsaya tana Raba ido Sai Alokacin Inteesar ta dago Tana ganinsa ta Saki baki Shima kallonta yake da dukkan Tunaninsa da Zuciyarsa.
Sakinta yayi kafin yadan matsa Baya jin jikinsa ya fara saki,kallonsu yayi Daya bayan daya kafin yace”Are u a kid..?manya daku kuzo kuna wasan banza..!?
Kowacce ta koma ta natsu kafin nayi kwallo da yarinya..!
Ai kafin ya gama mgana Munari da Hafsah sun bace afalon Inteesar ce ta Tsaya taki tafiya Kallonta yayi kafin yace” kin rainani ko..?Ok daman nace zan rike ki..? Kina son duka ne ko..?
Ai jin haka yasa ta Zaro ido kafin tayi narai narai da ido tace”Duka kuma Ya Imu..?
Kai ya gyada mata kafin yayi mgana ta wuce sum sum tana waigensa Dariya ta kamasa,sai kawai ya Murmusa ya wuce itama tana lekensa tana Dariya.
Cikin Ikon Allah Sai ga Khamis ya Riga su Sajida isowa ashe yana ganin Sakon ya nemi Uzurin Rashin Lafiyar kakarsa aka bashi kwana Biyu Jirgi ya shigo zuwa Gombe daganan ya Hayo Taxi zuwa Dukku sai dai aka gansa Kwatsan Mami Asma”u sai Murna Yaronta yazo ta saka Baba Asabe ta cikamai gabansa da Abun sha da ci.
Har kasa ya duka yana gaida Abba ya Dagosa ya Rumgumesa yana sakamai albarka haka suka Rumgume da Yusuf Cikin jin Dadin ganin juna haka suka Gaisa da Munri cikin Fara”a acikin Ransa yana Fadin She is Beautifull.
Imran ne bai gani ba yana cikin Daki Inteesar kuma Tunda taji Zuwan Khamis ta shige daki taki Fitowa bata Kaunar su hadu shi kuma ita yake tason gani karfin ma zuwansa Saboda itace yana so su hadu suga juna Ya gayamata Sirrin zuciyarsa Soyayyarta yana sakasa cikin wani yanayi gashi bata Daga Kiransa Ita kuwa Taki Fitowa gashi sai kiranta yake yi taki Dagawa.
Ya iso ba Dadewa sai ga Su Sajida sun iso,Umaima ce ta shigo Da Murnanta da Farincikinta banda Sajida Datake Tavwani Hura Hanci Mami Asma”u sai kai da kawo take kan ya”yanta Umaima ce taxo inda su Inteesar suka ta gaisa da Munari cikin Murnan Haduwa da ita banda Sajida wacce sai da Baffa Kabiru yayi mata mgana ta gaida Abba tana kallinsa tana Tuna kamanninsa.
Sanin Halinta yasa ba wanda ya Nemeta Cikin su Inteesar itama bata Neme kowa ba.
Imran kuma da Khamis basu Hadu ba sai da suka dawo masallaci Sallar Mangariba,ya gansa tare da Sagir yake Tambayan Sadam yamai bayani mamaki ya kamashi ganin ya mikamai hannu suyi musabaha Imran yaki bashi Hannu,sai kawai ya maida Hannuwansa Baya Sagir ne ya mikamai suka gaisa,shi kuwa Imran Kallo Daya yayi ma Khamis bai kara ba Saboda yaji bai kwantamai arai ba Shima Khamis din ransa ya baci da Wulakancin da Imran din yayi mai Da Farko yana Tunanin bai ganesa ba Ammh sai da yamai bayani sai yaga bai nuna ma wata alaman sani ba Sai Ransa ya baci Haka kurum yaji bai ji Dadin wannan Tozarcin ba sai dai bai nuna ba.
Haka suka Dawo gida suka Shigo Cikin Falon a Tare,Lokacin su Sajida da Mami Asma”u suna Zaune a Falon kowa ya samu waje ya zauna Su Abba Dakin Daada suka shige abunsu.
Kowa waje ya samu ya zauna kusa da wanda sukafi dasawa Sagir kusa da Basheer ya zauna Imran ne kadai ya Coge a tsaye Daga kofar Shigowa ya Harde duka Hannuwansa saman kirjinsa da kafarsa yana kadata Yana sanye da Riga mai Ruwan madara mai Dogon Hannu sai bakin Wandonsa wanda ya Tsukesa ta kasa Kansa yasha gyara Dadan nan ya kara yawa Fuskarssa a tamke yana Bin kowa da kallo Cikin Nazari.
Sajida dake Duba wayarta Sanye take da Riga da sikat na yan kanti pink colour kanta da Kitson galaba,mayafin data yane kanta Dashi ya dan zamo ta bayanta Kafarta Daya kan Dayane Tana gefen Mami Asma”u ne.
Daidai Lokacin data Dago kanta Shima Imran idanuwansa sun kai Kan ita Sajidan suka Hada Ido Hudu da ita Gaban Sajida ya yanke ya Fadi,yayinda ta Zurama Imran ido Tun daga sama Har kasa Tana karemai kallo cikin yanayin data kasa Fassarawa Yayinda Imran yaji Haushin Kallonta garesa ya Sake Hade rai ya Dauke kansa sama yana wani Dakuna Fuska kamar yaga Kashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button