GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana gama Fadin haka ya Sauke Hannunshi ya Wuce zuwa Dakinsa ya Shige ya Turo Kofa,Yusuf ya Bishi da kallon Kauna da Tsausayin Dan”uwansa kafin ya Girgiza kai yana Fadin”Kana Matukar Burgeni IMRAN ABUBAKAR MALAMI..”daga haka ya juya zuwa Dakin Abba Cikin Farinciki Domin ya sanar dashi Allah yayi zai yi aure wannan karan.


KADUNA..
Area:Anguwan Sarki..

Acikin anguwan Sarki acikin wani Tangamemen gida na Zamani Da misalin karfe 8pm na Dare wata yar Matashiyar Budurwa nagani wacce bata wuce Shekara 20 ba aduniya Doguwa ce sosai bata da Kiba Kirjinta kadai ne yake Tudu daga kasanta kuma ba wani abun kirki Sai Doguwar Fuskarta Kalar Fatarta baka ce ammh Ta samu Hutu da Jin Dadi,bata da Dogon Hanci Sai dai kana ganinta zaka Fahimci Ta Hada Jinsi da Fulani ko ta Uba ko ta Uwa tun bare ma yanayin Tsawonta da Idanuwanta Masu Dauke da gashin ido da kuma Gashinta Data Tufkeshi Har ya sauko Zuwa ga wuyanta.
Sanye Take da wata karamar Riga kamar Shimi Doguwa kanta ba Dankwali Sai Faman loda kaya take cikin wata Trolley bayan wadanda Tagama Durawa akwatuna Hudu gasunan a jere asaman Dan madaidaicin gadonta.

Har aka Bude Kofar aka Shigo Bata sani ba sai da taji Daga Bayanta ance”Auta wannan Uban kayan Duk na zuwa Kanon ne..?
Muryan wani Namiji ya Fadi hakan da Sauri ta waigo Tana kallonsa Shima kamar ita yake sai dai abun mamaki Shi Fari ne kuma ya Fita Dogon Hanci da Jikin Maza saboda yana da Dam Kiba ammh da tsawon da yanayin komai iri Dayane,Shekarunsa kuwa baza su wuce 30 aduniya ba

Zurawa Tayi da gudu zuwa gareshi ta Rumgumeshi Tana Fadin”Ya Bashir..Yaushe kazo..? Yana Mirmishi ya Shafa kanta yana Fadin”Autan Umma Kenan..Yanzu na Shigo nazo kawo su Abiden ne sun saka Rigiman wajen Umma yau zasu kwana..”Fuska Ta tabe kafin tace”Nifa ban gane musu bane..Suna so su kwacemin mtsayina wajen Umma da Da Daddy..”Yana Dariya yace”Wane su su kwace gwamnatin autan Umma da Daddy..Shalelen Ya Bashir da Anty Hauwa..”Tanajin wannan kirarin ta washe baki Tana Fadin”Shiyasa nake matukar sonka Ya Bashir..Zan yi kewarka in na tafi kano..”

Ta karishe Fada Kamar tayi kuka irin na Shagwabbun yara bai samu Zarafin mgana ba wata Mata Baka mai Fadin Fuska wacce sai da ta Shigo na Fahimci inda ta Dibo Bakin Fatarta da Hancinta irin nata ne sak,Sai dai ita bata da Tsawo a Shekaru bazata gaza 40 ba Tana Shigowa ta gansu ahaka ta Tabe baki Tana Fadin”Kana nan kana Biye Shiriritar INTEESAR KO.? tun Dazu nake mata mganar ta Rage wadanan kayan taki jin mganata Ta kwashe Rabin kayanta kamar Chaj zata koma Har Abada..!
Umma ta Fada Cikin kara Bayyana mamakinta Wacce aka kira da Intesar ta Fara Buga kafa na Shagwaba Tana Fadin”to ni Umma ba Karatu zan Tafi ba..Kuma ai ance yan Jami”a fa yan gayu ne sosai Dole nima naje da kayan gayuna kada wata ma ta Rainani..”Ya Bashir ya saka Dariya yana Fadin”Hakane fa Intin Umma..Gwara kije da Kayanki Jjc Student..”Ya karishe Fada yana Dariya jin Abunda yace ne yasa ta Nakwa nakwa kamar Zatayi kuka ta Kwashi Gudu Ta Fice Daga Dakin Tana Kukan Shagwabarta Tana Fadin”Sai na gayama Daddy..Kai da Umma kun hademin kai kuna min Dariya..!

Umma ta Tabe baki ta kalle Bashir Dake Dariya tace”Kabiya ta Kitchen ka Karbi Dambun Wajen Talatu katafin ma Hauwa”u dashi..”Cikin Ladabi yace”To Umma..Angode..”Batayi mgana ta Fice Daga Dakin Shima ya Rufa mata Baya Jin Daddy na Kiran sunansa Topa Auta ta kai Sunansa yau shi da Daddy sai Allah Dariya kawai yake kasa kasa Har ya Kariso Falon.

Shakira…
3/22/22, 23:02 – Ummi Tandama😇: GIDANMU..!
(Our House)
Book1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)

            *🅿�3*

“Da sallama ya Shigo Falon yana Danne Dariyansa ganin Inteesar dare Dare kan cinyar Daddy Tana ta Zubamai Shagwaba shi kuma yana ta Biye mata yana Lallashinta ga Abideen da Abida suna Tsaye gefe suna kallonta Daga duk alamu suna kan Jikin Daddy din ne tazo ta Turesu ta Haye Daman tace wajenta ne suke Neman su kwace mata.

ALHAJI MUSTAPHA HAMISU DUKKU ya Dago kyakyawan Farar Fuskarsa Tar da ita kamar ataba Jini ya Fito,Hancinsa Har baka yake kana masa kallon Farko zaka Shaida Tabbas Bafullace ne,Akallah Shekara bazai gaza Shekaru 58 aduniya ba Fararsa ta goge da jin Dadi da Hutu In ka kara kallonsa zaka Fahinci inda suka Dauko Tsawo da Doguwar Fuska Daga Bashir din Har Inteesar din sai dai Bashir Hasken Mahaifinsa ya Debo wanda Gashin kansa da Gemunsa suka Fara Zama Fari bakin gashin kadan ne Daga ganin sa yana da yalwar gargasa ajikinsa.

Cikin Muryansa ta Dattako ya kalli Bashir yana Fadin”Taho nan..Naji Meyasa kuka Tasa Autana agaba kuna mata Dariya kai da Mamarka..? Yafada yana dan Hade ransa ganin yadda Inti din ke kallonsa Bashir na kanne Dariyansa ya Zauna akasa Kusa da Kafar Daddy,Da gudu kuwa su Abiden suka Nufesa ya Daukesu ya aza kan jikinsa,Daga ganinsu yan Biyu ne saboda suna da Tsananin kama da juna Shekarasu bazai Wuce 3 aduniya ba yara ne kanana sai dai sun Debo Tsawon Babansu suna da Tsayi ba Laifi.

Cikin Ladabi yace”Daddy ba Dariya muke mata bafa..Ita Da Umma ne tana mata Fadan Ta Dibi kaya dayawa Shine tace saboda kada taje yan Jami”a su Raina Sai fa kawai nace Jjc shikenan fa Daddy ta Fara Shagwabarta..”Ya karisa Fada Daidai Lokacin da Umma ta Fito Daga Bedroom din Dake Cikin Falon,Ta kariso kusa da Daddy ta Zauna Tana Kallon Intisar Lokaci Daya Tana Fadin”Ke miye haka..? Ko kunya baki ji ba Godai godai Dake kin Ture yara kasa ke Kin Hau Cinya ko.? Anya Inti kina so ki Girma kuwa.? Yarinya kina Girma kina kara Komawa baya koda yake ba Laifin ki bane na Alhaji ne duk ya Sangartaki..”
Ko kafin tagama Mganarta Bakin Inti ya kusa Fadowa kasa Cikin Sangarta Ta kalli Daddy Tana Fadin”Daddy kaji Umma ko..? Shiyasa nake ta Murna zan Tafi na bar mata gidan..”Ta karishe Fada tana wani Tura baki.
Umma ta tabe baki Tana Fadin”Ai chan bazaki samu Damar yin wannan Sangarta ba..Yaya Amina ba Irin Sakarkarun Matanan bane atsaye take..Ga kuma yayanki Sagir zan ce mai da kinyi wani Abu ya Zanemin ke..”Kawai ba sai Inti ta Saki kuka Kamar wata karamar yarinyar Bashir sai Dariya yake Umma ta kalleta Sororo kafin tace”Yau naga Sakalci Inti wai yaushe Zaki Girma ne..? Kin fa wuce Shekara ashirin Kina Shirin Shiga Jami”a kina Tabara Yau ko aurar dake mukayi Badi war haka kin Haihu..”Ai jin haka sai Inti ta kara Sautin kukanta Tanayi Tana Fadin”Ni ba zanyi aure ba..Kuma bazan Haihu ba..”Kai Dagajin kukan kasan na Sangarta ne Daddy ke Lallashinta yana Fadin”To daman yaushe Autana  ta isa aure..!? Ai ba yanzu zaki aure ba sai kin kara girma…Shima sai naga Dacewar Mijin da Zaki aura wanda zai Rikemin ke ya Rika Lallabaki kamar yadda nake Lallabaki sai yayimin alkawarin kula da Hakan kana zan yarda na Bashi Autana..”Ya karishe Fada yana Shafa Kumatunta da Sauri ta Washe baki Lokaci Daya Tana Fadin”Shiyasa nafi sonka..Akan Umma Daddy..Kafi sona..Ita kuwa ssi ta cemin wai ni Shagwabbiyace..”
Daddy yace”Rabu da ita…Duk yan Bakin ciki ne..”Ya Bashir na Dariya yace’Hardani Intin Umma..? Tana wani mele baki Tace”Ni ba Intin Umma bace..Intin Daddynta ne..”Umma na jinta Tayi tsaki Tana Fadin’Nabarmai yayi ta kaya..Ni ai Bashir ne D’ana..Ni Daman ba Mamanki bace Daga Gidan Marayu Alhaji ya Dauko ki..”Baki ta Bare zata kara sakin kuka Daddy ya Riketa yana Fadin”Au kukan zaki mata..? Daman ta Fadane don ta saki kuka..Haushin kinfi sona ne Autana Rabu dasu..”
Washe baki Tayi tana Fadin”Yauwa Daddyna..Ammh zaka Kira Inna Amina kamata mgana ko..? Kaji fa umma nacewa Zata saka D’anta wai ya Rika Dukana..”Tafada Idanuwanta na Cika da kwallah Domin inti akwai Tsoron Duka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button