GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Kalma Daya akan Safiya..?kalma Daya akan Oga Ranka ya Dade Imu🤣Kalma Daya ga Inteesar Inteen Daddy da Ya Basheer Maryama Takwaran Daadan Alkali Dukku..!

Shakira….
3/22/22, 23:04 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)

        🅿�16

Bayan Sati Daya

Bayan kwana Bakwai da Auran Yusuf Da Safiya Abubuwa sun Fara Daidaita Gidansu Yusuf yanzu ya Fara Dawowa Daidai Tare da Mutanen Cikinta,kuma Duk a Dalilin Safiya Tuni ta Saka Yusuf ya kira mai gyara ya Saita Tv,Sai dai kaga Abba Zaune afalo yana Karatun Jarida Sanye da Gilashin sa mai karamai karfin gani ko kuma yana Karatun Littafin addini Safiya Dake kai kai da kawo Tsakanin Falon da Kitchen suna Taba Hira Sama Sama.
Ya kasance Duk Safiya Tare suke Breakfast,kuma Duk Dare suna Dinner Tare sai dai Imran ne bai Cika Zama Cikinsu ba,Ba wanda kuma ya Damu Sanin Halinsa Tun suna Lagos Shi yafi jin Dadin gudanar da komai na Rayuwarshi shi kadai batare da kowa ba.Mutane suna da matukar Muhimmanci a Wajensa,Bai yason Ka takuramai Shima yana Girmama Rashin Takura ga wasu koda su din Ahalinsa ne sai dai Kowa ya gansa yasan yana Cikin Farinciki Gidansu ya Dawo Gida irin na Kowa Bayan sunyi bankwana da Farinciki Da Dadewa.
Asatin Har Masallacin jumma”a Abba yaje Tare da Yusuf da Imran Cikin Farinciki kuma da Likita yazo Dubasa Yaji matukar Dadin ganinsa yace in Har Abba zai Cigaba da Tafiya haka Hakika Mgani bazai kara mai amfani ba Zai iya Dawowa Daidai  insha Allahu,Farincikin Haka yasa Yusuf yayi Shawara da Abba da Imran kan yana so ya gyara Shashen Dake Koridon Dakin Munari Safiya ta Tare acikinsa tunda wanda suke Zaune yanzu Ciki Dayane,sai kuma yana son Siyamata kayan sawa,Abba yaji Dadin Haka Saboda Safiya ta Chanchanci komai na Rayuwa Shi ya bashi Umarnin Ya taba Kudin Dake bankin Nura marigayi,Tunda akwai kudi Har yanzu yayi amfani Dashi Imran ma ya yarda da Shawaran.
Ranar Sati da auransu da Daddare suka Tafi Gidansu Safiya Shi da ita sai Tace Tare da Munari Zasu je Wanda Cikin Satin Daya sunyi matukar Shakuwa kamar yaya da kanwa In Munari bata je makaranta ba Suna Tare da Safiya aiki Tare suke yi Girki ma Haka wajenta tana ta kara koyin Abubuwa sosai Tunda ita Munari Da Karfi Da yaji ne ta iya girki,Lokacin Tana Karama Ba komai ta iya ba Sai dai ya Zaman mata Dole ne Tunda itace Macen Cikin yayyin nata da Taimakon Waya Online Clasess,Sai kuma Goggle yasa take kwaba Wasu abubuwan ammh Zuwan Safiya ya Kore mata komai,yasa ta gane ashe abaya Duk Shirme take yi.
Koda suka je Alhaji Alhassan Baya nan Ya Tafi Fagge,Mommy Tayi Farincikin Ganin yarta Cikin Kwanciyar Hankali Tayi Fresh na Amarci,Tasleem Ta Rumgumeta Tana ta Murna ganinta,Mommy bata Taba ganin Yusuf ba sai Ranar ta yaba Sosai da Zabin Diyar tata Domin a Fuska yana da Kamala da Cikar Zati Tayi musu Nasiha Sosai,Tasleem Taja Munari Dakinta suna Hira Mommy Taja Yarta Ciki Suka bar Yusuf da Labarai da ake Nunawa a Nta,gabansa Cike da kayan makulashe da yar aikin Mommy ta Cika Gabansa Dashi Ruwa Kadai ya iya sha.
Mommy take Fadama Safiya abunda yakai Abbun su Fagge kararsa ta kai Wajen Goggo,Bayan taje Gidansu ta Fadama Iyayenta Halin da ake Ciki Mahaifanta basu saka baki ba Sai dai sun Tausheta Datayi Hakuri Tunda aikin Gama ya Riya gamu,Yayartace ma Da ta ke binta Anty Saratu Dataji Ta Dinga Fada Dayake Tana da Fada sai Iyayensu suka Taka mata Burki Itace ta bata Shawaran su je Chan Fagge sun Fadama Goggo ko Yaya ne ai Mahaifiyarsace Zataji Rashin Jin Dadin Rashin Darajata da Yan’uwansa da Alhassan bai yi ba Shine sukaje ita da Anty Saratu suka Fadama Goggon komai sai da Tayi kuka Dataji Abunda ya aikata Shine ta Kirasa yaje yau Tun Dazu Kila Chan zai kwana Tunda Har Dare yayi bai Dawo ba,Daman Tun Bayan Faruwar abun Mommy ta Daukemai basu Dawo Daidai ba.
Safiya bataji Dadin Rashin Jituwan Dake Tsakanin iyayenta ba Har yanzu yasa ta Sanyaya rai ta Dafa Kafadan Hajiya Mero Tana Fadin”Mommy Sam bana jin Dadin Rashin Jituwan Dake Tsakaninki da Abbu..Don Allah ki manta Komai indai Saboda ni ne Wlh Tallahi bana Cikin ko Wata Mtsala Mijina yana sona Abba kamar Diyarsa Munari ya Daukeni Bana Cikin Wata Damuwa baki ga alama ba..!
Hajiya Mero ta kalleta ta Kada kai Tana Fadin”Ammh ai Da Farko shi da Kansa yace yayi Bincike basu da Kowa anan..Basa da wasu Dangi Anya Safiya Kina ganin hakan ba wata Mtsala bace…?kuma fa yacemin Mahaifin su Mahaukaci ne akacemai..,?

Safiya ta Murmusa Tana Fadin”Mommy wa kika Taba ganin ya Fado Daga sama bashi Da Dangi? Suna da Ahali da Dangi irin na Kowa Mommy kawai yanayi ne yasa kika gansu kuma Mganar Abba..,karya ne Mahaukaci bane Wlh Sharri ne..!Nan da nan ta Fara bama Mommy Labarin da Yusuf ya bata ba Domin komai ba sai Domin Hankalin Mommy ya kwanta,Agurguje ta gayamata komai ta Karishe da Fadin”Mommy Kinsan Rashin Uwa a gida Babban Gibi ne..Su kuma Rashin Uwa sukayi da yan”uwa Har Uku yaya zasu Fuskanci Wannan Rashin..? Abba kuma Yayi Rashin Mata ce Uwar yayansa..Kuma yayi Rashin Ya”yansa Har guda uku alokaci Daya..Yaya kike ganin Haka Amtsayin in ya Faru Dake Mommy..? Sannan kuma yan”uwansa suka ki Fahimtarsa Ballataa su Taimakesa kan Halin Dayake Ciki..!
Mommy ta Share kwallah Saboda Tsausayi tace”Allah Sarki ashe Hadarin Jirgin Daya kashe Mutane dayawa din na harda Mahaifiyarsu da yan”uwansu aciki..?Abun Tsausayi Allah ya jikanasu da Rahma..Wlh naga Kokarin yaran..Allah yayi miki albarka Safiya Yanzu Hankalina ya kwanta na Tabbata Mahaifinki bai kai Hannun banza kina Hannu nagari..!
Ina alfahari Dake Ki Cigaba da Abubuwan Dakike,Insha Allah ke ce Haske acikin Gidansu da yardan Allah..!
Rumgume Mommy tayi Tana Share mata Hawaye,Sun Dade aciki suna Tattaunawa sai da Yusuf ya kirata yace su Fito su tafi sun bar Abba Shi Kadai,nan ne ma Mommy ke mata Mganar Kayan Daki Take gayamta Yusuf yace shi Zai siya komai kawai abunda take Bukata Turaran TuraraGida sai na kaya,Sai abubuwan da ba”a rasa Mommy tace Insha Allahu zata kira Anty Saratu Zasu Shiga Kasuwa Zasu siyomata komai Sai Tajita,kafin suyi sallama sai ta bata leda guda Cike da kayan gyaran Jiki,Tace abunda bata gane ba ta Kirata Taji Takaichi yarda takai yarta Baatare da wani gyara ba Ammh ko Yanzu Lokaci bai kure mata ba Saratu Zata Hada mata komai Tunda itama Tana Taba Sana”ar kayan gyaran Mata..
Koda suka Fito Tasleem da Munari sun Gama Hadamata Duka kayanta Kadan suka bari akwati Uku suka Cikata Harda su Takalma da Takardunta na makaranta sai Littafan addu”o’inta,da Sauran littafanta na Karatu Novels na Turanci dana Hausa,Sakawa su kawai akayi a Mota Mommy da zasu Tafi Tayi ma Yusuf Gaisuwan Rashin da sukayi bai yi mamaki ba Sanin Safiya kila ta gayamata yaji Dadi sosai ya amsa yana Godiya Munari da Tasleen suka yi Sharing din Cantact din juna,Tace Sai tazo,Safiya tace ta na nan tana Jiranta suka Tafi suna Daga musu Hannu,Bayan Safiya ta bar Sallahun Agaidata mata Alhaji Alhassan in ya Dawo Mommy aranta taji bazata Fadamai ba Kuma Zata kwabi Tasleem So take sai ya Girbi Abunda ya aikata da kansa Tukunnah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button