GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


Su Baba Manu suna Tafe a Mota Safiya na gidan Baya ta saka kanta tsakanin Cinyoyinta,tana ta kuka Baba Manu na gaba Alh.Sadi na Tuki ammh an rasa mai cewa komai gabadaya lamarin ya Daure musu kai uwa uba ga Tsausayin wannan Baiwar Allah Safiya,Shiyasa suka rasa bakin Zaren kamawa.
Alh.Sadi ne ya juyo yana kallon Baba Manu kafin yace”Ina muka nufa yanzu Manu..?
Baba Manu ya sauke Numfashi yana Fadin”Mu tafi Gadon kaya..!
Alh.Sadi yace’Inda Matar marigayi Take zaune kenan..?.Baba manu ya Daga mai kai,nan da nan Alh.Sadi ya Take Mota Cikin Lokaci sai gasu a Kofar gidan su Sagir.
Firfitowa sukayi Baba Manu ya umarci Safiya Data fito ta FitoJikinta a sanyaye gabadaya Idanuwanta sun koma Jawur sun Kumbura saboda kuka,Ganin tana layi kamar zata Fadi ne yasa Baba Manu ya karban mata Trolley din,lokaci Daya yana leka Shagon Sagir sai yaga Baya Ciki sai yaransa,Nufar gidan su Sagir din yayi Bayan yace ma Safiya ta Biyoshi Shi kuma Alh.Sadi ya jirasa a waje yanzu zai fito.
Safiya dakyar take Daga kafarta hannunta Damke da Sadakinta da wayarta kamar ace kyat ta Zura da gudu sai bin ko”ina da kallo Takeyi Tana Tunanin bata taba Shigowa area din ba.
Mama Tana zaune a kofar Falonta Tana gyaran wake Bata so Sagir da Inteesar su Dawo daga makaranta bata gama abinci ba
Sama sama taji sallaman Baba manu ta Dago tana amsawa cikin Mamaki ganinsa jaye da akwati bata samu Damar mgana ba sai ga Safiya ta Shigo itama Da Hanzari Mama ta mike kafin ta samu Zarafin mgana Baba Manu yace”Amina miko Tabarma ina tare da bakuwa ne..!
Batayi gaddama ba ta shiga Ciki ta Dauko Tabarma Lokaci Daya tana Sanya mayafi ta Fito ta Shimfida musu Baba Manu ya zauna Lokaci Daya yana kallon Safiya yace”Zauna..yata..!
Jikinta a sanyaye ta Zauna agefe Kanta na kasa tana gaida Mama Ta amsa Cikin mamaki.
Kafin ta Dawo da kallonta kan Baba Manu tana Fadin”Baban Sagir lafiya kuwa..? Wannan kuma wacece..?
Baba manu yace”Sagir bai Dawo Daga makaranta bane..?
Mama tace”Bai dawo ba gaskiya..Domin daya dawo ko zai Tsaya Shago sai ya shigo..!
Baba manu yace”Bashi ma a shago Domin na leka ban gansa ba..!
Mama tace”Allah yasa dai lafiya..?
Kai ya girgiza kafin yace”Lafiya ba lafiya..Yanzu dai shi ga Yarinyar nan Ciki Amina kizo muyi mgana kana..!
Mama batayi gaddama ba ta Mike ita ta Dauki Akwatin Safiya Ita kuma Baba Manu ya Umarceta data bi bayan Mama zuwa Ciki.
Batayi musu ba tatashi ta Bita Sanan Daya Daga Cikin kujerun Falon ta zauna Mama ta kawo mata Ruwa ta ijiye tayi Godiya aranta Tana Tunanin kodai nan ne gidansu Yusuf din..? Ammh ai ya Taba gayamata Mahaifiyarsu ta rasu Dagashi sai kanninsa da Kanwarsa da Mahaifinsu suke zaune agidan..? To in ba nan bane gidan su waye nan..?
Mama duk ta kosa taji Abunda ke Faruwa Tana Fitowa ta Zauna Kafin ma Tayi mgana ya Rigata da Fadin”Wannan yarinyar dai da kike gani Yau mukaje Tambayan auranta Shine Ubanta ya Dauro auran kuma ya Hadomu da ita..!
Cikin mamaki Mama tace”Topha..kamar ana yaki..?to matar waye..?
Baba manu yace”Ina abokin Yaron nan Sagir..? Wayake da suna na manta..!
Mama ta Zaro ido Tana Dafe Kirji Lokaci Daya tace”Aure Imran yayi..?
Baba manu yace”Ba Imran din ba Yayansa..Na manta sunansa ko Wayake da suna ma..!
Mama da al”ajabi yagama kamata tace”Yusuf sunansa..?nifa na shiga rudu garin ya haka ya Faru..?
Baba manu ya gyara zama ya Shiga Rattabama Mama yadda komai ya wakana Tun daga farkon zuwansu Gidansa Sagir da Imran har yau da abunda ya Faru gidan Alhaji Alhassan.
Mama ta saka Salati da Salallami ta Dire Tana Fadin'”Wlh baban Sagir bansan komai game da wannan mganar ba..Yaron nan Sagir bai gayamin komai Yau Tun Safe ya tafi makaranta salaha da sukazo da megidanta kawo autan ta karatu suka Daukesa shi da Inteesar din zuwa Cikin makarantan har yanzu bai Dawo ba!
Baba manu yace”Wajen ki Zata zauna tayi karatun kenan..?.
Mama tace”Eh Wlh..!
Baba manu yace”Allah ya bada sa”a..Kin dai abunda ya faru yanzu ya zamu yi ne..?Me kika sani game da Gidansu yaron nan Amina..?
Mama ta gyara Zama Tana Fadin”Wlh bana ce maka nasan komai ba..Ni dai na san Imran din abokin Sagir ne Allah ya Hada Jininsu..Sai kuma nasan basu da kowa Daga Mahaifinsu sai shi Imran sai kanwarsu sai Mahaifinsu Dake kwance ba lafiya Domin na Taba shiga Gidan Sau Biyu na gaidashi..!
Baba manu yace”Ina mahaifiyarsu..?ina yan”uwansu da Sauran Danginsu..? Kuma laluran meye Mahaifin nasu ke Fama dashi..?
Mama tace”Wlh nidai bansani ba..Sagir dai ya gayamin yace Daya Takurama Imran din ne da Tambaya ya gayamai mahaifiyarsu ta rasu mganar Danginsu kuma Wlh shi kanshi Sagir din bai sani ba Imran din baitaba yarda ya gayamai komai ba Laluran Mahaifinsu kuma Ni bansani ba ammh Tabbas Bashi da lafiya yana Cikin Daki kwance ko Falo baya Fitowa..!
Baba manu yayi Shuru bai yi mgana ba illah Ajiyar rai Daya Sauke Lokaci Daya ya Zaro Wayarsa yana Fadin”Bari na Kira Sagir din yazo ya kira shi abokin nashi..!
Mama ta kada kai Alamun hakane din ne.
Baba manu ya kira Sagir,Shi kuma Lokacin yana cikin Makaranta ammh sun Dade da Fitowa daga Lacture,Inteesar yake jira saboda kada ya tafi ya barta bazata iya Dawo wa gida ba.
Yana Dagawa Baba Manu ya Tambayeshi ko yana ina..? Yace yana cikin makaranta nan da nan Baba Manu yace in babu Abunda yake yi ya zo gidansu gsshi yana Jiranshi
Hankalin Sagir ya tashi Dagajin muryan Baba Manu ba waasa acikinta,Gashi kuma Inteesar sun Fito Daga Lacture sun shiga wata kuma yana ma Department dinsu yana jiran Fitowar ta.
Ya rasa ya zai yi sai Allah ya Taimakeshi sai gasu sun Fito yamike ya isa bakin Hall din nasu sai gashi Inteesar din ta Fito Dauke da Jakarta da Wayarta sai Takardun Dake hannunta.
Tana ganinsa ta kariso gabansa Tana Fadin”La ya Sagir..?
Badai kana nan Tun dazu kana jirana bane..?
Sagir yayi Mirmishi yana Fadin”Eh mana..Kada ki Fito baki ganni ba ki fara kuka..!
Abun sai ya bata Dariya Sai data Dara kafin tace”Sai kace wata yarinya ya sagir..!
Yace”Eh mana ai yarinyar ce kada ki kira Babanki kice na barki ke kadai baki gane Hanyar gida ba.!
Inteesar tace”Laa..Zan iya fa komawa Gida dakaina Allah..Kuma ai in ina gaban Daddyna ne nake Shgwabata in ya barni ni kadai Am Mature ya Sagir..!
Mamakin Surutun yaji kafin yace”Wato Shagwabar ma Kinsan inda kike yinta ko..?
Dariya kawai tayi Tana Sunne kai Agogon hannunsa ya kallah Daya na Rana ta kusa ya kalleta yana Fadin”Daman gida nake son Tafiya an kiranibshine nake Tunanin bazaki iya gane gida ba in an tashi Ki kirani sai nazo Mu Dawo Tare..Tunda ni na gama da makaranta sai kuma Jibi in Allah ya kaimu..!
Da sauri tace”A’a kada na Wahalar dakai zan gane ba Gadon kaya ba..?in na samu mai adaidaita yana kawoni anguwan zan gane layin ina da Saurin Dauke abu akaina..!
Cikin son Tabbatarwa yace”Kin Tabbata zaki gane..?
Inteesar tace”Insha Allahu..!kai ya kada duk da haka bai yarda ba sai ya Fiddo wayarsa ya kirata sai ga wayarta na kuka acikin Jaka ganin tana kiciniyar Fitowa da wayar ne yasa yace mata”Nine na kiraki ga lambata nan ki kirani in baki gane ba..!
Kai ta gyada mai Tana Fadin”Thanks..!
Jinjina mata kai yayi kafin yace”In zaki yi sallah ki bi ayarin mata yan”uwanki zuwa masallacin Cikin makaranta in wani abu zaki siya ga Cafteria chan..Sai mgana karatu tunda an wuceki da yawa in kika Dawo sai mu Tattauna Dole sai mun samu Wani ko Wata Cikin Course mate dinki da zai mataimaka miki..!
Cikin jin Dadi ta amsa mai da haka sukayi sallama ya kama Hanya.
Minti Talatin ya bata saboda ya samu go.slow kafin ya kariso Gidan yana Shigowa ya iske Baba Manu har lokacin suna Tattaunawa da Mama Tuni ya Fita ya Sallami Alh.Sadi da Niyyar sau sun yi mgana ta waya ko sun hadu.
Yana Shigowa ya Durkusa yana gaida Baba Manu Mama ta kallesa Tana Fadin”Ina ka baromin yata..?
Sagir yace”Tana chan basu gama Lecture ba..Ammh ban barta ba sai da ta tabbartamin da zata iya Dawowa da kanta..Na dai bata lambata nace in bata gane ba ta kirani.!
Mama ta kada kai kafin tace”Allah ya dawo da ita lafiya..!
Ya amsa mata da Ameen kafin ya maida Hankalinsa kan Baba Manu Daya gyara zama yana Fadin”Ina abokin ka..?
Sagir yace”imran baba..? Ban sani ba ammh ina kyautata Zaton yana gida Duk jiya bamu hadu dashi ba..!
Baba manu yace”Kirasa a waya..Kace masa yazo nan gidan gani Ina tafe da Matar dan”uwansa..!
Sagir ya zaro ido yana Fadin”Mata kuma Baba..?
Mama ta karbe tana Fadin”Eh suna zuwa uban ya Daura auran.Kuma ya hado su da yarinyar tana nan cikin Dakina zaune..!
Sagir yayi Sakace yana bin Mama da Baba Manu da Kallo Cikin mamaki kafin ya Zaro wayarsa a Fili ya Furta”Dankari…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button