GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Da kallo ta Bisa Har ya shige cikin Gida Mirmishi ya kamata Miyau ta Zubar Daya cika bakinta afili ta Furta..’He is nice..ashe ya Lura ta kusa amai..!
Bata san da zuwan Munari ba sai taji kawai ta Dafa ta har ta Tsorata sai da ta Waiga ta ganta ta Sauke Numfashi Tana Fadin”Har kin bani Tsoro..!
Munari tace”Hala Ya Imran kika gani..? Yanzu na gansa ya shiga gida yana Cika yana batsewa..!
Inteesar tace”Kamar wani kabewa..!
Dariya suka saka Harda tafawa kafin su kama tafiya suka Fice wa Daga gidan.
Suna tafe suna Hira har gidan Mama akofar gidan sukayi sallama da Munari akan Gobe zata zo kafin Intee din ta wuce,Sai dai Inteesar ta Boyema Munari abunda ya Faru tsakaninta da Imran haka kurum taji bazata iya fadamata ba
Haka Inteesar ta shiga cikin Gida Tana nuna ma Mama Abunda Anty Safiya ta bada akai ma Umma ta Karba tagani Tana ta Godiya.
Ranar barci barawo ne ya sace Intee Saboda Murna asuban Fari tatashi Tayi ma Mama sharan Daki ta Share Tsakar gida,Ta zo ta saka Kettle daya Tafasa ta Juye tayi wanka Kafin ta Fito Mama ta Hada mata abun kari Saboda Murna ko Yunwa ma bataji sai da Mama ta Mtsamata ne tasha Tea kadan da Buredi.
Koda karfe 11am na safe Basheer na Falon Mama shi da su Abiden yazo,Shi daman dan akida ne baya son Tafiyar Dare kuma bayason bata Lokaci shiyasa suna gaisawa da Mama yace Intee ta Fito su Dauki Hanya
Sagir ne ya Fitar mata da kayanta akwati Daya zata koma dashi,sai Sakon Mama na Umma da nasu Inno,sai na Anty safiya,bawasu kaya me da yawa ba.
Tun tana cikin gida ta Kira Munari ta Fadamata ya basheer yazo zasu tafi Munari tace gatanan zuwa sai dai Shuru Har Ya Basheer din da Sagir suka Fita waje aka gama Saka kaya a Booth Munari bata zo ba,Ita kuma Har ta kawo Falo Taga Imran ya Fita Haraban gida sai ta Labe ta Leka taga ko ya Fita sai taga yana Jingine jikin Mashinsa yana Danna Wayarsa karama bashi ma da Niyar tashi,Ballatana ta samu ta Fita kuma ta Tabbata in ya ganta bazai barta ta Fita ba.,Sai ta tsaya nan falon tana Lekonsa Gashi ta bar Wayarta acikin Bedroom dinta Inteesar nata Kira Bata Dauka ba.
Ga ya basheer nata mata Fadan su tafi bayason Tafiyar dare ga yara yazo dasu,Dole tana ji Tana gani ta Fada Gidan Gaba Tana Tura baki Domin tasan ko giyan wake tasha bata isa tace su jira zuwan Munari ba ko kuma su Biya gidansu ba Dama Daddy ne yauwa tasan shi zai mtsamai ammh yau ba Daddy bata isa ba.
Saboda Haushi ma Abiden na Hawa Jikinta ta Harareshi ta Mtsa jikin Kofa Tana Tura baki Basheer bai Damu ba Kallonta kawai yayi ya kada kai,Abida Tana Jikinsa Ta lafe ita akwai son jiki ne Abiden din ne Sarkin wasa.
Haka suka tafi Sagir na Daga musu Hannu da Mama na Daga Zaure Itama Tana Daga musu hannu Allah Sarki Sabo Turken wawa.
Munari dai Dole Daki ta koma tana Cijon yatsa,Wayarta ta Daga taga Kiran Inteesar sai tabi baya,Inteesar na ganin kiran Munari taki Dauka sai da ya Katse ta Turamata Sako.

Muna hanya..Nayi ta Jiranki baki zo ba..

Munari na ganin Sakon sai da taji wani iri da sauri ta Rubuta mata da Amsa.
Am sorry Besty..Naso na Fito Ya Imran na gani aharaba shiyasa..Allah ya kiyaye Hanya ki gaida Daddy da Umma..!

Ta turama Inteesar wanda Tana gani sai da ta Murmusa da ta Tuna da Imran cikin Dariya ta Turama Munari..

Is ok..Ameen zasu ji..Ki kula da kanki da kowa da kowa Expecially Muradaden yayanki IMRAN..!
Tana gama Tura mata ta maida wayarta jaka tana Mirmishi Basheer na kallonta bai ce mata komai ba sanin ko yayi mgana bazata Tankasa ba Yau yasan Karansa Wajen Daddy Fada sai ya Toshe kunne.
Munari kuwa Tana ganin sakon ta Zaro ido a fili ta Furta.”ni ai bazan iya Kula da Ya Imran ba Tabdijam..!


Koda Inteesar ta Dawo Daddy baya gida,Umma ce Kadai sai Anty Hauwa Inteesar ta makale Umma Tana Murnan ganinta,Haka ta Rumgume Anty Hauwa Tana Murna ya basheer ta bari da Shigo mata da kayanta Murna ya mantar da ita,Shiyasa akace No place Like Home Inteesar ta Fahinci hakan
Umma ta yi mata Shinkafa da Miyar Kaza,sai kunun Aya,Inteesar ta Zauna taci ta koshi sosai,Daddy bai Dawo gidan ba sai Dare Intee ta Rumgumesa Tana Murna ganinsa shi kansa Bakinsa yaki rufuwa Saboda Dawowar yar Lelen nashi.
Ranar kusan raba Dare sukayi suna Hira,Daddy yasha Hirar Makaranta da ta Mama data Ya Sagir sai Hirar Munari da yan gidansu da sakon Gaisuwan Abba zuwa garesa.
Ta kuma bama Umma sakon Anty Safiya Umma ta Karba tana ta Godiya da Sakon Mama na Garin Dan wake,da Yaji sai Daddawa Dakakkiya da kuka da Kubewa,Haka ma Wanda ta aiko ma su Inno harda Garin Kunu Umma sai Murna take..
Inteesar sai da ta Duba ledan Kayan da Munari ta bata taci karo da sigarin data Karba Hannun Imran da Lether dinsa Saurin Dauka Tayi ta Jefa Cikin Tiolet tayi flooshing kada wani ya gani ta Shiga uku.
Inteesar Tana matukar jin dadin Hutunta agida,kwananta Hudu da Dawowa taje gidan su Nasara Ta wuni Daga gidan ta Biya badarawa ta gaida Inno da Mallam Babba sai Dare Muda ya Rakota ta Dawo gida aranar ne da Daddare Munari ta kira Suka gaisa da Umma Harda Anty Safiya bayan sun gama mgana ne Inteesar ta Nuna ma Umma Hotonsu ita da Munari da suke Dauka a makaranta Umma ta kurama Munari ido a Fili tace Kuna kama da kawarki taki Inteesar.
Inteesar tace mata haka kowa ke Fadi Umma kinsan ance kawayen juna wani Lokacin kamarsu na Rikidewa Umma na Dariya batace komai ba Suna Cikin hakane sai ga Daddy ya Shigo Daya Tambayi me suke ma Dariya Umma ta Fadamai bai ga Hoton ba Umma tace ya bari ya Huta Daganan ya manta itama Inteeesar din sai ta sha”afa.
Har gidan Ya Basheer taje ta kwana Biyu Dakyar kamar tana kan kaya ta Mtsa sai da ta koma Gida,Suna Waya da Mama Da Sagir Lokaci bayan Lokaci suna gayamata sunyi kewarta..
Munari kuma kusan kullum sai sunyi mgana da juna ta waya ko ta WathApps.
Kwanan Inteesar goma da dawowa Daga kano ta fara Zazzabi mai Zafi Wanda sai da ya kwantar da ita a asibiti.
Maleria ce ta mata mugun kamu,Sauron kano sun Debi Rabonsu Daddy nata Fadan meyasa ba”a saka mgani agidan Mama tunda akwai sauro Inteesar ta dawo da Maleria.
A dakin da aka kwantar da Inteesar din ne a kebantattacen Daki na Musamman,Asibitin kudi ne,Ya Basheer da Umma da Anty Hauwa da ya”yansu su Abiden din adakin Daddy ke ta Fada Tunda Likita yace Maleria ce ta kama Inteesar mai Zafi.
Ran Umma ya baci ta Dubu Daddy Tana Fadin”Haba Abban Intee kadaina Fadin haka fa kamar baka yarda da kaddara ba? Kuma daka ke Fadin an barta Sauro ya Cijeta Ita Ya Aminan zata zauna tana kula ita kada Sauro ya Cijeta ko..? Kuma ita da Sagir Da suke gidan Su ba Mutane bane Inteesar ce kadai Mutum Tunda yar so ce..!
Tafada Tana Bayyana Bacin Ranta Har Daddy zai yi mgana Basheer ya Girgiza mai kai ganin kada su Fara Fadansu na Fama gaban Suruka.Dole tasa Daddy ya bar mganar Ammh Umma sai Huci take ranta yagama baci.
Wasa wasa dai sai da inteesar ta Kusa Share Sati a asibiti,Saboda da taji Sauki Likita yace zai Sallameta Daddy ya Hana yace sai ta kara Hutawa kwana Shida tayi ta koma Gida Munari ta sani Tunda Data Kira Wayar Inteesar din Umma ta Dauka Ta gayamata Tana asibiti bata da Lafiya Hankalin Munari ya tashi Ta kuma tashi Hankalin su Abba bata Kwantar da Hankalinta ba sai da Taji Inteesar Ta samu Sauki har an sallamo su Daga asibiti ta Dawo gida..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button