GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina godiya masoyana na WhaApps da yan Wattpadian ina ganin Sharhinku Allah ya saka da alheri sai dai ina so nadan yi wani Tsokaci ne kan mganganun wasu masu Sharhi kan Suna Tantama Anya Imu kansa Daya..?wai ko yana da Aljanune..?ko kuma yana da mental problem..?Amsa itace Imran Lafiyayyan Mutum ne kamar kowa,Bai da wata Cuta ko Nakasu in kun Duba Labarin Tun abaya ba inda na saka yana da wani mtaala sai Mtsalansa D’aya na Rashin Controling kansa in Ransa ya baci,Kuma akwai mutane irin haka yana da zuciyar Fulani ne ajikinsa,in kun lura Saboda Sanin Halinsa yasa bai shiga Harkan kowa kuma baisan batama mutane rai koda ahalinsa ne,in kun karanta ko da yan gidansu bai Doguwar mu”amala saboda gujema bacin Ransa,Baya kaunar a batamai rai shiyasa yake gujema bacin ran Wadanda ke Zagayo dashi a labarina ban nuna inda Imran yayi wani abu haka kurum batare da an shiga Harkansa ba,Yana da zuciya mai kyau kuma ka in kiyayemai zaka ji Dadin Zama Dashi mganar ko Imran baida Lafiya to Lafiyarsa Kalau Tsarin Hallitarsa ne haka Team Imran da Team Inteesar duka sun ce suna Godiya Son so Fisabilillah

Shakira..
3/22/22, 23:06 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

        *🅿�22*

Tun bayan fitan ta bai motsa Daga inda yake ba Mganganunta sun kashe mai Jiki duk ba wannan ne Karo na Farko da aka sha gayamai shan Taba bai dace dashi ba kuma ba yau ya Fara sanin Smooking yana da Matukar illah ga Lafiya ba sai dai karon Farko ne ya Farajin Tasirin mganar acikin kansa da kwalkwalwarsa.
Kofar data Ficen ya kurama Ido Lokaci Daya Zuciyarsa na Bugawa da karfi da karfi a duk Lokacin Daya ganta ko yaji mganarta wani abun mamaki mganarta Tana da matukar Tasiri acikin Zuciyarsa.
Cikin kasala da Sanyin jikin da Kalaman Inteesar suka Sanyasa ya Tura Kofar Dakin nasa ya Shiga Kafin Fitar sa Yayi Niyyar Daya dawo zai Dora Daga inda ya tsaya na Busan Hayakinsa Tunda Kishirruwa ne ya Fitar dashi sai dai kuma Ya kasa Daukan karan Sigarin ballatana ya kunnata Haka kurum yake jin amsa Kuwwar mganar Inteesar tarika Tasiri acikin Jikinsa da Zuciyarsa yasa yana ji yana gani bai kunna karan Sigarin ba sai ma Tattarasu da yayi ya Tura Cikin Side Drower din gadonsa ya koma ya kwanta Ringigine yama Rasa wani Tunani zai yi ko zai kama.

Inteesar kuwa Tana Fita taci karo da Daddy da Ya Basheer da Sagir ya Rakosu a Mota sun gaji da Jiranta Tana Fitowa suna isowa kofar gidan Fitowa Daddy yayi yana Fadin”Bata nan ne..?
Kai Inteesar ta Daga kafin tace”Eh Daddy sun fita..!
Daddy ya Bi gidan da kallo Haka kurum yake jin wani irin yanayi Tare Dashi Kafin yace”Harda shima Yayan nata Dake kaiku makaranta..?
Inteesar tace”Harda Abba da Anty Safiya suka fita..Ya Imran kadai na Tarar a gidan..!
Daddy zai yi mgana Ya Basheer Dake Bangaran Direba ya Leko yana Fadin”Plz Daddy..Lokaci fa yatafi..!
Daddy yayi ajiyar Zuciya kafin ya Kalli Inteesar yana Fadin”Shikenan ki gaishesu in sun dawo..Shiga Mota sai mu sauke ku mu wuce..!
Yafada yana kara Bin gidan da kallo kamar kada ya tafi Zuciyarsa Tana jansa Tana jin kamar akwai wani abu mai Muhimmanci da in ya Tafi Daga Wajen zai rasa,Sai dai bai da wata Masaniya kan haka,Komawa Gidan gaba yayi ya Zauna yayinda Inteesar ta shiga Gidan baya inda Sagir yake.
Ba wanda ya kara mgana har suka kariso kofar Gidansu Sagir aka sauke su Inteesar sai da Idanuwanta suka cika da kwallah Lokacin Datake Dagama su Daddy Hannu har sai da Motarsu ta Kule ta Daina ganinta kana ta Juya Zata koma Cikin gida.
Sagir ya Kirata ta Juyo Tana kallonsa Kai Tsaye yace”Kinga Imu..?
Kai ta gyadamai batare da tayi mgana ba ganin yanayinta yasa bai kara magana ba Har ta Juya ta Shige gida.
Koda ta Shiga Mama ta Zagaya Makewayi Daki ta shige ta Fada Kan gado Cike da kewar gida Tana nan kwance Mama ta Shigo Tana Tambayanta lafiya ta ganta Kwance tace Lafiyalau nan take Fadama Maman bataji Dadi ba Daddy basu hadu da Munari sun gaisa ba Har gidan Taje basa nan..
Mama tace kada ta Damu akwai wani Lokacin zasu hadu su gaisa Tunda ana tare da juna.
Sai bayan Mangriba Munari ta Kira Inteesar tana bata Hakuri Dawowarsu kenan Salla kadai tayi ta Duba wayarta Sai taga Kiranta nan Inteesar ke gayamata Har gidan tazo bata Isketa ba Daddy ne yazo zai Wuce yace a Kirata su gaisa Munari ta Ciji yatsa tace ta zata bazasu Dade bane,Sai gasu sune Har gidan Zoo Shiyasa suka Dade basu Dawo ba Inteesar tace bakomai akwai gaba Kamar yadda Mama tace Daganan sukayi Sallama Akan sai Gobe In Munarin ta Biyo mata Tafiya makaranta.
Washegari Monday da Safe 8am suke da Lecture 7:30am suka shirya Ya Yusuf ya ijiyesu Kafin ya wuce Wajen aiki Har shi sai da Inteesar ta Fadamai Zuwan Daddy su gaisa jiya basa nan Shima bai ji Dadi ba yace sai dai Wani Lokacin da yardan Allah zasu Hadu su gaisa.
Ranar da Wuri suka Fito Daga Cikin makarantar,Shiyasa Inteesar taja Munari zuwa Gida ta Diban mata Dambun nama da kayan Snaks din tace ita dasu Abba Munari nata Godiya sai da Tayi Sallar La”asar suka ci abinci kana Inteesar ta Fito Zata Rakata Zuwa Gida sukayi Kicibis da Imran da Sagir akofar gidansu Imran din suna mgana,Da suka gansu Munari tafi Tsorata Domin jikinta sai Rawa yake yi Inteesar kuma mamaki take na yau Kadai da Tataba ganinsa baya Shan Sigari.
Yana Sanye Cikin Riga da wando,Rigar mai ruwan kasa Mai gajeren hannu sai Wandon baki ne Wanda yadan Kamasa ta kasa Kafarsa Sanye Cikin Wani Tattausan Takalmi,Kamar Koda Yaushe Hannayensa Zube cikin Aljihunsa.
Sagir kuma yana Gefensa Har Kafadunsu na Dukan na Juna duk da Imran din ya Fisa Girman jiki da Tsawo.
Tundaga Nesa ya hangesu sai da gabansa ya Fadi Daya ganta yarinyar nan Kamar Aljanna Jiya wuni yayi Tunaninta Haka kurum baisan Dalili ba Fuskarta na yawan Gilmamai acikin Idanuwansa.
Yau a tsarinsa bai ma yi niyyar Leko waje ba,ko Sallah acikin Dakinsa ya Dinga yi shi kadai yau din yana Son ya Zauna shi kadai baya son yaga wani Wanin kuma bazai gansa ba sai da Zuwan Sagir yasa Dole ya Fito,Har ciki ya shiga suka gaisa da Abba da Anty Safiya bayan ya Kirasa har ya gaji bai Daga ba Shi ya Bisa Har cikin Dakinsa ya jawosa nan waje yana Tambayansa Laifin me yayi mai ya Daukemai kafa..? Bai ma kai ga bashi amsan bane ya Hangi Tahowar Munari da Inteesar.
Ganin inda ya Raja”a Kallo ne yasa Sagir maida Hankalinsa wajen sai ya Ci Karo da Munari da Inteesar.
Karisowa sukayi gabansu Munari ce Cikin Rawar murya ta fara Fadin”Sannun ku..Ina yini Ya Imran..?Ya sagir ina yini..?
Tafada Cikin rawar Baki Tana kara Damke Jakarta Dakyau tana Jiran Imran yace kyat ta Zura da gudu Daman Ledan da Inteesar ta sakamata Su Dambun Naman yana Hannunta ne.
Imran kallo Daya yayi ma Munari ya gauda kai bai kara Kallonta ba kansa na kasa ya Kurama yan Yatsun kafar Inteesar Kallo da sukayi kyau Cikin wani Falt din jan Takalmi yatsun Dogaye ne suna da Haske sai jan Lallen data Cike Fararan kumbunanta dasu bai Taba Tsayama ya Kare ma Fuskar Mace kallo ba Ballatana Kafarta sai gashi yau ya shagala da Kallon Kyakyawan yatsun kafafun Inteesar Batare daya sani ba sai dai yaji Zuciyarsa na son Kallonsu Sun Burgesa sosai.
Sagir ne kadai ya amsa yana Tambayansu Karatu sukace Alhamdulillah Inteesar kuwa Ina yini Ya Sagir..! kadai tace aranta tace bazan gaisheka ba ka Dizgani Kanwarka ma bata Isheka kallo ba Ballatana ni Maras Mutumci mai shan Taba kawai Duk aranta take wannan Zencen cikin Takaicinsa.
Ita ta kama Hannun Munari suka Buga Kofar get din Iro ya leko ganin sune ya Bude musu suka Shiga Da Karamin kallon Gefen Fuska Imran ya Bisu dashi kafin ya Sauke ajiyar rai yana cije baki yace”Yarinyar nan bata kunya naga alama..!
Sagir ya Kallesa Cikin mamaki Kafin yace”Wata Yarinya..?
Ido nacikin ido Imran ya Kallesa kafin yace”Wata yarinya kake Tambaya..?kanwaka din nan wacce take zaune agidanku mana..!
Sagir ya karbe da cewa”Da tayi maka mene..!?
Imran yace”Bata gaisheni ba.ko kana Nufin Abunda tayi mai kyau ne. ?
Sagir ya saki karamin Tsaki kafin yace”Eh mai kyau ne..Saboda Halinka…Agabanta Munari ta gaishemu kaki amsawa kayi kamar ma baka ganta ba..kana Tunanin ko Nice zan gaisheka bayan agaban idona naga abunda kayi ma kanwarka..?
Imran ya Dakuna Fuska kafin yace”Wannan ba Hujja bane..Gaisuwanta Dabam na Munari Dabam..!.
Sagir yace”Duka Dayane Mallam..Kai dai kawai kace ka Tsani yarinyar nan Shiyasa naga ba tun yau ba kake Neman kowani Laifi ka goga mata..!
Tsaki Imran ya Saki kafin yace”Eh na Tsaneta ko zaka Daukan mata mataki ne Ubanta..?
Yafada yana Jefan Sagir da kallon kada ka karamin wannan mganar Banzar..
Sagir yace”Inafa..Ai Allah ne yakadai zai iya mganinka bani ba..!
Imran ya Murmusa kafin yace”Bettter Daka Fahinci hakan..Mallam zan shiga Ciki in baka da tacewa..?
Sagir yace”Yaushe zaka Dawo shago..?ko kuwa gabar da kake yi dani baka Saki bane…?
Imran ya Dakuna Fuska kafin yace”Gaba..? Ni Imran bana gaba da Wani ko wata..Sai dai in nagaji da Zama da Mutum nayi nesa dashi..Kai im zan yi gaba dakai Gaba da gaba Zan Tareka nace maka baka bani..Tunda kai ba Ubangijina bane Bana Fatan Watarana naji tsorom wata Hallita ba Allah na ba..!
Ya cigaba da Fadin”Kuma ba Daina zuwa shagon ka nayi ba saboda kamun wani abu ba..Kawai ina Bukatar Kadaici ne..In na Dawo Daidai zaka ganni kai dai ka Girma ammh kullum kana Dawowa kamar wani yaro..saboda cin kasa!
Ya karishe Fada yana Kara Hade rai Baki Sagir ya saki kafin yace”Nine wanda ke cin kasan..?
Imran ya juya ya fara Tafiya yana Fadin”To da waye..? Ya fada yana yar Dariya Kafin ya shige gida ya bar Sagir nan tsaye yana Binsa da kallo Tsaki yaja yana Fadin ba Laifinka bane nawa ne da nake binka kana gayamin mganar banza..daganan ya Juya Fuu ya Fara Tafiya aransa yana Fadin bazai Kara Neman Imran ba In ya Nemesa Shikenan in kuma bai Nemesa ba He don”t Care.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button