GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Atsarin Rayuwarsu Suna da Hadin kai da Zumunci a tsakaninsu kuma suna Girmama junansu Bayan Rasuwar Alkali Hamisu dukku wanda Ciwon Hakoribyayi sanadin Mutuwarsa Daga Dare zuwa safe,Su suka Cigaba da kula da Daada da kuma Baba Asabe da suka Taso suka ganta agidansu,Kabir yaso ya Dauke Daada Daga Dukku ta koma Wajensa a Abuja ammh Taki yarda tace Yarda Alkali ya Mutu acikin gidanan itama nan Zata mutu Domin ya rasu bazata Ki Burinsa na son Ta Rayuwa ita da ya”yansu a garin na Dukku ba sai dai bata da yarda Zatayi ne Tunda aiki ya Raba kowannesu Inda yake ammh Ita kam ba inda Zataje Tana Tare da Baba Asabe a garin na Dukku agidan marigayi Alkali Muddum rai.
Dole ya kyaleta Tunda ta kafe sai da yasa aka gyara gidan aka Maidashi na Zamani kowani Lokaci suna zuwa ganinta in suka samu dama.
Kayan alatun More Rayuwa kuwa da jin Dadi Daada sai dai ta bama wasu Komai na Rayuwa ya”yanta sun Dauke mata shi Taje ta Sauke Farali bata san iyaka ba bayan wanda marigayi Alkali ya kaita kuma suka je Tare,Hatta Baba Asabe taje ta sauke Farali Sau Biyu Adalilin Daada da Yayanta
Daada Tayi kokarin Hada kan ya”yanta da Jikokinta waje Daya suna zuwa mata Hutun karshen Shekara Duka matan da Mazan Domin kara Shakuwa tsakanin iyayen da kuma yaran sun san junansu da yan”uwansu gabadaya,ammh abun ya ki faskara sai da ya”yan nata su zo,ammh Ya”yansu basa zuwa sai Dai dai,in tayi mgana sai su kawo uzurin makaranta da aiki da sauransu.
Barrister Asma”u matar Kabir itace bata Shiga Mutane,Tana da Dagawa da Takama sai dai Tana da Fara”a in ta saba da Mutum,Taso tazo Daya da Umma Salaha,Suna dasawa sosai Ko Saboda yadda wata kakkarfan Shakuwa ke tsakanin mazajen nasu ne oho
Cikin ya”yanta Sajida ce kadai ta gado Duka Hallayarta Har ma ta fita sosai.
Sajida akwai Dagawa ga Takama ga Raini,Tana ganin tafi kowa Domin iyayenta sun tsaya mata sun kuma taka wani abu a Rayuwa,Yar gatace ta gaba da baya,agidansu basu san suyi aiki ba komai yan aiki keyi musu hatta da Girki kuwa,Inda Asma”u tayi kuskure kenan ko ita batace ta iya wani Girki ba Tun farkom auransu ta sakarma yan aiki Duka Ragamar Gidanta Har yau har gobe Abincin yan aiki yake ci kuma bai Taba Korafi ba saboda sun Tsara hakan Daman tun Kafin suyi auran
Khamis ne ya Debo kaf Hallayan Babansa,kuma ya Debo Hallayan Marigayi Alkali wanda yaci sunansa yaro ne matashi mai Hankali da natsuwa yana Bala”in son Tsohuwa Daada,Musamman Daga Anambara yake zuwa ganinta in ya samu Lokaci Waya kuwa Lokaci bayan Lokaci Tana jinsa kudi kuwa makudai haka yake Turomata,Duk Shekara sai ya Sauya mata Furniture din gidanta Shiyasa itama take matukar ji Dashi,Sai dai duk yadda take ji Dashi ba kai Soyayyar Datake ma kwara Daya Cikin Jikokinta ba Dukda ya kasance mai Budadden Hali da kowa baya jin Dadin mu”amala Dashi ita ahakan take matukar sonsa,sai dai Bata nunawa ba..Tunda bai Cika yawan Tako kafarsa Dukku ba sai da wani Babban Dalili Shima din sai Mahaifinsa ya Mtsamasa ne ya Tarosa suka Taho Tare,bawai bai Damu da kowa bane a”a yana Damu da Ahalinsa sai dai shiyanayin Rayuwarsa marasa son Doguwar mu”amala ce mara son Hayaniya da Zama Cikin Mutane, yana da Bambacin Ra”ayi da Mutame Koda kuwa yan”uwansa ne Shiyasa bai Cika Shiga Cikin yan”uwa ba,adangi ba wanda zai ce ya taba Doguwar mu’amala Dashi,ko da yan”uwansa da suka Fito Ciki Daya suna kuka da Hallayarsa masu Tsauri da Wuyar Fahimta.
Wannan kaunar ta samo asali ne da kaunar Datake yi ma Mahaifinsa ne saboda ya kasance mai sanyi Rai ladabi Biyayyah ko baya son Abu indai Daaada ta Ce abu kaza ne sai yayi shi Biyayyarsa da wannan Sanyin nasa yasa Daada ke matukar sonsa uwa uba kuma ta wanke Diyar kanwaarta Data Zama kamar itace komai nata ta Riketa ta bashi kuma ya karbs ya aura ya Zauna da ita Har Mai Rabawa ta Rabawa Duk da Ya kawo mata wacce yake so.
Shiyasa har Yau har gobe Daada bata daina kukan Rashinsa ba
Ta kamu da Ciwom Hawan jini Saboda Damuwa ya”yanta suke Wahala kan lafiyarta Musamman Kabir ya Daukan mata Likita wacce take zuwa har Gida Tana kula da ita Dr.Zubaida Cikakkiyar Likita a babban asibiti dake garin na Dukku.
Koda Daada ta tsufa Girma ya zo mata bata da Lalaci,kowa ya sani mace ce mai tsayawa akan kafarta Shiyasa bata Shiri da Sanganta da kiyuwa Sajida na yawan zuwa Hutu gidan Daada sai dai Rabuwa sukeyi ba Dadi Tun Kafin ma Hutun Sajidan ya kare.
Umaima kanwarta ta fita sanin ya kamata gata bata kiyiwa in tazo Shara gyaran Daki har girki Take Taya Baba Asabe,gidan ta koyi wasu girken girken Data koma Abuja ta gwada Ranar Diyar Lauyoyi Taga Fada kamar su Daketa suna Fadin kada ta kara Wannan kwarambanin Hannunta bai yi kwarin da Zata yi Girki ba kada ta kone
Itakuma Sajida Fadi take Tana Diyar Lauyoyin gwannati Jikar Alkalin akalai na kasa Duk da yayi Ritere,Kudi da jin Dadi sun gama Dabaibaye Rayuwa komai take kudi zasu yi mata Allah ya Tsareta da aganta tana aiki indai akwai yan aiki da kudi zasu yi mata komai Shiyasa basa Shiri da Yayanta Khamis Shima a tsaye yake a kullum yana tsawatar mata Da cewa ita macece Watarana Zatayi aure ammh Sai mahaifiyarsu da suke kira Mami ta Shiga mganar tana Fadin ya Daina Takura ma yarta yadda ta Samu jin Dadi agidan Mijinta itama Zata samu,Shidai kawai Shiru yake domin yasan Watan Watarana Zasu yi Nadaman wannan Rayuwar Bokom da Sakewan da suka Daukan ma kansu Shi Allah ya Taimakeshi Gombe yayi karatun Secondary Dinsa Bording in ya sami Hutu bai cika zuwa Abuja ba yana gaban Daada Shiyasa ya zama Dabam
Yar tsamar Dake tsakanin Inteesar da Daada kuwa bawata maiyawa bane..Duk da tafi kowa Murna da Akayi mata takwara sai dai basa Shiri saboda irin gatan da Alhaji Mustpaha yayi ma Inteesar saboda Samunta Lokacin da suka Fidda rai.
Inteesar ta shaku da Mahaifinta Fiye da kowa aduniya ko Mahaifiyarta bata Shaku da ita ba irinsa ba,Dalilin haka yasa bata da Sakin jiki da Mutane bata san kowa ba sai Daddynta sai Ummanta da yayanta Basheer sai kuwa Gidan kakaninta ta Bangaran Uwa gidan su Inno,Su da suke Biyema Sangartanta.
Inteesar bata san kowa a Dangi ba Domin bata zuwa ko”ina gwara Dukku ma in Alhaji Mustapha zai je takan Biyosa suzo Tare,Bata yarda ta kwana Kafarsa kafarta Duk kuwa da Mitan da Daada ke yi na bata son Shiga Cikin yan”uwanta.ita kuwa bata son Rabuwa da Babanta ne kuma tafi sabawa dashi Fiye da kowa.
Rabon Inteesar da Zuwa Dukku har ta manta saboda Korafin Daada akanta,Tayi ta cewa ta Cika Sangarta tayi ta ma Daddynta Fada kan ya Sangartata ita kuma abun Haushi yake bata yasa Daga Baya ta Daina Biyosa sai ta Fake saboda makaranta.
Ko Duka gidan Za”aje sai dai taje gidan Inno ko gidan Kawu Salisu Saboda yarsa Nasara sa”ar Intee ce kuma tasu tazoDaya
Shiyasa bata san kowa ba adangi su Inna Bintalo da Inna Maimuna sun gaji da mita sun Hakura Inteesar bata taba zuwa Gidan Daya Daga Cikinsu ba ko Za”aje bata zuwa bata son Abun mgana.
Tuni ta Dauke kafa Daga Dukku Tun Tana karamarta har saida taGirma Lokacin Data gama Candy Tana jiran Sakamako Daada ta matsa Umma ta Ce sai taje tayi Kwana Biyu achan,Daddy shi ya Lallasheta yakai ta da kansa Aranar Dataje Washegari Sajida ta iso Daga Abuja.
Inteesar bata ji Dadin Zaman Gidan Daada ba,Shiyasa Dukkun ta fita kanta Zaman da sukayi da Sajida Zama ne na kowa na Har kan gabansa Sajida girman kai da Dagawa..da nuna isa ita kuma Inteesar rashin Tsoro,itama tana ji Da gata sosai Shiyasa basu ga maciji,Daada ta Dinga Fada ita Sajida Kiyuwa da son jiki ita kuma Inteesar Da an fara mgana sai kuka Daada Tayi musu Fatata ta kira iyayansu suka zo suka Tarkasu,kowacce ta koma Gidansu da jin Haushin yar”uwanta,Sajida tana ganin kamar ita yar gata gaba da baya Diyar lauyoyi,yayanta Soja jikar Alkalin alkalai har wata adangi Zata Rainata Ina batazata yarda da wannan ba ita kuma Inteesar tana ganin ai Sajida bata fita gata ba bata isa ta taka ta ba.
Haka kowacce ta koma Gida da Korafin yar”uwanta Umma dai ta tsawata ma Inteesar din Ta nuna mata yar”uwanta ce ayayinda Mami bata tsawatarma Sajida ba sai ma Nuna ma Datake tafi Inteesar din gata nesa ba kusa ba Duk kuwa da suna Dasawa da Umma sai dai ita akwai son kanta Tana so a ko”ina akomai Ita da ya”yanta su fi kowa a Dangi Ba kuma iya Zuru”ar Hamisu Dukku ba Harta Daga Bangaranta Tana da wannan Dagawan.
Daga Lokacin kowacce ta ijiye yar”uwan nata awani muhalli na ban san kina Rayuwa ba,Basheer ne dan Dangi kowa ya sanshi kuma ba inda Kafarsa bai taka ba Tun yana Saurayinsa ma kafin yayi aure Dayake Jami”ar Bauchi yayi ya Zauna gidan Inna Maimuna Sosai yake da mu”amala mai kyau da kowa..
Inteesar kuwa bata taka kafarta Ko”ina ko Abuja gidansu Sajida Sau Daya taje Lokacin Tana karama da Tabi Daddy,daga wannan zuwan kuwa bata kara marmari ba,Lagos kuwa bata taba Zuwa ba tasan dai Tana da wani Uban achan lagos din inda yake Zaune shi da iyalansa ba kuma Tataba ganinsa ba sai Sau Daya sanda sukaje Dukku ita da Daddy Shima yazo shi da dansa bata dai san ko waye ba,Ta gansa alokacin ammh Tana karama bazata iya Shaidasa ba yanzu.Lokacin kuma da akayi Rasuwa anan Dukku aka Dawo aka karbi gaisuwa Lokacin Basu da Hutun makaranta Gidan Kawu Salisu tatafi abunta tayi Zamanta Saboda Nasara Domin aduniya Inteesar Bata da wata wacce ta Shaku da ita Kamar na Nasara kuma tasu tazo Daya daga ita sai Inno da Malam Babba Saboda yadda suke ji da ita sai kawunta Muda,shima akwai Biye ma Shiriritanta…
Sajida Ta fara karatun Jami”a a Base University Abuja a wannan Shekara yar Jarida take son Zama,Journalist itama Inteesar Tana so ta karanci Fanni Tsumi da Tanadi Wato Economics,Ta lula kano Inda Zata Fara Sabuwar Rayuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button