GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


Cikin Sati Biyu da sukayi suna Gurzan juna da Amarcin da basu ci ba abaya Imran Har wani kiba ya kara da Kyau ita kanta Inteesar din ta kara Kiba da Cika da Kumatu Imran bai yi kasa a gwiwa ba,Ba mganar Girma bata Indai Zai Samu abunda yake so Girman yaci Batan Ubansa..! haka yake Marairaicema Inteesar yana Fadin”Plz Intee na kara Ko sau Daya fa..?sau Daya fa..!
Ita kuma Tana jamai aji Duk da yadda Jikinta ya Riga ya saba ita kanta Tana Bukatar Bakuncin nashi Sosai sai ta Gama jamai aji da yanga sannan tace”To Wlh sau daya..Kuma in ka kara Har na gobenka..!
Dariya kadai yake yi Saboda yasan Lagonta da zai saka tayi mukau Har sai ta jigata kana yake kyaleta sai Daga baya ta koma Tana Fushin Ba Gaira ba Dalili Alhalin Tana ji kuma ammh Tayi Lamo acikin Jikinsa Da ita sukaji Dadin Duk yana an kare da ita bai Hana anjuma ko Gobe ya kara Lallabowa yana magiya..
Haka Rayuwarsu ta Cigaba da Cikin Tsafattaciyar Soyayya Basu da Lokacin Kowa sai kansu ko Waya Indai Yana Gidan Inteeasar bata ta kanta tunda suna nane da juna Shi kanshi bai Taba Nadamar aikin Banki ba sai a lokacin yaso irin kasuwancin yake yi Kullun yana Gida Tare da Inteesar yana Lallabata yana amfana da Romon damokuradiya.
Ko Gidan Abba ba wanda yaji Duriyansu ba kuma wanda ya Nemesu Shiru ke sa aji Shuru Sagir ma Haka yajisa Shuru aransa yace Shege ya samu Wajen Hutu ganinsa zai Fara mana Wahala haka ya Kira Khalil sukayi ta Gulma suna Dariya shi baima san sunayi ba sai da Sagir ya Kirasa yana mai Tsiya Tsaki yaja yana Fadin”Ina Tsausaya maka Sagir..Ka Kokarta kayi aure Ko Zaka samu wannan Rabauta da jin Dadin da muke samu..!
Bai jira amsar sa ba ya Kashe Wayar yana Dariya Sagir yayi ta Kiransa bai Dauka ba daya gayama Khalil cewa yayi ya Kyalesa kwana nawa ne suma Zasu je Sahunsa Domin shifa har ya gabatar da mganar Munari ga iyayensa kuma yana nan zuwa Kano Domin su kara Fahimtar juna shima Sagir yace ya Fadama Mama komai tace Bakomai yaje ya samu Baba Manu su Tattauna Tunda shine Ubansa yanzu.
Sun ta Gulman Imran suna Fadin ya samu yarinya karama ya Tsote mataa albarkatu ammh yana cewa baya son Raini Oho dai shi baima san sunayi ba yana Chan yana Hango su yara basu san Dadin da shi yake ji ba Ko nace yake kwasa ba Dadin Daya fi karfin yara sai dai Manya irinsa Shi wani Lokacin Har mamakin Jarumtar Inteesar yake abaya yana ganin Tayi mai kankanta sai gashi Tsab Take Dauke Dukkan wani Bukatunsa Bai Taba Zaton Zatayi ba sai dai ya kara yardan ma kansa Dan Hakin Daka Raina Shike tsole maka ido Watarana gadai Inteesar nan tana Daukesa Tsab Dinsa Dashi da Duka Bukatunsa.
Sati uku da Dinkewarsu Ranar Lahadi Tun Safe suka sTaho Gida sai dai su Abba su ka gansu Kwatsan Shima Din Inteesar ce ta Matsa sai kuma Abba Daman da Ya Yusuf sun Kira suna Tambayansa Lafiya suka jisu Shuru yace suna neman sune bayan an Koresu Shine Abba yace suna Biko..
Nan suka Wuni Har Gidan Mama sun je,Imran dai sai kafa kafa yake da Inteesar yana wani Tsare Giransa bai barsu ma sun kebe da Munari ba Saboda gani yake kamar Zata gayamata wani abu ai in Munari taji ya gama yawo abunda bai sani ba Yana mata Kallon Biri ne tana yi mishi na Ayaba.
Ranar imran har gidan Baba Manu Sagir ya Rakasa Kuma Yaji Dadi sosai chan sukayi Sallar Isha”i kana suka je Gidan Ya Sadam sudan jima Daganan suka Dawo Gida sukayi ma su Abba Sallama suka koma Gidansu yaji da Rigiman Inteesar na sai taje Kaduna Kafin su koma makaranta da wannan Damar Imran ya samu yana ta Shagalinsa Domin yace adadin Kwanakin da zatayi in taje kaduna adadin yadda Zata basa Dama yasha Budurinsa ita kuwa Tana son zuwa ta Sakar mai Ragamar Rayuwarta yana ja Sanda yaga Dama.
Sun yi mgana da Abba kan zasu Tafi Kaduna Ranar Jumma su Dawo Lahadi shi da Inteesar Domin bazai iya Jimarin Rashin wannan Wajen ba Har na Kwana Biyi ba kuma ya Saba da ita in Tatafi ta barsa zai Tagyara Jin haka yasa Abba ya Bashi Shawaran su kwana daya Kaduna Su wuce Abuja su kwanan ma Baffa Kabiru Daya Imran bai yi gaddama ba Saboda Baffa Kabiru kam yanzu ai Tsakaninsu sai Mutumtawa..
Haka kuwa akayi Farko Inteesar ta gayyato Munari a Tafiyar Imu yace Sai dai Ta Zabi Daya ko su tafi su biyu da ita Dashi ko kuma Afasa Tafiyar Dole Inteesar ta bama Munari Hakuri daman Batayi Ra”ayin zuwa ba Inteesar ta matsa mata sai taje..
Kaduna suka Fara zuwa Umma da Daddy suka rasa ina zasu sakasu Saboda Farimciki,baki yaki Rufuwa Umma Farimciki ya Cikata ganin Inteesar taki Kiba sannan ta Rage rawan kai ba kamar baya ba.
Ya Basheer najin zuwansu Ya kawosu Anty Hauwa da cikinta ya Tsufa da yara suka Dira Gidan nan fa aka Hadu murna Inteesar tazo Ganin gida ta kira Nasara ta Fadamata gata Kaduna Nasara tace bata yarda ba sai da ta bama Umma Taji Muryanta kana ta yarda sai mamaki take yi ya akayi ya Imu ya Barta tazo..?uhm basu san yadda ta Saki Jiki bane Oga yaji Dadi shiyasa.
Nan suka kwana Imran Daki na Musamman aka Saukesa Inteesar ta Gudu Wajen Umma ta kwana suka kusa Raba Dare suna Hira Washegari Imran ya Fadama Daddy Abuja zasu je gaida Baffa Daddy yaji Dadin haka yace hakan yayi kyau ammh Kafin su Tafi Daddy yace Imran yayi Hakuri Inteesar takai sa Gidan su Inno da gidan Kawu bala da gidan su Nasara ai kuwa sai da suka lelleka kafin su Wuce Nasara ga Gulma abakinta ba Halin mgana Oga Imu na Wajen ya Tsare Gira Dole suka bar mganar sai sun Hadu ta waya.
Baffa Kabiru bai san da zuwansu ba Ranar yana Gida Dashi da Umaima Sai Sajida Da Baffa Kabiru yace maza ta Dawo gida tayi Hutunta bata da yarda Zatayi ammh Da Farko Taso tayi Zamanta a Hostel ne
Su suka kasance su kadai suke Rayuwa agidan sai yan aiki sukaga Imu kwatsam da Intee Umaima ta Rumgume Inteesar Tana ta Murna Baffa Kabiru ya Rumgume Imran yaji Dadi sasai har ya kasa Boye Murnansa Sai zuwan da sukayi ne Inteesar tasan Mami sun Rabu da Baffa Itama Umaima ke Fadamata Sajida kuwa Gwanin ban Tsausayi ta Rame Duk Ta Lalace kamar ba ita ba Duk Rashin Jituwarsu da Inteesar data ganta sai da ta Firgita ta Fara Tambayan Umaima ko Sajidan Tayi Ciwo ne Umaima tace bata sani ba Sajidan bata Dade da dawowa Daga makaranta ba Baffa Kabiru ma ya Zaunar da ita yayi Tambayan Duniyanan Tace lafiyanta Kalau sai ya Kyaleta ammh kowa ya ganta yasan Bata da Ishashiyar Lafiya.
Harta Imu Daya ganta ya Dade yana kallonta kamar wacce ta Shekara Tana Ciwo Ita kanta Sajidan bata so Fitowa ba Baffa Kabiru ne yace Umaima Ta Kirata tazo ta gaisa dasu Imran wanda Tunda taji zuwansu ta ki Fitowa Domin ganinsu kamar Fami ne acikin Zuciyarta.
Ta dade tana kallon Imran kallon iri na so da kauna da kuma Kallon Yanzu Shikenan na rasaka..?
Shikuma Har ga Allah ya Tsausayamata Uwarta ta sakata Cikin Bala”i Shiyasa yake kara Godema Allah Daya sa Baffa Kabiru ya Saketa ya Tabbata Zuwa yanzu ta Fara Karban Sakamakomta Daki Daki
Tunda suka gaisa Sama sama ta Koma Daki Tana ta kuka Zuciyarta na Suya Tari ya Sarketa ta yi Saurin Shigewa Tioler sanin in dai Tayi Tari Har da Jini Jini yake Biyowa.
Imran ne suna Zaune da Baffa suna Hira ya Tambayesa Khamis Cikin Jimami Baffa Ke fadamai Kwata Kwata Tunda ya Tafi basu kara Samunsa a waya ba ba Labarinsa Imran yayi Shuru kafin ya bama Baffa Kabiru Shawaran zuwan chan Anambara ya gani ko Lafiya..?
Baffa Kabiru yaji Dadin Shawaran Imran Da Tuntuni bai kawo Tunanin ba..
Ya Tabbatar mai da cewa da aiki yayimai Sarari zai je chan din yagani Insha Allahu.
Sun sha Hira sosai Hira ta Tsakanin d’a da Uba Hirar da suka Dade basu yi kamarsa ba.
Washegari da wuri suka kama Hanyar har suka tafi Basu kara ganin Sajida ba,suna Hanya Sai da tayima Imran Zencen ya Hade rai yace ko kin bar mata ne..?
Harara ta sakarmai Tana Juyamai Baki Dariya kawai yayi yana Fadin”Juya Dakyau akwai Biyan Bashi Duk zan fashe..!
Jin haka yasa ta Daidaita Natsuwarta Tana Fadin”Bafa haka mukayi dakai ba..Ba kayi har da na tafiyar nan ba..!?
Yana Danne Dariyan sa yace”Ni yaushe..?bamu yi haka Dake ba Malama bana son Runto..!
Inteesar harda kukan Shagwabanta duk don ya Kyaleta yayi mata Fuska suna Isa Kano duk wannan Gajiya sai da ya karamata wani Da ta Fara Shagwaba yace zai Fanshe Har da Na Zuwansu Abuja Dole ta ke kama bakinta Tayi Shuru Fadan Dayafi karfinka sai ka maidashi wasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button