GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ki fito falo kici Abinci..,!

Ya turamata ya ijiye wayar a gabansa Daada Dake kallonsa Tace”Imrana kaci abincin mana..ko Baka cin Tuwon ne a sama maka wani abu..?
Da sauri ya Girgizamata kai kafin yace”Wannan ma is ok Daada Zan ci.!
Kai ta gyadamai Lokaci Daya Tana kara Nazarinsa Juya Cokalin yake yi Sai ya Dauki Lokaci kafin ya karaci yanayi yana kallon Wayarsa Zuciyarsa ta fara Zafin ganin bai ga sakonta ba,atsawon Mintina Hudu kafin yaji Sakonta ya shigo da Sauri ya Dauka ya Duba.

“Nasha Tea Ya imu..!

Da Sauri ya Rubuta mata Amsa da cewa”No..Do as i say Inteesar!!!..Kinsan bana son gaddama ko..?

Ya turamata kafin ya ijiye wayar Yana Sauke Numfashi.
Daga bangaran Inteeear kuma ganin Sakon Imu yasa Dole ta mike sanin Halinsa kada tayi laifi Dogon Hijabin Hafsah ta saka Ja,mai hannu Dama karamar Rigace ajikinta mai kama da Shimi shiyasa ta saka Dogon Hijabi,Allah yasa Munari ta tasheta Tayi sallar Isha”i ta matsa mata ta sha Tea.
Cikin Tafiyar kasala ta fito daga Cikin Dakin zuwa Falo lokacin data Fito ma Wasu sun gama cin abinci wasu ne basu gama ba Tukunnah,Tana yin sallama acikin Falon idanuwan Khamis ya fada kanta ya wani Kuramata Ido kamar zai lasheta,Imran ma ganinta yasa yaji sanyi shi kallo Daya yayi mata bai kara ba ya waske yaji dadi tanajin mganarsa,Bai ma lura da kallon da Khamis ke Binta dashi ba.
Ta gansa sai dai tayi kamar bata gansa ba ko barayinsa bata kallah ba Wajen su Abba ta nufa ta duka ta gaishesu suka amsa mata suna Tambayanta ya jiki ta amsa musu da sauki,Daddy ya Dafa kanta yana Tambayanta ya jikinta ta amsa mai cikin Shagwaba kamar ta Kwanta ajikinsa sai dai ba Hali tashi tayi ta koma wajensu Umma Tana gaida su goggo Maimunatu,ita kadai ta amsa mata cikin Sakin Fuska banda Goggo Bintalo Sama sama dai bata damu ba ta Lafe jikin Umma,Umma ta Tureta tana Fadin ta dagata Shagwabe afuska Tayi goggo Maimunatu nayi musu Dariya Daga Khamis har Imran kallonsa na kanta shi khamis irin kallon nan ne ma marasa aji yayinda Imran yake kallonta ta kasan Idanuwansa wanda ba wanda zai Fahimci yana kallonta ne.
Tashi tayi ta koma Wajen su Anty Safiya inda suke Hira dasu Munari Kafin taje ta gaida Daada Wanda Imran ke gefenta,Lamgwabe tayi jikin Daada Tana mata Shagwaba Daada na tambayanta jikinta ta amsa tana kallon Imran wamda ya Dauke kansa kamar bai ganta ba.
Daada ta Umarce da akwashe kwanunka da aka gama cin Abinci nan da nan kuwa su Munari suka Mike dasu Anty Safiya suka Tattara komai suka maida Kitchen Munari da Hafsah da Umaima suka Share Wajen suka Goge.
Daada ta Umarce ya”yanta su Matso kusa da”ita Inteesar tatashi ta koma Cikin su Munari yayinda Imran ya koma Chan karshen kusa da Sagir bai da yarda zai yi ya gudu saboda Daada bayaso yayi abunda zai bata mata rai.
Sai da kowa ya natsu kana Daada ta fara da Sallama ta Umarci Sadam daya Bude Taron da addu”a ya Bude aka Shafa Daada ba wani Dogon bayani tayi ba Abba ta bama Daada ya bama Kowa Labarin inda suka Shiga bayan barinsu Lagos.
Abba bai yi Nauyin baki ba ya gyara Zama ya shiga bada Labarin Abunda ya sani na Komawarsu kano daga Bakin ya”yansa dayasha ji da kuma Wanda ya sani ya Karishe da Fadin”Ya”yana sune garkuwata sune Duniyata..Musamman ma Yusuf gashi nan dan albarka ya Dauki Ragama da Nauyin daya kamata ni zan dauka ya kula dani..Ya kula da Kannensa Munari da Imran,ya Dauke komai a Wuyansa Imran ma ba”a barsa abaya ba Yana da kwanjin Kula da Ahalinsa Babu Abunda Zance musu sai Godiya da Fatan Allah ya basu masu Rama musu..!
Yafada cikin sadda kai Lokaci Daya aka amsa da Ameen.
Kafin Abba ya Dago ya cigaba da Fadin”Daada kiyi hakuri ki yafemin keda Sauran yan’uwana..Har ga Allah ba”a san raina Suka yanke wannan Hukuncin ba Lokacin bani da lafiya Sanda na Dawo Cikin hayyacina babu abunda zan iyayi saboda Ina neman Lafiyata ne kafin komai..!
Daada ta jinjina kai Tana Fadin”Bakomi Malami ban taba Rikon ka acikin Raina ba Tsakanina Dakai sai addu”a da Fatan Alheri..Ba kuma Laifinka bane ba kuma Laifin su Imrama bane Laifin Yan”uwanka ne da suka kasa Fahimtarka Musamman ma Kabiru..!
Tafada Tana nuna Baffa Kabiru Wanda ya Dago yana kallonta Hakama Ya”yansa da Matarsa suka Dago suma kallon Daada.
Cikin Muryan Tsufa ta Cigaba da Fadin”Da basu  rika ganin Laifinka ba..da duk haka bata faru ba..Da sun jaka ajiki da duk haka bata faru ba..Ammh tunda kaga ka dawo Alhamdulillah kuma sun gane kuskuransu..Yanzu kai kabiru da Mustpaha ku juya ku bama Dan”uwanku Hakuri..!
Abba zai yi mgana Daada ta Hanashi Tana Fadin”Ku bashi Hakuri..nace..!
Daddy ne ya fara mgana inda ya kalli Abba yana bashi Hakuri Abba ya girgiza kai yana Fadin”Bakomai Mustpaha Wlh bantaba Kullatanku ba..!
Baffa Kabiru kamar bazai yi mgana ba Mami Asma”u sai Hararan Daada take yi Sajida ma ranta duk ya baci gani take kamar Daada ta Dizga Dad dinsu gaban Mutane bai isa ya Tsallake Umarnin Daada ba ya juya yana bama Abba Hakuri ya girgizamai kai yana Fadin”Wlh ko daya ban taba Rike hakan Araina ba..!
Daada ta murmusa Tana Fadin”Naji dadin jin haka..Daman fa”idan haka ku hada kanku Waje daya ne..Naji dadi sosai Allah ya kara Hada kanku..yayi muku albarka Gabadayanku ku da Zuru”anku..!
Dukkansu suka amsa da Ameen
Abba ya gyara Zama yana Fadin”Daada ina son na gayamiki wani abu kada ki gani kice ban Fadamiki ba..!
Da mamaki Daada ke fadin”Meya faru Malami..!?
Abba juyawa yayi yana kallon Imran Wanda kamsa ke kasa kamar baya jin Abunda ke Faruwa nan kuwa yana jin komai,Maida kallonsa yayi kan Daada kafin yace”Faruwar abunda ya Faru ya Sauya Imran sosai..har Sigari ma yana sha..Sai dai nasan Tunda komai ya Daidaita zai daina sha da Izinin Lahi..!
Shuru falon yayi Imran kuwa ko Dago kai baima yi ba,Kamar ma bai ji ba Haka ya nuna,Mami Asma”u ta tabe baki tace”Ai wanda ya fara ShayeShaye..Da wahala kaga ya iya barinta..!
Tafada kai Atsaye ba wanda yabi ta kanta Sajida kuwa Gabanta ne ya Fadi Imran ke Shaye shaye..? Gabanta ya kara Faduwa ta fara Wurga idnuwansa nemansa Cikin Falon sai chan ta Hangosa kansa na kasa ta na kara Nazarinsa taga Yayi mata kama da mai Shaye shaye ko A”a..? Sai dai bata ga wata alama ba.
Inteesar kuwa Mami Asma”u ta kallan Tana Mamakinta ita meyasa bata kama Girmanta ne..!
Daada kuwa Mirmishi tayi kafin tace”Ai ya gayamin ma Malami Dazu da safe..!
Gabadaya kowa ya Kalleta Cikin  mamaki kai ta gyada tana kallon Imran kafin yace”Eh da kansa ya Fadamin..Halinsa iri dayane da na Mahaifinku Alkali baya karya komai zai Fada iya gaskiyansa kenan..Bakomai Allah yayi mana mganin komai..!
Suka amsa da Ameen Tabe baki Mami Asma”u tayi ba Haka taso ba taso ne Daada tayi fada sosai.ta zageshi sosai ta kuma ji ta tsaneshi sai dai hakan bai samu ba Daada ta nuna ko ajikinta ma.
Imran kuwa yana Duke dan Mirmishi kawai yayi bai ce komai ba acikin Ransa yana auna wasu abubuwa.
Kwatsan yaji Daada tace”bayan haka akwai wani abu da nike son gabatarwa..Wanda na zauna na yanke Hukunci ni kadai da Zuciyata Kuma ba Shawara bace Umarni nake so na baku koda shi kadai ne abu na Karshe da zan gudanar ina da Rayuwa..!
Kowa Hankalinsa ya maida kanta Domin karin bayani.
Daada ta gyara Zama Kafin ta Cigaba da fadin”Mustpha,Malami da kai Kabiru kune Maza manya..Ina son ku Hada Auran Imran Dan wajen Malami Da Sajida yar Wajen Baffa Kabiru Saboda Dalilina na kara Hada kanku ya”yana da Jikokina waje daya..!
Gabadaya Falon sai da kowa yaji mganar Daada kamar Daga sama Baffa Kabiru ya zaro ido yana kallon Daada Abba kuwa Daddy ya juya ya kallah Shima shi yake kallo cike da mamaki.
Zuciyoyi uku kuma sun Buga Lokaci Daya Zuciyar Imran data Sajida sai ta Inteesar wacce ta kwalalo ido Tana kallon Imran wanda ya Dago kansa Cikin mamaki yana kallon Daada yayinda Sajida ta rasa gane yanayinta Farinciki ko bakinciki.
Munari da Hafsah suka kalli juna cikin mamaki haka su Yusuf su kansu mganar tazo musu a bazata.
Inna Maimuna kuwa jinjina abun take ita da Umma suna Hango Tashin Tashina kan wannan mganar.
Mami Asma”u kuwa kamar ma bataji Daidai ba Idanuwanta kan Daada kafin tace”Sajida fa kikace Daada..?
Wata Sajidan..?
Daada kai Tsaye ta kalleta Tana Fadin”Wata Sajida kika sani..? Sajida dai Yar wajenki Asma”u..!
Ai da sauri Mami Asma”u ta Zabura ta Mike Cikin Hargowa take fadin”Na Rantse da Allah Daada bazai sabu ba..Arasa wa za”a bama Dan Shaye Shaye Tsageri fitsararre mara kunya sai Ya”ta..?
Ina wannan mganar bama mai yuyuwa bace Sajida bazata taba auran Dan iska ba wanda baida Sana”a sai Shaye Shaye..!
Tafada Cikin bacin rai Lokaci Daya tana Tada Jijiyan Wuya da nuna Rashin yardanta kan mganar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button