GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Alhamdulillah Godiya ta Tabbata ga Allah Subuhanu Wata”ala daya bani ikon Fara wannan labarin kashi na Farko gashi yau yazo karshe Ina godiya ga duka Masoyana da suka Taru suka nunamin Soyayyarsu kan wannan Labarin nawa Nagode kwarai Allah ya bar zumunci ina godiya ga Tarin Zaurinka da suke jimarin Bin wannan Labarin da kayattacen Sharhin su nagode kwarai Allah ya Biyaku da aljannah Firdausi Ameen

Nayi muku labarin Gidanmu Kashi na Farko kyauta sai dai kashi na Biyu na kudi ne kuyi hakuri kila hakan bazai yi ma wasu daga cikin ku Dadi ba sai dai daman chan bai kamata Labarin Imu yazo duka a kyauta ba,Acikin wannan Labarin ko Rabinsa ma bamu yi ba,kuma bama muce komai ba akwai Sauran Rina akaba Kina Bukatar son ganin wani al”amari ne zai Faru a Falon gidan su Yusuf..?Imu zai yarda su bi su Daddy zuwa Dukku..?in sun isa mezai Faru..?Mami Asma”u tana gefe ga Sajidan wacce ta kyasa Imu batare datasan ba wanda ya Tsana sama da iyayenta ba,Kun Hango Badakala da Chakwakiya a falon Daada..?yaya mtsayin makauniyar soyayyar Intee da Imu..?Imu zai gane yana sonta..? Zai sauya saboda ita..?Na Tabbata Imu kuka sani ayanzu baku san shi a anihin BANKER IMRAN ABUBAKAR MALAMI ba,na Tabbata zaku so ganin Imu ya Juya Harshensa Cikin Tsaddacen Turancinsa kuna kuma son gani yadda Soyayya zata kai su shida Intee in sunyi aure ya zasu yi Zaman auransu..?kada ku manta akwai Khamis fa agefe Daya gashi Daada Tayi alkawarin Daidaita kan Zuru”arta kafin ta bar Duniya kada na Cika ku da Surutu Akwai abubuwa Dadama da Zasu Faru mai bukatar cigaban wannan Tafiyar Saboda Ku masoyana da kuma yanayin Rayuwar da muke ciki zaku biya Kudin karatu akan #300 Kachal zaku turo kudin karatu ta wannan asusun bankin 0552179550 JAMILA UMAR GTB,,Sai aturo shedar biya ta wannan Lambar 09069067488,masu katin waya kuma zaku iya Turo hoton katin ku ta wannan Lambar 090690674488,Zan Fara posting din Book2 da Zarar Mutane 100 sun yi payment Insha Allahu ina godiya Masoyana kuma ina Maraba da ko akoda yaushe.

Tanque
08/03/2022
Janafty
Intelligent writer”s asso
3/22/22, 23:13 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?1

Ki biya ki karanta cikin Salama da Aminci,Ki sani ki kara sani Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun sata wannan Littafin na kudi ne kan Naira 300 kachal ki biya ta wannan asusun bankin 0552179550 gtb ko kuma a Tuntubi wannan Lambar kai Tsaye 09069067488

Bai damu da yanayin kallon da ilahirin falon suke binsa dashi na mamaki ba banda Yusuf da Abba da su munari wadanda suka sansa suka san zai iya aikata abunda yafi haka.
Mami Asma”u cikin mamaki da al”ajabi ta juya tana kallon Baffa Kabiru bata samu bakin mgana ba,Imran ya kara gyara tsayuwa Hannunsa guda daya na cikin aljihun bakin wandon dake jikinsa dayan hannunsa kuma yana rike da karan sigari kansa Tsaye idanuwansa basu Rusuna ba yake bin Fuskar kowa da kallo kai Tsaye Fuskarsa bata bayyana Fara”a ko sakewa ba,ya hade ran ya dakuna Fuska kamar an aikomai mala’ikun mutuwa.
Daddy ya kalli Baffa Kabiru cikin mamaki shima ya kallesa,Kafin su maida kallonsu kan Abba wanda ya Dafe kai cikin Takaichi.
Imran ya kara Kausasa Muryansa yana Fadin”Eh da gaske nake yi..ba inda Zamu je bama bukatar zuwa ko”ina wannan shine gidanmu..!
Yafada yana Kai sigarin bakinsa ya zuka ya sake Fesar da Hayakinta Cikin kwarewa.
Yusuf ne ya mike da Hanzari ya isa garesa Lokaci daya yana Fadin”Imu..Imu saurareni..!
Kallonsa yayi ido cikin ido ganin haka ya sa Yusuf yace”Ka koma Dakin ka wannan ba mganarka bace..Mganar Abba ne da yan”uwansa bakai bama ko mu da muke gaba dakai bai dace mu ce wani abu ba..So ka koma cikin dakinka don Allah..!
Yana mganar ne Imran namai kallon Tara saura kwata gira daya ya Dagamai cikin Salon rainin wayau kafin yace”Oh Really..Sai yanzu ne su sakansa shi dan”uwansu ne..? Meyasa lokacin dayake bukatar Taimakonsu suka Juyamai baya..?meyasa alokacin basu nuna ma Duniya su din Ahalinsa bane suka yasar dashi,suka Kyalesa suka Rika aibatasa da kaddaran da bashi ya Dora ma kansa ba wani kokari ko Himma sukayi wajen Sauya wannan al”amarin nace ka Fadamin wani kokari sukayi..?
Yafada cikin Tsawa Ransa ya fara baci Idanuwansa sun sauya Launi Tuni jijiyoyin kansa suka Mike Radau suna Harbawa.
Gabadaya kowa shi ya zuba ido yama kallonsa yana Sauraransa,Daddy ya sunkuyar da kansa aransa yana Fadin anzo wajen dayake ta gudu Tuntuni Baffa Kabiru kuwa mamakin Rashin kunya irinta Imran kadai yake,Matan kuwa kowa sai mamaki Mami Asma”u kuwa bawai ta kasa mgane bane mamakin al”amarin ne ya isheta Abba Take kallo Tana ayyana Abuubuwa da dama ganin yadda ya zauna yayi Shuru Yaronsa na Diban albarka ya kasa mgana.
Yusuf dayasan Imran in ransa ya baci zai iya Fadar komai yasa ya Rikesa Gam yana Fadin”Is ok muje ciki don Allah Imran..!
Kwace jikinsa Imran yayi yana Fadin”Wlh ba inda zan je..ai da Farko bam ce komai ba saboda ba”a kawo gabar da zan yi mgana ba yanzu ne Lokacin da zan ce wani abu..Daman Tuni ina jiran wannan Ranar da wani Daga cikinsu zai zo yace Mu koma Gida to bazamu koma ba..Naji dadin da kuka zo kuka ga Abba ya warke yasamu Lafiya yanzu kun Tabbatar da Ko da ku ko bako zamu iya Rayuwa..?kun tabbatar da Abbanmu ba Mahaukaci bane kaddarace ta Fadaamai kuma cin jarabawa da Daukan kaddara duk na Allah ne wanene acikin ku zai iya jure daukan Girman Raunin da muka Dauka?
Abba ya rasa Anni mata take garesa Uwar ya”yansa ta rasu ko gawanta bai gani ba Ya rasa ya”yansa uku aLokaci daya acikin ku waye zai iya daukan girman wannan Raunin..?waye zai iya Tsayuwa da kafafunsa in wannan Jarabawan ta Fadamai ehe?Masu cewa Abba yaki yarda da kaddara su in haka ta faru dasu zasu iya daukan..? Masu cewa Abba ya zama Mahaukaci su in haka ya faru dasu waya sani ko zasu kashe kansu ne..? Masu ce mana muma bamu da amfani muna kara Raunana Abba su din sun manta Muma Uwa muka rasa da Ginshikin Ahali har uku..?sun manta muma muna sonsu ko sun manta muma muna da Zuciya da kwanjin in muka rasa namu mu nuna?ko shikenan mu ba Mutane bane Dabobbine da zamu yi wannan Babban Rashi kuma mu dawo muna Dariya Lokaci daya..?meyasa baku jamu ajiki kun Lallashemu ba..? meyasa baku nuna mana gata da soyayyah ba..?
Meyasa baku rika nuna maana amfani Hakuri ta Lallashi da nasiha da ban baki ba..? Wlh har yau har gobe ina jin kunar kalmar Mahaukaci da wannan Mutumin ya Kira Abba dashi ina jin zafin hakan zafin daya kan kusa kona Kirjina in na Tuna Nayi ma Daada Uzuri yafi sau saba”in saboda Raunin Tsufanta ya bayyana kuma kamar yadda muke da Rauni haka take dashi itama Tana neman Mai Tallafamata ne in nayi ma Baffa Mustapha uzuri bai wuce Uzurin ya kasance mai Sanyi Hali kamar Abba kuma bai taba aibatamu saboda Kaddaran data Fadamana sai dai ina ganin Laifinsa na Hana Baffa Kabiru Aibata kaddaranmu na Hana sa Zagin Abbanmu da kiransa Mahaukaci Laifinsa na kin gayamsa gaskiyan kan Abunda yake Aikatawa abunda baitaba Tunanin yaya mu ya”yansa zamu ji acikin kirjinmu ba Ko ka manta Cewa Yadda ya”yanka suke awajenka Haka na kowa suke..?ka taba Tunanin ya ya Nauyin mganarka zata Kuntatamana..? Ka taba Tunanin yaya ya’yan Dan”uwanka zasu iya juran wannan Tozarcin naka..?baka taba Tunani ba Shiyasa kake komai naka kanka Tsaye shine yau zaka zo kace Abba ya bika ka kaima Daada shi Saboda tace ka dawo mata shi..? To ba inda Abba zai je Gari na wayewa kowa ya watse ya kama gabansa nan ne Gidanmu yanzu duk wanda ke son ganinmu sai dai ya tako yazo kamar yadda kuma kuka zo..!
Ya karishe Fada yana Sauke Numfarfashi Cikin zuciya Idanuwansa sun kara sauya kala har sun cika da kwallah Saboda Tuna Abunda ya faru Baya,Gabadaya Falon kowa jikinsa yayi sanyi masu Saurin kuka Irin su Munari har ta Fara Inteesar na Lallashinta itama kwallar take ganin yadda Duk kafiyar zuciya iri nta Ya Imu yau Rauninsa ya bayyana Su kansu su Sadam jikinsu yayi sanyi basu da sani kan Abunda ya Faru Lokacin ammh indai Hakane Tabbas ba”a kyauta musu ba kuma suna da Ikon suce wani abu a wannan gabar.
Baffa Kabiru ransa ya baci saboda kara kara Imran ya ambaci sunansa ya Nuna dashi yake cikin bacin rai ya mike yana kallon Abba Lokaci Daya yana fadin”Malami a gaban idonka kama ji kana gani D”an daka Haifa yana neman cin Zarafina ka kasa ceewa komai..?
Yafada cikin mamaki yana kallon Abba Kafin Abba yayi mgana Daddy ya Rigasa cikin Kwantar dakai Yace”Barrister mganar gaskiya Imran gaskiya ya fada..Daman Ranar da nake ta Tsoron zuwanta kenan Ranar da wani Daga cikin ya”yan Yaya Malami zasu Tuhume mu da Laifi da kuskuran Gudumuwarmu wajen Nesanta kansa da yayi damu ina ta jin Tsoron wannan Ranar..Kada ka manta ko Zuwan mu dukku na Karshe kiran Daada kenan kuma ta fada ta kara Laifinmu ne laifin mu ne Ya Kabiru kaima ka sani..!
Yafada cikin wani yanayi Umma ta Jinjina kai Batayi mgana ba,Sanin duk abubuwan da suka Faru,Baffa Kabiru yana da kaso mai tsoka kan Faruwar komai bai daukan abu da Muhimmanci indai bai Shafi matarsa da ya”yansa ba bazatace dai komi baa Saboda ba Huruminta bane bata taba mgana Kan Lamarinsu Daddy indai bashi ya tace wani abu ba.
Mami Asma”u da mamakin kalaman Imran suka Daskaran da ita ta kasa wani Motsi tafa san gaskiyane saboda ai Da ita ake komai da gudummuwarta a Lokacin tana gayamai bai kamata ya zauna yayi ta Wahala da Abban ba ai ba yaro bane kuma baida ilimin sanin Mutuwa ce da zai zauna yana wani abu kamar mara Hankali Tana nunai ai da gangane saboda su ya rika Hanasu Harkokin gabansu da irem iren wasu maganganu alokacin koma meya faru da saka Hannunta ammh Dayake ita Macece mai son kanta bata iya ganin hakan ba sai take ganin kawai ana neman cin Zarafinsu ne.
Mikewa tayi Tana Tafa hannu Cikin mamaki kafin tace”Au har dakai Baban Basheer..?Yau da bakin ka kake Bude baki kana Fadin Abban Sajid bai kyauta ba shi keda laifi kai ka cire kanka..? To Tunda shi keda alhakin komai meyasa alokacin daka Fahimci haka kai bakayi kokarin gyara komai ba tunda kai ka Fahimci shi ya bata komai..?
Tafada tana kallonsa bai yi kaurin baki ba yace”Kin ji sanda na ce shi kadai keda Laifi Barrister Asma”u..? Cewa nayi dukkanmu munyi laifi ya sani na sani Kowa ma ya sani Tunda Daada gaban duka ya”yanmu ta fadi haka..!
Mami Asma”u ta dagamai hannu Cikin Fusata tana Fadin”Bana son jin komai Mustapha..ai ka riga ka gama mganarka Abban Sajida kaga abunda nake Fada maka ko..?ai daman na fadamaka kune kuka damu dashi shi kam bai damu ba yana nan yana Rayuwarsa Kama gani Harda dan Shaye shaye ma ya samu cikin ya”yansa..Baya bukatar kowa..Ka taso mu tafi Abuja batamana Nisa ba bayadda zan zauna ina ji ina gani ana Tozarka ba..!
Tafada Tana isa garesa Lokaci Daya ta kamo Hannunsa Shi dake tsaye ya kasa mgana saboda baida ta cewa,shi kanshi ai yasan bai kyauta ba to shima Selfish bazai barsa ya iya Daukan haka ba da kuma Ego irin nashi Daman dagashi har matar tashi They are d same.
Maimakon ya nuna mata hakan datace bai dace ba sai ya kada kai yana Fadin”Yes hakane abunda ta Fada..Daman duk abunda nake yi saboda Daada ne..Tunda kuma shima Malamin ya nuna yana bayan mganar Da”nsa bani da tacewa..Ma”u muje..!
Yafada suna Kokarin barin Falon kowa ya Bisu da kallo baki sake Abba Dai na Zaune duke da dakai bai cekomai ba Har wannan Lokacin.
Daddy ne ya mike yana Fadin”Haba Barrister ya zaka Biye mata..? Itafa macece ya kamata ka zauma mu Fahimci juna..!
Ko juyowa basu yi ba suna Shirin barin Falon Imran ya saki wata Dariyan Basawa Cikin Kaushin Muryansa yace”Ka kyake su tafi Baffa..Daman ai ba komai ya kawosu ba sai son kai irin nasu abunda kuma suka zo dominsa sun ga ba Nasara Abba bazai je ko”ina ba..!
kalamansa yasa gabadayansu Juyowa kowa sai da ya jinjina mganar Umma ta kada kai aranta tana fadin yau an samu mai daidai da Asma”u Sa”id da Sadam suka kalli juna,hakama Matansu suna ayyana Tabbas Tsaurin Idanuwan Imran sun wuce Tunaninsu.
Mami Asma”u ce ta nuna kansu tana Fadin”Mume kake kira masu son kansu..? Lalle shaye shayen ka yayi maka Rana..Tunda har kakiramu masu son kai.kuma kake Tunanin Daada ta tako kafarta ta Biyoku lalle Kwayarka bata Fadamaka daidai ba mara kunya..!
Imran ya Dakuna Fuska yana kallonta ido cikin ido Tabarsa ya zuka Hayakim ya sakesa ta Hancinsa harta Kunni cikin kallon sama da kasa yace”Ni kin ji sanda nace Daada tazo nan..? Ai ni ina girmama Daada..Ko bakomai Daada ta nuna Rauninta kan abunda ya same mu,nifa da ku nake bada Daada ba, kada kuma ki kara Kirana Mara kunya bake kika Haifeni ba mganar kwaya kuma in ma na sha ai ba da kudin Lauyoyi na siya ba ko..?
Kowa ido ya zaro da jin kalamansa Yusuf ya Dafe kansa cikin Takaichi Mami Asma”u taji ta Muzanta ta kalli Baffa Kabiru wanda yake bin Imran da kallo yana Tunanin Tsegerancin yaron zai saka ma ya iya Zaginsu kila ma Har malamin ya gagaresa Tunda gashi ya kasa mgana.
Yana neman hanata mgana ta Kwace hannunta ta fara taku zuwan gaban Imran tana nuna kanta Lokaci Daya Tana Fadin”Ni kake fadama wannan mganar..? Kasan wacece ni..?
Irin kallon sama da kasa na Rainin nan yayi mata Irin to ke din wacece cikin Gadaransa yace”To ke din Wacece..? Ai b..!
Bai karisa ba ya yaji tsawar Abba ta karade Falon cikin bacin rai yace
“Kai IMRAN…!
yafada yana Huci Huci mai zafi Tun dazu ya kasa cewa komai saboda Yasan tankwasa Imran ba abu bane mai Sauki Daman yasan tabbas sai haka ta Faru,sai dai an kawo gabar da Dole yayi mgana yana da Tabbacin da bai Tare Imran ba cemata zai yi kedin ai ba uwata bace..Zai iya Zaginta Duk mganarta yana da amsarta shi ya Haifi Imran yafi kowa sanin baya da Shayi ko Tsoro ba Asma”u ba ko Baffa Kabiru zai iya kallah yace mai ai ba Ubansa bane shi ballatana ita.
Imran ya wani kalli Abba a karkace kafin yace”Abba daka koma ka Zauna..Na dade ina sauraran mganarka ammh yau kam bazan saurareka ba..!
Yana Fadar haka ya juya wajen Mami Asma”u Lokaci daya ya saka Hannunsa ya Murje Sauran Taban Hannunsa Data rage da Wutar da komai ya saki Sauranta a kasa Hannunsa duka Biyu ya maida cikin Aljuhun wandonsa yana Fadin”Arm kika ce ma me..? Yauwa na tuna bansan ko wacece ke ba ko..? To ni ina ruwana da saninki Tunda ke ba Uw….!
Abba ya kara Dakamai Tsawa yana Fadin”Wlh in ka kara cewa Tak anan Wajen sai naci Mutumcinka imran kaji ma na Fadamaka..!
Yafada cikin kakkausan Murya yana nuna shi da yatsa.
Imran ya dago yana kallon Abba Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska.
Mami Asma”u tayi wiki wiki kamar mara Gaskiya Dariya kowa ke kunshewa aciki ganin yadda tayi,Basheer da Sadam suka kalli juna suna Mirmishi Inteesar kuwa sai da ta Dara Tana Rufe bakinta aranta tana godema Ya Imu yau taga mai mganin iskancin Mami Asma”u saura Diyarta Tsagera mara kunya,Hatta Umma abun yayi mata dadi kanta na kasa tana Dariya kasa kasa wato mganin Mami Asma”u sai tsageru irin su Imran Daddy na gefe bai ce tak aransa yana fadin in bata kama girmanta ba ai yaron zamani zai tayata kamawa.
Abba ya karisa wajen su Baffa Kabiru yana Fadin”Ya kabiru don Allah kuyi hakuri ku dawo..Bai kamata ka Dauki wannan abun da zafi ba..wajena kuka zo ba Wajen Imran ba kuma Imran bai isa ya hanani Abunda nayi Niyya ba..Kuma bai isa ya Raba jinin dake Tsakaninmu ba Ya kabiru..!
Baffa Kabiru ya kada kai yana Fadin”Ammh kana ji yana neman Zaginmu ni da iyalina..!
Baka iya dakatar dashi ba..?
Abba yace”Ai na Dakatar dashi Baban Sajida..kuyi hakuri..!
Kafin ma Baffa ya samu bakin mgana ta tareshi da cewa”Ka tareshi lokacin Daya gama Tozarta mu ba?
Wannan gabar Daddy ne yayi magana yana fadin”Yaya ya kamata ka Dakatar da Asma”u kan saka baki cikin mganar nan ba Huruminta bane..nan wajen fa akwai mutane kuma bataji kowa ya tanka ba..Mganace Tsakanimu iya mu nan manya bai kamata matarka tana Sako baki ba..!
Su Sa”id dake gefe suka kada kai alamun gaskiya ne.
Mami Asma”u tabi Daddy da Harara Tana Fadin”Sai nayi shuru ana cin Zarafin Mijina ko..? Ni Asma”u nasan Ciwon kaina kan Mijina da ya”yana zan iya yin komai domin sune iyalaina anan duniya..!
Daddy yace”Musan wannan kowa anan ai Ya”yan nasa da matarsa sune iyalansa kuma don su ma muke fita nema ammh bai kamata kina Tsallake in da ba Huruminki ba..!
Ta bude baki zatayi mgana Baffa ya Rike mata Hannu ammh duk da haka sai da ta Furta cikin bacin rai tace”Ammh shi Tsagerun yaron naku daya Tsoma baki sako cikin mganar kukayi..?
Daddy zai yi mgama Abba ya Hanashi ta Hanyar tareshi yana Fadin”Mustapha ba girman kabane..Kyaleta don Allah
Yaya kabiru Asma”u don Allah kuyi hakuri ku dawo ku zauna ba domin kowa ba saboda girman Allah da kuma Girman zumunci..!
Yafada yana Hada Hannayensa alaman Roko Imran Dake Tsaye yaji Haushi ya kamashi Karamin tsaki yaja kawai bai ce komai ba.
Jin haka yasa Baffa Kabiru ya kalli Mami Asma”u yana Fadin”Muje mu zauna..!
Zatayi mgana ya hanata bayan ya Girgizamata kai dole ta Bishi ya koma in da ya tashi ya zauna itama Haka sai Harare harere take yi tana waige waige,kowa yayi kamar bai ganta ba.
Suna Zama Abba ya koma ya Zauna Kafin yayi mgana Baffa Kabiru ya Rigasa da cewa”Malami Imran Shaye Shaye yake yi..?
Yafada yana kallon Abban Imran Dake gefe kamar yace”Eh ko zaka iya Daukan mataki ne..? Sai dai ba Halin mgana saboda Abba ya hanasa ammh Kallon kafa fara cikani yake ma Baffa kasa kasa Yusuf na gefensa bayaso ya bar Wajen domin Imran bazai damu da ya Zubar da Halin nashi ba.
Abba ya dan Murmusa Kafin yace”Imran baya Shaye Shaye Yaya..Taba kadai nasan yana sha..!
Baffa Kabiru yace”Taba..? Kaidai ita kagani ammh daga ganin yanayinsa bazai rasa shan kayan maye ba Allah ma ya kyauta bayashan giya..!
Yafada yana kallon Imran din daya ji kamar ya Durama Baffan Ashariya.
Abba yace”Eh bazan yi shaidansa ba..Sai dai nafi kowa sanin Imran duk cikin Ya”yana shi kadai ne bayamin karya..Yana fadin gaskiya komai Dacinta Inda yana shan wani kayan Maye bilahil azim kaji Rantsuwan musulaimai sai na fara sani..!
Baffa Kabiru ya jinjina kai bai kara mgana ba Abba ya gyara zama yana Fadin”Yanzu dai ya mganar zuwan mu Dukku gobe..Ina so naje naga Daada na roketa gafara..!
Yafada cikin wani yanayi Baffa Kabiru ya dan zakuda kafada kafin yace”Aini na gama mganata..Gobe nace daga nan mu isa Dukku bana so kowa ya Fadama Daada sai dai ta ganka kawai ammh naji Yaron ka yace bazaka je ba kila ita Daadan kake so tazo ta sameka..!
Abba ya girgiza kai yana fadin”Ban isa nace haka ba Yaya..!
Baffa Kabiru yace”D”an ka ya yanke maka Hukunci kuma baka iya cewa komai ba..!
Imran da ransa ya gama baci ya Budi baki yace”Ba Hukunci bame haka ce zata Faru ba inda zamu je..!
Abba ya Mike ransa yana Fadin”Imran..Imran me na gayamaka..?
Cikin Dakuna fuska yayi yana Fadin”Kace kada na sake mgana..!
Abba yace”Shine kuma saboda ka Rainani ka sake yin din ko..?
Imran yace”Ammh Abb..!
Rufemin baki kafin Raina ya baci na tsinke ka da mari..!
Abba ya katseshi  cikin Fusata kafin ya Cigaba da fadin”Ina Ruwanka da mganarmu.?kana sako baki cikin mganar manya yaya fa Yayana ne Uba yake gareka ya isa dani Ubanka bama kai ba..!
Imran ma kunkuni acikin ransa yana fadin Tab ni dai ba Ubana bane wlh.
Kowa yaga Motsin bakinsa Hatta Abba sai dai bai bi takai kada ya Matsa ya fada da karfi kowa yaji ya kuma san ba abu bane mai kyau ya fada ba.
Cikin Kaushin Murya Abba ya Nunashi da yatsa yana Fadin”To kul na sake jin kayi mgana anan wajen..Mganar Tafiya Dukku kuma da yardan Allah Gobe zamu tafi dukkanmu dani da kai da Yusuf da Munari da Matarsa In kaga dama kabiyomu in kaga dama kada kaje..!
Yafada cikin Fushi Imran yabudi baki yace”Fine..ni tunda bakace Dole naje ba Allah ya kiyaye hanya..!
Yana fadar haka ya juya zai koma Dakinsa Abba ya rike baki cikin mamaki kafin yace”To na fasa..Wlh sai kaje!
Imran ya Juyo cikin mamaki yana fadin”Abba..!
Yace”Eh sai ka je Umarni ne Daga ni Mahaifinka in kuma ka Sauya wani Uban ne zan gani..!
Yana gama Fadar haka ya koma Wajen Zamansa Ransa na baci.
Imran kamar zai yi mgana Ya dago ido keman suka Hada Ido Hudu da Inteesar kai ta girgizamai tana Lamgwabe kai alamun kada yace komai batajin dadin Fadan da Abba kemai yana sata jin wani iri.
Shi kuma Saboda ita bazai iya cewa komai ba Idanuwanta suna da kaifi a gareshi yasa ya juya kawai ya Shige Dakinsa ya bango kofa.
Abba ya jinjina kai kawai bai ce komai ba ya juya yana kallon Baffa Kabiru da Daddy yana Fadin”Kuyi hakuri dashi..Haka yake sai fatan Allah ya shirya..!
Ameen kawai sukce ba wanda ya kara mgana Abba ne ya mike yace su Daddy su tashi su shiga Dakinsa sa tattauna achan sauran matan kuma Safiya ta kwashi gayya zuwa Shashenta Inteesar da Munari da Hafsah suka tafi Dakinta Yusuf kuma yayi ma su Basheer jagora zuwa Dakinsa na baya.
Shi kuma sai ya yanke Shawaran kwana Dakin Imran tunda yana da Tabbacin ko giyan wake yasha bazai Tura wani Dakin Imran ba.
Shashensa ya koma ya iske Safiya ta bama Kowa wajen kwanciya Bedroom dinta ta sauke su Aneesa.
Dayan kuma ta Sauke Umma da Mami Asma”u wacce ke ta wani shan kamshi Umma dai sai dariya acikin ranta to shan kamshi me ke da yaro ya gama Tsage miki gaskiyarsa.
Imran na Kwance yana fama da Nauyin Umranin Abba bashi kuma da yarda zai yi ya Tsalleke mganar sai Mami Asma”u dayake Tunanin sai yayi mata kyakyawan zuwan da zata gane Waye shi zata kiyayesa dauka take ita wata ce..? Shi ko Baffan mijin nata ba ganinsa yake da wata kima ba ballatana ita karan kada Miya.
Yaja tsaki yafi sau ba adadi shi kadai kafin yaji Shigowar,Yusuf dago kai yaga waye zai shogomai daki sai yaga Yusuf da kayan barcinsa da Blanket da Safiya ta kawomai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button