GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Bangaran Sajida Mami Asma”u ta dawo kanta ganin Khamis ya koma bakin aikinsa,Ta riga ta kudura ma Ranta Tsarwatsa auran nan kuma ta Lashi Tokobin sai ta Wulakanta Imran Tana Fatan ya tako kafarsa zuwa Gidanta sai ya Raina kansa.
Tattara Sajida tayi tace ta koma makaranta Zasu fara Test,Daman A Hostel take zaune sai dai bayan 2 weeks take Dawowa Gida tayi weekend wani Lokacin har Sati ma Tana Dawowa Gida sai in Sun Fara Test ne ko jarabawa take zama acikin makaranta sosai wannan karon Mami bata ma barta tayi Tunanin makomarta ba ta Tarkatata makaranta da kanta ta kaita ta maidata bayan ta mata Fadan ta Cire komai acikin Ranta tayi Facing din Karatunta kamar wani abu bai Faru ba Sannan ta Gargade ta kada ta Sake ta fadama wani an mata aurre..Domin kaskanci ne sosai wani yaji wannan Labarin Sai ayi mata Dariya.
Sajida a makaranta bazatace ga Halin Datake ciki ba,Zuciyarta da Duka Tunaninta suna wajen Mijinta Imran ne bata San ta wata Hanya zata bi ta samesa ba,Ba mgana take da kowa ba Acikin Dangi ballatana ta saka ran Zata samu ko wajen wata ne,Bata kuma da lambar Munari Umaima ce ke dashi kuma tana gida bata san kuma ta Kirata Mami taji Labari ita ko bata Dama ta gana da Mijin nata ba”ayi ba abubuwa suka zo suka Faru ba Dadi ita dai koma Menene bazata yarda Mami ta rabata da Imran ba Tana son shi tana Kaunarsa ya Dace da Duka Zabinta bata damu da Hallayarsa ba shi take so kuma bata Damu da Rashin Jituwansu da Mami ba Ballatana Ya Khamis ba yare Daya take Fahimta Shine Son Imran mijinta Har wani alfahari take da hakan kuma bazata jura ko Ganin wani ya Shiga Tsakaninta da abunda take so ba, koda Mamin ne da kanta.
Haka take Sukuku bata da wani Karkashi Allah ne ma ya Taimaketa Kwakwalwarta naja shiyasa ta iya Tabuka wani abu a Test din da sukeyi ammh Rabin Hankalinta da komai nata suna ga Imran ne duka Mafarkinta nashi ne.
Ta bari ne su gama Test ta dawo gida Sai ta san yadda tayi ta mallaki lambarsa su rika mgana Kila jin Muryansa zai Rage mata wani Radadin ba ruwanta dashi bai Nemeta ba,ita din zata Nemesa saboda Shi din Mijinta ne nata ita kadai.


Kano..

Yau ta kama Jumma”a ne a masallacin Jumma”a suka Hade tsakanin Sagir da Imran,Daman nan suke Sallar Jumma”a Shida Sagir,Abba kuma na chan Tsallaken Gadon kaya yake zuwa ,Tun ana Huduba Imran ya iso masallacin,shiyasa ya samu Shiga Cikin masallacin aka gama Huduba aka Tada Sallar sai da aka idar irin Tururuwan Fitowana nan sukaci karo da juna.
Tsayawa sukayi suna kallon kallon juna Sagir na sanye Cikin Sabuwar Shaddansa Fara Dinkin zamnii na Riga da wando Da Hulansa Zanna Bukar,sai Dardumansa Dake hannunsa yayi kyau sosai kuruciyarsa ta kara Bayyana da Samartakansa..
Yayinda Imran ke sanye da Jallabiya mai Ruwan madara,bata da tsawo sosai sai ya Hada da wani bakin Wando kafarsa Cikin Takalminsa Sawu Ciki na Fatar damisa,kansa ba Hula sai dai yasha gyara Hannunsa kuma Agogon Fata ne baki na Fatar Damisa fuskarnan ko kadan ba Fara”a Ya wani Kara Dakuna Fuska da suka Hadu da Sagir.
Sagir bai damu ba Mirmishi yayi mai Lokaci Daya yana bashi Hannu alamun Musabaha bai yi gaddama ba ya mikamai suka gaisa Daganan suka jera har Wajen masallacin Mutane nata Xirga Zirga tafiya masu ababan Hawa nayi masu Tafiyar kasa nayi.
Sagir ya kalli Imran yana Fadin”Kazo da Mashin ne..?
Ko tankasa Imran bai yi ba Hanyarsa ya Dauka ya Fara Tafiya wanda hakan da yayi shi ya bama Sagir amsa sa bai Hakura ba ya taka ya Bisa suka Fara Jerawa Suna Tafiya Kafada da kafada ammh ba wanda ya kara ma wani mgana sai Sagir ne ya kallesa yana Fadin”Na kiraka baka Dauka ba..Hala wayarka Ta lalace ne..?domin naga baka Biyo baya ba..?
Imran ya wani kara Tamke Fuska Hannuns Daya Cikin Aljihun Jallabiyansa kamar bazai yi mgana ba sai chan yace”Bata lalace ba..Kawai bana Ra”ayin mgana Dakai ne..!
Sagir na Dariya yace”Nagane..Daman mai Amarya Danyan Sharaf irin Sajida ina zai yi ra”ayin mgana Damu..!
Kamar ya watsamai Wuta haka yaji mganarsa Da ace ba domin suna Bakin Titi bane da sai ya Daki bakin Sagir ya Fitar da jini sai dai yaci Daraja Daya suna Cikin Mutane ne da yau ya gane Kuransa na gayamai wannan mganar.
Kala bai kara cemai ba Sai ma kara Hade Rai da yayi yana wani Bude Hanci ganin ya kunnosa yasa Sagir bai kara mgana ba sai Kunshe Dariyansa yake yi.
Haka suka rika Tafiya kamar kurame har suka kariso kofar Gidan su Sagir din wanda yayi ya shiga ya gaida Mama yace bazai shiga ba kuma Shima Sagir din bazai shiga Gidan ba yanzu Sagir ya Tsaya yana kallon Ikon Allah ga Shagonsa yaronsa Auwal ya Rufe sun tafi masallaci Da alamun ya Rigasu dawowa.
Bai ce komai ba ya gyara Tsayuwa suna Tsaye kafada da kafada suna Bin Hanya da kallo kamar masu kirga wani Abu.
Ta bangaran Imran ba haka abun yake yau yaji ya gaza Inteesar kadai yake son gani,in bai ganta ba ji yake kamar zai iya Mutuwa gashi ta Daina Kiransa kwana Biyi bai ga Sakonta ba Ko ta Daina Damuwa dashi ne..?
Juyawa yayi yana kallon Kofar gidan Mama Tun jiya bai ji Motsinta ita da Munari agidan ba,kila Gidan Mama suka kwana kuma yau har yabar Gida bai gansu ba Abba da Anty Safiya ya bari agida Yusuf na wajen aiki.
Kallon Kofar gidan yake kamar yana so yaga Inteesar din ta Fito Sagir Dake Lura dashi Tun dazu ya Juyo yana kallonsa Cikin Nazarinsa kafin yace”wai wakake nema ne sai kallon Waje Daya kake yi..?Nace kuma kazo mu shiga kace A”a..!
Imran bai ce komai ba sai ma Mtsawa Da yayi gefe ya Fito da wayarsa Dake Cikin Aljihu Sagir na gefe Hannunsa Saman Kirjinsa yana kallon ikon Allah Cike da Nazarin Imran din.
Sako ya Tura mata saboda yana son yaji ko Tana ina ne..?

‘”Kina ina ne..”?

Haka kurum ya Turamata ya koma yana Jiran Tsammanin amsarta Sai dai Har wajen Shudewar Mintina Goma bai jita ba sai kallon Wayar yake yana Sakin Siririn Tsaki wata Zuciyar na Fadamai kila Fushi Take yi Dakai tana Kiranka baka Dauka Ransa ya kara baci Wato ita ce ma Zatayi Fushi ita bata ga abunda tayimai ba ko?
Kwafa yayi kawai yana kokarin Daidaita kansa Sagir Dake lura dashi ya matso kusa dashi yana Fadin”Wa kake ta kira ne haka..? Ko yaki Dauka ne naga sai Tsaki kake ja kai kadai..ko Amarya ce taki Dauka tana ja ma Ango aji..!
Ya karisa Fada yana yar Dariya wani banzan Kallo Imran ya Bisa Dashi kafin ya maida wayarsa aljihun Jallbiyan Dake jikinsa Kokarin Dunkule hannu yake yakai ma Sagir din Wani Naushin da Kila sai Bakinsa ya Zubda Hakora Lura da Hakan da yayi ne yasa yamtsa da Sauri yana Fadin”Daga mgana..? Allah ya Huci Ran angon Sajida ya Dade..!
Yake Fada yana Dariyan ganin yadda Fuskar Imran din tayi saboda Haushi Kwafa yaja kafin yace”Banza Dan saka ido..Ai daka Tssya Daka gane Ango yau..!
Yafada yana kara Sakin wani Tsakin ya koma gefe wayarsa ya kara Fiddowa Shuru bai ga Sakon Inteesar ba Ransa sai ya kara baci,Ga Sagir Sai Dariya yake yi mai Banza Dashi yayi bai bi ta kansa ba Duk da Sunan Sajidan Dayake ambata kamar ya Juya ya Watsamai mari da ashariya haka yake ji.
Sagir ganin Imran din bai kula sa ba sai ya Daina ya Matso kusa dashi ganinsa sai Bini Bini ya Duba Waya yana Sakin Tsaki ya Fahimco wani abu na Damunsa Cikin Lallami yace”Meke Damunka Imu..?na lura dakai kamar Miskilancin naka yau yafi na koyaushe..!
Imran yayi kamar bai jisa ba Sai chan yace”Ina Ruwanka..?
Sagir ya kada kai yana Fadin”Au Daga Tambaya..? Nima Allah karamin da nake kokarin jin Damuwarka kaga Tafiyama ka Dade damuwar bata Kashe ka ba Tunda kai baka son Abun Arziki ba..!
Yafada Lokaci Daya yana wucewa Shagonsa ya shige Daman Tun dazu suna Tsaye su Auwal din suka Dawo suka zo suka Bude shagon da kallo ya Bisa shifa bama Sagir ne agabansa ba..Damuwar Dayake ciki tafi karfin ya Tsaya yana bi ta kansa wanda yasan anjuma nan zasu Shirya kansu.
Ganin Shuru Shuru bai jita ba yasa ya yanke Shawaran Kiranta Duk da baya son Kiran nata ammh Zuciyarsa ta Rinjayi gangar Jikinsa Daya kasa Hana kanshi Sai dai ya gansa kawai yana Kiranta,Zuciyarsa Bugawa take da Sauri da Sauri so yake ji Muryanta ko ya Samu Salama,Sai dai me yana Kiran nata ta shiga yaji Call Waiting ma”ana Tana amfani da wayar kenan Wani Rugugin bala”i Imran yaji sun Saukomai acikin kansa Har wani Jiri Jiri yake gani bai Katse Kiran ba Sai da ta yanke da kanta,Kansa ya Dafe yana jin wani Daci Daga kasan Ransa Wato ma Tana ganin Sakonsa Tayi banza Dashi..? Da ganga taki kulasa..?kan Bala”i bata san Waye Imran ba Ya zama Dole Abunda yake so ayimai in kuma akaki yimai ba Zaman Lafiya.
Wani Tunanine ya shiga kansa Kodai da wannan Banzan gayen take waya ne..? Domin ai yaji Daada ta bashi Umarnin ya Nemi yardanta in ta Amince shikenan Tuna Haka da yayi sai da Idanuwansa suka Sauya Launi Kirjinsa ya Fara tashi yana komawa da wani bakin Kishi da shi kanshi baisan yana da shi ba Tana Waya dashi Shine tayi banza Dani..Ina Bata isa ba..Shima khamis din bai isa ba Inteesar bazata taba Zama nashi ba Har Abada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button