GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


Washegari ta kama Lahadi ne Tun Safe Inteesar ta tashi da Murna Domin Tayi mgana da Daddy yace suna Hanya shi da Ya Basheer ammh sai sun gama abunda ya kawosu zasu zo nan gidan Maman,Gabadaya ta kasa Zama Saboda Murna Mama natayi mata Dariya Ya Basheer na son Alala shi tayi mai Abba kuma Tuwon Semo Tayi mai miyar Kubewa Bushashiya Sai wajen 1pm ta Gama komai ta shiga wanka ta Shirya ta Zauna zaman jiransu Ko abinci ta kasa ci,Mama sai Fada Take mata kan ta Rika cin Abinci ammh ta kasa ita Haka in tana Zakwadin Abu abinci ma Baya gabanta.
Duk bayan Mintina sai ta Kira Daddy taji ko sun gama abunda ya kawosu suna Hanyar zuwa Gidan Mama sai yace Mata A””a har ta gaji da kira ta Hakura tana ganin kamar bazasu zo bane Har Munari ta Kirata Tana Tamnayanta ko Daddy ya iso tace eh Yana cikin kamo sai dai basu kariso ba
Tace to bara tayi wanka gatanan zuwa,Da haka suka rabu kuma sai ta Jita Shuru karfe 3:00pm na rana Daddy da Ya Basheer suka iso ho zo kuga Murna wajen Inteesar ta makale Daddy gamgam Tana Fadin tayi kewarsa Hakama Ya Basheer ta Rumgumesa shima ya Riketa Cikin Farinciki Mama itama Murna Duk ya kamata ta rssa ina Zata sakasu haka take akwai son Yan”uwanta sosai.
Bayan sun zauna sun sha Ruwa da Inteesar ta gama jera musu aka Fara gaisawa Sagir na gefe Daman yana Shago yaga Isowarsu shi yayi musu Jagora zuwa Cikin Gidan.
Mama da Sagir suka basu Waje su gana Da Inteesar nan ta zauna tana Zubamai Shagwaba da Tambayoyin ina Umma..!? Talatuwa..? Anty Hauwa ina su Abiden ya Basheer gajiya yayi da amsa mata yayi Shuru yana cin Alalansa Dakyar ta bar Daddy yaci Tuwonsa  yaci sosai jin Intee tayi mai,bayan ya gama ya Kira Umma ya bata sukayi mgana inda tace ta bama Dadynta sakon Dambun nama da Kayan Snkas,Roba Biyu ne Daya nata Daya na Mama nan tace ma ta kaima Mama Wayar suyi mgana nan ta Fice Tsakar gida ta Mikama Mama Wayar sukayi mgana da yar”uwanta sun Dade suna mgana barin ma mganar Kan auran Yarinyar Wajen kaw Bala ne nan da Wata Biyu.
Daddy sai da sukayi Sallar La”asar sukayi Shirin Tafiya bayan ya cika Mama da kudi Tana ta godiya kuma sun sauke mata kayan abinci Inteesar harda Lemonta Freshyo,Katan uku Daddy ya Taho mata dashi ya bata 20k a Hannunta Ya Basheer 10k ya bata Kuma ko Sati ba”ayi ba Daddy ya Turamata 20k ta bankinta ko Tabata batayi ba.
Sam ta manta da Munari sai da Su Daddy suka fito ta Rakosu ita da Sagir Daddy ya Kalleta yana Fadin”Banga Kawarki da muke jin Labarinta ba Intee..Ko bata nan ne..?wanda kikace yayanta na kai ku makaranta..?
Sai alokacin Inteesar ta Tuna da Munari ta Bude baki Tana Fadin”Laa..Daddy kaga zuwanku ya sa na manta..Munyi mgana da ita Tun dazu tace zatayi wanka tazo bari na kirata naji plz Daddy..!
Daddy ya Murmusa kafin yace”Anything For my Angel..!
Ya Basherr na gefe yana waya da Anty Hauwa Tana Tambayansa suna Hanya ne yace yanzu dai zasu taso.
Inteesar Tana ta Kiran Munari Tana Ringing bata Dauka ba ganin yadda ta Dakuna Fuska ne yasa Daddy ya kalleta yana Fadin”Baki same ta bane..?
Inteesar tace”Na sameta bata Dauka ne Daddy..!
Tafada cikin Shagwaba ya Basheer Daya kamalla wayarsa ya Kalleta yana Fadin”Sai ki bari Next time in muka Dawo..Yanzu pass4 kuma kinsam Kaduna muka Nufa..!
Inteesar ta Marairaice Tana Fadin”Kai ya Basheer..Tafa ce zata zo wlh..Gidansu nan nan kusa Daddy naje na Kirata..?Itama tana so Taga Daddyna ne fa..,!
Kafin Daddy yayi Mgana Basheer yace”No Daddy..Lokaci na tafiya in ka Biyema Shirmen Intee zamu yi Dare a Hanya..!
Sagir yayi Saurin cewa”Ai gidan ba Nisa..Nan fa kusa ne..!
Daddy ya kallesa yana Fadin”Ai mun Riga mun yi Daran Basheer barta taje ta Kirata..!..
Basheer bai ce komai ba kada kai kaawai yayi,Inteesar taji Dadi ta Fara Tafiya Tana Fadin”Tanque Daddy..!
Gudu Gudu Sauri Sauri Take Tafiya Har ta isa Gidansu Munari Saboda Saurin Datake yi ne yasa bata Tsaya kula mganar Iro ba shi kuma yana so ya gayamata ba kowa agidan sun Fita Har da Abba Amotar Yusuf.
Tana ta Sallama Bayan ta Turo kofar Falon ta Shigo ba”a amsata ba Tayi mamakin rashin ganin Abba zaune yana Kallo ko yana Karatu Falon tabi da Kallo alamun Shuru ba kowa Tayi Tsam kafin aranta tace ko basa nan ne..!
Tuna haka yasa kawai ta Juya Zata koma sai taji Karan Bude kofa Tana Juyowa suka Hada ido Hudu dashi.
Imran ne yana Tsaye yana kallomta Yana Sanye da Dogon Wando baki da Wata Farar riga amles,Hannunsa Daya Cikin Aljihun wandonsa Dayan kuma Karan Sigari ce tana kunne Hayakinta na Turiri.
Gabanta sai da ya Fadi Data gansa Haka Duk gabar jikinsa tana waje sai ta gansa wani Kato dashi.
Baya taja cikin Rawan jiki zata kara Juyawa Taji yace Cikin Kaushin murya”Wa kike nema..?
Yafada Lokaci Daya yana wuceta zuwa Saman Dining.
Ruwa ya Dauko a wani Jug ya samu karamin Kofi ya Tsiyaya ya Dago yana kallonta Daga sama Har kasa Lokaci yana Kurban Ruwannsa Hade kuma da zukan Hayakin Sigarinsa..
Inteesar Dataji gabanta na Dukan Tara Tara bakinta yayi Nauyi ta kasa mgana.
Shi kuma Ransa ne ya Fara baci da Yarinyar lokaci Daya cikin Dakiyarsa yace”Ke kurma ce..? Ina mgana kina min banza..I Hate it..Ya zama Dole in nayi mgana abani Amsataaa..!
Yafada cikin Tsawa da Daga Muryan Dayasa da Sauri ta Dago Tana kallosa Itama Mamakinsa take ji yadda yake Zukan Taba Kuma yana Kurban Ruwa anya wannan yasan abunda yake yi kuwa..! Itafa duk sadda zata gana yana Shan Taba ne ko Lafiyarsa ma Bayaji..?
Ganin kamar ya fara Takowa ne yasa da Sauri tace”Ina yini..Wajen Munari nazo..kuma inta kiranta a waya bata Dauka ba..!
Kwayar idonta yake kallo yaso ne ya isa gabanta yayi kwallo da ita sai kuma yaji ya kasa Muryanta da Idanuwanta kamar wani Kaifin Dafi ne garesa sai yaji ya kasa komai.
Dakyar ya iya kauda kai yace”Bata nan..!
Kallonsa Tayi ta gefen ido kafin tace”Ina taje..? Abba fa da Anty Safiya..!?
Yaso ne ya Daka mata Tsawa sai kuma ya kasa Cikin kosawa yace”Suma..!
Daga haka ya tsuke bakinsa Cikin mamaki take kallonsa tace”Suma basa nan..?
Kai ya gyada mata Domin ta Fara Takuramai da mgana.
Abun sai ya bata mamaki tace”Ina sukaje haka..?
Yana jinta yayi kamar bai jita ba Har ta Juya sai taji yace”I don”t know..Kamar dai sun shiga cikin gari ne..yama sunan wajen wasannin nan.?
Da sauri Inteesar ta waigo tace”Shoprite..,!
Kofin Hannunsa ya Ijiye bai yi mgana ba Inteesar an samu waje sai ta karkace tace”Wato Family Outing sukaje yau kenan..? To kai me ya Hanaka Zuwa..?
Da sauri ya Dago Jajayen Idanuwansa yana Kallonta Sauri ja da baya Tayi Domin Warin taban ya Isheta zuciyarta ta Tafara tashi kuma ba Halin Toshe Hanci.
Cikin kallon kin Rainamin wayau yace”Ni nayi miki kama da yaro ne Dan goyeko mai Tatata..?am not a Boy kin gane..?
Yadda yayi mganar kamar ta saka Dariya sai ta kanne nan kan Dinning din ya Mutseki Sigarin ya wuce zai shiga Dakinsa,bayansa tabi da kallo Haka kurum taji Tsausayinsa itafa har ga Allaj kallon mara Lafiya take mai.
Cikin gwarin gwaiwa tace”Don Allah ka Daina shan Sigari bata dace dakai ba Sam..!
Cak ya Tsaya Daga Dora Hannunsa kan Handle din bedroom dinsa ya Waigo yana kallonta
Sagir da yusuf suna Fadamai shan Sigari bata dace dashi ba bai taba jin mganar ta shigesa ba sai yau.
Ba karamin Juriya tayi ba wajen Kallon kwayan idanuwansa ba ta Cigaba da Fadin”Ba domim Iyalanka ba..Ko Domin Lafiyanka Don Allah kabari..nasan ka sani sai dai zan kara Sanar dakai a likitance Shan Sigari Tana Illah ga Lafiyar Dan”adam..Domin Lokaci Daya take yima Huhun Mutum illah..!
Tana Gama Fadin haka ta Juya da Sauri ta Fice jin wayarta na Vibration kuma ta Tabbata ko Daddy ko ya Basheer ne suna jiranta.
Ficewa Tayi Daga Falon tana Sauke Numfashi Miyau ta Zubar Jin Hancinta na Budewa Tana so ta Shaki iskar Haraban gidan ne ko Hancinta zai Daina Shako mata Warin Sigarin Dake Neman sakata amai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button