GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


Kaduna

Da Ihunta da Murnanta ta Shigo Falon Tana kwala kiran”Umma..! Umma..!
Umma Dake Kitchen Tana Hadama Alhaji Tea dinsa taji Kakakin kiram suanta da Inteesar keyi ta Fito Tana gyara Daurin Zanin Atamfarta Golding Dake jikinta.
Cikin Takaichi tace”Wai ke Inteesar yaushe zaki koyi Sallama ne ba ihu ba..?
Tura Baki Inteesar din Tayi kafin ta Zube kayan Hannunta kan kujera Tana Fadin”Kai Umma ba nayi sallama ba..Ki Tambayi ma ya Bashir..!
Tafada tana wani Diddira kafa na Shagwabbanun yara.
Tabe baki Umma Tayi daidai Lokacin da Bashir yayi sallama ya Shigo,Umma ta amsa mai ya kariso Falon sai da ya Zauna ya Fara gaisheta ta amsa Tana Fadin”Ya ka baro su Hauwa”un..? Dazu yaranan sai kuka suke Shine da Babanku zai kai Inteesar gidan Inno nace ya biya da ita ta kaisu wajen Mamansu..!
Yana yar Dariya yace”Umma Rigiman yaye ce kawai..Chan ma sai Rigiman suke mata..!
Umma tace”Daman sai a Hankali..Tana ma kokari kai ne nace maka ka samo mata wacce zata rika taimaka mata..!
Bashir yace”Umma itace fa taki..Ammh nima nayi mata mganar..!
Umma tace’Ai shikenan Tunda bataso..Daman Wahala Renon yara ake jiyemata ga kuma Laulayin sabon Ciki..! Jin haka yasa bai yi mgana ya Sadda kansa kasa Domin Bashir akwai kunya.
Sanin haka yasa Umma bata kara mgana ba ta maida Hankalinta kan Inteesar Dake ta Faman Bule Lodojin Data Shigo Dasu bakinta kamar gonar Auduga saboda Murna..!
Umma tace”Ita kuma wannan ina ka samota..? Naga sai Murna take me ta samo ne?
Bashir yace”Umma Daddy ne ya kirani yace naje na Daukota gidan Kawu Salisu na Daukota..!
Umma ta Rike baki Tana Fadin”Au har chan sai taje kenan..Nifa Daga gidan ka naceta Hau adaidata ta karisa wajen Inno Tana min mitan kada Inte tatafi Batazo mata ssllama ba..Dama bai Dade da Dawowa ba sai Mitan yake Inte bata dawo ba yafa gaji wai zai kara Fita ya Daukota nace sai dai ya kiraka..!
Kafin Bashir yayi mgana Inteesar ta Daga wani maroon dim Hijabi mai kyau ta kara ajikinta Cikin Murna tace”Umma ni fa yar gatace..Kalli kiga kayan da na samo..Wadanam Hijaban Anty Hauwa ta bani kala Biyar tace na Zuwa makaranta..Wadanan Gyale da Takamim kuwa Mamarsu Nasara ta bani Kawu Salisu kuma ya bani 10k Umma Inmo ta bani Gwarin da Kuli da yawa da yaji Data Dakamin,Mallam Babba kuma ya bani 5k Umma..”
Ta karishe Fada Cikin Bayyana Farincikinta tana nuna ma Umma kayan da kudin Dake hannunta.
Umma ta kariso tana Fadin”Nagani Kin gode..Ammh meyasa baki barma Mallam Babba kudinsa ba..?
Inteesar ta Tura baki Tana Fadin”Shifa ya bani sai naki karba..Kuma ance ma raina kadan..!
Umma ta kaimata Dundu Tana Fadin”To uban nawa ne barawon..? Intesar na Dariya ta gaoce Bayan ta Tattara kayanta Tana Fadin”Nifa ba haka nake nufi ba.Ni bari ma naje na Nunma Daddy…Umma Daddy na Ciki!
Umma tace”To mara Hankali yana Hutawa kya Bari da safe ko..?
Inteesar tace”Umma da safe ba Tafiya zamu yi ba..,?
Umma tace”Kafin ku taho..Tunda ba Sammako zamu yi ba ai ba yaki bane..Ba kuma kanki Farau jami”a ba..!
Bashir ne Dake Dariyansu Tun Dazu yace”Umma Dake za”a Raka Autan Daddy ne..?
Umma tace”eh.Da nace bazani ba Tunda tace ni ba uwarta bace..Sai nace bari dai naje ko na ga Yaya Amina mun dade bamu Haduba ni ban je ba kuma ita batazo ba ko zuwanta na karshe iyakarta gidan Inno,ni kasan Lokacin bama nan mun Tafi Dukku ni da Alhaji da Inte!
Inteesar Dataji da Umma za”a je kaita kano ta Daka Tsalle Tana Fadin”Da gaske Umma Dake zamu Tafi..?
Umma tace”Ba don Halin ki ba.?Ihu ta saki kafin tace”I love u Umma..!
Ta kwashi gudu da kayanta Zuwa Dakinta Umma ta rakata da kallon kafin ta Girgiza kai tace”Kai bansan yaushe yarinyar nan zatayi hankali ba Allah ya Shirya..!
Bashir ya amsa da Ameen yana Fadib”Zatayi Umma..Bari karatun ya kamkama..!
Umma tace”Allah yasa..!
Ya mike yana Fadin”Amern Umma bari na koma ki gaida Daddy Gobe da Safe kafin ku wucen zan biyo muyi ssllama da Auta..!
Umma ta mike Tana Fadin”Shikenan ka gaida Hauwan da su Abiden..Allah ya Tashemu Lafiya..ya amsa da Ameen yana Ficewa Daga Falon Kitchen ta koma ta Sauke Ruwan Tea din Dayaji Na”a Na”a ta samu mug karami ta Zuba akai sai ta saka Siga kadan da Lemin Tssmi ta Dauka ta Fice zuwa Dakin Megidan nata.

Shakira
3/22/22, 23:03 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)

        *🅿�6*

“Da misalin karfe 8:40am na Safiyar Ranar Laraba Daddy da Umma da Inteesar suka kama Hanyar Kano Booth din Daddy cike da Kayan Inteesar kamar wacce in tatafi sai bayan Wata Shekara zata Dawo saboda Uban kayan Data Diba akwatuna Biyar Shake da kayan sawa da Takalma sai kuma Sauran kayyakinta na Kwalama da kayan kwalliya.
Inteesar na Gidan Baya Umma ce agaba Fushi take yi Sosai bakinta kamar ya Fado Fuskarta a Dakune saboda ta Shiga gaban Mota Da zasu Taho Umma ta Rankwasheta akai ta Fito da ita tace sai dai ta Shiga baya don Ubanta Daddy ransa ya sosu ya Fara Fada yana Fadin”Salaha kina fa min abunda bana so..? Ina wani abun Duka anan Menene abun Damuwa Domin inte ta shiga gaba..? Ba yarki bace ke sai ki koma Baya ki Zauna..!
Kallonsa kawai Umma Tayi kafin ta kada kai Tana Fadin”Wlh Alhaji ba Domin agida na Haifi Inteesar fa Tsab zan ce ba yata bace An Sauyamin ita a asibiti ne..Kuma inda yau bani na Haifeta ba Kishiyar uwa nake gareta Tsab zan ce kana Fifita komai na Yarinyar akaina..!
Tafada Tana bayyana irin Takaichinta game da abubuwan da Alhaji yake yi komai Inteesar Tayi daidai ne koda kuwa abun Fada ne da Sakarci.
Shuru yayi bai ta amsa ba sai ma Juyawa da yayi bayan Motan yana Faman Lallashin Inteesar din wacce saboda Sangarta Harda kuka batayi Shuru ba sai da ya bata wayarsa Zata yi game Sabuwar Tata saboda Sauri bata Tsaya kwashe Apps din Datake da shi a acikin Tsohuwar ba Kuma ta manta ta agida Duk kuwa da yadda ta Shirya kayanta Duka.
Umma na gaban Mota ta kallesu ta watsar Da karamin Tsaki Inteesar ta kalleta Tana Tura mata baki acikin Ranta Tana ta kunkuni.
Bata kara bi ta kansu ba ta maida Hankalinta kan karamin azkar din Data Taho dashi Ba saboda komai tace zata Raka Inteesar ba din ba saboda Yaya Amina ne ta kwana Biyu bata leka ba kuma Tajata gefe ta bata Umarnin Da Zarar Inteesar tayi wani Rashin Ji ta rika saka Bulalane tana Jibganta kada ta Dauki wannan Sangartanta ta da Ubanta ne kadai zai iya da ita.


GOMBE STATE..Dukku local goverment
Area:Balikaje

A karamar Hukumar Jahar Gombe,Wato Garin na Dukku, awata anguwa da ake kira BALIKAJE yau anta tashi da sanyi sanyi kadan na Wucewar Damina da Shigowar Sanyi
Acikin anguwan daga farkon farkonta akwai wani Katafaran gida wanda kallo Daya zakayi mai ka Fahimci gidan ba fasalin ginin yanzu bane Tsohon gini ne Daya samu gyaran Masihan magina da kuma wadanda suka san Zanen Fasalta Gini yayi kyau har ya kawatu.

Tana Daga Cikin kuryan Dakinta Tana Zaune kan Darduma Misalin 9:40am na Safiyar Ranar laraba Idar da Sallar Walhanta kenan Carbi ne a Hannunta Tana ja Lokaci Daya bakinta na Motsi Wata Farar Dattijuwa ce mai akallah Shekaru 82 a Duniya yanayin Jikinta Tana dan Kiba,da kuma Tsawo Kallo Daya zakayi mata ka Shaida kirar Fulanin Dukku ne duk da Tana daga Zaune ne,
Duk da Shekarin sun ja ammh Farar Fuskarta da karan Hancinta basu Boye kansu ba..Da tsantsan kyau da Zati irin nata wanda in da zaka ka ganta Lokacin Kuruciya sai ka Tsaya Jinjina kyau da Zati irin na wannan Tsohuwar Lokacin Kuruciyarta.
Gefe gefen Fuskarta Duk Karkasan Gashi ne gashin nan yayi Fari Fat hakama Gemunta akwai Tsirarrun Fitowar gashi Haka Halittar take mai yalwar Gargasa ne hatta Hannayenta gasu nan sun kwanta Duk da kuwa Ta kwana Biyu a Duniya uwa uba gashinta kanta Dake Dunkule shima ya koma Fari Saboda Shekaru.
Sai dai aduban Farko in kayi mata sai ka Fahinci Tarin Jin Dadi da Hutu take Tattare da ita Duba da Dakin Datake Ciki da suka ji kayan alatun kawata Daki na Zamani kamar ba Dakin Tsohuwa ba
Sai dai kuma yanayin Fuskarta da yadda ta kurama waje Daya ido Zaka Fahimci Duk da wannan Jin Dadin wani abu wanda Ya Dade yana Murkusanta yana Damunta acikin ranta wanda Har ya Bayyana kan Fuskarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button