GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Inteesar da Wuri Tayi barcin Tana idar da Sallar Isha”i Ta ci Danbun namanta da Umma Tayi mata,Ta hada da Lemo har mamana mganar bazai taso mata da Daddare ba..?Umma tace”Wannan ki kyaleta inda kika barta Shan zaki da kayan Kwadayi nan tafi auki babu abunda yake mata..!
Mama tana Dariya tace muna da lafiya ne,Inta dai Intee Kayan Barcinta ta saka ta Bi Lafiyan gado sai barci,ta bar Umma da Inna Amina suna ta Hira Sama sama take jin suna waya da Inni da Mallam Babba,Sai kuma taji Ya Bashir ya kira ta wayarta Data Manta da ita saboda gajiya Umma ta Dauka sukayi mgana har tabama Inna Amina suka gaisa.
Kusan Raba Dare sukayi suna Hira kafin su kwanta Umma kusa da Inteesar ta kwanta,Ita kuma Mama ta yada katifa ta kwanta.
Da asuban Fari suka tashi..Mama ta Fita waje ta saka musu Ruwan wanka kana tazo tayi sallah Bayan ta idar suka gaiggaisa ta kara Fita Bayan Fitantane,Umma ta karayima Inteesar fada tana Nuna mata ta Rika Taimakon Mama da wasu ayyukan Inteesar tace Insha Allahu.
Mama tayi musu abun karyawa bayan ta juyo musu Ruwan wanka Umma ta Farayi kana Inteesar,suna gama Shirya suka iske kayan Karyawansu tea da Buredi da Soyayyah kwai sai Umma datace Kosai take so da koko suka zauna suka karya atare,Suna Hira cikin Sha’awa Inteesar bata wani ci Abun kirki ba Bata iya cika Cikinta in Zata Fita wani waje ta Dade,Umma ta matsa mata sai da ta saka wata Sabuwar amtafa da Ummanta Ta Dinkamata Doguwar riga Chiganvi mai kalan green ssi tayi amfani da green din mayafi da Takalmi da Jaka.
Sagir ma yayi wanka yana Dakinsa yana karyawa sanda Daddy ya karisowa shi ya Fita yayi mai Jagora zuwa Cikin gidan suka gaisa da Mama Da Umma lokacin sun gama suka Tashi suka Fara Shirin Tafiya.
Daddy ya duka har kasa yana Damka Amanar Inteesar wajen Mama tace ta karba Tayi alkawarin Zata kula da ita kamar yadda Zata kula da Sagir.
Yaji Dadin haka ya Dire mata kudi 30k tace bazata karba ba ya Fice bai Dauka ba.
Umma ta Dauka ta bata bayan ta Hada mata da 10k tace ta Rike ahannunta Mama nata Godiya Inteesar kuma sai Hawaye kamar sallaman kenan bata Dauka haka abun yake ba da bata Zabi Karatu a Kano ba.
Har waje Mama ta rakasu tana Godiya Tana Daga musu Hannu.Umma ta shiga Gaba Inteesar da Sagir abaya wacce ke ta Sharan kwallah Daddy na gaba yana Tuki hankalinsa na kanta kamar shima ya saki kukan.
Daganan basu Dire ko”ina ba sai Cikin Jami”ar Bayero,Sagir bai Rabu dasu ba sai da komai na Inteesar ya kamallah Zata Fara Daukan karatu Daddy har bakin Hall din inda yan Department din su ke karatu suka Rakota Wato Itama Zata karanta Fanni Tsumi da Tanadi wato Economics.
Inteesar Tayi kuka kamar Ranta zai Fita ta makalkale Daddy taki sakinsa Harta Umma sai da ta sakata kwallah,dalibai suna ta wucewa suna ganin abun mamaki kuka a jami”a..? Kamar wata yar sakandiri.
Dakyar ta saki Daddy,bayan ya Share mata Hawaye,Ya lallasheta kana ta juya ta shiga Hall din Tana Daga musu hannu.
Bayan ta Shige ne Sagir sukayi sallama yace shima zai Shiga karatu ne,Daddy ya kara Damka Amanar inteesar a hannunsa yace bakomai yanzu hakama Umma ta bashi Lambarta zai jirata su gama karatu su koma Gida Tare kafin ta saba Daddy yaji Dadin haka 10k ya bama Sagir ya karba yana ta Godiya Daganan sukayi sallama suka Shiga Mota suka kama Hanyar kaduna shi kuma ya wuce Department dinsu yana ta Sauri Tunda yasan an Shiga Tun Dazu!
Wayarsa ya Fito da ita yana Dubawa yana tafiya,karamin tsaki yaja ganin har yanzu bai ga kiran Imran ba alhalin tun safe yake kiransa bai Daga wayarsa ba Jiya kwata kwata basu hadu ba yadai kirasa yace ya Turamai lambar Baba Manu ya tabbata ya kai mai kudin Da sukayi mgana ne,Yasan waye Imran in yace zai yi abu baya saba alkawari zai yi din ne yana so yaji yau su Baba Manun zasu je neman auran..? Ammh bai Daga kiransa ba Shiyasa har ya karisa cikin ajin yana ta sskin tsaki.!
Abunda Sagir bai sani ba jiyan Banki Imran yaje ya Ciro kudi a Bankinsa wanda baya amfani DashivSai Lokaci bayan Lokaci,Sai kuma yaje Banki ya Cike Form yake iya Fidda kudi Gabadaya kudin bankin nashi Dubu Dari uki suka Rage bai yi mamaki ba yau da gobe bai bar komai ba yana Cire kudi Lokaci Bayan Lokaci yayi Hidimansa kanar siyan takalma,Kaya da Sauran abubuwan da baza”a rasa ba!
Sauran dawaniyar Yusuf ke gudanarsu da albashinsa in ya gagara sai ya taba kudin Dake Bankin Abba ko na Marigayi Yayansu Nura saboda Dawaniyar Abba da Likitan Dake zuwa Gida Dubashi da kuma Dawaniyar mganguna,Ammh shi baya karba ko Naira Biyar wajen Yusuf da kudinsa Daya tara lokacin Daya fara aiki a inda suka zauna yake amfani.
Bashi da Zabi Dubu dari Biyu 200k,ya ciro ya Dawo Gida a kuma Lokacin ya kira wayar Yusuf yace ya sanar ma Safiya ta Fadama Babanta mgabatansa suna tafe gobe,ya kashe nan take kuma ya kira Sagir yace ya bashi Lambar Baba Manu yana Turomai ya kirashi yafadamai sunansa yace ga kudin nan zai kawomai shi kuma yace ya bari zuwa anjuma yanzu yana gareji ne.
Haka kuwa bayan Isha”i Imran yaje yakai ma Baba Manu kudin yau ko Rakiyar Sagir bai nema ba.
Yusuf kuwa bai yi mamaki ba Sanin Halin kaninsa Duk Abunda yace zai aikata baya Runtsawa sai ya Tabbatar dashi..Safiya ya kira ya Fadamawa,Sai taji abun kamar wasa Cikin Tsoro Ta sanar ma da Mahaifiyarsu Hajiya Mero ita kuma ta sanar ma da Alhaji Alhassan bayan ya Dawo ya Cije a lebe a Fili ya Furta.”Allah ya kawo su lafiya..!
Domin ya gama Shirya abunda zai yi goben da Zarar sun zo..Shi da kimarsa da mutumcinsa agari bazai bari saboda Dalilin Safiya wannan Shegen yaron Mara kunya ya Zubarmai da Daraja ba.!

Ba na fara saka Lokacin Posting bane kamar yadda wasu ke Tunani ba,Ni bana Ware wasu ranakun Lokacin Posting,Ina yi duk rana alokacin da na samu dama da Lokaci sai dai in Rashin Lafiya ko ciwo ko wani Uzuri,Domin daman kana naka ne Allah yana nashi na Allah kuma shine Daidai Jiyan nan na wayi gari bani da Lafiya shiya kawo Tsaikun Rashin posting dina ajiyan..Ina ganin Comments dinku ina matukar godiya Yan Wattpaddian Voting dinku yayi kasa fa ya kamata ku kara kaimu nayi muku alkawarin Bazan baku kunya ba Insha Allahu

Shakira..
3/22/22, 23:03 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)

       *🅿�08*

“Asalin sunanta MARYAM MUSTAPHA HAMISU DUKKU ne Saboda taci sunan Mahaifiyar Babanta Daada yasa ake kiranta da INTEESAR.
Alhaji Mustpaha Hamisu Dukku Haifaffan garin Dukku ne na Jahar Gombe,ya kasance d’a na uku a jerin ya”yan Daada Maryam da Mahaifinsu Alkalin Kotun Musulunci Alhaji Hamisu Dukku.
Hajiya Maryam(Daada) Haifaffiyar garin Dukku ce ta uwa Data Uba Bafullatanan Dukku Ta gaba da Baya,Auran Zumunci ne tsakaninta da Megidanta marigayi Alkali Hamisu Dukku,Domin alokacin Makoci Tamkar Dan”uwa yake wajen makocinsa iyayen Daada da iyayen Hamisu Dukku sun yi Zaman makota shekaru masu yawa wanda Sanadin haka yasa suka Zama Tamkar yan”uwa wannan Dalilin ne yasa suka Hada auran ya”yansu Wato Maryam(Daada) da Alkali Hamisu Dukku.
Maryam(Daada) bata yi Zurfi a Karatun Boko ba iyakarta Sencondary Alokacin ma agidan Mijinta Alkali Hamisu Dukku Tayi Candy,Tayi aure da kananan Shekarunta,Saboda Tana da Shekara Goma sha Shida ne alokacin.
Alkali Hamisu Dukku,yayi karatun Zamani Dana Boko ya tafi Jami”ar Abu dake Zaria inda ya karanci Shari”a Low,Bayanan yayi Degree dinsa na Farko sai ya Dora bayan haka ya Hallaci Courses masu yawa akan Abunda ya Shafi karatunsa agidansu Shi kadai ne yayi karatun Boko mai Zurfi Duk da basu da yawa shi ne kuma Babba.
Yayi aiki a mtsayinsa na Cikakken Lauya ya taka mataki mataki na Rayuwa sun Fara zama da Daada a garin Dukku agidan iyayensa inda ya gada Tunda Lokacin Allah yayi ma Mahafinssa Rasuwa kafin ya samu aiki a babbar katun Jahar Gombe ya mallaki gida da Motar Hawa ya Dauki matarsa suka koma Chan da Zama..
Sun koma ba Dadewa Daada ta samu Ciki,kuma yana bata Wahala sosai Dalilin dayasa Alkali yasa aka nema mata yar aiki kenan Allah ya Hadasu zama da Baba Asabe Tun tana da Danyen Shekarunta Ita take Taimakon Maryam(Daada)da abubuwan Cikin gida,Alkali Hamisu Dukku da Matarsa Maryam(Daada) suka Rike Asabe Tamkar wata jininsu ko nace Yar”uwansu.zuwa Lokacin duka sun rasa iyayensu saidai yan”uwa da abokan arzuka.
Kabir shine Babban Dansu sai Abubakar,sai Mustpaha sai Fatima (Bintalo) sai auta Maimunatu,azuwa Lokacin da daya Tara ya”yansa Biyar ya samu Dukkan Cigaban Rayuwa,Asalin Komawarsu Dukku samun Alkalin alkalai na Babban Kotun musulunci Dake Dukku ne yasa yayi Ginin Zamani ya Tattaro Duka iyalansa suka Dawo nan da Zama Dindin Daman shi Alkali Hamisu yana da Kishim kansa yafi Sha”awar Zama a Kauyensu Fiye da Ko”ina To itama Maryam(Daada) domin duk inda zasu je basu da kamar Dukku.
Alkali Hamisu Dukku bai bar Gidan Duniya ba sai da ya kwafa ya”yansa suka samu Wadattacen ilimin Zamani Dana Boko,Kabir Shine ya gado sa shi ya karanci Harkan Shariya,Abubakar kuma ya kasance Malamin makaranta ne kowa yasan Burinsa Tun yana karami Shiyasa Alkali Hamisu yake mai Lakabi da MALAMI..!
Bai kuma bar gidan Duniya ba sai da ya aurar da duka ya”yansa Daga matan har mazan
Bintalo Tana aure anan cikin garin Gombe,Tana auran wani ma”ikacin Fire service na Jahar Gombe kuma agidansa tacigaba da karatunta ayanzu haka Lacture ce itama anan Jami”ar Gombe Yayanta Uku Dayake bata cika yawan Haihuwa ba saboda Karatunta,Siyama da Hamida sai Hauwa”u Duka matane kuma Suna Gijajen mazajensu sunyi aure suma sun Haiyayyafa.
Sai Maimunatu Tana chan Garin Bauchin yakubu Tana auran wani Soja ne,Ita tana da ya”ya sun kai bakwai,Manyan ya”yanta itama mata ne sai Mazan Sa”id da sadam.
Sai kabir wanda ke Zaune a chan Birnin Tarayyah Abuja Yana mtsayin Cikakkem Lauyan gwannati ne,yana da mata Daya Asma”u wacce ta kasance Diyar Masu kudi ce Diya ce ga Alkalin akalai na kasa gabadaya,Sun hadu ne a wani Course Dayaje karanta a Washington,Itama taje Dukkansu Lauyoyi ne suka Fara Soyayah har takai su ga aure duk da Mtsayinta da Nasabarta Barrister Asma”u taga Barrister Kabir Hamisu Dukku kuma tayi na’am Dashi Mahaifinta bai hanata abunda take so ba Tunda su yan Boko ne abunda duk kake so Shi zakayi.
Dagashi har matarsa Lauyoyi ne masu Zaman kansa,Tsarin Gidansu tsarin Gidan yan Boko ne gaba da Baya Gabadaya Haka suka Tsara Rayuwarsu Shiyasa ko a tsarin Haihuwa ya”yansu Uku ne Biyu mata daya Namiji Babba ne Namiji mai suna Hamisu wanda yaci sunan Marigayi Alkali Hamisu Dukku suna Kiransa Khamis,Yana Chan Anambra inda yake aiki a mtsayin Sojan Ruwa Navy.
Sai kannensa Guda Biyu Sajida da Umaima wadanda Tazara ne mai Nisa a tsakaninsu dashi..Hakama Tsakanin Sajida da Umaima akwai Tazaran shekaru kamar Hudu haka.
Sai Abubakar wanda Shima yayi aure kuma shima yana da ya”ya,
Sai Lokaci Daya aka Nemehi aka Rasa Shi da iyalansa Wadanda suke a Rayuwa a lagos,Tunda Shi Abubakar din Malamin Philosopy ne a University of Lagos achan baya kafin wata kaddara ta Gitta musu wacce Tayi Sanadiyar Faruwar duk abunda ya Faru.
sai Mustapah wanda ya kasance Dan kasuwa ne,kasuwanci ya karanta Domin Shine Burinsa,yana kasuwancin sai da kayan Mota,sai kuma yana Kiwo Harda gidan gona gareshi achan kaduna matarsa Salaha itama yar kaduna ce a Badarawa,Ita yar Talakawa ne ba masu Hali ba Inno da Mallam Babba,wanda yake sana”ar sai da Hatsi,su Biyar ne agidansu Yaya bala ne Babba,sai Yaya Salisu,sai yaya Amina sai Salaha(Umma)kenan sai karamin kaninsu Mudanssir.
Auran Soyayya sukayi Tsakanin Shi da Salaha Allah ya Hada auransu yana Zaune anan garin kaduna anguwan Sarki inda ya Gina katon gida,Allah ya sakama Kasuwancinsa albarka Shima din za”a sakasa Cikin Jerin masu Dashi.
Ya”yansa Biyu ne rak aduniya Basheer shine Babba wanda Bayan Haihuwarsa har sun Fidda rai da Haihuwa bayan Shekara Goma kana suka samu Haihuwan Inteesar wacce taci sunan Daada Maryam.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button