
Shakira..
3/22/22, 23:03 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1
Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janaftyâ¤ï¸
DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)
Jiya 16/02/2020 muka wayi gari cikin Rashi..Rashi mai girma na Rasuwar Wanda yar”uwarmu zata Aura Wato Habieb din Sadiya Sidi Said wannan rashi babban rashi ne gareta garemu gabadakidaya Ya Allah muna rokon ka ka jikan Habieb din Sidiya Allah ya kyautata Zuwansa Allah ya sadasa da Mala”ikun Rahma Allah ya jikansa da Rahmarsa Allah ka bama baiwarka Sidiya ikon da Zuciyar karban wannan Kaddaran nata Allah ya tallafi Rauninta Allah ya bata Dangana da Hakuri Ameen ya Allah
*🅿�09*
“Alhaji Alhassan Buhari Fagge Haka yake Tafiya cikin Sassarfa zuwa Shashen gidan nasa,hannunsa Rike da Sadakin Safiya,bayansa kuma Megadi ne ke Binsa Dauke da Kwalayen Cingam,da Minti da Dabino.
Bai ji yayi Nadamar abunda ya aikata ba ko kadan ba sai ma Wani Saukayau Dayaji,aduniya Alhaji Alhassan ya tsani Mutane na ganinsa da Daraja da kima,wannan kimar ta Zube,Uwa uba ga Matarsa da ya”yansa Da basu san me yake aikatawa ba ya Tabbata matukar Boyayyen Zunubansa ya bayyana Hatta Jami”ar Bayero sai ta Koreshi,Asirinsa ya gama Tonuwa Mutanen gari Dana anguwa Da suke ganinsa da kima Duk zasu daina Dalilin Safiya gwara ya mika musu ita chan su karata Tunda itataji Ta gani Shi akan Kada kimarsa ta Zube zai iya yin komai.
Bai damu ba wasu mutane ba,Inta Danginsa ne bai da Wata Damuwa ko kara ya saka a gidansu bamai Tsallaketa Saboda Shi kadai ne yayi karatun Boko agidan,Shi din Haifaffan garin Fagge ne na Jahar kano,Iyayensa Talakawa ne Futuk Mahaifinsa bashi cin yau ballatana na Gobe a baya Noma yake sai yazo ya samu Ciwon Baya ya kasa kuma Alhassan ne Babba Sauran kannen nashi Duka matane.
Karatun da ya samuyi Da Taimakon wani malami ne inda aka kaisa Almajiranci a Dala,Sai Allah ya Hada jininsu da Mallam Iliya,Wanda Da Taimakonsa ya kawo wannan matakin ya Tabbata Da yana Raye shi kadai ne zai Tsawatamai yaji to Ya rasu Da Dadewa,Goggo ce kuma Matukar sonsa Datake yi komai yayi Daidai ne ballatana Sauran kannensa mata da shi ne komai nasu Shiyasa Basu da tacewa.
Matsalan ma Daga wajen Hajiya mero ne da Danginta Yar nan cikin Kano din ne a Rijiyar Zaki. Itama Din bata isa ba shi ke da iko da ita da ya”yan da suka Haifa guda Biyu a Duniya Safiya da Tasleem..
Tundaga Falon kasa yake kwalama Hajiya Mero wacce ke Falon sama zaune tana jiran Tsammani Gabadaya yanayin Alhaji yasata Fargaba.
Sai kuma taji yana kiranta kiran Daya sa har Safiya Dake Cikin Dakinta ta jiyo Daman tana kwance ne Tana game a wayarta,Sun gama waya da Yusuf kenan yana Tambayanta ko Bakin sun zo..?
Tace bata sani ba Ammh kamar basu zo ba saboda har Abban nata ya Fita bata sani ba ta Shiga,wanka Dayake bata zuwa ko”ina Wanchan Shekara ta gama karatu Computer Sciencies ta karanta,Bata fara aiki ba sai dai Tana zuwa wani Cafe Dake nan bayansu Tana aiki dasu Duk ba wai tana musu aikin Parmanent bane,a hanyar zuwan ta ne ma suka Hadu da yusuf wata Bakwai da suka gabata.
Abban nata bai yi Niyyar ta Fara aiki ba,Shiyasa bai neman mata ba Tasleem ne kadai ke zuwa makaranta sai wannan Shekaran zata gama Candy.
Yusuf bai isa ya kira Imran ya Tambayeshi wani abu ba Domin shi bayason yawan Tambaya da Takura sai dai yafi kowa saninsa in yace Abu to ssai ya Tabbatar dashi ya Tabbata zasu zo din.
To sun gama wayar kenan Tana kwance kan gadonta Tana Game taji kiran da yake ta kwalama Mommyn nasu shi ya sakata Zabura ta Sauko Daga kan gadon tazo bakin kofa sai kuma ta kasa Fita jin Saukowan Hajiya Mero Tana Fadin”Abban Tasleem irin wannan kiran fa..? Lafiya..?
Hannunta ya Riko ya zaunar da ita kan Daya Daga cikin kujerun Falon kafin ya juya yana Fadin”Buba ijiye kayan hannunka..Kada ka tafi ban gama Dakai ba.!
Jikin Buba Megadi na rawa ya ijiye kayan Hannunsa ya Zube kasa yana jiran Umarni.
Hajiya Mero tabi kwalayen da kallo Cikin Faduwat gaba kafin ta maida kallonta kan Alhaji Alhassan Tana Fadin'”Nifa bangane komai ba..Wadanan kwalayen fa na miye.?
Zama yayi gefenta Lokaci Daya ya kama Hannunta ya Damka mata kudin Dake hannunsa Lokaci Daya yana Fadin”Sadakin yarki ce Mero..Yanzu nan na Daura Mata aure da wanda ta kawo..Tare da Shaidun Waliyansa daya aiko Guda Biyu,da kuma Shaidata Data Buba megadi gashi azaune..!
Yafada yana kallon Cikin Idanuwanta Cikin wani yanayi Buba megadi ya jinjina kai yana Fadin”Tabbas..Mun shaida Hajiya..Yanzu nan muka Tabbatar da auran..!
Ai da wani Sauri Hajiya Mero ta Mike Lokaci Daya kudin suka Biyota suka watse a kasa kamar Saukan aradu haka taji mganar Safiya ma Dake kofar Dakinta Tana leken Falon bata ji me ya gayamata ba sai dai Yanayin yadda Ta miken ya Fadar mata da gaba sai ta kara Sako kanta Domin Taji meke Faruwa.
Cikin wani Bacin rai ta kallesa daga Sama har kasa tana Fadin”Wani irin aure kuma..? Aure sai kace muna garin Gaba gaba Alhaji..?
Juyawa yayi yayi ma Megadi inkiya da Hannu daga haka ya Mike ya Fice Domin zamansa baida Muhalli a wajen.
Kafin ya maida kallonsa kanta Cikin Halin lko in kula yace”Auren gaske dai wanda kika sani..Miye amfanin jeka ka dawo..? Nayi mgana na Raba yarinyar nan ammh Taki jin mganata Ta rainani Ta turomin su kinga ai gwara na Aura mata shi Taje chan ta karata..!
Yafada yana zakuda kafada Cikin Karaji Hajiya Mero tace”Wlh baka isa ba Alhaji..Yata bazata yi aure a wannan gidan ba..Gidan da kace ba gidan arziki bane..Gidan Yan shaye shaye..? Inace ba kanagani yaron nan yazo yaci Zarafin mu Ammh Duk da haka kace suzo zaka basu yarka..? Wlh ban yarda ba yata ba yar tsana bace Su Biyu kadai na Haifa bazan Taba bari ka Lalata musu Rayuwa ba Baka isa ba!
Ta karishe Fada Cikin karaji wanda kaf mgangunta suka Fada kunnuwan Safiya wanda taji mganar Kamar Daga sama sai dai bata gama Fahimtar ina mganar ta Dosa ba.
Alhaji Alhassan Babatun Hajiya Mero bai Dameshi ba ya kalleta yana Fadin”Ai na ma isa Mero..Tunda har na Daura auran..Kinga ki adana mgangunki Zuwa wani Lokaci Yanzu dai ki shiga ciki ki taya yarki Hada kayanta Waliyan Mijinta suna jiranta zasu wuce da ita..Daga baya in muka zauna muka Tattauna sai musan abunda Zamu yi mata a mtsayinmu na Iyayenta..!
Yana Fada Lokaci Daya ya saka kai zai Haura sama Hajiya Mero da Zata out of Control bata san sadda ta isa garesa ba ta Chakume Rigarsa ta Baya lokaci Daya tana Fadin”Baka isa ba..Wlh Alhassan baka isa ba ba inda Safiya Zataje Domin ban yarda da wannan auran ba..!.
Ta karishe Fada Tana Fashewa da kuka Mai tsanani Kwace Rigarsa yayi yana Fadin”Mero wannan wani irin Raini ne? Ina Mijimki Uban ya”yanki zaki Chakume min Rigata..? Kada ma ki Fara wannan mgana aure na Riga na Daura kuma Wlh kinji Rantsuwan Musulmai Yau zata tafi Gidan Da ta zaba sama da mu..!
Yana karishe Fadar haka ya Tureta gefe sai da ta kusa Faduwa ya nufi Dakin Safiya wacce Rigiman iyayenta ya Tsorarata da kuma Abun ta fahimta yasa ta Bayyana atsakiyar Falon batare data sani ba Idanuwanta sun kala sunyi Jajir,kiris take jira ta Fashe da kuka aure abbanta ya Daura mata..?koda yusuf yake Zabinta ammh ai Tana so tayi auran gata da kowacce mace take yi.
Kusa cin karo yayi da ita wanda yasa yayi Saurin ja Baya yana Hararanta Lokaci Daya yana Fadin”Au daman kina jin mu ko..? Toba sai naa maimaita ba ki Shiga Dakin ki ki Hada komai naki da kikasan zaki Bukaceshi Domin na Sallameki gabadaya kije Gidan da kika Zaba Fiye damu Farimcikin iyayenki na Daura Miki aure yanzu nan kuma Waliyan shi wanda kika Zaba suna waje suna Jiranki kada ki Fara Bata musu Lokaci..!
Hawayenta ne suka zubo Sharr Cikin Rawan murya tace”Abbu aure..!
Bata samu Damar karisawa ba ya Dakatar da ita yana Fadin”Aure nace don Ubanki bashi kike so ba..?har kina saba Umarni na..?Maza ki shiga ki Hado kayanki kizo ki ki wuce kafin na Ci Mutumcinki yanzu anan wajen..!
Yafada Cikin Tsawa da Umarni Safiya ta Fashe da kuka Abunda Mahaifinta yayi mata kamar bai Taba ganinta ba taShiga Dakinta ya Bita yana ta Sababin Fada Tana Tusa kayanta Cikin karamar Trolley dinta yana Tsaye kanta yana Bala”insa ta Dauki mayafinta da wayarta ta Sakamayafi ya taso ta suka Fito suka iske Hajiya Mero na tsaye tana Kuka.
Suna Fitowa ta Mike ko kallonta Alhaji Alhassan bai yi ba ya Nufi inda ta Zubar da kudin Sadakin yazo ya Tattara ya Sakama Safiya a Hannunta yana Fadin”Kije ni ba zan ce kije kiyi hakuri ba..Sai dai nace miki kada ki kuskura wani abu yasa kice zaki Dawomin gida Bazan karbeki ba Na riga na baki Zabi kuma kika Zabi Gidan da zaki yanzu sai nace Allah ya bada Zaman lafiya ga Sadakin ki nan Hakkin ki ne..Sauran abubuwan kuma Daga baya in muka Tattauna da mamarki Zaki jimu..Zan sauke hakkina na Uba gareki a karo na Biyu..Na cika na aure Tunda na aurar dake..!
Daga haka yasaki Hannunta ta jimke kudin Tana jin wani irin Tsausayin kanta me ta aikata haka..? Daga tace Yusuf take so..?menene aibunsa Da har za”ayi mata wannan auran kamar wacce bata da gata..!
Kukan ta ya Fito Sarari Hajiya Mero Ta mike Cikin kuka ta kasa Mgana,Alhaji Alhassan yace”Mero kiyi sallama da yarki..Suna waje suna jiranta..!
Hajiya Mero taji wani Bakinciki Cikin azama tataho ta Rike Safiya Tana Fadin”Wlh baka isa ba..Ba inda yata zataje..!
Tafada Cikim kuka jin haka yasa Safiya ta Fada Jikinta Tana Fadin”Mommy..!
Lokaci Daya ta saka kuka mai Cin Rai,Karamin tsaki yaja yana Fadin”Don Allah ki saketa Mero..Miye na wani kuka sai kace anyi mutuwa..? Miye na ganin Laifina abunda yarki ta Zaba kenan kuma na bata..!
Tana rike da Safiya tace”Baka isa ba..Bazan yarda ka Gurbata Rayuwar yata ba…Nima ina da iyaye da yan”uwa Zan kira su na gayamusu ina da hakki akan ya”yana Kamar yadda kake dashi..baka isa na Zura maka ido ka Lalata Rayuwar yata ba Alhassan..!
Tafada Cikim kuka Wani Shekeke ya kalleta lafin ya saka Hannu ya Bambare Safiya ajikinta yana Fadin”Ai nafi son haka ma..Kije ki kira duk wanda zaki kira..Sai dai ina mai Tabbatar miki ba wanda ya isa ya Tada wannan auran koda kuwa Goggo ce..!
Ai fadin haka da yayi yasa ta san yakai makura Tunda ya iyacewa Harta uwarsa bata isa ba to waye ya isa..?
Babu shi Tana ji Tana gani ya tasa Safiya agaba Tana kuka Tana kiran sunanta ya Fice daita yana Fadin”Ga Shaidar Daurin aure nanki Raba Biyu..Kashi Daya na mutanen Fagge Daya kuma na Yan”uwanki..Kada wani yace bai sani ba Shaida ne..!
Daga haka ya Tasa Safiya suka Fice Daga Falon Yana tafe yana mata Fadan ba ita ta Zaba ba to kukan Uban miye take yi..?ita kuwa Tafe take kawai Tana Jimke da kudin Sadakinta a hannunta da wayarta Dayam kuma tana Faman Jan Trolley dinta.
Aharaban gidan suka iske Alh.sadi da Baba Manu su kansu sai da sukaji kamar suyi ma Safiya kuka ganin irin yadda take Shatatan Hawaye wanman wani irin Tozarci ne? Ace budurwa ba bazawara ba A daura mata aure ba wasu Mutane kuma za”a kaita ba wannan wanda zai rakata sai Waliyan Ango..?babu tsinke ballatama wani abun arziiki Gaskiya Alhaji Alhassan bai ji Dadin Rayuwarsa ba kuma Hakki da Kiwon ya”yansa sai ya kamashi.
Suna isowa gabansu ya Tura Safiya gabansu yana Fadin”Ki Duka kigaishesu..Sune wanda kika Zaban yayo Haya suka zo Neman auranki..!
Yafada kai tsaye yana kallonta kamar wacce aka Damkwafar a kasa haka ta Duka ita da kayan hannunta Tana Fadin”ina…ina..kwananku..!
Cikin muryan kuka Da Rauni Tuni Tsausayinta ya kama Baba Manu da Alh.sadi yaji kamar yayi kwallah Bai san sadda ya isa gareta ba yasa Hannu ya Dagota Tsaye Lokaci Daya yana Rike da Duka Kafadunta yace”Yata ki Daina ki Share Hawayenki..Wlh ba Domin ganin idon ki ba..Ni ba wanda yyi Hayata kan nazo Neman auranki..Ra”ayin Kaina ya sani Zuwa da kuma Dalilin kanin Mijin da kika aura..Duk da ban Taba ganin wanda kika auran ba ammh ni naji ji ajikina kin Shiga Zuru”a mai kyau da Nasaba..Sannan kuma ina da Tabbacin suma kamar kowa ne sai dai wani al’amari wanda mu bamu sani ba..Sai dai ina da Tabbacin Zaki zama Sanadiyar Gyara Zamantakewar wannan Gidan ki Cika sa da farinciki Shigowarki ya zameusu Alheri Har karshen Rayuwarsu.!.
Yau ta Taba ganinsa ammh mgangunsa sun yi matukar Tasiri acikin Zuciyarta wanda suka sakamata wani Dakewa da Juriya Bata ji ta karaya ba Tana kaunar Yusuf da Zuciya Daya kuma Tayi alkawarin sai tayi Sanadiyar dawomai da Farincikin Data lura yarasa Shi da Sauran yan”uwansa.
Da wannan kwarin gwiwan ta Dago Tana kallon Baba Manu kafin tace”Insha Allahu..!
Tafada Lokaci Daya Tana Share Hawayenta sai yaji Dadi ya Dafa kanta yana Fadin”Allah yayi miki albarka ya albarci Sabon Gidan daZaki..!
Ita acikin Ranta ta amsa Alh.sadi ya amsa afili Alhaji Alhassan kuwa baki yaTabe kafin yace”Gata nan..Nagama nawa Saura naku..Safiya ki kula kada ki kuskura kice zaki Dawon gida da wani mgana kinji nagayamiki..!
Kai ta girgiza Idanuwanta na Cika da kwallah Tace”Insha Allahu sai alheri zai kawo ni Abbu..!
Daga haka ta Rike Trolley dinta Dakyau ta Fara Tafiya tana kuka Baba Manu ya mikama Alhaji Alhassan Hannu sukayi musabaha hakama Alh sadi kafin suyi mai sallama subi bayan Safiya Harta Megadi sai yaji kamar yayi kwallah Ballatana Hajiya Mero Dake kofar Falon da Haraban gidan Tana kallon Duk Abunda ke Faruwa,Hawaye na Zubo mata kamar famfo,Suna Ficewa Daga gidan Alhaji Alhassan ya Sauke ajiyar Zuciya acikin Ransa yace”Sai yanzu Hankalina ya kwanta..!
Daga haka ya juya zuwa Cikin Falon Nan yaci karo da Hajiya Mero Tana kuka ya wuceta yana Fadin”Kina da aiki Mero..Waya isa ya Tada Hukuncin Allah.!
Tana jinsa ta kasa mgana sai kuka acikin Ranta kuma Fadi take”Hukuncin Allah ko Hukuncin ka..?
Daga haka ta juya zuwa Cikin Falon da gudu tana kuka ko Kwalayen Mintin Dake tsakar Falon bata bi takai ba ta Shige Dakinta ta Fada Kan gado Tana wani Gunjin kuka gabadaya ta rasa mafita ballatana ta kamo Zaren yadda Zatayi.