GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


Bayan La”asar Yusuf ya baro wajen aikinsa zuwa gida,ko da ya Dawo ya iske Imran na Dakin Abba yana bashi Tea,Tunda Munari bata dawo Daga makaranta ba ballatana Tayi abinci.
Yana Shigowa gidan Dakin Abba ya Fara shiga nan yake Imran ya Dago yana kallonsa Mirmishi ya sakarmai Ammh Shi Imran din sai ya kauda kansa Abba ne Cikin Fara”a yace”Yusuf…Ka dawo ashe..? kariso mana ka tsaya Daga bakin kofa..!
Jin haka yasa ya shigo Dakin Yana Sabe da Jakarsa ta aiki a Kafadansa Gefen kafafun Abba ya Zauna Tunda Imran ya Zaunar dashi shi kuma yana Zaune gefensa.
Yana zama yace”Abba ya jikin ka?
Abba yace”Jikina da sauki Yusuf..Yau dan”uwanka yayi ta kula dani..Dukkan ku Allah yayi muku albarka,ya jikan yan uwanku da Mahaifiyarku..!
Gabadayansu sai da sukayi mamakin kalamansa Domin ya Dade baya Fadar haka tun Farkon Lamarin,Kallon juna akayi Tsakanin Imran da Yusuf Mirmishi ya Bayyana Saman Fuskarsu da Sauri Imran ya mike Tsaye rike da Mug din Tea din yana Fadin”Da alamu dis Time around Abba ya fara samuwa..!
Yusuf ma kusa da Abba ya Dawo ya Rike Hannayensa yana Fadin”Abba ka samu lafiya ne..? Abba Don Allah ka warke..Ka Dawo Abban mu da muka Saba Dashi..,!
Abba ya saki Mirmishi kafin ya Dafa kan Yusuf yace”Na samu Sauki Yusuf..Dole na manta da komai na Fuskanci Rayuwar da Allah ya zabamim ko Saboda kai da Imran da kanwarku Maimunatu..!
Dukkansu Bakinsu yaki Rufuwa Yusuf ya kara Jimke hannun Abba yana Fadin”Abba Daman na dawo ne na Fada maka wani Daddaan Labari..Abba nayi aure..Abba Imran ya Girma shi yabiyamin Sadaki shi yayimin komai na aure na Abba..!
Abba yayi jim yana kallonsa kafin ya sauke Numfashi yana Fadin”Duk a yaushe akayi neman auran har akayi Auran ni bansani ba..?Kuma shi Imran din ne ya Shige maka gaba har aka baka auran.?
Yusuf ya girgiza kai Kafin ya Fara Bama Abba Labari Kamar yadda Imran ya Bashi Labari da irin yadda Alhaji Alhassan ya hanashi Auran Safiya sai da Imran yaje kana..!
Abba kafin yusuf ya gama Bada Labarinsa yaji Hawaye sun Fara kwaranya acikin idanuwansa Cikin Muryan kuka da Sarewa yace’Waye ya Gorantamuku Rashin asali..? Ku din yan asali ne ya”yan Dangi..Ba laifi na bane Bakuma ni na gayyaci Kaddran Data Fadamin cikin Rayuwata ba.
Allah ne ya Doramin kuma Wlh ba Kamar yadda Sauran yan”uwana ke Fadi bane na yarda da Kaddara kuma na yarda da Allah da ya bani Zuwaira shi ya Karbi kayansa..Haka kuma Allah da ya azurtani da Haihuwan Nura da Asma”u da Salima shi ya karbi kayansa..Sai dai wannan Gagarumin rashi a lokaci Daya basan yadda zan iya Daukan Lamarim ba..Wlh ban sani ba..!
Ya karishe Fada cikin gunjin kuka wanda ya kusa saka Yusuf kuka da Sauri ya Rumgume Abba Imran kuwa yana gefe tsaye ya Coge yana kallon kasa ba wanda ya iya Fahimtar wani Hali yake Ciki ba.
Yusuf ya Dago Daga Jikin Abba ya Saka Hannu ya Sharemai Hawaye kafin yace”Ka daina kuka Abba…Don Allah kada muma ka sakamu..!
Abba yayi Mirmishi Lokaci Daya yana Kara rike hannuwan Yusuf kafin ya Dago yana kallon Imran Lokaci Daya ya fara mgana”Yusuf..Imran..Babu abunda Zan ce muku sai godiya..Allah yayi muku albarka na baku Wahala akan Lalurata..Ga rikon kanwarku..ammh Duk da haka Ban ji Dadi da kuka yanke Shawaran neman auran yusuf Batare da kun nemi Daya Daga Cikin Iyayenku ba..Duk da ko Dawowarmu wannan gidan Ban ji Dadi ba..Ina jira ne na kara Samun Sauki Dole zamu koma Gida na nemi yan”uwana kuma ku nemi yan”uwanku Kowa Rayuwa ta koma mai yadda ya fara..!
Wannan Karon Imran ne ya Motsa kafin yace”Abba Ka bar wanman mganar..Mutanen da sukayi ta Bleming din ka akan ka Zama mahaukaci saboda Rashin Daukan kaddara..Basu Tuna kai Dan”uwansu bane alokacin basu Duba Halin da kake ciki ba basu Duba irin rashin da mukayi ba su Rika Zargin ka suna ganin Rashin Hakuri ne da kaddara ne ya jefaka Cikin Halin dakake ciki..Ai gwara da mukayi nesa dasu muka dawo nan muma Rayuwa a inda ba wanda yasan Labarin Mu yafi yemama Zama inda ansan Laluranka ammh kuma baza”a Taimaka masa wajen ganin ya Rabu da Lalurarsa ba sai kara Doramai Cuta.Abba ka bar wannan mganar ni Na rantse ko Komawa zakayi sai dai Yusuf da Munari su Bika ni ina nan ba Inda Zani..!
Ya karishe Fada Cikim kumfar baki Lokaci Daya kamar wani Kabubuwa ya Fice har yana Banko Kofar Dakin
Daga Abba Har yusuf da kallo suka Bisa kafin su girgiza kai Abba ya Cije baki yace”Ashe har yanzu Imran bai Chanza ba Yusuf..?
Yusuf yace”Sai ma abunda yayi gaba Abba..!Abba ya koma kawai ya kwanta kafin yace”Allah ya Shiryesa..Yanzu ita yarinyar tana ina..?
Yusuf yace”Tana gidan Maman abokinsa Sagir yaron nan Dake zuwa Dubaka..!
Abba ya gyada kai kafin yace”Allah ya bada zaman lafiya..!
Daga haka bai kara cewa komai ba yayi dai Shuru ya Lumshe idaanuwansa kamar mai Barci ganin haka yasa Yusuf ya mike ya Fice Jiki a sanyaye sai da ya Fita ne kana Abba ya Bude idanuwansa yana Bin Kofar Dakin da kallo wasu Siraran Hawaye suna Biyo kunnuwansa a Fili ya Furta”Kiyi Hakuri Daada..Ki yafemin..!
Yusuf Dakinsa ya wuce yayi wanka ya sauya kaya zuwa wata Farar Shadda Riga da wando da Hularsa Zanna Bukar,Yasa Bakin Takalminsa Rufaffe na Fatar Damisa.
Ya fesa Turare yana Tashin Kamshi Dakin Imran ya Shiga ya Iskesa ya Turnike Dakin,da Hayaki sauri Yusuf ya karisa Shiga Dakin da Sauri ya Zage Labulyen Windows din Dake dakin ya Dage Glass din Yana Fadin”What Wrong with u ne Imu..? Kana zaune acikin Daki Hayaki ya Turnike ga na Cikin ka ga na Sarari illah Nawa kake so kayi ma kan ka ne.?
Imran na Zaune yana jinsa bai tankasa ba sai ma kara Zukar Sigarinsa da yayi ya Fesar da Hayaki bai ko kalli barayin Yusuf din ba.
Karamin tsaki ya saki kafin ya Tako gabansa ya saka Hannu ya karbe Sigarin yana sakata Cikin Farantin Dake gefen Imran din inda yake kashe sauran Sigaran nashi da wani Jajayen idanuwa Imran ya Dago yana Kallonsa Kafin yayi mgana Yusuf ya Rigashi da cewa'”Kafi kowa sanin Shan Taba tana da illah ga Lafiyar Dan’aman Imu..A baya Lokacin kana Banker Imran Abubakar malami na sani ko Warin taba baka so..Ammh Rana tsaka na tsinceka ka fi wadanda ma suka dade cikin shanta iya Zukanta da Shanta ma..Don Allah ka Rage shanta hakanan Tunda ba Abinci bane..!
Saboda Bayason Hayaniya baya Cikin Mood mai Dadi yasa yace”Naji..!
Da haka ya dauke Kwalim Sigari da bai fi Saura Daya ba Da Lether din ya Tusa cikin Aljihin wandon Dake jikinsa
Yusuf yace”Yauwa..Tashi ka rakani gidansu Sagir din.!
Imran ya wani Dakuna Fuska kafin yace”bazan je ba..Haka kurim sai kaje dani Daukan Amaryan taka..?
Yusuf ya Dafa kafadarsa yana Fadin”Ai ba cewa nayi ka Daukomin ita ba rakani kawai zakayi bazan gane gidan ba..!
Yafada da Sigan Lallashi
Imran kamar bai zai tashi ba sai da yaga Dama kana ya tashi ya Fice batare Dayace ma Yusuf din komai ba Shima sai yabi bayansa a Haraban gidan suka Hadu sai da Yusuf yayi Riverse da Motar yazo gaban Imran kana ya Bude gidan gaba ya shiga suka Fice Daga gidan
Shi ya nunamai hanyar gidansu Sagir din sai gasu sun iso sun iske Sagir din a Shago ya Taso da Sauri yana gaida Yaya yusuf kana yamai Jagora zuwa Cikin Gida Domin Imran yace yana waje shi bazai Shiga ba,Dole Yusuf ya Shiga shi kadai Mama tayi ta ina ta saka dashi har Falonta Safiya na Ciki inda tayi Sallah Mama ta bata abinci taci kadan Tayi ta mata Nasiha harta Daina kuka Bayan sun gaisa ne Sagir yayi ma Mama bayanin Wanene Yusuf Ta washe baki suka kara gaisawa,kan yusuf na kasa yace”MAMA nazo tafiya da ita ne..!
Mama ta mike tana Fadin”Masha Allah..Ammh ai bana barta ita kadai ba in ba Damuwa sai na Rakata gidan naku..!
Yusif yaji Dadin haka da Sauri yace”Bakomai Mama mungode
Batace komai ba ta Nufi Ciki ta iske Safiya tsaye tana kuka Rikota Tayi tana Lallashinta,Hijabinta ta saka ita Maman ta kuma Dauki akwatin Safiya suka Fito sun iske su Sagir sun Fice suna Waje suma Wajen suka Nufa Safiya ta Shige Cikin mayafimta Tana kuka Kukan bakkn ciki irin auran Wulakancin da Mahaifinta yayi mata.
Mama ta rike da hannunta da alwatinta Imran na Waje tare dasu yusuf,Domin tunda yace Mama tace zata raka Safiya bai ce komai ba Mama ta Chanchanci komai.
Yusuf kallo Daya yayi ma Safiya bai kara ba a jin kukanta yake har Cikin Ransa Mota ya Shige Tunda Imran suje shi zai taho
Mama kuma ta juya tana barin ma Sagir Sallahu in Inteesar ta Dawo ya amsa mata Daga Maman har Safiyan gidan baya suka Shiga Yusuf na gaba Yajasu suka Tafi.
Suna barin kofar gidan ba Dadewa Imran ya Zaro Sigarinsa ya kunna ya Cigaba da Fesar da Hayaki Sagir na gefensa Yana kallonsa kai kawai ya kada bai ce komai ba.
Daidai Lokacin da mai adaidata ya ijiye Inteesar akofar gidansu Sagir din ta Fito Tana Duba Jakarta ta Daukoma mai Adaidaita kudinsa ta Mikamai ta Jiyo cikin Rangajinta Dauke da Jakarta da wasu Takardu a hannunta Idanuwanta sun kankamce saboda Gajiya Tunda ga Nesa Sagir yake washe mata baki Cikin mamakin gani ta gane Tunda Gashi har ta kawo kanta gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button