GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Shakira…
3/22/22, 23:04 – Ummi Tandama😇: GIDANMU..!
(Our House)
Book1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

          🅿�11

“Itama tundaga nesan ta Hangoshi Tsaye sai wanda suke taren ne bata Damu Data kalli ko waye ba ammh Tabbas tasan yanatare da wani ne a Tsaye.
Kafin ma ta Kariso Sagir ya saki Mirmishi yana Fadin”Kai ashe kanwar tawa dai da gasken gasken Zata iya Dawo da kanta Gida kamar yadda tafada..?
Ya karishe Cikin Zolaya,Cikin Hararan wasa lokaci Daya Tana Dakuna fuska Daya Zame mata jiki tace”Kaji fa Yaya Sagir ce maka akayi bazan iya Dawowa ba..? Ai daman na Fadamaka ina da saurin Dauke waje in dai naje koda Sau Daya ne..!
Tafada Daidai Tana Gama Tsayuwa agabansu Cikin gyada kai yace”Ah Lalle naga alama kuwa..To ya makarantar..? Hop karatun ba wahala..!
Inteesar ta yi naka naka da fuska kamar ta Saka kuka Tana Fadin”Wlh yau kamar na Dora hannu akai nayi ta Ihu..Karatu ai daman akwai Wahala ya Sagir ga bakunta ga rashin Sabo..gabadaya Jikina Ciwo yake kamar anyimin Dukan Tsiya..!
Ta fada Lokaci Daya tana kara hura Kafofin Hancinta jin kamar Warin Data Tsana aduniya warin da in Ta Shaka yake Fitar da ita daga Hayyacinta Wato Warin SIGARI.
Sagir bai Fahimta ba yace”Ke dai kawai kice ke Raguwa ce..!
Inteesar najin Zuciyarta na tashi da Warin Taban Dataji kuma bata ga Sagir Dashi ba..Kuma Tunda tazo wajen Hankalinta bai bata tama kalli Barayin Imran ba kamar yadda Shima ko Sau Daya bai kalleta ba Karan Sigarin Dake hannunsa Tuni ta Kare sai ya Murjeta a kasa koda Inteesar tazo Warin kawai ta iske,Hankalinsa kwata kwata baya kansu yana kallon Gefe ne yana wani Tunani,Tunanin yadda komai na Rayuwarsu ke zuwa Daga wannan sai wannan.
Inteesar Da tsayuwar wajen ya Fara Gagararta Ga tashin Zuciya Tana jin kamar Zatayi amai Tunaninta bai bata Sagir ke shan Sigari ba Sai tayi Tunanin kila wani ne yazo yasha a wajen Shiyasa taji wari.
Cikin Dan Dauriya ta Harareshi kafin tace”Hakama yanzu Ya basheer ya gama Tsokana.munyi waya dasu sun kai gida tun dazu..Umma tace tana ta kiran Wayar Mama bata Daga ba.tacemin in na Dawo na Hadasu suyi mgana ni kuma 5:30pm muka Fito Lacture,sai na Tsaya na Tambaya aka Nunamin Classrep din mu na Karbi Lambarsa Saboda Shedules din makaranta Tunda bansan kowa ba kuma an wuceni Kafin nazo..!
Sagir yace”Daz a very Gud Idea…Hakan nada kyau kinga sai ya nunami ki inda akayi kafin kizo..Mama kuma Wlh ta Fita nan Makota yanzu bada Dadewa ba tace in kin Dawo abinci na kitchen har ruwam Zafi ta saka miki a Falas yar gatan Mama..!
Inteesar Tayi dariya tana Fadin”Eh din ko kaji Haushi ne nazo na kwace gwannatin ka..? Kamar mama ta sani na gaji wanka nake so..Ga yunwa duk wunin yau Cway ne kadai Acikina..!
Sagir ya zaro ido kafin ya samu Zarafin mgana Hayakin Sigarin da Imran ya Zuka ya fesar har Wajen Fuskar Inteeaar wacce taji abun kamar Al”amara nan da nan Hankalinta ya tashi Taja Baya Jikinta na kyarma Lokaci Daya tana Jan Gefen mayafinta ta Rufe Hancinta Tana Fadin”A’UZUBILLAHI MINAL SHEDANIR RAJIM..’
Haka ta fada jin yadda Zuciyarta ke tashi Cikinta na Hautsina ga Miyau ya Taru a bakinta tana gabda da Amai alokacin.
Sai a wannan Lokacin gabadayansu suka Kalli Juna shi Imran Bai san Inteesar na wajen ba har Lokacin Shifa Tun sanda ta Nufosa yaga Sagir na mata mgana ya Shiga wani Sabgan Aduk a tunaninsa sun gama mganarsu ta Wuce Imran Mutum ne da bai Cika Damuwa da Mutane ba Shi d’an i Dont Care ne.
Ta”awizin Data Sakarmai yasa yasan tana Wajen Har ya Dago yana so yaga wata Yarinya ce take Sakarmai ta”awizi haka Charaf kuwa Idanuwansu suka Hadu waje Daya wanda nan take Zuciyoyinsu suka buga atake tare da wani bakon Lamarin da basu gane ko na miye ba ammh dukkansu sun kurama juna ido Cikin Wani yanayin da suka,kasa Dauke Kallonsu Daga kan junanasu Tare da bugun Zuciyan da basu Gane ko na Miye ba,Ita Inteesar tana kallonsa zuciyarta nayi mata rawa sai take ji kamar ta sansa,yanayinsa bai yi mata kama da bakon data ta taba gani yau ba.
Shi kuma Kallonta yake da mamakin Furucinta Shi bazai iya tuna Yaushe Rabon Daya tsaya yana kare ma Wata mace kallo ba,Ammh yau sai gashi yana Kallon Inteesar Dayaji ya kasa Daina kallonta,Sannan kuma Ransa ya gama Kuna da baci da jin ta kiramai Ta’awizi,uwa uba kuma Tana Faman Toshe Hanci kamar taga kashi.
Ita kuwa Inteesar,Warin Sauran Sigarin Dake Hannun Imran ne ta isheta Gabadaya ta kasa Hadiye Miyan Bakinta ga Zuciyarta na Tashi Amai nataso mata,Yasa ta kauda kanta da Sauri ta Zubar da miyan Daya Taru a Bakinta sagir Dake Tsaye,Yaga abunda ya Faru,nan da nan ya juya yana kallon Imran yaga yanayinsa sai yaga ya Hade rai ransa Tamau kamar ma yafi koyaushe,Sai wani kallon Sama Da kasa yake Bin Inteesaer Dashi.
Ganin haka yasa ya juya ga Inteesar yana Fadin”Inteesar lafiya kuwa.?
Cikin kara Toshe Hanci tace”Ya Sagir Warin Sigari…Bana son Warinta sam..Amai yake Sakani Da Tashin Zuciya…”
Daga haka bata ma tsaya kara mgana ta kwasa da gudu zuwa Cikin Gida Jin Aman yana Kokarin Fito da kansa ganin Haka yass ya bi bayanta yana kiran sunanta,sai bata tsaya ba Har zai Bita cikin gidan sai kuma ya Tuna da Imran sai ya fasa sai dai me yana Juyowa shima Imran Din yaga Bayanan,sai ya hangesa ya mika Hanyar Gida baki ya Rike aransa Yana Fadin Allah ya Huci Zuciyarka Inteesar ta tabo wanda bata sani ba.
Sai ya koma Cikin Gidan nan ya iske Inteesar sai Sheka amai Take Duk Sai da Ta amayar da Cake din Dataji da Lemo Sagir Shi ya Taimakamata da Ruwa ta wanke bakinta,ya kuma kwasan mata Littafanta da Jakarta Zuwa Cikin Falon mama.
Sai da ta Zauna Tana kana ta Shiga Sauke Numfashi Sama sama.
Cikin Tsausayamata yace”Sannu..!
Da kai ta amsa Kafin tace”Yauwa..Yaya Sagir ina ka samo Aboki D’an iska..?
Sagir ya Zaro ido yana Fadin”Waye Dan iskan..? Wai Imran..?
Inteesar ta Dakuna Fuska Kafin tace”Oho..Ni nasan ma sunansa..Eh mana..Sigari fa yake Sha agaban Mutane bako kunya..!
Sagir yayi mirmishi Kafin yace”Ai Shan Sigari ba Iskaci bane Inteesar..Sai dai Kawai kice Tana Illah ga Lafiyan Dan”adam…!
Inteesar ta saki karamin Tsaki Kafin tace”Duk Daya..Ni Wlh Tun ina karamata Daukan masu Shan Sigari nake yan iska..Ballatana Warinta bama Sonsa amai yake sakani da Tashin zuciya.
Sagir yace”Sai don haka..Ammah shan Sigari ba Iskanci bane..Hakama Abokina ba yadda kike Tunani bane..!
Tabe baki kawai Inteesar Tayi bata kara Mgana ba,ganin haka yasa Sagir ya mike Tsaye yana Fadin”Bari na Leka Shago..Komai kike Bukata ki Duba Kichen ko kina Bukatar wani Abun ne..?
Inteesar ta girgiza kai kafin tace”Bana Bukatar komai..!
Daga haka sagir yayi mata Sallama ya Fice Daga Gidan Inteesar ta kwashi Jakarta da Littafanta zuwa ciki Tana kunkuni ita kadai Tana Fadin”Allah ya isa..ya sani amai duk naji ma bana jin cin komai..Allah ya isana Wlh..!
Haka take ta Mita ita Kadai kyan Jikinta ta Cire ta Duba Flas din Mama Taga Ruwan zafi ta Juye ta shiga wanka Dashi Ta Fito bayan ta Dauro Alwala jin ana kiran sallar mangariba Lokaci Daya Tana mamakin ina Mama taje haka..? Bata samu mai bata amsa ba,Ta Sauya kaya zuwa wasu Riga da Wando Marasa Nauyi ta Dauko Donut Din Da tazo Dashi Taci Kadan ta fito Falo ta Duba Fridge din Mama ta ga Lemon Cy,ta Dauka tasha Kadan ta Hada da Dunot din kana ta koma Ciki Ta tada Sallar Har ta idar ba”a Kawo Wuta ba Duhu ya Fara sai ta kunna Fitilar wayarta ta Fito Falo ta Dauki Tsintsiya ta Share Falon,Kana ta Dauki Littafanta da abunda akayi musu karatu yau ta Fito Falo Tana dubawa Lokaci bayan Lokaci Tana Duba Hanyar na ganin Dawowar Mama ba ita ba Sagir Kiran Daddy ya Dauke mata Hankali Daga Kadaicin Datake yi ita kadai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button