GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Safiya na Zaune inda Mama ta Zaunar da ita Har yusuf ya Fita ya barta bata Motsa ba Duk yace ga Tiolet nan ta Shiga Tayi Alwala Tazo tayi Sallah kafim ya Dawo ammh ta kasa Tashi Abubuea ne ke Dawomata Daki Daki.Na yarda auranta ya Faru kamar almara Allah Sarki mommy,ta Tuna Sadda take kuka tana Rike ta Tasan Laifin Abun su ne da Ta Mommy ce bazata bari ayi haka ba,Anfi karfinta ne Tuna Haka yasa ta Dauko Wayarta Dake Jikinta ZAta kira Mommy sai ta iske Missed call dinta ba adadi Jikinta na Rawa ta Bi bayan kiran,kira Daya taji an Daga kiran lokaci Daya Taji Muryan Tasleem da Mommy alokaci Daya suna Tambayanta ina ta Shige ne suna ta kiranta bata Daga ba.
Safiya taji kuka ya kawo mata Cikin kuka tace”Ina Gidansu Yusuf Mommy..Wayata Tana Silent Banji ba..!
Tasleem ta Saka kuka itama Tana Fadin”Anty Safiya..Nadawo naji Abunnda Abbu ya aikata Miki..Nayi kuka Mommy ma sai kuka take Kuma munso mu Boyoki Abu ya hana yace ba yanzu ba..!
Safiya na Sharan majina tace”Kada ki Damu Ina nan lafiya Safiya..Kuma Zaki zo inda nake Abbu zai barki kizo Insha Allahu..!
Tafada Tana Sharan kwallah kafin Tasleem din Tayi mgana Mommy ta karbe Wayan Tana Fadin”Safiya zan zo na Tafi Dake..Bazan yarda da wannan auran ba..!
Safiya na Zubar kwallah tace”A”a Momny kada ki yi abunda Abu zai Yimiki Abunda mu bazamu mu manta ba ….Kinsan Halinsa fa kiyi Hakuri Insha Allahu ba Mtsala..Gidan Maman Abokin Kaninsa suka kaini Ba Dadewa yusuf dun yazo ya Daukeni zuwa Gidansu ita Maman abokin Ta Rakoni zuwa Gidansu Yusuf din..Mommy kada ki Damu ki barni nayi Zaman aurena Abba mahaifin Su Yusuf yace min kamar ya nake garesa zai rikeni kamar yar daya Haifa ta Cikinsa..!
Mommy ta Sauke Numfashi kafin tace”Shikenan..Ammh bazan yarda ya aurar dake a wulakance ba..Sai na kwatan miki yancinki..Ki rika barin wayarki kusa Dake zamu Dinga kiranki..!
Ta Bude baki Zatayi mgana kenan Munari ta Shigo Dakin Tana Fadin”Hello Bhabi..!

Shakira…
3/22/22, 23:04 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

          🅿�12

“Safiya tana ganin Shigowar Munari Ta Sanyaya Murya Tana Fadin”Mommy zan kira ku zuwa Gobe..Ki lallashi Tasleem Plz..!
Hajiya Mero Dagachan bangaran ta share Hawayenta Tana Dafa Kan Tasleem Tace”Shikenan Ki kula da kanki Don Allah..!
Safiya ta gyada kai Lokaci Daya ta katse kiran bayan ta dago Fuskarta Tana kare Munari kallo ko da bata Taba ganinta a Zahiri ba a kallo Daya zata gane Ita din Jinin Yusuf ce Ballatana Ta taba ganinta a Hoto a Wayar yusuf ya nuna Mata kuma Labarin Munari da Imu har Ta gaji da ji Ta Haddaceshi Saboda Karya ne Yuauf yazo wajenta ko ya kira Wayarta su gama Hira bai ambacesu ba ko bai Fada mata ba ta Tabbata su din sune Jinshkin Mijin nata.
Shiyasa ta Saki Fuskarta kamar yadda Itama Munarin ta Washe mata baki Gefen gadon ta Zauna Tana Fadin”Anty Safiya Wlcm to Our House..Ina miki Fatan Alheri..Sunana Maimunatu Abubakar malami ni lilsister din Mijinki ne ya yusuf..Ina Farimcikin Zamowarki Daya Daga Cikin Ahalin gidanmu ayau..!
Tafada Lokaci daya Tana mika mata Hannu alamun Musabaha.
Safiya Tayi Mirmishi kafin ta mika mata nata Hannu suka Sarke lokaci Daya tana Fadin “Nagode Sosai Munari..Nima ina Farincikin Haduwata Dake sosai..!
Munari ta Washe baki kafin tace”Waya Fada miki ana kirana Munari.?
Safiya tace”Wazai Fadamin banda Yayanki..? Abakinsa naji Sunanki mai Dadi munarin Abba Auta ko.?
Munari taji Dadi sosai Soyayyar Dan”uwanta na Ratsata tace”Yes..Haka kirarin yake..Ina jin Dadin sunan sosai Saboda Abba ne ya Sakamin Sai kakata wacce ta Haifi Abba na Daada Dayake Sunan Autanta su Abba naci Goggo Maimuna..!
Safiya tace”Allah Sarki..Duk suna ina..? Ita kakar taku da goggon taku..?
Sai Munari taki Cewa sanin ba Huruminta bane safiya na Nazarinta Sai ta Waske Kafin Tace”Yanzu dai ba wannan ba..Naga Abba Sauran Imu bangansa ba ko baya nan ne..?ko shi ne Dazu muna Falo ya Shigo a Fusace ya Shige Daki ya Bugo kofa..?
Munari ta kalleta Har Lokacin Suna Rike da Hannun Juna tace”Bansani ba ko ya Dawo..Nima ai yanzu na Shigo Gidan Tun safe ina makaranta Buk nake Karatu Fanni Economics..!
Safiya ta jinjina kai kafin Ta gyara Zama Tana Fadin”To dawa kuke barin Abba in kika Tafi Makaranta Yusuf ya Tafi wajen aiki..? Kuma meke Damun Abba ayadda na Fahimta a labarin da Yusuf yake bani kullum yana Daki baya Fita ko”ina ko Bai da Lafiyan Kafa ne..?
Da Sauri Munari tace”Lafiyar Kafarsa Kalau..Bashi da lafiya ne Shiyasa Su Yaya yusuf basa yadda ya Fito ko Falo ne..!
Safiya Tayi Shuru Tana kallon Munari Kamar Zatayi mgana sai ta fasa aranta Tace kada tace Na dameta da son jin kwakwaf,sai ta Share mganar Ta kara Damke Hannun Munari Tana Fadin”Amtsayina na Bakuwa bani Labarin Ya yusuf da Ya Imu..? Wanne yafi kula dake wa kuma kika Fiso..? Saura kuma Kice My Dear baya Kula Dake sosai sai na ciki Tara..!
Munari ta samu abunda take so wanda ZAta ganta Gata tana Hira da Dariya ta saba Rayuwa ita kadai adukan Shekarun da suka Dawo kano da Zama Banda Yaya yusuf bata samun Sakewa da kowa sai kuwa Abba Shi kuma Bashi da lafiya in kwana Biyu ya samu Sauki Zuwa Chan sai abun nashi ya kara Rikicewa Dama Ya Imu bamai sakashi a lissafi ko abaya ba abokin Hirarta bane Shi,Ballatana yanzu da abubuwa suka Lalacemai sosai.
Ko amakaranta ya Jamata kunni Kada ta kuskura ta yi wata kawa ko Wani Mutumcin da zai ka ga Har a san Gidansu,Sharudda ya kafamata Sosai kafin ya yarda ma Ya yusuf ya biya Kudi mata kudi a wata Makarantar Kudi ta Rubuta WAEC Da NECO,Da Jamb Har ta samu Gurbin Karatu a Jami”ar Bayero Tunda Lokacin da Suka Baro Lagos Tana SS2 ne,Duk somta da Mutane ta Ware kanta Tun yan ajinsu na Shigemata tana kauce musu Har sukayi banza da ita kowa ya kama kansa bata da Lambar Kowa Itama ba wanda ke da nata sai dai ta karbi Na Class Rep dinsu saboda In wani abu ya taso ta Rika sani Har Group dinsu na Department dinsu na Wasop ya sakata Tana gani ana Hira da Dariya bata da ikon cewa wani abu,sai da ta Shiga tagani in an bada Wani Assigment ko wani Infomartion mai amfani ta Duba Duk yadda taso Rayuwarta Tatafi yadda Hallitar take bazata iya Bijirema Umarnin Yayyinta ba itama Bazata zo ta Fuskanci Wulakaci da Tozarcin da Yayyinta ke Fuskanta kan Gidansu ba.
Safiya ce ta Girgiza hannunta ganin Ta Shiga Dogon Tunani Da Sauri ta Dawo Hayyacinta Tayi Saurin Zare Hannunta Tana Goge Ruwan Hawayen da suka Fara kokarin Zubomata Cikin Dariya Dariya ta Fara Fadin”Ai baza ma ki Hada ba Anty Safiya..Abaya Ni yar gatace ta gaba da Baya..yar gatan Abba da Anni yar gata kowa agidanmu..ayanzu kuma Ni yar Gatan Abba ne Duk da bai da Lafiya Dagashi sai Ya yusuf,Bai Hadani da komai ba..Zai iya yin komai Saboda Farincikina Baya iya Runtsawa sai ya Tabbatar da naci Abinci na kwanta sannan zai iya barci..Ya yusuf Mutum ne mai Zuciyar Zinare,mai kirki mai Dattako mai Sanyin Zuciya Dana Hali bashi da Hayaniya ballatana Saurin fushi Zan iya ce Miki ban Taba ganin Fushinsa ba yana da Raunin Zuciya kamar mace Irin Zuciyar Abbanmu garesa suna da Bala”in Sanyin Hali da Dadin Zama ga waanda ya Zauna dasu..Zasu iya Sadaukar da komai Saboda Ahalinsu,ZAsu iya Sadaukar da Dariyansu da Farimcikinsu Saboda Ahalinsu,Anty Safiya bawai ina Kuranta Yaya yusuf bane Domin yana Yayana ba A”a sai Domin Halin Mutum ka Fadeshi bai taba ganina Cikin Damuwa ya barni ba sai ya Tabbatar da Fuskatata cika da Farinciki Shiyasa nake matukar sonsa acikin Zuciya naji Dadi da kika Kasance Abokin Rayuwarsa Anty Safiya Ki Rikemin Yayana Amana ina mai Tabbatar Miki Baza ki Taba yin Nadama ba Domin yana Sonki kuma Shi din Tamkar Misalin mijin Maraniya ce.!
Ta karishe Fada Hawaye suna wanke mata Fuska Lokaci Daya tana Riko Hannuwan Safiya wacce itama kalaman Munari suka kara Raunana Nata Zuciyar Dayake Daman a Raunane.
Safiya ta Saka Hannu Tana Share ma Munari Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin”Shii..Ki Daina kuka..Bayan Ya Yusuf yau nima gani Zan ninka Kulawar da yayanki yake Miki Fiye da Sau Goma Nayi Miki alkwarin Zaki Sameni mai kyautatawa da kulawa da abun da Mijina yafi so da kauna.!
Sai ga Munari na Dariya da kuka Tace”Da gaske..?Zaki zame mana Haske a wannan gidan Anty Safiya..? Wlh Farinciki ya Dade da Kaura a wannan Gidan Don Allah kizama Sanadiyar Dawomana da Farincikin da muka rasa..!
Sai kuka Jikin Safiya ya kara yin Sanyi ta kama Munari ta Rugume tana Lallashinta Lokaci Daya Tana Fadin”Da yardan Allah.ammh sai kin Bani Dukkan Hadin kai!
Munari ta Dago Tana Fadin”Insha Allahu ina Tare Dake..!
Safiya Tayi Mirmishi Tana Fadin”Yauwa..To maza Share Hawayenki Kuka ya Kare..Bani Labarin Ya imu..?Shi dai Duk da ban Zauna Dashi ba Yusuf na bani Labarinsa yafi ye Fushi da Zuciya ko..?
Munari na Share Hawayen tace Cikin Dariya,”Rigimamme kenan.ai Ya imu Dabam yake acikin Gidanmu..Bamai irin Halinsa..Shifa Ya Imu bakomai ke Damunsa ba Baya Shiga Abunda ba Ruwansa Ko kuma yayi shisshigi kan Rayuwar wani yafi Damuwa da kamsa Fiye da kowa abaya..Ya Imu yana da Wuyar Sha”ani ko kema sai kinyi a hankali kin bi a Sannu Zaki iya gane wasu Daga Cikin Hallayarsa,Yana da Murdaddan Halin Da bamai iyamai sai Allah Daya Hallicesa ko Abba sai dai ya Kada kai ya Bisa da Allah ya Shirya Ballatana Ya Yusuf Shi din kaifi Daya ne In yace Abu to baya barci sai ya Tabbatar Dashi Baya Saba mganarsa Mutum ne Dabaya karya,Baya kuma shayi ko Tsoron Fadin mgana koda Za”a Kashesa ne yana Da Dakakkiyar Zuciya irin na Jaruman Maza,Bashi da Fara”a ballatana yawan Dariya Miskiline sosai na Bugawa a ajarida Bashi da Sakewa da Mutane infact ma Baya son Mutane ya Imu yafi jinDadin Rayuwa Shi kadai Fiye da Cikin Mutane ko da yan”uwansa ne Bashi da Sakewa da Mata koda kannensa ne Koda Nice Bashi da Sakewa dani..Tsakanina Dashi ke ina wasa Dake ni..?ni sa”anki ne..?kin Raina mutane ko..? Tashi ki tafi Dakinki ki ba Mutane waje kafin na Sauya Miki Kammani..! Ya tsani Raini Shiyasa Tun yana amsa sunan Imran dinsa Baya Harkan Mata Nifa ko Daidai da Rana Daya bantanajin Yayi Budurwa ba,Ammy nasan a Yadda yake Kyakyawan nan wannan bazai rasa masu Sonshi ba Ni kaina Wasu Hallayar nasa suna Burgeni Barin ma Kaifinsa yana da Zuciya Bakar Zuciyar da in Ta tasomai kowa sai ya Tsorata,bazan Tsaya Misalta Miki ya Imu ba sai dai nace Miki Shi din na Dabam ne da Duk yadda kika ga kai ga Hangenki baki isa ki iya Ganosa ba Duka ba sai dai ki San wanda kika sani Shidin kamar Wahainiya ce kullum Chanza Launi yake..Baya Lallashi sai dai Shi a Lallasheshi bashi da Rauni ko kadan Dakiya garesa da Kafiya In aka Taba wani nashi nan ne Za”a ga waye Ya Imu Bashi da Sakin jiki da Ahalinsa ammh Acikin Kirjinsa yafi kowa sonsu..Na Rantsw har ga Allah ba wanda ya isa ya Dagama Gidanmu yatsa kafin ya Saukr ya Imu bai karyasa ba Salon Soyayyarsa ba irin Takowa bace tashi Salon ta Nuna kwanji ne..!
Munari ta karishe Fada Tana Sakin Mirmishi Safiya Tace”Ai nima nagani DAyazo Gidanmu Duk Fadan Abbu Sai da ya Sauraramai..!
Munari tace”Haka yake..Bashi da abokai Rayuwar Duniya bata Damesa ba..Baruwansa da kowa Shi kawai Rayuwarsa ya sani shi kadai sai Abokinsa Daya Sagir wanda Mamansa Abba yace ta Rakoki..Shi ne kadai abokin Ya Imu..Shima din abotarsu Wani kaddararran Lamari me Daga Allah..Allah ya Riga ya Hada Jinsu Bayan Kaunar abota akwai Kauna wacce Allah ya Hadata a tsakaninsu Duk yadda Imu yakai ga yakice Sagir bai Yakican mai ba,Dole ya Rabu Dashi zasu hadau suyi Fada kuma Duka Fadan Ya Imu ne ke jansa Shi Mutum ne da in ba kansa ba ko Allah sa ba bamai iyamai ammh Kuma ahakan suke Tare ko Daya bai Nemi Daya Daya zai nemi Daya kuma Dashi da Mahaifiyarsa kadai Muke Mu”amala kuma sune suke Shigowa Gidan nan kai Tsaye Batare da wani Shamaki ba..!
Safiya ta jinjina kai kafin Tace”Tabdijam..Wannan matar da zata aureshi nake Taausayamawa..!
Munari ta kwashe da Dariya kafin tace”Ai ba Matar da Zata iya Zama Dashi.. Nifa aganina..Shifa bai Damu ba..Da ya Imu yayi aure mace ta Rainasa Ya kuma zama akwai wacce yake kula da ita bayan kansa gwara ya To ya Mutu bai yi auran ba bari ma Kiji na gayamiki..!
Safiya ta Zaro ido tace’Bala”i..!
Me Munari Zatayi ba Dariya ba sai itama Safiyan tabiye mata suka yi Dariya Sosai Har da Tafawa Hira Tayi Dadi.
Safiya tace”Nidai bani Dan satan amsan yadda Zan zauna dashi..Kada watarana nayi mai Ba daidai ba ya Chanxamin kamani..!suka saka Dariya atare kafin Munari tace”Bazai Dake ba..Ai Baya Duka sai Ransa ya baci..Ko ni bai taba Dukana ba yasha Dai Fadan zai Dakenin a baki,Sai da mari ko tokari..kawai ki kiyaye baya son yawan gaisuwa,Baya son Hayaniya bayason ana Bugamai Kofar Daki ko kwana yayi bai Fito ba Kada wanda ya Nemeshi,Bai cika Cin Abinci ba yafi shan Fruit sai abu na Karshe Yana Shan Sigari kuma yana bata Muhimmaci..sannan koda baka son Warinta indai yana wajem Dole kayi Hakuri ka Shaketa ya tsani ka Toshemai Hanci Saboda gani yake Kamar shi kake kyama in kika Kiyaye wannan Babu wani abunda Zai Hadaku kila sai kuyi Sati Baku Hadu ba..Shi bamai Sakewa da mutane bane Yafi jin Dadin Rayuwarsa Shi kadai ko afalon nan baya Zama a koda yaushe in bai Fita ba yana Dakinsa ne..!
Safiya ta jinjina kai kafin tace”Ai indai Wannan ne zan kiyayemai kada Watarana yace Min Safiya Kin rainani ko..?
Gabadayansu suka Saka Dariya Suka Tafa jikake Tass..Har sai da kaji karan hannuwansu in ka kallesu alokacin kamar sun Shekara da sanin juna.
Safiya ce tace batayi Sallah mangariba ba jin ana kiran Sallar Isha”i Ita kuma Munari tace Tayi mangariba Saura Isha”i su tashi suyi Sallah kafin Ya Yusuf ya Dawo.
Nan suka Mike Safiya ta Fara Shiga Tayi alwala itama Munari Ta Shiga Tiolet din Yusuf tayi Alwala Dayake ita ke gyaran Dakin koda yaushe ba inda bata sani a ba adakin.
Tare sukayi Sallar adakin Safiya tayi mangariban ta Ta Dora da Isha”i Ita kuma Munari Tayi Sallar Isha”i din da batayi ba,bayan sun idar suka Dasa kuma wata Sabuwar Hira Zuciyoyinsu ta Cika da Farinciki ita Munari ta Murnan Zuwan Safiya a Rayuwarsu Farincikin da suka rasa zai Dawo ta kuma Samu abokiyar Hira ita kuma Safiya Tana Murnan Ta samu kanwa Bayan Tasleem,Bazata yi kewa mai yawa ba,kuma nasan Ta Tabbata bazatayi nadaman Auran Yusuf ba.
Suna tsaka da Hiran nasu
Daidai Lokacin Yusuf ya Turo kofar ya Shigo da Sallama da Ledoji Guda Hudu a hannunsa na Tambarin kamfanin Gidan Abinci.
Yadda ya gansu sai da yaji Zuciyarsa Tayi sanyi,Suna ganinsa suka Mike Ita Safiya Tana gyara Zaman mayafin kanta Ita kuma munari baki ta washe Tana fadin”Sannu da zuwa Ya yusuf..!
Lokaci Daya tana karisa garesa da Niyarvkarban Kayan Hannunsa.
Bakinsa Shima a washe ya amsa mata Lokaci daya yana kallon safiya yace”Babe kina samu akun Abba ko..? Nasan munari tayi keeping dinki Company..Nasan kanwata akwai son Hira..!
Safiya kanta na Kasa ta Murmusa Tana wasa Da Gefen Mayafinta tace”Yes She so so Nice..I love her..!
Munari najin Haka ta saka Tsalle Tana Dariya Shima Yusuf din sai da ya Dara Lokaci Daya yana Fadin”Ke kullum baki san kin girma ba Lilsis..? Above 20 fa..Kuma kina Yar jami”a Nan da Shekaru uku masu zuwa u are Going to become a Graduated in Ecocomics..!
Sai ta Daina Tsallan Ta koma ta Natsu Tana Fadin”Wlh kuma hakane Yaya..Na bari..Yanzu ai am Mature ko..?
Tafada Tana nuna masa kanta Dagashi Har Safiya sai da suka Dara Ledan Dake hannunsa Guda Uku ya mikama Munari Dayan kuma ya ijiyeta nan kasa sai dai ta karba yace mata”Ur Dinner..!
Munari ta karba Tana Fadin”Allah yasa Fride rice ce Ya yusuf..!
Yana Dariya yace”Mayar Fride Rice itace..Ki Dauki Dayan Ledan Is Urs..Daya kuma na Abba ne ki Tabbatar kin Bashi yaci yasha Mgani ya kwanta..Dayan kuma is for ur Brother Imran..!
Munari tayi Narai Narai da ido Tace”Is He at Home..?
Yusuf yace”Check his Room..!
Munari ta Kara narke fuska Tana Fadin”Kasan He warning me kan Bugamai Room dinsa ko Ya yusuf..? In ba so kake ya Sauyamin dis My Beatifull Face ba is ok sai naje..!
Yusuf ya kada kai yana Mirmishi yace”Shikenan ki aijiye Cikin Frigde din Kitchen if He Wanta Zai Shiga ya Dauka..Daman Choice dinsa ne Kayan Lambu!
Munari tace”Tanque Ya yusuf..Sai da Safe..Anty Safiya see u Tomorrow..!
Tafada tana Daga mata Hannu itama Safiyan Dagamata Hannu Tayi Tana Fadin”Ok see u Lilsis..!
Daga haka ta Sa kai zata Fice yusuf ya Kirata ta waigo yace mata”U make Sure kin kwanta da Wuri..No Chart no Reading ko..?
Kai ta gyadamai Tana Fadin”I promise u bazan yi ko Daya Daga ciki ba sai Barci..Basai kazo Dubani ba Ka zauna ka kula da Anty Safiya Dakyau asha Amarci Lafiya..!
Tana Gama Fadar haka ta Fice da Gudu ta Rufo Musu kofar suka Bita da Dariya dukkansu.
Sai alokacin Yusuf ya juyo zuwa ga Safiya ya Fara takawa Zuwa gabanta Idanuwansa kyam a kanta Ita kuma gabanta na Fadi kanta na kasa.
Sai da ya iso gabanta bata Tsammaci Haka ba taji ya Rumgumeta Kamkame kamar wani Zai kwaceta sai kuma Taji ya saki kuka Cikij kukan yake Fadin”Tanque so Much Babe..Kin yimin Abunda Har na koma ga Allah bazan manta ba..Allah ya bani ikon Rike ki Cikin Aminci da kauna kamar yadda kika Nunamin..!
Sai kuma ya kara Sakin mata kuka Tuni Taji ta Rude itama bata san Sadda Ta Saka hannu ta Rumgumeshi ba ta Saki nata kukan Tana Fadin”Basai kamin Godiya ba..Ka Chanchanta My Dear..Kaunarka gareni ce ta Sanya ka ganni Tsaye acikin Dakin nan a kuma Cikin Gidanku nidai Fatana ka Rike da Amana My Dear Ka soni Sosai Fiye da yadda nake sonki..!
Yusuf na jan Majina yake Fadin”I do..Wlh I do..!
Haka kurum yake Fada Kamkame Juna Sukayi kowannensu na kukan Fitar da Abunda ke Cikin Ransu Har sai da suka gaji suka koma suna Lallashin Juna gefen gado ya jata ya Zaunar da ita kan Jikinsa yana Fadin”Babe don Allah kiyi alfarman bazaki gayyatomin kowa Daga Barayinki ba Nan kusa Har sai na gama Gyara Miki Bangaranki na Saka miki komai na kuma yi miki kayan Lefen da kowani Namiji ke yi ma wacce yake matukar so ya ganta Zai Aura..!
Safiya ta Sakarmai Ido Cike da kwallah Kafin tace”Ban yi maka wannan alfarman ba My Dear..!.
Cikin mamaki ya Tambayeta”Saboda Mene Babe na..?
Safiya ta Runtse ido ta bude kafin tave”Kayan Lefe na yafe maka su..Kayan Daki kuma ai ba Harumin ka bane na Iyayena ne..Ni ka kyaleni nan Dakin bai Ishemu Rayuwarmu bame Dagani sai kai..?
Ga falo chan ga Kitchen ga komai na Bukatar Rayuwa..?me kuma nake nima Ni Safiya banda Kwanciyar Hankali da Zama Lafiya da Mijina da Sabon Gidan dana Tsinci kaina..!
Ta karishe Fada Hawaye suna kwanroyomata Da Sauri Yusuf ya Rumgume tsam yana Fadin”Ba Saboda Ke zan yi kayan fa..Saboda kaina ne ki Rika sakawa kinamin kwalliya Dasu..Mganar Kayan Daki kuma ba Ruwanki Zamu koma wanchan bangaran nan da wani Lokaci ba Saboda ke saboda kyawawan Ya”yan da Zaki Haifamin nan gaba..Ni su Abbu sun gama min komai Tunda suka Bani ke bana Kuma Bukatar Komai Daga Wajensu!
Ta Dago kanta ta Bude baki Zatayi mgana ya Hanata bayan ya Dora Hannunsa saman Lebenta yace”Shii…Zamu je mu gaishesu in muka Samu Natsuwa..Ammh all i say hakan ne Zai Faru..!
Bata da ikob Sake mai gaddama sai ta koma Bisa Kirjinsa ta Lafe yana Rike da ita kamar wani zai kwaceta.
Ahaka ya sauko Da ita saman Cafet ya jawo Ledan dan ya Fito musi da Takeway din Daya yi musu sai kaZa Gashashiya da yourghot,mai Sanyi Dakyar taci Shinkafar ya Hadamata da Kazan da Madaran sai da ta kusa amai ya kyaleta kana Shima yaci Sosai yasha Madaran Daga gani kila ya Wuni bai ci komai bane Kamar Tayimai Hawaye,bayan sun gama Tana Nokewa ya kwasheta zuwa Tiolet ya sakarmusu Shower Dole suka yi wanka Bayan sun gama Nanikan juna Duk da Yusuf din bai mata komai ba sai dai Rumguma da Kiss haka.
Alwala suka Dauro,ya jasu Sallah Raka”a Shida Bayan sun Idar yayi musu addu’o”i sosai na Zaman lafiya kafon suyi Shirin Barci Shi ya Bude akwatin Safiya ya Dauko mata Wata Rigar barci guda Daya wacce wajen Tuso kayaneta Shigo ammh ko Barayin kayan Barcinta bata Bude ba Tana Nokewa Tana komai ya Dauketa ya aza kan gado ya Cire mata Doguwar rigar Data sakata yanzu Tunda kayanra sun Jike suna Tiolet Yusuf ya Shanya mata.
Hakan nan ta Runtse ido ya sakamata Rigat barcin Shima ya Tube Dagashi sai Boxers ya Hayo gadon ya Ciccibita ya sakata Cikin Jikinsa ya Nadesu Cikin Blanker Bayan ya Rage Hasken Dakin yana jinta yadda Take Mutsu Mutsu da kuma yadda Zuciyarta ke Bugawa.
Cikin Mirmishi ya Sunkuya kunnenta Yayi mara Rada yana Fadin”Relax babe Babu Abunda Zan yi miki ayau din nan..Ban kuma ce Gobe ma haka ba kawai dai kafin mu Zama Daya Dani Dake nake so na baki Labarin GIDANMU..labarin da kika so kiji ban Taba Fadamiki ba Labarin da ban Taba Gayama kowa ba sai ke yau din nan..Ba saboda komai ba sai Saboda Daga yau din mun Riga mun Zama Abu Daya Komai nawa naki ne Komai naki nawane haka Sirrina naki ne kamar yadda Sirrinki yake Nawa Babe na..!
Safiya Dataji Abun kamar a Mafarki ta Dago da kanta bata ganin Fuskarsa Saboda Duhu sai dai tana iya ganin Shedar Fuskar tashi Cikin Tsananin Farinciki ta Damke hannunsa Tana Fadin”are u Serious..!
Kai ya Gyada mata kafin yayi mata Kiss a goshinta cikin so da kauna Rumgumesa Tayi sosai Tana Fadin”Tanque Dear..Uhm…Am all Hears..!
Yusuf ya kara Riketa ajikinsa Bayan ya zagayo da Hannyensa Bayanta zuwa Saman Cikinta lokaci Daya ya Sauke ajiyar rai Dana Zuciya Tuna abunda ya Faru dasu Shekaru uku Zuwa Hudu da suka gabata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button