GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Shakira…
3/22/22, 23:04 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)

         🅿�13

DR.ABUBAKAR HAMISU DUKKU (Malami) shine Asalin sunan Mahaifinmu,Dr ne a bangaaran Ilimi kuma Malami ne Daya shafe fin shekaru Goma yana koyawar a Jami”ar Lagos, Wato a University of Lagos Fanni Sanin Hallayar Dan Adam Wato Phsychology
Sunan Malami kuma da Abbanmu ke Amfani Dashi ya samu asali ne akan Tun yana karami yake kaunar Zama Malami Dalilin haka yasa Mahaifinsa Marigayi Alkali Hamisu Dukku ke kiransa da Malami Tun yana amsa Sunan Abubakar Hamisu Dukku Har Dukkun ya bace bat ya koma amfani da Abubakar Malaminsa Duk wanda ya sansa da wannan Fitattacen Sunansa ya sansa.
Mahaifinmu asalin Bafullatanin Gombe ne ta Uwa ta Uba,Daada da Marigayi Alkali Dukkansu Haifaffun gombe ne,A karamar Hukumar Dukku Dake Jahar na Gombe.
Awajen Mahaifinsu su Biyar ne Uku Maza Mata Biyu Abba ne D”a na Biyu awajensa,Akwai Baffa Kabir,sai Baffa Mustapha,sai Goggo Bintalo sai Karamarsu wacce Munari taci Sunanta Maimunatu.
Abaya kafin Rayuwa ta Juyamana Gidanmu Gida ne na Soyayya da kaunar Juna da kuma Hadin kai.
Mahaifiyarmu Hajiya Zuwaira auran Zumunci ne Tsakaninsu da Abbanmu,Domin Daada Mahaifiyarsu Diyar kanwartace ta Dauketa ta Riketa awajenta Har ta aura ma Abba ayadda Anni ta sanar Damu Lokacin Abba ya kawo wata tace da Niyyar ya aura Wata Shatu wacce suka Hadu da ita a Jami”ar Jos,inda yayi Karatu Sai Daada Ta nuna A”a ta kuma wanke Mahaifiyarmu Anni ta bashi bai Mata Gaddama ya saka Hannu Bibbiyu ya karba Domin Shi Mutum ne mai Sanyin Hali da Biyayyah.
Da Farko ba a Lagos su Abba suka Fara Zama ba sai da suka zauna a nan Cikin garin Gombe,Lokacin yana Assistan Lacture ne a jami”ar Gombe Bayan Kamallah Degree dinsa na Biyu ne Ya samu aikin Bayan auransa da Anni kuma ya Daukota Zuwa Gombe.
A garin Gombe aka Haifi Yaya Nura da Ni da kuma Imran Sai Zuwa Lokacin Abba ya gama Hada Phd dinsa Ya samu Sauyin aiki Daga Jami”ar Gombe da Tuni Daman ya koma mataayin Senior Lacture.
Muka Tattara muka koma Lagos da zama acikin Tsakiyar garin Lagos A wata anguwa mai suna Vitoria Inland..!
A lagos muka Dora Sabuwar Rayuwa,Daman Tun a gombe Ya Nura da ni mun Fara zuwa makaranta Dayake Dukkanmu Har Imu Haihuwa Kai kai ne Cikin Shekaru Hudu Anni ta Haifemu mun taso Gabadayanmu kanmu Daya ne,Da muka koma Lagos ne Abba ya Sanyamu a Wata makarantar kudi mai kyau mukaci Gaba da Zuwa,A kuma garin ne aka Haifi Asma”u da Salima sai Munari Itace Auta.
Yusuf Daya kawo nan a Labarinsa Safiya Taji shuru Tana jinsa ta Muskuta ta Dago tana kallonsa jin yayi Shuru Duk da bata ganin Fuskarsa Tace”Ina jinka My Dear sai akayi yaya..? Ina Anni ina Ya Nura da Salima da Asma”u..? Ina kuma yan uwanku na Dukku Sauran Yan”uwan Abba..? Kuma wani Dalili ne ya Dawo Daku Rayuwa A kano Bayan komai naku yana Lagos..? Me kuma ya Faru da Abba Har ya samu wannan Rashin Lafiya..? Kuma meneme ainihi yake Damunsa..?
Ta karishe Fada Cikin zumudi da son Jin karshen Labarin Gidansu Yusuf.
Yusuf Da Jikinsa yayi sanyi Baya son Tuna Labarin nan ko kadan Ammh Ya Zama Dole ya Karishe ma Safiya Labarin nan ko Zata Fahimci ba Wai Da gangane ko Rashin asali ne ya Maidosu Rayuwa su kadai ba Wani Kadaddaran Al”amari ne da Allah ya Riga ya Rubuta sai ya Faru.
kara kamkameta yayi ajikinsa Kafin ya Cigaba da mgana Cikin Sanyin Murya da Sarewa.
Mun taso Cikin Soyayya da kauna ta Kowani Fanni Abba Mutum ne mai Dattako da Sanin ya kamata mai kula da Iyalansa da Danginsa Duk da muyi Nisa ammh kusan Duk wata yana Hanyar Gombe zuwa ganin Daada Bayan Rasuwar Mahaifinsu Alkali Hamisu Wani Lokacin Tare da Anni suke Tafiya wani Lokacin kuma Shi kadai mu kuma muna Zuwa makaranra Tun safe sai yammah in mun Dawo gida akwai malamin da Abba ya Daukar mana yana Koyamana Karatun addini Sakamakon ba Lokaci sai ya kasance sai mu Fi Shekara bamu Taka garin Gombe ba,gwarama ya Nura Dani mukam bi Abba Gombe in zai je Hutun Karshen Shekara sai abar Anni da su Asma”u a gida Kafin mu Dawo Shiyasa Duk Cikin mu muka Sanin Dangi Dangi ma suka fi Sanin mu.
Lokacin gaskiya Zumunci yafi karfi ta Bangaran iyayanmu mu ya”ya bamu Damu dashi ba Kowanne ya”yansa na makaranta gashi ba”a zaune waje Daya,Ballatana arika Ziyarar juna akai akai Ballatana asan juna Sosai.
Bamu san kowa ba sai Abba da Anni sune Duniyarmu Gaba da Baya Abba ya Sadaukar da komai nashi Saboda mu Anni kuma ta Sadaukar da Lokacinta da Lafiyanta Wajen Tarbiyantar damu da kula da mu,Lokacinta da komai namu ne Muna Matukar sonta da kaunarta Domin Duk Fadin garin Lagos Daga Anni sai Abba sai sauran yan Gidanmu kadai Muke Dashi Duka Dangi Basa kusa Baffa Kabiru yana Abuja Baffa Mustapha yana Kaduna Sai Goggo Bintalo tana aure a gombe ne Goggo Maimuna kuwa Tana aure a Bauchi ne Daada kuma Tana Asalin Gidansu na Dukku ne sai dai Aje Chan adubata.
Duk Cikin mu Imran ne kadai yayi makarantar kwana acikin Garin Lagos yayi karatun Karamar Secondary Dinsa har Zuwa babba Primary ne Kadai yayi ta Jeka ka Dawo,Ba wanda Yayi mamakin Zabinsa Saninsa Shi bamai Son Sakewa da Mutane bane da Hayaniya Shiyasa yana garin Lagos ammh Sai an Samu Htu kamar Sauran Dalibai yake Zuwa Hutu Gida Shiyasa Gwara Kowa Dashi Ko Dukku Sai ya fi Shekara uku bai Taka ba,ko ya Dawo Hutu in Abba yace ya Shirya aje Dashi Sai yacFara Ciwon karya Saboda Bayason Zuwa Ballatana ya Shiga Mutane ko acikin Gida kowa yana Zaman Falo banda Imu Shi din Hallitarsace Miskilanci da Rashin Son Sakewa,Kowa Daya Fahimci halinsa ne sai kowa ya kiyayemai Ammah banda Asma”u itace Sakon sa Shiyasa Take Shan Wahalansa Kusan in ya Dawo Gida Hutu Kafin ya koma Sai ya Barta da Tabbai Akwai Lokacin da Ya Daketa Har sai da ya Sumar da ita Ran Anni ya Baci ta Mareshi Shine Imu yayi Fushi Lokacin yana Farkon Shiga SS3 NE daya Koma makaranta bai kara Waiwayan Gida ba sai da ya Zana Jarabawarsa Duka ya gama da makaranta ya Dawo Lokacin Ni da Nura Mun samu Gurbin Karatu a Jami”ar Lagos,Tsakanina Dashi Shekara Daya ne shiyasa Karatun namu yake Tafiya kai da kai.
Abun bai bama Kowa mamaki ba Da Imran ya Cike Jami”ar Ibadan,Sanin Halinsa Chan ya Tattara ya Tafi karatu inda ya Zabi bangaran accounting,Wani Lokacin sai ayi Hutu Nawa bai zo Gida ba sai dai Abba Ko mu mu kai Ziyara Abba ma yafi Zuwa wani Lokacin in ya Dawo Daga Gombe yana Biyawa ta Wajensa Tunda Shi ya Haifi Abunsa yafi Kowa Sanin Halin kayansa Anni ce ke Damuwa Tayi ta Fadan Imran bayason yan”uwanshi Ballatana Danginsa Tunda bayason Zama Dasu,Abba ke Tausanta Lokacin yana Fadamata ta Cigaba damai addu”a Halinsa kenan,Tayi ta Korafin Dangi ba wanda yasan sa sai dai sunansa Tun yana karami Rabon Daya Taka Gombe Duk Zuwa sai Daada Tayi Mita da Korafi Sai dai Imu bai Damu ba yafi Damuwa da Abunda ya sakama Gaba Fiye da komai a Rayuwarasa.
Haka Rayuwarmu ta Cigaba da Tafiya Ni da Nura muka kamallah Digree din mu na farko muka Dora na Biyu da Kwarin Gwiwan Abban mu Asma”u kuma ta Fara Karatu a Lagos state university Lasu Dake Lagos, Tana karantar phamarcy Salima kuma Tana Shekarar Karshe a matakin Secondary,Munari kuma Tana baya Saboda ita din Daga Karshen Anni ta Haifeta Bayaan Salima ta Shekara bakwai a Duniya.
Zuwa Lokacin mun san Dadin Dangin mu da kanmu mukan Shirya mu Ziyarcesu ko da Abba baice ba Barin ma Nura yafi kowa son Zaman arewa Domin yace yana Burin ya samu aiki a arewa Yayi aure ya koma Chan da Zama,Shiyasa Duk bayan Wani Lokaci muna Ziyartsu Munje Har Gidan Baffa Kabiru da Baffa Mustapha da kuma Goggo  Bintalo,Da goggo Maimuna kuma sun ji Dadi Sosai Daada kuwa Muna da Lambar ta Lokaci Bayan Lokaci muna kiranta muna gaisawa Sai dai Koda yaushe mukayi Waya da ita Zencen ta Daya kenan Imu,Shi kuma Yana Chan makaranta ba Sosai ma yake zuwa Gida ba.
Sai Lokacin Daya gama Degree dinsa na Farko yazo Gida Hutu Lokacin ne Abba ya Rutsashi ya iza keyarsa Har Zuwa Dukku Gaban Daada Sai da suka kwana Biyu suka Dawo a wannan Zuwan ne Har su Baffa Kabiru sun zo Sun gansa Shima Lokacin yazo da’ Wajensa Khamis Sa”an Imu din ne ammh Har suka Rabu Wata kyakyawan Mu”amala bata Hadasu ba  imran bai da Sakin jiki Sam da Mutane Daada Tayi mai Nasiha yayi bakam Kamar yaji yana komawa gida ya yi Cuku cukun ya koma Ibadan ya Dora Degree dinsa na Biyu,ya manta Da Fadan Daada.
Rayuwarmu Gidanmu Mun ginata Cikin Karatu Mai Zurfi ne Duka Dana Arabi Dana Bokon Harta Salima itama Tabi Sahu Ta Fadama Jami”ar Lagos ita Fanni Abba take karanta Wato Physchology
Muna gama Hada Degree din mu na Biyu Muka Samu manyan ayyuka Nura ya samu aiki a Federal Inland Revenua Service(FIRS)Wato Hukumar Haraji ta kasa Dake Jahar Lagos,Yaso ya samu a arewa sai kuma Allah ya Rubuta nan ne wajen cin Abincinsa.
Ni kuma na samu aiki a Hukumar INEC,rejen Jahar Lagos muka Fara aikin mu Cikin Lokaci kadan Cikin Naaara da Sa”a bamu Rufe Shekara Daya ba muka mallaki Motocin Hawa Dani da Nura,Da kudaden da muka Fara Ragema Abba Wasu Hidimdimun Ko Chan Dukku baya sanin muna turama Daada Sako Sai dai in ta Kirashi Tana Godiya ya sani.
Asma”u ma Ta gama Karatunta Har ta Fara aiki a wani State Hospital na Lagos a phamarcy, Dake Garin Lagos Salima ita kuma Tana Karatun ne bata gama ba,ita Burinta so Take ta Zama Dr.Salima Watarana Ta gaji Abba Ashe Ashe Burinta bazai Cika ba Domin Lokacinta aduniya bamai yawa bane..!
Yusuf ya Fada Hawaye masu Zafi suna kwaranyomasa Jikin Safiya yayi Sanyi Gabanta ya Fadi Cikin karyewar Murya tace”Innalillahi badai Rasuwa Tayi ba..?
Yusuf yaji Rauninsa ya Bayyana Cikin Karyewan Zuciya Dana Murya yacCigaba Da fadin”Imran ma ya gama Karatunsa ya Fara aiki da Bankin GT reshen Jahar Lagos Shima ya mallaki Motar Hawansa,da kudaden Daya Tsaya kan Kafafunsa..
Faruwar al”amarin Daya Faru damu ko nace ya afku ga gidanmu kaddaran Da bamu isa mu guje mata ba,..Gaddaran Datayi Sanadin da muka Rasa komai namu Kaddaran Dayasa muka bar komai namu muka zo nan muna Rayuwa inda bamu da kowa..
Watarana ce da Zukata da gangar Jiki bazata Taba Mantawa Dashi ba,Baffa Kabiru ne ya samu Hatsari Daga Garin Abuja zai je Dukku bai ma yi Nisa ba saosai al”amarin ya Faru aka Dawo Dashi Specialist Dake Abuja aka Bashi Taimakon gaggawa Jikin nashi Da Sauki ba karaya sai dai Yaji Ciwo Kadan kadan Motarsa ne tayi Dameji bama Zata taahi ba Hankalu suka Tashi Kwarai Abba da Anni Ranar basu Iya barci ba Abba Sai Mtsawa yake a samu Buking din Jirgi Zuwa Abuja,Allahu akbar Allah Sarki Rayuwa Nura Shi yaje Filin Jirgi yayi Cuku Cukun komai,Allah ya Rubuta Lokacin Abba aduniya Bai kare ba wani Taron Malamai ya Tsaidashi,Ni kuma A wajen aiki ba”a barni ba Imran kuma Bama wanda yabi ta kansa Sanin Halinsa Ganin haka yasa Abba yace Nura da Anni da Salima da Asma”u su  Farayin gaba Kafin mu muzo Daga Baya Tunda Lokacin Munari suna Jarabawa a makaranta,Abba kuma Zai Tsaya Taron su na Malamai sai Zuwa Gobe in sun gama Ni dashi Zamu Bi Jirgi zuwa Abuja muje mu Duba Baffa Kabiru Tunda Duka yan”uwa sun isa Chan Abuja.
Har yau bazan manta da wannan Ranar ba Imran Tun bakwai na Safe ya Fita Zuwa Wajen aikinsa Munari na makaranta Ni Abba yasa na kai Su Anni da Nura da Asma”u da Salima Filin Jirgi na Murtala Muhammed ban kuma bar Wajen ba sai da Jirgin su ya Tashi ya Lula Sararin Samaniya.
Na Dade tsaye Afilin jirgin bayan Tashinsy Na kasa Shiga Mota na koma Wajen aikina Haka kurum nake jin kaina wani iri kamar Wani abu Zai Faru Dani ashe ashe kuwa hakane Na koma Office na kasa Tabuka komai ko Cikakken Minti Talatin banyi ba Wayar Abba ta Shigomin ina Dagawa Naji Abba Cikij karaji yana Tambayana Jirgin su Anni ne ya tashi Minti Talatin da yawuce..!?
Ni kaina na Rude bansan ina kaina yake ba Cikin Rudewa nace ma Abba Eh Sune Daganan ban ji komai ba sai karar Faduwar Abu naji Da Hayaniya Daganan naji Shuru Hankalina ya Tashi na Fito Jikina narawa anan naji Labarin Dayayi barazanar Tafiya da Numfashina Wai Jirgin Airic Daya Tashi Daga Filin Jirgin Murtala Muhammed Daga Lagos Zuwa Abuja Minti Talatin da suka Wuce ya Fadi a wani Daji Bayan ya bar Lagos.
News na gani a Tv Dake ma”ikatan mu…!
Yusuf yana kawo nan ya Saki kuka mai karfi Safiya ma Tuni Ta Fashe da kukan Cikin kukan Take Fadin”innalillahi Wa”inna Ilaihirraju”un..Daman yan Gidan ku na Cikin wannan Hadarin Jirgin Daya Cinye Rayuwanka Yan arewa Da yawa..!?
Yusuf na Kuka yace”Da yan gidanmu Safiya..Da Anni da Nura da Salima da Asma”u Sun konee kurmus ko gawansu bamu gani ba kawai nidai na Farkane na ganni a asibiti Imran na Gefena yana ta kuka Kukan Da Tunda nake dashi ban Taba ganinsa yayi kuka ba,ina mikewa na Fara Tambayansa ina Abba sai dai bai min mgana ba ya Nunamin Abba Dake gefena Kwance Shima anamai karin Ruwa,Safiya bazan Tsaya baki Labaein Irin Tashin Hankalin da Muka Tsinci kanmu aciki,Abba ya Farka yana kuka yana Fizge Fizge yana Kiran sunan Anni da Nura da Asma”u da Salima Likitoci sun kasa Controlling dinsa Bamu da wani kwarin Gwiwa Domin Rashin da mukayi Babba ne wanda Babu Wani Abunda zai iya maida wannan Gibin.
Ni da kaina na kira Wayar Baffa Mustpaha na Sanar dashi ina kuka Chan ma Hankula suka taahi Domin Gabadaya Hadarin Jirgi a Karade kasa Tunda Yawanci Duk yan arewa ne da Wasu manya a gwannati.
Dagani Har Imran bamu kwana agidanmu ba Ni naje makaranrar su Munari na Daukota muka Koma asibiti muka Hada kai mu uku muna kuka Tun Munari bata gane Har ta Fahimta nan muka kwana da Abba asibiti,washegari kuma Baffa Mustpha da Baffa Kabiru Da ciwon da komai ya tashi ya Taho,sun same mu Cikin Wani Hali,Abbanmu kuma ya Fara Fita Daga Hayyacinsa Batare da Shawara damu ba suka Gama Cuku Cukunsu sukayimana Bukking din Flight Bayan sun karbi Report din Abba na asibiti din Abba Suka Tarkatamu Zuwa Gida muka Debo kayanmi Harda na Abba Dana munari Suka Tasamu agaba Sai Filin Jirgi Duk da Tsorata da Hawa Jirgi daya shiga Ranmu Hakanan muka Shiga bazan manta ba sai da Imran ya Suma Saboda Firgita.
Daga Lagos Gombe muka Sauka Mijin Goggo Bintalo yazo ya kwashemu sai Dukku Gidan Daada koda muka isa Gida ya Cika da Dangi ana ta Koke koke Daada Tayi kuka kamar Idanuwanta Zasu Makamce,anan akayi karban Gaisuwa Har akayi Sadakan Bakwai Abba Baya Cikin Hankakinsa sai sambatu da Surutai,Mukan mu gamu nan kawai ammh Komai ya Fita kanmu da Rayuwarmu Gabadaya Bama da Wani Tunani sai abunda aka Fadamana Tunanin mu da komai ya Tsaya Cak.Har gwarani akan Imran da Munari ana ganin kamar bai Damu da Danginsa ba Ashe ashe abun sai yafi Tabasa Fiye da kowa.
Saboda Halin da Abba yake Ciki yasa bamy koma Gida ba muna Dukku gaban Daada sai dai duk Sati Baffa Kabiru da Baffa Mustpaha suna Hanyar Zuwa ganin Abba ya Kamu da Cutar nan ta Depression yasa Suka Daukesa suka kaisa asibiti aka Dubasa aka bashi mgunguna da Shawarwari da Farko Abun kamar yayi aiki Daga Baya sai Abba ya Kara Rikicewa Bawanda zai Fahimci Halin da Abbanmu ke Ciki  sai mu da muka Dandanin Zafin Abun,Shiyasa cikin Yan”uwan Abba suka kasa mai Uzuri Ballatana su Fahimci Wani Hali yake Ciki basu Taba Dadanin Zafin Rashin Daya Dandana bane Shiyasa suka Fara ganin Laifinsa suna Fadin bai da Takwalli ne Dagashi har mu da kullum bamu da aiki sai mu tasaahi muna kuka ai ba kanmu Farau Mutuwa da Rashi ba Anni da Asma”u da Salima da Nura Sun Tafi kenan har Abada bazasu Taba Dawowa ba..Daada ce Kadai ta Fahimci Halin da Abbanmu da mu kanmu muke Ciki Baffa Kabiru yafi kowa Daukan Zafi Daga Karshe sai ya Zare hannunsa kan Abbanmu Tunda Likita yace Mgani baya aiki Tunda Abba bai Rage Damuwa ba kuma yaki ya manta da Abunda ya Faru Dashi..? taya zamu manta da wannan Rashin..? Ai har Abada Gidanmu ya Shiga kuncin da Bazamu Taba Fita acikinsa ba.
Tun bamu gane ba Har muka gane irin Yadda yan”uwan Abba ke kallonsa a Saboda Rashin Takwalli Ya koma Mahaukaci bashi da aiki sai Sambatu,Mukuma ya”yansa mu Bar komai nami mun dawo muna Rayuwar kawai Saboda Baffa Kabiru yayi yayi Dani da Imran mu koma Lagos Saboda aikin mu muka ki..Imran ya Nunamai Aduniya Bamu da wani abunda ya Ragemana Bayan Abba Saboda Haka ba inda Zamu muna Tare Dashi Dalilin haka yasa muka kusa Wata Shidda a Dukku,ayyukan mu Duka sun Tsaya an gaji da kiranmu an kyalemu,Munari Tuni Karatunta ya Tsaya Cak itama Bata da wani Sauran abunda Zata Dora.
Ni ban yi Tunanin Dauke Abba mu bar Dukku ba Imu ne ya kawo mana Wannan Tunanin Tun Lokacin Daya iske su Baffa Kabiru sun Tarun ma Abba suna ta mai Fadan yaki ya yarda da Kaddara ya Dawo Daidai ya Zauna yana Biyemana yana kwana kuka Mutuwa ce Dayace kuma wanda ya Mutu baya Dawowa Abba na kuka bayacewa komai Domin alokacin basu san Dacin Dayake ji ba Daada ma kukan Take ammh sun kasa Fahimtarsa,Suna cewa ya zama Mahaukacin karfi Dayaji kamar ba Musulmi ba,Baffa Mustapha baya mgana sai Baffa Kabiru yafi kowa Zakewa wannan Dalili yasa Imran ya mtsamin kan muce Zamu Tafi da Abba Lagos muje Chan muka Cigaba da aikin mu muna kula Dashi..Abun mamaki da muka Furta Daada ce kadai tayi musu ammh Banda Sauran yan”uwan Abba nan da suka amince acewarsu kila zai fi Samun Sauki batare da Rakiyan kowa ba Muka bar Dukku Zuwa Lagos,a mota muka Yi Tafiyar Domin Tun Abunda ya Faru Har Abada muka Tsani Jirgi.
Mun Dawo Gidanmu na Lagos da Zama sai dai Babu abunda ya Sauya Nidai ban koma bakin aikina ba Hakama Imran,Ballatana mu kokarta mu maida Munari makaranta Duk wani Farincikin Gidanmu sai ya Gushe sai kunci da Bakinciki Abba koda yaushe yana Daki yana kuka yana Samabtu mu kanmu bamu da Wata natsuwa.
Bayan Dawowarmu da Wata Daya Baffa Kabiru ya zo ganin mu Cikin Wannan Halin ya kara Bata ransa yayi ta Zaginmu yana mana Fada Abbanmu kuwa kamar ya Dakesa Daga karshe yace yaje yayi ta Haukansa In ya Haukace ni da Imran sai mu kaisa Gidan Mahaukata ko Zama bai yi ba ya Juya shima zuwan da yayi Daada ce ta matsamai yazo ya Dubamu.
Awannan Ranar Ran Imu ya baci ya Fita,Fitan da bai Dawo ba sai da ya kwana Biyu yana Dawowa na gansa ya iya Busa Sigari,shi kuma ya ce Dole ne muyi Nisa da Komai namu in muna so mu Cigaba da Zama Lafiya Inda ba wanda yasan Labarin Gidanmu Ballatana akira Abbanmu da Mahaukaci muyi nisa da komai nanu asali,Nasaba Dukiya aiki da Komai na Rayuwa Ni kuma na amince Domin Lokacin na Fara Tsorata da komai kada Imu ya Fada wani Hanyar Banza.
Bamu saida komai namu ba Gida Motoci Duka suna Lagos sai dai mun kai Takardan Barin aiki Daga Ma”aikatanmu da Muke aiki sai muka Tattara kudi Katin bankin mu Dana Abba dana Nura dana Asma”u da Takardun makarantarmu Dana Munari sai kayan sawanmu,muka Diba iya wanda Zamu iya muka Baro Lagos Bayan mun Sallami mai Gadi mun kulle Gidanmu bamu ma Tunanin Zamu Dwo Watarana ba sai Domin yin hakan Shine Mafitarmu Mun Taho da Abba Kano bai Cikin Hayyacinsa a Hotel muka Sauka Ni na Fita Na Bincikamana Gida Cikin kwana Biyu muka kara mallakan Wani gidan,Shine wanda muke Ciki,Muka Tattaro muka Dawo Domin Gina wata Sabuwar Rayuwa Bayan mun bar Duka Layukan mu da Wayoyim mu a Lagos Da komai inda Za”a Same mu saboda bama Bukatar Taimaakon kowa Tunda ankasa Fahimtar,Radadin Dake Cikin Babban Rashin da mukayi.
Ganin in na Zauna Haka Rayuwar Gidanmu Zata kara Lalacewa Cikin kunci,Sai na yanke Shawaran Fita Neman aiki Duk da bamu rasa komai ba Muna da Kudi,ammh ban Zauna ba Cikin ikon Allah na samu aiki a hukumar Inec ta nan Reshen Jahar Kano,Ni ne na Zama Uwa da Uban Imran da Munari na Zama Garkuwan Abba na Daukan Mai likitan Dake Zuwa Gida yana Dubasa Duk Bayan Wata Daya,koda Abba ya Fara Dawowa Hayyacinsa ya Fahimci Abunda muka aikata yayi ta kuka sai dai Bai Da Cikakkiyar Lafiyar da Zai iyq Tambayanmu meyasa mukayi hakan..?
Da albashina na Siya Motan Hawa na Siya ma Imran Mashin Tunda yace bai Bukatar Mota aiki ma yace bazai koma ba,Shi Baahi da Sauran wani Buri kuma,nayi nayi na Rabashi da Shan Sigari na kasa Saboda ya Riga ya Zama Jikinsa bazai iya Awa Daya bai Sha Sigari ba,duk Wasu Sabbin Halaye Rashi ne da Rayuwa suka maida Imran haka,Ni nayi Tunanin Inganta Rayuwar Munari Tunda ita Kadai take Ragemana na maidata makaranta..
Da farko ban Yi niyyar Fara Neman aure ba sai nayi Tunanin auran nawa Zai Tamaka ma Rayuwar Imran da Munari Sai dai kash Duk inda na Nemi aure sai mgana ta kamkama sai ta watse duk inda akayi Binciken Gidanmu aka gano wani abu duk da bama Hulda da kowa abun mamaki labarin komai sai ya fita, bamu da kowa kuma Abba bashi da lafiya yana Ciwon Hauka Dalilin haka Imran ya karya Hannun Kawun Wata Asma”u Dana Nema aka Hanashi Daga Karshe shi kawun nata yaci Zarafin Gidanmu Shari”a Dakyar na iya kasheta Na nemi aure kusan sau uku bana samu sai a kanki kema din da kokarin Imu na Sameki Tun kuma Bayan Tafiyarmu Har yau wani Daga Cikin Ahalin mu baisan inda muke ba bamu sani ba ko sun neme mu mudai bamu nemi kowa ba Har Rana mai kama ta yau..Ko naso mu nemi gida Imran ke Hanani Domin shi yafi Daukan Abubuwan da suka Faru  Fiye dani Kaina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button